DAFIN HARSHE BOOK ONE BY Maimunatu Iyam.txt

Author :  Maimuna Tijjani Iyam Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   31 / 32

90K to 93K   out of 95.1K words

faru ba". Ya ƙarishe zancen cikin matuƙar takaici daidai lokacin da Anty Sawwama take shigowa ɗakin cikin tsananin damuwa da alamar ta saurari duk abin da na muka faɗa.

"Allah ba ka jarabtan Bawa da abin da ba zai iya yi. Ya Allah don ƙarfin zari da ikonka ka ba mu juriya da haƙurin jure wannan jarabawan da ka jarabce mu da shi".

"Amin ya Allah".

Duk suka haɗe baki wajen furtawa amma ni kam sai a zuciyata na amsa don bakina ya kasa motsawa.
"Umma yanzu ya ya za a yi?". Anty Zulaihatu ta tambaya muryarta tattare da tarin damuwa.

"Dole mu je mu yi magana da mahaifiyarta don yadda ta yi watsi da Amatullah a wannan yanayin da take ciki abin yana damuna matuƙa. Zuwa yamma in sha Allah za mu je gabaɗayanmu mu same ta". Duk suka yi na'am da abin da Anty Sawwama ta furta ni kam na yi shuru tamkar wacce ruwa ya cinye ta. Zuwa bayan sallan asr suka sauƙa daga napep a ƙofar gidanmu.
Na waiga na hango masallacin da Abba yake salla kuma yake yawan zama a bakin wajen, na ga tarin dattawa zaune a wajen sai dai duk cikin su babu Abba, mutuwa kenan mai raba zumuci da daɗaɗɗan alaƙa.

Sai da Anty Zulaihatu ta ja hannuna kafin na ja ƙafafuna muka shiga cikin gidan, yara da manya suka taru suna ganina kamar ba su taɓa ganina ba kaina a ƙasa tun da muka shigo amma hakan bai hana su magana ba.
"Wannan ce annobar kenan? Ni kam da haihuwar irin wannan ai gwara ka zo duniya har ka gama rayuwarka ba tare da ka haihu ba". Cak na tsaya bisa sauƙan furucin da na ji a kunnuwana da ya damalmala mini dukkan lissafina ya farraƙa nutsuwa da gangar jikina.

"Amatullah ke ce haka duk kika lalace kamar mai cutar ƙanjamau?". Maman Adnan ta yi zancen tana iso ta tsaya a gabana kafin na ba ta amsa ta ci gaba da zancen tana taɓe baki.
"Ai daman ƙarya fure take yi ba ta ƴaƴa kuma komai nisan daren dole gari zai waye haske ya mamaye ko'ina, ashe duk sintirin da kike yi da sunan da zuwa islamiyya fakewa ake yi da guzuma a harɓi karsana to an yi walƙiya mun gan ku".

"Malama idan har kin san cewa bakinki ba zai furta alkhairi ba, to zai fi dace ki yi shuru". Anty Zulaihatu ta mayar mata da martani a zafafe tana jan hannuna muka shige cikin ɗakinmu, muka tarar da Umma tare da wasu mata biyu muka yi sallama sai dai cikinsu babu wanda ya amsa mana muka shigo muka zauna, ina satan kallon Umma sai dai ko kaɗan ban ga ta yadda na yi tsammanin ganin ta ba. Na yi zaton kamar yadda mutuwar Abba ta girgiza ni haka ita ma lamarin zai taɓa zuciyarta sai dai kash! Ashe kallon kitse nake yi wa ruwa hange dala nake yi wanda ya ke ba shiga cikin birni ba ne.

"Hafsatu ya muka ji da haƙuri?".

"Alhamdulillah". Ta amsa da shi tana yatsina fuska.
"Na zo mu yi magana da ke ne amma na ga ki na da baƙi, na ce ko za mu shiga cikin uwar ɗaka?".

"Babu inda zan motsa daga idan kuka riske don haka duk abin da za ki faɗa ki faɗe ta a nan. In ba za ki iya ba kuma ki wanke ƙafafunki ki koma inda kika fito ba lalle ba dole ai".

Lamarin ya ƙullar da Anty Zulaihatu har sai da ta tanka"Maman Amatullah izuwa yanzu kam ai na yi tunanin komai ya wuce, ya kamata mu bayar da hankali mu fuskanci abin da yake gabanmu. Mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen nemawa yarinyar nan nutsuwa da farin cikin ko don daidaituwar rayuwarta". Umma ta gyara zamanta tana fuskantar Anty Sawwama da kyau tare da faɗin.
"Ku yanzu har ku na tunanin cewa a cikinku akwai wanda ya fi ni son Amatullah ne, na fi kowa son ganin rayuwarta ta gyaru shi yasa nake yi duk waɗannan abubuwan. Wallahi duk daren duniya ba na iya runtsawa saboda baƙin cikin abin da wannan yarinyar ta aikata, ni kaɗai na sa irin son da nake yi wa Amatullah ko har kun manta irin wahalar da sha yayin raino da haihuwarta".

Kalamanta ya sanya idanuna kwaranyowa da hawayen da na daɗe ban tsiyayar ba, na ja gwiwoyina na gurfana a gaban Umma na ɗaura kaina a bisa kan cinyoyinta.
"Umma na tuba ki yafe mini wallahi ni ma shaida ce na san cewa ki na yi mini irin soyayyar da babu wanda zai yi mini kwantan-kwacinta a cikin duniyar nan. Amma zan so ki zauna ni dama na yi miki bayanin abin da ya faru wallahi ba laifina ba ne ƙaddara ce ta faɗa mini Umma kin san da hankali da tunanina ba zan aikata wannan abun ba, don Allah ki sassauta mini ki ba ni mafaka na sama sassauci a wajenki".

"Amatullah na riga da na cire ki daga cikin raina, tun ranar da abin kunyar da kika aikata ya bayyana na sallamar da ke a duniya......".

Da hanzari Anty Sawwama ta katse ta"kar ki yi mata baki Hafsatu ki saurare abin da za ta ce da ke don Allah".
"Babu wani abun da ya yi saura wanda za ta sanar da ni da ban ji shi a bakin al'umman gari ba. Amatullah na sallamar da ke ga duniya daga yau ni Hafsatu ba ni da wata ɗiya a duniya, don haka ki tashi ki bi su kar ki ƙara zuwa inda nake balle ni ma baƙin cikinki ya kashe ni kamar yadda ya yi silar mutuwar ubanki".

"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Allahumma ajirni fi musibati. Ya Allah ka kawo mana sauƙi wannan lamarin".

Wani irin kuka nake yi mai raunana zuciyar mai saurare babu shiri na ɗago kaina sakamakon dukan da na ji kalaman Umma sun yi mini. Duk yadda na so na yi magana na kasa yin haka sai ma tashi da na yi da sauri har ina haɗawa da gudu-gudu na bar cikin ɗakin kai tsaye ɗakin su Amira na nufa na zube akan kujera ina ci gaba da kukan.

"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Amatullah me ya faru kuma? Tun ɗazu nake so na je ɗakin nakun sai kuma Ummata ta ce ai da baƙi a ciki shi yasa na dakata". Na tsinkayo muryar Amira cike da kulawa yayin da take zama kusa da ni tare da ɗago kaina. Ta soma goge mini hawayen da suka ɓata mini fuskana.

"Amira me yasa munanan abubuwan suke faruwa da ni? Da farko an yi mini fyaɗe ciki ya bayyana a jikina, Abba ya mutu da baƙin cikin da na yi silar cusa masa sannan yanzu Umma uwar da ta haife ni ta furta cewar ta sallamar da ni ga duniya ba ta buƙatar gani na a kusa da ita. Amira ya ya ake so na yi rayuwata? Allah ma fa da kansa mu na yi masa laifi ya yafe mana to me ya sa Umma ta kasa fahimta na akan wannan lamarin balle har ta dube ni da idon rahama, jin ƙai tare da tausayi. Wallahi zuciyata ta soma saƙa mini wani mungun tunani, duk abin da na aikata kar ku ga laifina wallahi na rasa mafita ne".

Na yi zancen cikin wani irin yanayi mai wahalar fassaruwa cikin kalmomin baki, Amira ma kanta sai da hawaye suka zubo mata daga idanunta. Ta kasa lallashina illan kukan da muka haɗu ni da ita mu na yi.
"Duk laifina ne Amatullah ni na fara kawo shawaran zuwa gidan Tasalla. Kuma bayan abin da ya faru ya faru na goyi bayan a ɓoye lamarin. Komai ya faru ni ce sila ina ma a kaina wannan abun ya faru ba ke ba Amatullah ina ma....". Ba ta ƙarisa ba sakamakon kukan da ya ƙwace mata mai ƙarfin gaske muka haɗu duk mu biyun muna yin sa. Ummanta ta shigo ta tsaya a kanmu na tsawon lokaci kafin ta yi magana.
"Haƙuri za ku yi don duk abin da ya faru kuka ko shiga tsananin damuwa ba ya gyara shi. Ƙaddara ce da ta riga fata cikin mu babu wanda zai iya guje mata". Ta dafa kaina kana ta ci gaba"Amatullah ki yi haƙuri na san cewa ke mai haƙuri ce da juriya da kuma tawakkali. Duk layin nan da ke ake buga misali da kwatance idan za yi maganar tarbiyya, kamun kai, hankali da kuma nutsuwa kuma ina da tabbacin kowa zai shaide ki cewar hakan ba halinki ba ne. Ki tashi ki share hawayenki ki fito ku tafi ga su can suna jiranki a waje".

Na kuma fashewa da wani kukan mai tsuma zuciya ni nake yi zuciyata tana yi mini hura. Muka fito har zaure hannuna saƙale cikin na Amira suna fitowa waje muka ga dandazon mutanen unguwa ƙwansu da ƙwarƙwatansu wai duk su zo kallona.

"Dube ta simi-simi kamar na Allah ashe kura ce lulluɓe da fatan akuya. Allah dai wadaranki da kuma mungun halinki, ga shi yanzu ki kashe mahaifinki har lahira Allah sarki! Malam Manniru bawan Allah da ya san irin annobar da zai haifa kenan na tabbatar da ya gwammace ya rayu har ya koma ga Allah babu ɗa babu jika".

Kalaman da suka sauƙa a na'urar naɗan sautina kenan da ya gigita ni numfashina ya soma sama da ƙasa, ashe kowa zargina yake yi da akan mutuwar Abba?. Da ƙyar na isa wajen napep ɗin Anty Zulaihatu ta tsayar na shiga na zauna.
"Amatullah don Allah kar ki aikatawa abin da zai cutar da ke ko ya jefa mu gabaɗaya cikin wani ruɗanin. Ki yi ƙoƙari ki cire damuwa a cikin ranki in sha Allah gobe da sassafe ni ma zan zo, kuma Mansur ma ya ce a yi miki gaisuwa kafin ya zo da kansa". Kaina kawai na jinjina mata muka rabu, ko da muka isa gidan Anty Sawwama su Yaya Alhassan sun hi matuƙar baƙin cikin abin da ya faru Umar sai da ya yi kuka tsabar takaici.

A daren ranar sai da aka ƙara mini ruwa leda biyu aka yi mini allurai da sauran magungunan da na sha. Ina kwance a ɗaki kamar gawa Yaya Alhassan ya shigo ya yi mini sannu na amsa can ƙasa maƙoshina.

"Amatullahi ki cire damuwar komai daga cikin ranki in sha Allahu duk wanda ya yi miki wannan abun sai na nemo sa ko ina ya shiga a cikin duniya sai kuma na tabbatar da cewar an hukunta sa, bisa tanadin doka. In sha Allah farin cikinki zai dawo za ki rayu cikin nutsuwa da walwala kamar yadda kike a baya".

"Yaya Alhassan ni da samun farin ciki mun yi hannun riga".
Ya yi hanzarin katse ni"zan dawo miki da farin cikinki zan tabbatar da cewar duk matsalalolinki sun kau. Amatullahi ki ba ni dama in har kin aminta da ni kuma ki na jin za ki iya rayuwar aure da ni to zan iya ki".

Take na wartsake na tashi na zauna ina kallon sa cikin son tabbatar da abin da kunnuwana suka jiyo mini.
"Ƙwarai da gaske ni zan aure ki don ba zan ba ri aure ya kai ki inda za a wulaƙanta ki ko a yi miki gori bisa ƙaddarar da Allah ya ɗaura miki ba".

"Yaya Alhassan rayuwarka tsarkakkiya ce babu wani mummunan abu a cikin tarihinka. Don Allah kar ka gurɓata tarihinka ta hanyar haɗa jini da ni".

"Ko a gidan karuwai kike rayuwa Amatullah zan iya aurenki. Balle kuma ke ɗin ƴar uwata ce ta jini. Sai dai ba zan yi miki dole ba don yanzu farin cikinki shi ne abin da na fi so don haka ki je ki yi tunani da zuciyarki".
Na sunkuyar da kaina ƙasa kafin na ce"Anty Sawwama ta san da wannan zancen?".
"Sai da na fara tinkarar ta da maganar kafin na zo wajen ki". Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya ban iya cewa wani abun har ya tashi ya fita daga cikin ɗakin, ji nake yi kaina yana juya tamkar ba a cikin duniyar nake ba ga wani jirin da yake ɗeba ta don da kasancewar a zaune nake. Na koma na kwanta hawaye suna tsiyaya ta gefe da gefen idona.
Tabbas Yaya Alhassan mutumin kirki ne mai ƙoƙarin kame mutuncin kansa da kuma na ahalinsa a ko da yaushe, mutum ne mai nutsuwa da sanin ya kamata me yasa Anty Sawwama za ta amince masa akan auran watsatstsiyar da ta yi cikin shege ta kunyatar da iyayenta da duk wani wanda ya yarda da ita a idon duniya. Hatta mahaifiyarta ta nuna rashin buƙatata a kusa sai ita ce za ta buƙaci ɗanta ya kasance a tare da ni?.

Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya ina gyara kwanciyata, ba zan zama silar rugujewar rayuwar Yaya Alhassan ba. Don haka na gwammace na tafi can wani wajen da ban san kowa ba ni ma ba sanni ba na je na yi rayuwata. Ko zan sama kwanciyar hankalin da na rasa a yanzu. Gwara na shiga duniya kamar yadda Umma ta yi ikirarin ta sallama ni gare ta.
[10/30, 4:03 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

______________________________________

Page 4️⃣0️⃣

Haka na kwana ina tunani da saƙa da warwara cikin raina, ganin bacci ya ƙi kawo mini ziyara hakan ya sani tashi na fito na ɗaura alawa na koma ciki na gabatar da salla raka'a biyu. Na ɗaga hannayena dukka biyu sama sai dai na kasa magana rawa kawai jikina yake yi. Na kifa kaina a bisa gwiyoyina ina rero kukan marar sauti. Ban runtsa ba har sai da aka yi ƙiran sallan asubahi Anty Sawwama ta shigo da nufin tashi ta iske ni zaune ta dalle mini idanuna da haske tocila.

"Lafiya na gan ki a zaune kamar ba ki runtsa ba?".

"Na runtsa kawai na tashi ne da na ji ƙiran salla". Ba ta ce da ni komai ba ta juya ta fita na bi bayan ta alwala na yi na zauna na buga tagumi a gaban botan har Yaya Alhassan, Amir da Umar suka fito domin tafiya masallaci.
"Amatullah lafiya kuka zauna kika zagba tagumi?". Na tsinkayo muryar Amir a tsakiyar kaina na yi figigi na dawo cikin hayyacina.
"Lafiya ƙalau ina kwananku". Suka haɗe baki wajen amsawa kana suka fita, na tashi na koma cikin ɗakin na shimfiɗa sallaya a zaune na yi sallan don ji nake yi tamkar ƙafafuna ba za su ɗauke ni ba tun ina raka'an farko nake kuka har na yi sallama na ɗaga hannayena dukka biyu zama ina kirari ga Ubangijina.

"Ya Allah kai mai ikon akan kowa da kuma komai. Ya Allah kai ne masanin sirrin dake taskace cikin tsokar zuciyar dake a ciki ƙirji, Allah ka kawo mini mafitan halin da nake ciki. Zan tafi na je can wani wajen da ba a sanni ba ni ma ban san kowa na je na ci gaba da rayuwa a can, don na fahimci zama a nan shi ma wani matsalan ne. Tun da har Umma ta furta ba ta buƙata ta ta sallamar da ni ga duniya zan tafi can wani wajen na je na yi rayuwata, ba zan zama matsala ga rayuwar wasu ba. Ya Allah ya dubi lamarina ka kawo mini komai da sauƙi ka ba ni ikon cinye wannan jarabawan da ya faɗa mini. Allah kai mai rahama ne Allah ya lulluɓe Abbana da rahamarka, Ya Allah kai mai gafara ne Allah ka gafarta masa".

Na shafa addu'ar cikin sanyi da mutuwar jiki wasu hawayen suna gangarowa daga idanuna, na ji ƙarar buɗe ƙofar hakan ya sa na yi saurin komawa na kwanta ba tare da na cire hijabin da na yi sallan ba. Aka shigo aka zauna kusa da ku dab har ina ji sautin ajiyan zuciya da take sauƙewa akai-akai.
Ta dafa goshina tana shafawa har zuwa kaina"Amatullahi Baiwar Allah ina son rayuwarki ta inganta ina don ganin ki cikin farin ciki. A yanzu ba ni da burin da ya wuce na gan nutsuwarki ya daidaita kin sama kwanciyan hankali da walwala ki yi rayuwa kamar kowa cikin sakewa wannan dalilin ya sa nake son Alhassan ya aure ki. Don hankalina ba zai kwanta ba matuƙar kika yi aure a wani wajen kika shiga cikin wasu dangin da wataƙila su goranta miki akan abin da ya faru da ke ko ma su wulaƙanta ki. Amatullah tun ranar da aka kawo mini gawar Manniru a gaba babu rai a tattare da shi na yi wa kaina alƙawarin ba zan taɓa barin abin da ya haifa ta wulaƙanta ba bayan ransa, zan yi tsayiwan tsayin daka wajen tabbatar da cewar rayuwarki ta inganta. Ina da yaƙinin ko bayan babu raina Alhassan ba zai taɓa bari ki wulaƙanta ba".

Ta ƙare zancen tare da gyara mini Kwanciyata ta ja hijabin ta lulluɓe mini ƙafafuna da shi, ta fita rufe ƙofan da ta yi ya yi daidai da bugawan da zuciyata ta yi tamkar za ta ɓalle allon ƙirjina ta fito waje ta daka rawan disko. Tausayin kaina da na ahalina ya mamaye mini ruhina hawaey suka jiƙa mini fuska lajab kaina ya sara ƙirjina ya ci gaba da tsananta bugu.

A bayyane na furta"Anty ki yafe mini wallahi ba zan iya zama ba. Gwara na fi can inda ba a sannin ba kuma ban san kowa ba sai na fi samun kwanciyar hankali". Na ƙarƙare zancen ina tashi na zauna daɓas na leƙa ta taga na ga har gari ya soma yin haske na buɗe ƙofar ɗakin har na saƙalo ƙafata waje na hango su Yaya Alhassan suna shigowa da alama sai yanzu suka dawowa daga masallaci na yi wuf na shanye ƙafata na tura ƙofar ina leƙan su, zuciyata ta harba ganin Yaya Alhassan ya nufo ɗakin yayin da Amir da Umar suka shige ɗakinsu. Ban san abin da ya tuna ba sai kuma na ga juya ta ya bi bayan su Amir, na sauƙe ɓoyayyan ajiyan zuciya ina dafe ƙirjina da yake bugu.
Sai da na ɓata a ƙalla mintuna biyu ina tsaye kafin na buɗe ƙofan a hankali na fito, filin gidan wayam babu kowa don ranan Anty Zulaihatu a gidanta

31 / 32