Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : Romantic Hausa Novels
na ce"nan ne gidan Ta salla matar marigayi Alhaji Bashiru mai kwanuka".
Ya yi ɗan jim kamar mai nazarin wani abun kafin can ya ce"shikenan za mu magana da Ummanki, Allah ya sa ta yarda don in ba ta yarda ba. Ba zan yi mata dole ba, zan kuma yi bincike akan gidan ita Ta sallan".
A sanyaye na ce"na gode Allah ya ƙara girma".
Kafin ya kai ga amsawa Umma ta fito tsam Abba ya miƙe zai je gare ta, ta buga masa wani uban hararan da ya tsaya sa tsayawa cak har sai da ta iso ta zauna kana shi ma ya koma mazauninsa ya zauna, yana yi mata sannu da fitowan da ko amsa masa ba ta yi ba. Na gaishe ta ta amsa fuskarta babu yabo babu fallasa.
"Ranki ya daɗe daman wata alfarma muke nema a wajen ki". Abba ya yi zancen cikin matuƙar ƙanƙan da kai da girmamawa.
"Ina jin ka". Umma ta amsa da shi cikin isa da gadaran da ya haɗe da tsantsan izza.
"Daman ɗiyarki ce ta zo da wani batun da na yi na'am da shi, ta ce tana so su na zuwa gidan Ta salla suna kwana tare da Amira saboda yanayin ɗakunan namun. Ga shi kuma kullum yaran ƙara girma suke yi akwai abubuwan da bai dace sun ji ko suna gani ba, gare ni kam babu matsala na yarda sai dai duk yadda kika ce haka za a yi ranki ya daɗe".
Ta yi banza da shi na tsawon wasu mintuna da har sai da na ji daman ban zo masa da zancen ba, wataƙila da ban ja masa wannan abun ba. Sai da muka cire rai da samun amsarta kana ta buɗe baki ta yi magana.
"Ka san ƴar uwarka ma ta zo da makamancin wannan zancen amma ban amince ba. Duk da ba na son abin da zai sa Amatullah ta yi nisa da ni amma ina ji zan iya amincewa da wannan ko don na nunawa ƴar uwarka cewar na isa da gidan aurena kuma ina da ƙarfin gwiwan juya komai". Cikin sanyin jiki da na murya Abba ya ce"yanzu dai ki na nufin kin amince kenan?".
"Na amince".
"To muna godiya sosai ranki ya daɗe. Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai amfani, Allah ya bar mana ke ki yi tsawon rai ki yi shekaru irin na dabino".
Abba ya yi kalaman tamkar zai yi mata sujjada tsabar ƙanƙan da kai da biyayya. Ni ma godiya na gabatar mata ta ce na je na dama kunun don yau ba ta jin daɗin jikinta.
Na fito waje na ja kujera na zauna na zabga tagumi, ban yi aune ba na yi an watsa mini ruwa a fuskana. Ko gizau ban yi ba don na san babu wanda zai yi mini hakan face Amira. Ta ja kujera ta zauna kusa da ni tana faɗin"me ye kuma ya faru kika zo kika zabga tagumi haka?". Na ƙi na kula ta amma hakan bai hana ta ci gaba da faɗin abin da yake ranta ba.
"Ya ya kuka yi da Abban?". Na zame hannuwana kafin na kwashe duk yadda muka yi na sanar da ita hatta da maganan zuwa na kwana gidan Ta salla da muka yi, ta yi ta murna tana zantuka cikin jin daɗi. Haka na dama kunun na gama komai na kashe wutar ina wanke tukunyar Ummi ta fito daga ɗakinsu ta ci kwalliya tana zaunar chew gum ƙas ƙas. Amira ta yi wuf ta sha gabanta.
"To tauraruwa mai wutsiya dilallalan sharri ke da uwarki. Kun yi tunanin kun yi mata sharri kun ci banza kenan ko? To wallahi bashi kuka ɗauka sai na nuna muku bambamcin dake tsakanin ruwa da wuta, sai na haɗa miƙa gurmin da duk danginku ba za su iya kawo ƙarshensa ba. Sai kin zubar da hawaye kin yi kuka fiye da yadda Amatullah ta yi".
"Ahayye nanaye. Har da su kaza a cin danƙo? Ai ko giwa ta faɗi ta fi ƙarfin kiyashi su ja ba. Sanin kanki ne ni Ummi na yi muku nisan da har a naɗe duniya ba za ku iya iske ni ba". Amira ta bushe da dariya har da tafa hannu kana ta furta"to ina abin yake wai maye ya ci jajiri, ai ke ma kin san cewa ruwa ba sa'an kwando ba ne. Kuma ko da girgiza kurna ta fi magarya zaƙi, Ummi ga fili ga mai doki mu zuba ni dake sai mu ga wanda zai kwashe. Haka za ki ƙare da saurayi guda ɗaya mai jaraban nacin tsiya babu ko sisi a aljihunsa don lalacewa ma kwanon abincin safensa, rana da dare duk yana gidanku. Ban da rashin sanin ciwon kai". Da alama maganar ya yi matuƙar girgiza zuciyar Ummi don sai ta gaza cewa komai illa cizon ƴatsan da take yi cikin takaici. Ganin mutane sun fara fitowa daga ɗakunansu ya sani tashi na je na janye Amira ina ba ta haƙuri sai ba ta fasa zazzago zancen ba har sai da Ummi ta fice.
"Ban san yaushe za ki dinga ɗaukar abubuwa a hankali ba Amira. Yanzu dai ki je ki shirya ki zo mu tafi". Harara ta banka mini ta yi shigewarta ɗakinsu ta bar ni tsaye. Sai da na gama duk abin da nake yi na shiga ciki na tambayi Umma ko za a kawo mata abinci ta ce ba yanzu ba don haka na shiga ɗaki don na ga alamar kamar akwai abin da suke tattaunawa.
"Hafsatu ki yi wa Allah ki yi Manzon da ya karɓo mana sallalo biyar da muke yi a yini. Ki cece ni sau sausauta wannan hukuncin da kika yanke ya yi min tsauri, Maman Umar kamar uwa take a gare ni kuma ta yi ɗawainiyya da ni da tun ina yaro, ta sadaukar da abubuwa da yawa da suke mallakinta domin ji daɗina. Ta kan iya kana cikinta abinci ta ɗauka ta ba ni tana son duk wani abun da nake so ko da kuwa ita a ranta bai yi mata ba. Ta kan saurare ni ta ji damuwata kuma ta magance min ita, ba taɓa zuwa wajen da wani buƙatar da ta gaza biya min ita ba. Ta ya ya kike tunanin zan iya kallon tsabar idonta na ce da ita kar ta sake zuwa gidana don matata ba ta buƙatarta?".
Daidai lokacin da nake shiga cikin ɗakin na ji zancen Abba ya sauƙa a kunnena, na shiga daga jiki na tsaya a jikin labule ina ci gaba da saurara don ba kaɗan ba zancen ya ja hankalina.
"Ai kuwa sai dai ka zaɓa ko ni ita Maman Umar ɗin. Don duk ranar da ta ƙara zuwa cikin gidan nan, to ka ƙaddara a ranka cewar a ranar a gidanmu zan kwana".
A raunane tamkar mai shirin yin kuka na jiyo muryan Abba yana cewa"kin san ko da wani mahaluki aka haɗa aka ce na zama ke zan zaɓa Hafsatu akan kowa da komai. Amma ki dubi girman Allah ki janye wannan ƙudurin nakin, na yi imanin wannan abun da ya faru ma zai sa ta taƙaita zuwan da take yi ba sai na je mata da wannan zancen ba".
"Manniru idan ba za ka iya ba ni ba, ni ka ba ni iznin na wanke ƙafafuna na je na iske ta har gida na sanar da ita". Da hanzari Abba ya furta"A'a ba sai kin je ba zan je da kaina na sanar da ita". Sulalewa na yi zuwa ƙasa na durƙushe akan gwiwoyina ina kuka marar sauti, jin motsin za a shigo ya sani na yi wuf na tashi na ɗauko kayana na fito banɗaki na shiga na yo wanka na saka kayan da na shiga da su. Don tun ranar da Baban Vector ya bankaɗo ƙofar banɗakin Ina wanka na fara shiga da kayana inna gama wankan sai na saka su na fito abin na tsaf.
Sanda na fito na iske Abba har ya fita na shirya, na yi wa Umma sallama na fito na tarar Amira har ta shirya ni kawai take jira. A zaure muka tarar da Ummi da Auwal suna zancen muka wuce su bayan Amira ta buga musu wani uban tsaki tamkar ta ga kashi.
Har muka bar cikin layinmu ban ce komai hakan ya sanya Amira cewa"ke kuma lafiyarki Madam?".
Na ja dogon numfashi na fesar kafin na ce"Amira a iya sani na a bisa addini da al'adarmu na Malam Bahaushe mace ita take yi wa mijinta biyayya. Bai dace ta ɗaga murya ga mijinta ba amma gabaɗaya Umma ba haka take ba. Yanzu Abba har shakkan ta yake yi idan zai yi mata magana har jikinsa ruwa yake yi".
"To ke me ye matsalarki da hakan?".
Na yi mata wani kallo"a ganinki hakan ya dace ne Amira?".
"Ko mai dace ba to ke ina ruwanki da rayuwar da suke yi a tsakanin su? Ke yanzu babu dama mace ta zauna da mijinta lafiya sai ki yi wani tunani na daban Amatullah. Ai so da ƙauna gami da zaman lafiya shi yake kawo hakan in ba ki sani ba na gaya miki". Ban kuma cewa da ita komai har muka isa tashan duk da kuwa yadda ta yi ta ja na da hira, ranar Bashir ma bai sama kaina ba muna barin tashan na ce Amira ta raka ni gidan Anty Sawwama ta ce kar na je yanzu na bari abubuwa su lafa tukunnan. Ta shawarce ni akan ko zan je to gwara na je wajen aikin Yaya Alhassan na same shi mu yi magana, na amince da hakan.
Kamar yadda na yi zato ban sama Umma a gida ba Amira ta kawo mana abinci muka ci kana na soma shirin tafiya islamiyya, don so nake yi kafin na wuce na tsaya a wajen aikin Yaya Alhassan duk da hanyar ba ɗaya ba ne.
[10/18, 1:53 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
__________________________________
Page 3️⃣1️⃣
Ban ɗau lokaci ba na isa wajen aikin Yaya Alhassan na gyaran shinkafa, na tsaya a waje ina ta hange-hange kafin can na hango wani saurayi yana fitowa daga cikin wajen na yi hanzari na isa gare sa bakina ɗauke da sallama. Ya amsa yana kafe ni da idanuna.
"Don Allah wani taimako nake nema".
"Ina jinki".
"Ina so ayi mini magana da wani ne a ciki, sunansa Alhassan". Ya yi ƙuri yana kallona kafin can ya furta"a wani sashi yake aiki? Kin san akwai ɓangaren masu zuba ita shimkafan a buhu akwai masu ɗinke bugun sannan akwai masu lissafi". Na yi shuru ina cizon ɗan ƴatsa, kafin na kai ga furta wani abun ya katse mini hanzari.
"Mu je ciki sai na saka a duba miki shi. Amma me ye haɗin ki da shi Alhassan ɗin?".
"Yayana ne". Ya jinjina kansa yayin da ya yi gaba ina bin sa a baya muka bi ta wani ƙaramin ƙofa mun ɗan yi tafiya mai nisa kafin na tsaya saboda ganin wajen shuru babu gilmawar mutane.
"Malam wai ina za mu je ne?".
"Ina kike tunani?". Na yi zancen yana riƙo gefen hijabina na fizge ina nuna sa da ƴar manuniyar ƴatsata.
"Kar ka sake ka yi kuskuren taɓa jikina, don ina mai tabbatar maka da cewar hakan da za ka yi shi ne kuskure mafi girma da za ka yi a rayuwarka".
Da mamakina sai na ga ya fashe da dariya yana ƙara matso ni. Na sa dukkan ƙarfina na hankaɗe sa ya faɗi sai dai kafin na yi wani yunƙuri tunin ya tashi ya finciko ni ya ɗaga hannu da nufin zabga mini mari. Na yi saurin runtse idanuna cike da tsoro ina jira na ji ta wani ɓangare zai sauƙe mini marin, jin shurun da na yi na sanya ni buɗe idona a hankali.
Tagwayen ajiyar zuciya na sauƙe bisa ganin Yaya Alhassan da na yi tsaye a wajen ya riƙe hannun mutumin da ya ɗaga da nufin zuba mini mari.
"Halilu ashe har yanzu ba ka sauya wannan halin nakan ba?. Ina maka nasiha da ka tun kafin lokaci ya ƙure mata ka sauya zuwa mutumin kirki wanda iyaye da al'umma za su yi alfahari da shi".
Yana gama faɗin hakan ya sakar masa hannunsa, cikin rawar jikin da borin kunya mutumin ya bar wajen tana ta muzurai tamkar wanda ya yi wa sarki ƙarya.
"Amatullah me ye ya kawo ki wajen nan?".
"Wajen ka na zo Yaya Alhassan".
Ya murtuƙe fuskarsa tamkar bai taɓa yin dariya ba"me ye kawo ki? Me ye da ba za ki iya zuwa gida ki same ni ba. Yanzu da ya yi galaba akan ki fa, ki wuce ki tafi islamiyyarki in kun tashi zan zo na same ki a can".
"Don Allah Yaya Alhassan ko minti biyu ne ka ba ni, ka saurari abin da na zo da shi".
"Ki wuce ki tafi". Cikin tsare gida ya yi zancen da hakan ya hana ni cewa komai haka na wuce na tafi har na isa islamiyyar ina ji na wani iri, ina shiga aji na kifa kaina akan benci ina kuka marar sauti ban gushe ina yi ba har sai da Malam Suleiman ya shigo ajinmu kana na ɗago kaina fuskana ya kumbura ya ya tsimtim yayin da idanuna suka yi ƙulu-ƙulu tamkar za su faɗo ƙasa.
Har aka fito salla jikina gabaɗaya babu ƙwari tamkar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki. Ko tambayoyin da Rauda da Ammi suke haɗe suna yi mini ban amsa musu ko guda ba ko da suka matsa mini cewa na yi da su ba ni da lafiya ba, dole suka rabu da ni bayan sun yi mini addu'ar samun sauƙi.
Tun kafin mu fito daga cikin aji na hango Al'amin da alama ni yake jira haka kawai na ji raina yana ɓaci ba tare da wani dalili ba.
Ko da aka shafa fatiha mun tattaunawa sosai akan walimar sauƙarmu da yanzu ya rage saura kwanaki ashirin cif, an tsara komai yadda zai gudana domin abubuwa su tafi yadda ake so a kuma fita kunyar baƙin da aka gayyata.
Muna fitowa daga ajin na yi wa su Rauda sallama na ɗauki hanyar har na yi nisa na ji ana ƙiran sunana. Ya tsaya ina dafe goshina don muryar Aliyu ce, ban motsa ba har iso gabana.
"Saurin me ye kike yi haka? Tun da kuka fito nake ƙiran sunanki amma ba ki waigo ba".
"Aliyu yau ba na jin daɗi ne so nake yi na tafi gida da wuri". Cike da kulawa ya furta"Ayya! Sannu ai ban sani ba da ban tsayar da ke ba. To amma don Allah ina neman alfarma ina son gobe idan kin shigo akwai maganan da za mu yi da ke".
"To ba matsala sai goben". Na furta ina barin wajen ba tare da na jira abin da zai ce ba. Ina shawo kwanan layinmu na hango Yaya Alhassan akan mashin ɗinsa yana zaune yana latsa wayar hannunsa.
Na ƙara sautin da nake yi na isa gare shi bakina ɗauke da sallama sai dai duk jikina ya bi ya yi sanyi ganin yanayin da ya amsa mini sallamar fuskarsa babu walwala balle annuri.
"Sai yanzu aka tashe ku?". Na yi ƙasa da kaina"mun tsaya mun tattaunawa akan walimarmu ne shi yasa na ɗau lokaci". Ya jinjina kansa yana kallo ya furta"gani kin ce za mu yi magana".
Kunya gabaɗaya ta yi mini dabaibayi na yi ƙasa da kaina"daman na je na ba ka haƙuri ne akan abin da ya faru". Ya ɗaga mini hannu alamar na dakata. Ya cira kai yana kallo na tare da faɗin"ba ki yi min komai abin da ya faru kuma ai ƙaddara ce wacce ba ta wuce rana da sa'ilin ta. Don haka ki ma manta da abin da ya riga ya faru, damuwata ma shi ne kar hakan ya sa Abba ya yi fushi da mu".
"Abba bai yi fushi ba. Don ya fahimci mu sosai kuma ya yi imanin cewar ba za mu aikata abin da suke zarginmu da shi ba". Ya yi ɗan jim kafin can ya ce"amma gaskiya mutanen nan sun ba ni matuƙar tsoro. Na sha jin ana cewa ka guji sharrin mace ai ranar na ga zahirinta".
"Yaya Alhassan sharri ai dodo ne mai shi ya kan ci". Ya jinjina kansa cike da gamsuwa"haka ne kam. Yanzu dai ya batun sauƙan nakun me da me ake buƙata".
Na lissafa masa komai da komai da za mu yi. Bai ce komai har sai da na gama lissafin ya ɗago ido ya kalle ni"shikenan ko akwai sauran wasu abubuwan?".
Na waro idanuna"kai! Yaya Alhassan to waɗannan ɗin ma da na lissafo ba dole sai na yi su dukka ba. Hijabi daman Umma ta ce za ta yi mini ko atamfar ma ka yi mini wallahi ta isa".
"Ko atamfar ma ka yi mini wallahi ta isa". Ya kwaikwayi muryata da hakan ya sani murmusawa ina rufe fuskana.
"Duk abin da kika lissafa da ma wanda ba ki saka su cikin lissafin duk sai na yi miki su Amatullah. Gobe idan kin taso daga islamiyyar ki bi ta wajen Anty Zulaihatu zan ajiye miki a can sai ki karɓa".
Na turo baki ina furta"kar ka ɗaurawa kanka nauyi da yawa fa".
"Ke ɗin ce za ki zama min nauyi? To ashe in haka ne ni ma wataran zan gaji da ɗaukar nauyin kaina da kaina. Amatullah ke ƴar uwata ce kuma ba zan gaji da yi miki ɗawainiyya ba har abada, yanzu dai ki wuce gida magriba ta kusa". Godiya na gabatar masa sosai kana muka yi sallama ya wuce yayin da ni kuma na ƙariso gida, ina shigowa ana ƙiran sallan magriba don haka sai da na yi alwala kana na shiga ciki na yi salla, na sauya kaya na fito na haɗa wuta na ɗaura girki. Ina girkin ina biya karatun da aka yi mana haka Amira ta zo ta iske ni har sai na kai ayan da na ɗauko kana na kallo ta tare da cewa"yau ba za ki ke tallan taren ba ne?".
Ta dafe ƙirji"ni jikar mutum huɗu rufa min asiri. Ai wataƙila in dai ba wani ikon Allahn ba kuma na daina tuya awarar dare".
"Me yasa?".