DAFIN HARSHE BOOK ONE BY Maimunatu Iyam.txt

Author :  Maimuna Tijjani Iyam Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   15 / 32

42K to 45K   out of 95.1K words

iso wajen ban tsaya ɓata lokaci ba ya ja hannunta muka bar wajen har sai muka tsallaka titi kafin na sakar mata hannu, daidai lokacin da ta sama sararin jefa mini tambayar lafiya?. Na yi kunnen uwar shegu da ita na ci gaba da tafiya ita ma ta yi banza da ni har muka iso gida cikin mu babu wanda ya ce ko kanzil. Muna shiga zaure ta riƙo bayan hijabina na juyo a fusace ina kallonta.
"Ga shi in kin ga dama ki ɗauka in kin ga dama ki bar shi a wajen. Tun dai ke duk abin da mutum zai yi ba ya yi miki gwaninta". Ta ƙare zancen tana ajiye mini ledar da ke hannunta a gabana, har za ta shige ciki na dakatar da ita.

"Ki yi haƙuri Amira wallahi raina ne a ɓace, da ya kai matakin da har na kasa sarrafa fushina".

"In ce dai ba ni na kar zomon ba rataya aka ba ni ko? Don haka sai da safe". Na yi wuf na sha gabanta tare da zayyana mata duk abin da ya faru, ita ma kanta na hangi mamaki kwance akan fuskarta.

"Amatullah me ye kai sa'in'sa da shi? Irin su fa billahillazi ba a yin ja-in-ja da su yanzu kana zaman zamanka sai su jawo maka wata masifar da babu mai iya fitar da kai. Shin ke ba ki san hanyar da za ki bi ki kuɓuce masa ba sai kin bi wannan hanyar".

"Magana ake fa ta kare mutunci da kimata Amira. Shin na yi laifi don na kaina da kimata?".

"Ba za ki gane ba Amatullah amma ina fatan nan gaba kaɗan ki gane duk karantun da nake yi miki, ba tare da kin nema fassaran su". Na sauƙe gauron numfashi kafin na furta"ba na fatan na gane wannan karatun har duniya ta naɗe". Ba ta ce da ni komai ba illa jinjina kanta da ta yi ta wuce ciki, nima na rufa mata baya bayan na ɗauki ledar.

A ƙofarmu na hango Abba tsaye yana riƙe da tocila a hannunsa kallo guda za ka yi masa ka fahimce nutsuwa da kwanciyar hankali sun yi hijira daga gare sa. Yana ganina ya iso inda nake cikin hanzari.
"An samu kuwa Amatullah?".

"E an samu".

Na amsa da shi yayin da nake miƙa masa ledar dake hannunsa, sai da ya sauƙe numfashi kafin ya duba ya gani ya ce"alhamdulillah! Allah ya miki albarka Uwata, wuce mu je ciki". A raunane na amsa da kalmar amin na wuce gaba yana baya na har muka shiga ciki.

Na zauna a falo yayin da shi kuma ya wuce cikin ɗakin wajen Umma. Tun ina lissafin fitowarsa nan kusa har sai na kishingiɗe ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba, sai ji na yi kamar a mafarki ana ƙiran sunana na yi firit na tashi. Kafin na tsinkayo muryar Abba.
"Ki tashi ki je ki kwanta dare ta yi". Ban ce komai ba na wuce ciki na kwanta saboda gajiyar da na yi jikina gabaɗaya ciwo yake yi mini, ko sallar asubahi a makare na yi ta bayan na iddar na soma karatun alƙur'ani har lokacin Umma ba ta tashi ba, shigowa huɗu yana tambayar ko ta tashi na ce masa a'a. Har sai da na yi shara na shigo ɗakin na samu a sa'ilin take tashi na tsuguna har ƙasa na gaishe ta ta amsa mini a daƙile.

"Umma me ye za a ɗaura?".

Ta yi banza da ni sai can ta ce"ki dafa ko ma mene ne".
"To". Na amsa ina ƙoƙarin ficewa daga ɗakin ta tsayar da ni.
"Zo ki ɗauki wannan ledar fankasau ɗin ki fitar min daga ɗaki". Kamar yadda ta buƙata haka na yi na je na ɗauki ledar sai jin ta da nauyi alamar ba a ma buɗe ta ya hana ni fita.
"Umma ya kamar ba ki ci ba?".
"Ba a kawo min ita a lokacin da nake so ba ne".

"Umma da kin yi haƙuri kin ci ko kaɗan ne. Wallahi ba ki ga irin ƙoƙarin da Abba ya yi ba, har kasa kwanciya ya yi sai da ya ga an samu miki fankasau ɗin nan. Ko kaɗan ki ci ai shi ma zai ji daɗi....". Kallon da ta tsare da ni shi ya tursasa mini yin shuru ba tare da na gama furzar da zancen ba.
"Ba zan ci ba idan kuma dole ne cin sai kin sani dole na gani". Na sadda kaina ƙasa kafin na ce"ki yi haƙuri". Na fita daga ɗakin na je ƙofanmu na zauna na tisa ledar a gaba na zabga tagumi ina hashasho irin abubuwan da suka faru da ƙoƙarin da muka yi da Amira kafin mu samo fankasau ɗin nan.

"Tunanin me ye kike yi kuma?". Muryar Amira ta sauƙa a kunnuwana. Na bi ta da kallo yayin da take ɗauko kujera ta zauna kusa da ni kafin na yi magana da ci gaba da cewa"wannan ba ledar jiya ba ce?". Ba ta jira na ba ta amsa ba ta buɗe ganin ba ci ba ya sa ta kallona tana faɗin"ya haka kuma Amatullah?".

"Yadda kika gan shi ni ma haka na gan shi, Umma ta ce ba za ta ci ba wai ba a kawo mata shi a lokacin da take buƙata ba".
"To Abba kuma ya ya ya yi?". Na zame hannuna daga tagumin da na zagba kafin na ce"ya ya zai yi kuwa? Dole shi ma ya haƙura ai". Ta saki dariya mai matuƙar sauti da hakan ya sani kafe ta da ido.
"Mata masu duniya, lalle Umma ta na sha'aninta. Tana gara Abba kamar ƙwallon tamula wallahi shi yasa wani lokacin har cikin raina take burge ni don mazan yanzu sun zama zuma dole sai da wuta".
[9/21, 10:16 AM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_______________________________________________

Page 2️⃣1️⃣

Harara na bi Amira da shi da ta yi furucin tana sheƙewa da dariya gami da tafa hannu.
"Ke Amira ba na son rainin wayo fa, me ye hakan kuma? Yanzu wannan abun ne ya zama abin dariya a wajenki?. In ce dai da ke muka sha wuyar nemo wannan fankasau ɗin na yi tunanin ai za mu haɗu ne mu taya juna jimami da takaici, amma sai ki bige da dariya". Na ƙare zancen a kulefe don ba ƙaramin cusa mini takaici dariyar tatan ta yi ba.
"Ki yi haƙuri ƙawata, me ye laifin maganata fisabillillahi? Ai ni ina ga hakan ma abin alfahari ne gare ki da tunƙaro. Ko a gaban waye za ki tinƙaho ki bigi ƙirji domin mahaifiyarki sarauniya take a cikin a wajen mahaifinki kuma tana iya juya gidan kaman waina a bisa tanda".
Na bi ta d irin kallon da mai hankali yake yi wa zautacce kafin na furta"yanzu ke a irin tunaninki wannan abin wayewa ne?".

Ba tare da shakkan komai ba ta ce"ƙwarai kuwa, ai duk wacce kika ga mahaifiyarta ta isa da gidansu ta huta gaba da baya kuma ta wuce raini". Na jijjiga kaina tsabar takaicin da ya zarge muni wuya ya haifar nuni da wanzuwar ɗaci a cikin maƙoƙarona.
"Wani lokacin idan kina yin magana sai ki jefa ni cikin tunani, na yi ta hashashen anya kina amfani da ilmi da hankalinki kuwa wajen haɗa kalmomin da bakinki zai furta. Amira ina wayewa a cikin wannan lamarin? Yanzu fa in gaya miki gaskiya samari sun waye ko aure za su nema sai sun tabbatar da cewa uban yarinyar ya isa da gidansa, kuma yana da cikakken ikon zartar da ko wani irin hukunci ta yadda ko kara ya ajiye babu bai ƙetare shi".

"Wannan kuma ra'ayinki ne. Kin faɗi naki ni ma na faɗi nawa, don haka kowa sai ya riƙe na shi".

Tana ƙare zancen ta soma cin fankasau ɗin zallarta ba tare da ta haɗa da miyar ba. Ban ƙara cewa da ita komai ba har izuwa lokacin da Umma ta fito daga cikin ɗaki, Amira ta gaishe ta ta amsa fuskarta babu yabo babu fallasa kafin ta juyo gare ni.

"Wai ina mutumin nan ya shiga ne?".

Cikin rashin fahimta na ce"Umma waye fa kenan?".
"Waye kuwa ban da wannan lalatacceb uban nakin. Ina magana kin wani tsare ni da ido shegiya tanbaɗaɗɗiyar yarinya wacce ba ta yi gadon abin azurki ba".

Kalamanta suka sanya jikina yin sanyi ƙalau har da na rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa, muryata a shaƙe na furta"tun safe da ya fita har yanzu bai shigo ba".

"Haba! Ke kuwa baiwar Allah ki dinga sasauta harshenki mana akan yarinyar nan. Wallahil azim bakin uwa guba ne ga ƴaƴansa wanda da yawan uwaye ba su san hakan ba".

Furucin ustazun gidan kenan wanda bai daɗe da kama hayar ɗakin da yake kusa da na Naman Vector ba, daga shi sai matarsa amarya wanda a cewarta aure su wata huɗu kenan.
"To fa! Ɗankari manƙari har da su kaza acin ɗanko?. Wanene kake da suna?".

Ya yi hanzarin faɗin"Abdulwahab nake".

Umma ta gyara tsayiwarta kafin ta ci gaba da furzar da zantukan dake kan harshenta masu nauyin gaske, wanda kunnuwa ba za su yi mararin ƙara sauraran su ba ko da bisa kuskure ne kuwa.
"Zan ɗaga maka ƙafa ne kawai don kai baƙo ne a cikin gidan nan, amma wallahi bacin haka babu abin da zai dakatar da ni daga yaga maka rigar mutumci a tsakar gidan nan a gaban kowa. Don ni da kake gani na ɗin nan abun kunya gaba na ba shi ba baya ba. Ka jira tukunnan idan ka sama naka ɗiyar sai ka yi yadda kake so da ita amma ba yanzu ba, Amatullah ƴata ce babu wanda ya fi ni ƙarfin iko akan ta".

Cike da takaicin zantukan Umma, Ustaz ya jijjiga kansa tare da sadda kansa ƙasa.
"Allah ya kyauta, Allah ta yi mana mai kyau". Ya furta yayin da yake ficewa daga cikin gidan ba tare da ya ɗago kansa ba.
"To ku kuma munafukai masu kunnuwan son jin gulma da tsegumi, sai ko wacce ta ja jikinta ta bar nan". Umma ta yi zancen tana wurgawa Maman Adnan da Asabe da suke yi cirko-cirko a ƙofar ɗakunansu harara, kafin ta ja dogon tsaki ta shige ɗaki.
Ban san sa'ilin da ƙwalla suka soma tsere a bisa kuncina sai ɗuminsu na ji suna sauƙa a saman haɓarta, daidai lokacin da Amira ta dafo kafaɗuna tana doge mini hawayen da suka ɓata mini fuska. Ta ja hannuna zuwa ɗakin su a nan ta dinga lallashina da kalaman masu kwantar da hankali da haifar da nutsuwa a cikin rai da ruhi.

Wayarta ta soma ruri ta ɗaga ta sanya a kunnenta, hankalina baya gare ta hakan ya sa ban ci abin da take faɗa ba har sai lokacin da na ji ta duga ihu gami da tashi tsaye ta daka tsalle. Na fita da kallo ba tare da na ce da ita ko kanzil ba har sai da ta gama wayar kafin ta kallo ni, fuskarta kamar gonar auguda bakinta har kunne ta soma cewa"albishirinki Amatullah".

"Goro".

"Fari ko ja?".

Na juya idanuna kafin na ce"fari ƙal kamar haƙwaranki".
"Yau Mansur zai dawo kuma ya yi min alƙawarin yana shigowa garin nan a ƙofar gidan nan zai tsaya. Saboda ya yi wa kansa alƙawarin da ni zai fara tozali da zaran ya dawo".

"Allah ya dawo da shi lafiya, Allah kuma ya bar ƙauna".

Cike da annuri ta furta"Amin na gode". Ta ƙare maganar tare da rungume ni. Mun ɗau lokaci muna tattaunawa har Ummanta ta gama toya waina ta zubo mana muka ci, na baro ta akan za ta shiga wanka. Na iske Umma har ta kammala dama kunnun na yi mata sannu da aiki ta yi banza da ni, sai da na jira Amira ta fita kana ni ma na shiga na yi wanka muka shirya muka fita muka yada zango a inda muke zama a tasha.

Kan ka ce kabo mutane sun yi mana rumfa sanyan waina da kunun ake yi babu ƙauƙautawa, tun daga nisa da na hango Bashir na fara haɗe fuskata ban bar wata ƙofar da zai iya yi mini kowacce iriyar maganar ba. Ya iso ya zauna suka gaisa da Amira suka ɗan taɓa hira ina jin su ban soma baki ba.
"Bari na kai wa Naziru masarsa kafin ta yi sanyi". Na tsikayo muryar Amira. Na bi ta da ido don na san da gayya ta yi maganar, na yi tsam na riga ta miƙewa ta kafe ni da ido alamar son ƙarin bayani.

"E mu je na raka ni, tun da muke tashar nan fa kin san babu inda na taɓa zuwa a cikinta".

"Kin san ke ma ai hakan ba zai yiyu ba. Kayan kuma a waye za mu bar wa". Na saurin tarar numfashinta" ba ga Bashir yana zaune a wajen ba, sai mu bar mi shi".
"Bashir kuma?".

"Ƙwarai kuwa, Bashir ko kana da wani uzurin ne?". Na yi zancen cikin sanyin murya mai cike da taushi gami da jawo hankali mai sauraro.
"Kin san ance ai sayon giwa ya take na raƙumi, ko ina da wani uzurin ai ya sama dole na zauna na jire muku kaya tun da Gimbiya da kanta ne ta buƙaci hakan". Ya yi zancen yana washe baki kamar wanda aka yi wa kyautar kujerar hajji da umra. Ta yi masa fari da ido kafin muka bar wajen tafiya ce mai ɗan nisa muka yi kafin muka iso bakin wasu shagona biyu.
"Ki jira ni anan bari na shiga na kai masa".

Na yi wuf na riƙo hannunta"Amira shiga za ki yi? Kamar ɗaki ne fa?".
"Ba ma kama ba ne ɗauki ne, ke dai kawai ki jira ni yanzu zan fito". Ba ta jira abin da zan ce ba ta fizge hannunta ta shige ta bar ni tsaye a wajen ina kallon ikon Allah buwayi gagara misali.
Tun ina tsaye akan ƙafafuna har sai da suka gaji Amira ba ta fito ba, ɗakin da yake kusa da wanda Amira ta shiga aka buɗe ƙofar aka fito, wata mai tallan awara ne ta fito daga ɗaƙin riƙe da roban awaran a hannunta yayin da wani mutum yake bayanta daga shi sai singileti da gajeren wando.

Ya miƙo mata kuɗi yana faɗin"yau fa ba irin farashin kullum zan biya ba, don ba ki yi min yadda nake so ba don haka ga wannan ki je ki rage zafi". Ta yi masa wani mungun kallo kafin ta amsa kuɗin" kawo ai an ce raba arne da makami ibada ne". Ta kai aya tana kwafce kuɗin daga hannunsa.Ya ɗaga hannu zai maka duka ta yi hanzarin kaucewa.
"Matsalan ƴaƴan matsiyata kenan kana son su da azurki kuna ɓokarewa. Da ni kike zance yarinya". Ya yi zance a kufule yana yin ƙwafa.
Daidai sanda zai shige ɗakin muka haɗa ido da shi ya yi mini ɗagowa, da hakan ya sanya ni sauri rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa, kafin kakkauran muryarsa suka dira a ƙofofin kunnuwana.

"Ke dan ubaki me ye kike yi a nan? Kuma me ye kika tsaya kina kallo?".

Na ji maganar ƙarshen a kusa da ni na cira kaina na gan shi tsaye a gabana. Gaba ɗaya na ruɗe hakan ya sani gaza cewa komai. Har Amira ta fito ta same mu a haka.
"Amatullah me ye yake faruwa? Me ye ya haɗa ki da shi?".

"Babban yarinya daman kin san ta ne?".

"Ƙwarai kuwa tare muke da ita".

Ya gyara tsayinsa yana kallona tun daga ƙasa har sama kafin ya ce"ga ta kuwa ƴar ɗas da ita komai na ta cif-cif. Cikakken ƙirji ga kuma faffaɗan ƙugu". Take na ji wani jarumta ya zo mini ruɗewan da na yi lokaci guda na neme shi sama ko ƙasa na rasa shi, na nuna shi da ƴar manuniyar ƴatsata idonuna har sun soma ƙanƙancewa don masifa.
"Ahir ɗinka ko kai maye ne sai dai ka ci kanka". Ina ada aya anan na figi hannun Amira kamar zan raba shi da gangar jikinta muka bar wajen, ba mu tsaya ko'ina ba sai wajen kayanmu na zauna a mazaunina ina jin zuciyata tana tafasa tamkar talgen da aka ɗaura a bisa wuta.

"Har kun dawo kenan?". Bashir ya tambaya.

Na yi buga masa wani mungun kallon da bai ƙara yin gigin kallon inda nake ba balle ya yi nuni wata magana. Sai Amira ce ta ba shi haƙuri ta ce gobe ya dawo, muna gama sayar da kayanmu muka haɗa su almajiran da suke kwasar mana suka ɗeba suka yi gaba muna biye da su.

"Don Allah ki dunga ɗaukar abubuwa a hankali Amatullah. Rayuwar nan fa sai ana kai zuciya nisa". Na galla mata hararar"babu wanda ya isa ya yi nuni maganar banza ba tare da na mayar masa da martani ba".

Ta sheƙe da dariya mai isarta kafin ta ce"ai kuwa duk mazan yanzu haka suke, maganar batsa ya zama ruwan dare a wannan zamani tsakanin samari da ƴan mata. Sai dai in ba za ki yi soyayya ba balle aure don duk maza halinsu ɗaya ne. Musamman ke da Allah ya bai rage ki da komai ba kina da kyawun sura da diri ina yaƙinin babu namijin da zai ganki bai yabi surarki ba, Amatullah surarki jikinki kawai ya isa namiji ya so ki. Shi yasa kowa ya ganki sai ya yabe ki".

Na ja dogon numfashi na fesar"Amira akwai na tabbatar akwai. Akwai namijin da muka rabu da shi bai yi mini magana akan kyawun sura na ba. Shi ne mutum na farko da na taɓa haɗuwa da shi har muka rabu bai yi mini maganar banza ba".

"Amatullah ƙarya kike yi in akwai kuma ki faɗa min wanene wannan? Ni kuma zan tabbatar miki da a cikin biyu dole akwai ɗaya, ko dai ba shi da cikakken lafiya ko kuma idanunsa ba sa aikin su yadda ya kamata".

Na tsaya cak a inda nake ina kallonta cike da yaƙini na ce da ita"ki yarda da duk abin da zai fito daga bakina, tabbas akwai".

[9/28, 9:31 AM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_____________________________________

Page 2️⃣2️⃣

Tsare ni ta yi da ido tana bi na da irin kallon da mai hankali yake yi wa zautacce, ta jijjiga kanta alamar duk abin da na furta

15 / 32