Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : Romantic Hausa Novels
rauni na ce"don Allah Umma ki yi haƙuri mana".
Amira ta riƙo hannuna tana faɗin"Amatullah mu je daga waje mu ba su waje su tattaunawa". Ban yi mata musu na tashi muka fita muna fita wani kuka mai ƙarfi ya kubce mini na kifa kaina a bisa gwiwa ina rero sa cikin durshashewar murya. Duk ƙoƙarin da Amira ta yi na ba ni haƙuri da lallashina na gaza sarrafa kaina kukan ne kawai nake jin yana yi gaban kansa yana fitowa. Har sai da Ummanta ta fito ta nema jin ba'asin me yake faruwa Amira ta yi mata bayani ita ma ta lallashe ni sosai ganin ba ni da niyyar tsagaita kukan hakan ya sanya ta jan hannuna zuwa ɗakinsu, ta umarci Amira da ta ƙarisa girkin da na aza bisa wuta.
Ko anan ɗin ma hawayen sun kasa tsayawa da ƙyar Umman Amira ta lallashe ni ta zubo mini wainar da take toyawa sai dai na kasa kai ko da loma guda cikin bakina. Haka har Amira ta zo ta iske ni .
"Don Allah ki kwantar da hankalinki babu komai fa,Anty Sawwaman ma fa yanzu na ga ta fito za ta tafi".
Na zabura na miƙe zan fice Amira ta riƙo hannuna ta riƙe gam" ina kuma za ki je?".
"Zan je wajen ta ne kafin ta tafi mana".
Ta gizgiza mini kanta"bai kamata ki je yanzu ba Amatullah. Idan maganar da suka tattauna ta shafe ki to ko ba ki je ba za a ƙira ki, amma tun da kika ga ba a neme ki to maganar ba ta shafe ki ba ne ta kowacce fuska".
Cikin sanyin jiki na koma na zauna tare da buga wani uban tagumi, ganin yadda Amira ta dage ita da Ummanta wajen kwantar mini da hankali hakan ya sani dole na saki fuskata ba don na daina jin raɗaɗi da zogi a cikin raina ba. Haka kawai na ji gabaɗaya zaman gidan ya ishe ni har yunƙurin ƙiran Anty Sawwama na so yi da wayar Amira sai dai ban haddace lambarta a kaina ba haka dole ina ji ina gani na haƙura.
Umma ta soma ƙwala mini ƙira tana shelanta mini na fito na gama dama kunnun, sai da na yi wanka na shirya kana na ɗauki tallan muka fito tare da Amira yayin da almajirin da yake tafiya mana da kayan ya yi gaba.
Inda muka saba zama kamar kullum yau a nan muka yada zango, ba mu yi awa guda cikakken ba muka sayar da komai.
"Bari na yi sauri na je na kai wa Naziru masarsa kar ki gaji da zaman".
Amira ta yi zancen tana miƙewa tsaye, taɓe baki na yi ina faɗin"ni yau gabaɗaya ma wallahi ba na sha'awar komawa cikin gidan nan. Don tashin hankalin cikinsa ya fi komai yawa".
"To Amatullah ya ya za mu? Tun da ƙaddara ta jefo nan kam ai haka za mu yi haƙuri".
Haka kawai na ji wani sanyi a raina da na hango Bashir yana nufo wajen har sai da na kasa haƙuri na fito da abin da yake raina, wanda ni ma kaina ban taɓa zato da tsammanin bakina zai iya furta makamancin irin wannan kalamin ba.
"Yauwa! Ga can Bashir ma yana tahowa, za mu yi hira da shi kafin ki dawo don na lura mutumin akwai shi da barkwanci".
Sakeke Amira ta yi tana kallona hakan ya sani ankara da fahimtar cewa na kwafsa, sai dai ban bari na bugo jirgin nawan da wuri ba na yi wuf na gyara maganan.
"Malama ni fa ba wani abu nake nufi ba don na ga kina ƙoƙarin fassara ni ta wani fuskan daban".
Ta sheƙe da dariya mai isarta sai da ta tsagaita kafin ta ce"a yi dai mu gani in tusa tana hura wuta".
"Ni fa ba abin da kike nufi ne a cikin raina ba. Kawai ba na son komawa gidan nan yanzu gabaɗaya shi yasa". Ta yarfa hannayenta alamar babu abin da ya shafe ta da abin na furta, daidai lokacin da Bashir ya iso wajen bakinsa har kunne.
[10/1, 1:48 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
_______________________________________
Page 2️⃣5️⃣
"Barka da warhaka yake tauraruwar da ke haska ilahirin birnin zuciyata. Ban san yadda zan kasancewa a duk lokacin rana ta fito ta faɗi ba tare da na yi tozali da wannan kyakykyawan fuskarta kin ba, da ke nake kwana a cikin raina haka zalika da ke zan farka ƙunshe a ƙirjina, zan so ki ba ni dama don na nuna miki ainihin yadda nake yi akan ki Amatullah".
Na tallafe kuncina ina kallonsa tare da cewa"to wani irin dama kake buƙata daga gare ni ya kai bawan Allah?". Da alama maganar tawa ta haifar masa da wanzuwar farin ciki a cikin ransa da har sai da ya bayyana ɓaro-ɓaro a bisa fuskarsa.
"Ki ba ni dama shiga cikin zuciyarki ni ma na yi miki alƙawarin wadata da dawwammen farin ciki kuma ba zan taɓa sanya ta yi dana sanin zaɓina ba".
Na saki taƙaitaccen murmushi kafin na sama damar cewa"ga shi kuma babu abin da yake zama dawwammen a cikin duniyar gabaɗaya, face ikon Allah". Ya ɗan rusunar da kansa ƙasa yana sosa ƙeyarsa haɗe da cewa"to na ji amma na ba ki tabbacin ba za ki taɓa yin kuka ba idan ina kusa da ke".
"Ikon Allah sai kallo wai na zaune ya faɗi. Amatullah ke ce dai wacce na sani ko kuma gizo idanuna suke yi min?". Amira ta yi furucin cikin zallan mamaki da al'ajabina.
Na yi fari idanuna kafin na furta"wai daman ba ku tafi ba ne? To dai ki yi sauri don ba zan tsaya jiranki da yawa ba". Ta sheƙe da dariya haɗe da cewa"wannan kuma zance kike yi". Tana dasa aya a nan ta juya ta tafi kai wa Naziru masarsa.
"Ina so ki ba ni dama a yau domin na fallasa sirrin zuciyata izuwa na ki zuciyar. Don so nake yi na tabbatar mata da cewar ta sama abokiyar rayuwa na har abada wacce ba ta san komai ba face so da ƙaunarta".
Kalaman Bashir kenan da suka yi silar dawo da idanuna kansa. Har yanzun fuskarsa ɗauke da maɗaukakin annuri haka kawai na ji na tsinci kaina da kallon fuskarsa da take zagaye da kwantaccen saje baƙi wuk da shi har wani sheƙi yake tamkar yana shafa masa mai.
"Tafi kanka tsaye wajen isar da saƙon da yake ƙunshe a cikin zuciyarka".
Da alama ya ji daɗin zancen nawan, ya gayara zaman yana fuskanta na da kyau kafin ya soma zubo jawabi babu ƙakkautawa. Yi kawai yake yi ina ji da sauraronsa yayin da na gaza ɗauke idona daga gare sa har ya kai aya wanda hakan ya yi daidai da canzuwar bugawar zuciyata da hakan ya haifar mini da runtse idanuna.
"Tauraruwata lafiya kuwa? Na ga gabaɗaya yanayinki ya sauya".
Na furzar da zazzafan iska mai ɗumi daga bakina kafin na ce"ba komai". Ya yi hanzarin katse ni"ai kuwa yanayin ki ya nuna cewar akwai wani abu da kike ɓoyewa. Sanar da ni mene ne? Don yanzu zuciyata da taki sun zama aminan juna babu abin da za mu ɓoyewa junanmu".
Ya ƙare zancen yana ƙara matso da bencin da yake zaune a kai kusa da ni, na cira kai na yi masa wani irin kallo da ya sanya sa shan jinin jikinsa.
"Na ce maka babu koma ko za ka yi mini dole ne?". Na yi zancen fuskata a ɗaure mur tamkar magribar ɗinya.
"Ki yi haƙuri ba nufina kenan na ɓata miki rai ba". Ban tanka masa ba na miƙe na soma harhaɗa kayanmu, ina cikin aikata hakan Amira ta dawo.
"Har kun gama hirar da ku kenan? In kuma ba ku gama sai na koma na ba ku waje".
Na wurga mata harara da wutsiyar idona"in za ki zo mu tafi ki zo. In kuma ba yanzu za ki tafi ba sai ki sanar da ni". Maimakon ranta ya ɓaci bisa yanayin da na yi mata maganar sai ma murmushin da ta saka ta ce"daɗina da ke saurin hawa Amatullah. To haɗa kayan sai mu tafi". Muryar Bashir ta katse ni daga tattare kayan da nake yi na tsaya cak.
"Ki yi haƙuri idan ni na ɓata miki rai, na roƙe ki har ki azabtar da zuciya da ruhina ta wannan hanyar".
Haka kawai na ji gabaɗaya ilahirin jikina ya yi sanyi ƙalau na ja dogon numfashi na fesar kafin na waigo, na yi turus ganinsa durƙushe akan gwiwoyinsa. Na runtse idanuna ina faɗin"don Allah ka tashi kar mutane su ganka haka".
Ya marairaice murya"ba zan tashi ba har sai kin tabbatar min da cewar ba ni na yi silar canzuwar yanayin fuskarki ba Amatullah".
Banza na yi da shi ba tare da na ce da shi uffan ba na ci gaba da aikin gabana sai da na haɗa kayan tsaf, almajirin da yake ɗauka mana kayan ya zuba su a wheelbarrow ya yi gaba da su. Ganin Amira ba ta da niyyan tafiya hakan ya sani jan hannunta muka bar wajen har mun yi nisa sai na ji ta tsaya cak ba ta tafi, na ja hannunta ta ƙi motsawa hakan ya sani waigowa don ganin abin da ya hana ta tafiya.
A zafafe na soma cewa"me ye hakan Amira ina jan ki kina turjewa? In ba tafiya za ki yi ba ai sai ki sanar da ni". Ta jijjiga mini kanta alamar duk abin da na faɗa ba su hau gwadaben dalilin da ya hana ta tafiya ba.
"Amatullah don Allah ki duba lamarin Bashir, na yi wa masa farin sani kuma duk wanda zai ba ki labarin halinsa to a bayana yake. Ban taɓa jin ya furtawa wata mace kalmar so ba a kaf cikin tashar nan sai ke, ina da tabbacin da dukkan zuciyarsa yake sonki. Duba ba fa ki ga tun ɗazu yana kan gwiwoyinsa bai tashi ba".
A faƙaice na juya na kalle shi har yanzu yana durƙushe akan gwiwoyinsa bai gusa ba. Tagwayen ajiyar zuciya na sauƙe ina dafe goshina saboda sarawan da kaina yake yi mini tamkar zai tsage gida biyu. Ban ce da ita komai ba na koma wajen Bashir na tabbatar masa da cewa ni bai yi mini komai ba.
"To indai har ki na so na yarda da duk abin da kika furta sai ki yi min wani alƙawarin guda".
Na ware idanuna"wani irin alƙawarin ne haka? Faɗi ko mene ne matuƙar bai fi ƙarfina ba zan yi maka shi Bashir".
Sai da ya gyara tsayiwarsa kafin ya ce"ina so yi min alƙawarin gobe za ki ba ni lokacinki don mu tattaunawa". Ba tare da tunanin komai ba na tsinci kaina da faɗin"in Sha Allah na yi maka wannan alƙawarin". Cike da jin daɗi ya amsa da cewa"to ina godiya, mu je na yi muku rakiya ko?".
Na jijjiga kaina"ba buƙatar hakan, kai dai kawai ka koma wajen sana'arka".
"To shikenan yadda kika ce haka za a yi ranki a daɗe". Murmushi kawai na sakar masa na bar wajen muka ci gaba da tafiya tare da Amira. Har mun yi nisa da tashar na tsaya.
"Lafiya kuma kika tsaya?". Amira ta jefa mini tambayar cikin zaƙuwar son jin amsa daga gare ni.
"Wallahi da zarar na tunkaro hanyar gidan nan sai na yi gabana yana faɗuwa. Haka nake jin ba na son komawa cikin wannan gidan saboda tashin hankalin da zan tarar a cikinsa ko na sakan guda ba na samu farin ciki".
Ta riƙo hannuna dukkan biyun ta sanya cikin nata kafin ta soma magana da laulausan amon mai ratsa ƙalbi.
"Amatullah sai fa kin cire damuwar komai daga cikin ranki, kin ga rayuwar nan kowa da irin na shi ƙaddarar da kuma ƙalubalen rayuwarsa". Na yi saurin tarar numfashinta"Amira ni fa ba dogon magana nake son ji ba. Kawai ba na son komawa gidan nan ne a yanzu na fi so sai lokacin tafiya islamiyya ya gabato kafin na koma, ni wallahi gwara mu koma tashar ma mu yi zamanmu".
A tsorace ta waro idanunta ta buɗe su tar a kaina"tasha kuma Amatullah?".
Ba tare da tsoro ko shakkan komai ba na ce"ƙwarai kuwa, zaman cikin tashan nan ya fi mini kwanciyar hankali fiye da zama cikin gidan nan".
Ta riƙe haɓa cike da mamaki tare da faɗin"tirkashi! Lalle lamarin ya girmama. Amatullah yau ke ce da bakinki kike furta kin fi son zaman tasha fiye da gida". Na yi shuru na gaza ba ta amsa don na rasa ƙwarin gwiwar buɗe bakina. Take wani tunanin ya faɗo mini a rai tamkar faɗuwar aradu na yi caraf na ce"ko dai mu je gidan Anty Sawwama ne?". Ta yi sakeke kawai tana kallona kafin can ta yi magana a taƙaice.
"Indai har za ki sama nutsuwa a can ɗin, to mu je mana".
Murmushi muka sakarwa juna kafin na ja hannunta muka fice daga layin, tudun nabawa muka nufo da yake bayan layinmu, tun daga zaure muke zabga sallama har muka isa cikin gidan, gidan wayam da alamun Umar ya tafi makaranta don daman shine mai zama a gida.
"Wa alaikussalam sannunku da zuwa".
Muka tsinkayo muryar Anty Sawwama daga bayan mu da hakan ya sa mu juyawa dukkanmu. Anty Sawwama ce da alama daga banɗaki ta fito ta ajiye bautar da ke hannunta kafin ta yi gaba muka bi ta a baya har cikin ɗakinta. Sai da muka zazzauna kafin muka gaishe ta ta amsa mana fuskarta babu
yabo babu fallasa.
"Daga ku kuwa kuke da wannan ranar?".
"Daga wajen tallla muke". Na amsa mata a gajarce, sai dai na lura da yanayin fuskarta ta sauya gabaɗaya ta yi ɗan jim kafin ta can ta ce"Allah dai ya kyauta, ki je kitchen ki ɗauko muku by ragowar abincin safe ku ci".
"To". Na amsa da shi yayin da nake tashi na nufi kitchen na ɗauko Mana abincin na ajiye mana muka ci tare da Amira sai da muka gama ci tas, kana na tambayi ko akwai wani aikin da za mu yi mata ta ce sai dai mu haɗa mata wutan abincin rana.
Kamar yadda ta buƙata haka muka fito muka fara aikin, na soma haɗa wuta yayin da Amira ta ɗauko doyan ta soma ferewa. Sai da muka haɗa komai har ruwan ya tafasa muka zuba doyan kana na tashi na shiga ciki wajen Anty Sawwama yayin da na bar Amira tana zaune tana waya da Mansur.
"Sannu da hutawa Anty Sawwama".
Ta gyara kwanciyarta daga gishingiɗan da ta yi kafin ta amsa muni cikin faɗin"yauwa uwata sannunku da aiki".
"Anty daman na zo ne musamman don na ba ki haƙuri akan abin da ya faru tsakaninki da Umma ɗazu da safe. Ina mai ba ki haƙuri a madadinta kuma ina so ki yi mata uzuri".
Ta jinjina kanta tana sakin taƙaitaccen murmushi kafin ta ce"tabbas albasa ba ta yi halin ruwa ba. Uwata ba komai ai ya riga da ya wuce, kin ga ni har na manta ma ai".
"To amma Anty me ye kuka tattaunawa haka da ya ki tafiya da wuri? Ko sallama fa ba mu yi ba sai fito na yi na iske har kin tafi".
Ta sauƙe tagwayen ajiyar zuciya mai matuƙar sauti da har da kunnuwana suka ji yo mini sautin.
"Uwata ba wata magana ba ce da za ki tada hnakalinki, daman na je na roƙi alfarman Manniru da ki dawo wajena da zama saboda yanzu kin girma ke ba yarinya ba ce, sannan a can gidan falo ne kawai ne da ɗaki dole ne wani lokacin iyayenki suna buƙatar yin sirri a tsakaninsu wanda babu damar yin hakan. Da a tunanina na ce idan ki gama haɗa haddarki sai ki dawo idan kin ga nan ɗin ma bai yi miki ba sai ki koma wajen yayarki Zulaihatu".
Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya mai nauyin gaske, duk wasu gaɓoɓin jikina suka yi sanyi ƙalau. Anty Zulaihatu ita ce babbar ɗiyar Anty Sawwama sa take aure a cikin gari, kuma ita ɗiya ɗaya tilo mace sauran ukun duk maza ne. Yaya Alhassan shi ne yake bin bayan Anty Zulaihatu wanda yanzu haka yana aiki a ma'aikatan shinfaka yana samu sosai don hatta gidan da suke ciki shi ya saya musu, daga shi sai Yaya Walid wanda ya ci sunan Abbana aka ɓoye masa suna ana ƙiran sa da Walid wanda yanzu haka yake karatu jami'ar jiha sannan autansu Umar wanda tazarar tsakaninmu da shi kaɗan ne. Kalaman da ta ɗaura da su su suka yi silar dawo da ni izuwa duniyar zahiri daga na tunanin da na dulmiya a cikinsa.
"Amma tun da Ummanki ba ta amince da shawarar da na je da ita ba. Daman shawara ce ba komai ba".
"To Anty ki bari zuwa bayan kwana biyu mana sai ki ƙara komawa ki sama Abba shi kaɗai, ko a wajen aiki ne wataƙila ya amince". Na ƙare zancen cikin marairaice murya yayin ƙwalla suke ciki mini kurmin idaniyata. Kafin ta yi magana muka ji yo sallamar Yaya Alhassan muka amsa masa kafin ta shigo ciki na tashi na amsa ledar da yake hannunsa kana na gaishe shi. Ya ɗauke kansa gefe kamar bai ganni ba yana cewa"ai ni kam na yi fushi Amatullah. Na ma yi tunanin ko kin manta hanyar gidan namun ne ai".
Na girgiza kaina"Yaya Alhassan wane ni na manta hanyar gidan nan, akwai kwanakin nan ba na samun zama ne saboda sauƙarmu ta gabato".
Ya faɗaɗa annurin fuskarsa tare da faɗin"haka Umma take sanar da ni, yaushe ne sauƙar takun?".
"Yanzu sai saura sati uku". Ya jinjina kansa"Allah ya kaimu lokacin kafin lokacin ma kuma sai ki zo ki ƙara sanar da ni".
Cike da jin daɗi na ce"to in sha Allah, bari na je na duba girkin na bar Amira ita kaɗai a waje". Har zan fice Yaya Alhassan ya dakatar da ni.
"Ai kuwa na zo a daidai ba zan tafi ba sai na ci girkin ƴar ƙanwata".
"Lalle kam! Yaushe rabon duniya da ayyaraye Alhassan? Ni ba zan iya tuna ranar da ka ci abincin rana a cikin gidan ba ko an ce ka saurara ka ci za ka kawo uzurin cewar kana sauri. Amma yau da yake Amatullah ce ta girka ko tayi ba