Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : Romantic Hausa Novels
mafi sauƙi a wajensa wajen aikatawa.
Sai da ƙuran ya lafa kafin na sama damar ba wa Amira haƙuri tana buƙarewa akan za ta jira Ummi ta dawo su ɗora daga inda suka tsaya. Da ƙyar da suɗin goshi na shawo kanta ta haƙura. Sai da aka magarib kafin Umma ta ce na tafasa tafiyar murji kamar yanda ta ce haka na yi na ci nawa na kai mata nata ɗaki na zuba na Abba a kula na ajiye masa. Na yi sallan isha'i na kwaso littattafain da nake koyar da yara da su na fito gidan ya haɗe da gurmi. Don mahaifiyar Ummi ta lashi takori akan sai an bi wa ɗiyarta haƙƙin zubar mata da jini da aka yi ba gaira ba dalili. Ta ƙira Mahaifin Ummi da yake legas a waya tana shaida masa abun da ya faru ya fi sau shurin masaƙi.
Tunin na tarar da yaran da nake koyar da su a zaure suna jirana babu ɓata lokaci muka fara karatu har mun yi nisa Abba ya dawo na miƙe tsaye da fara'ata ina yi masa sannu da zuwa sai kafin ya kai ga amsawa wani yaro ya shigo.
"Wai ana sallama da Amatullah a waje".
Daga ni har shi duk muka yi mutuwar tsaye kafin ya tsayar da idanunsa a kaina tamkar yau ce rana ta farko da ya fara ganina. Cikina sai ƙugi yake yi haƙwana suka datse harshena lokacin da Abba yake tambayar yaron da har yanzu yana tsaye bai gusa ba.
"Waye yake sallama da ita?".
"Wani ne ya zo akan babur ya ce a ƙira ta".
"Ke waye ya zo neman ki?". Tambayar da ya watsa mini ta sanya hanjin cikina kaɗawa jikina ya soma rawa kamar mazari.
"Ba magana nake yi miki ba? Waye ya zo neman ki a daidai wannan lokacin?". Ya kuma maimaitawa a karo na biyu cikin tsantsan buƙatuwar sn jin amsar tambayarsa.
"Ka yi haƙuri Abba ni ake nema ba Amatullah ba. Wani ne muka haɗu da shi kuma ya ce min zai zo gidanmu, yanzu ma muka gama waya da shi, ni ce na ce masa sunana Amatullah saboda ya takura min a lokacin".
Da wani irin hanzarin na waigo ina ƙarewa Amira da ta yi maganar cikin takewa da ƙwarin gwiwa kallo haka nan ma Abba shi ma kallon natan yake yi.
"Ita ba ta da bakin kare kanta sai ke?". Cikin girmamawa Amira ta amsa da faɗin"Abba ba ta san komai ba ne shi yasa ta kasa cewa wani abu. Amma ina mai ƙara ba ka haƙuri na san yadda kake taka tsantsan da tarbiyyan Amatullah. Ka yafe min akan kuskuren da na yi na ba ta sunanta a matsayin nawa".
Sai da ya yi ɗan jim kamar mai tunani ko nazarin wani abun kafin ya ce"ba komai amma dai a dinga kiyayewa. Ke ma bai dace kina tara samari a ƙofan gidanku ba ki nutsu ki fitar da wanda kike so a cikinsu, don haka ne daraja da kimarki a matsayinki ta ɗiya mace".
"In sha Allah Abba kwana nan zan fita da guda daga cikin su. Ku dai ci gaba da yi mana addu'a Allah ya ba mu na gari". Cike da jin daɗi Abba ya ce"Amin amin ya hayyu. Kuma in kin je kar ki daɗe Amira, ni sai na rasa ma me ye kuke tattaunawa su yi awanni suna zance".
"Ba zan wuce mintin talatin ba ina sha Allah". Kansa kawai Abba ya jinjina ya wuce ciki sai da na tabbatar ya gama wucewa kafin na fizgo hannun Amira.
"Waye kika kika ba shi sunana har yanzu gida nema na?". Ta fizge hannunta"dalla! Ki nutsu mu yi magana. Malama ni babu wanda na ba wa sunanki balle har ya zo gida ne nemanki, na yi haka ne kawai don na ƙwace ki daga tuhumar Abba. Yanzu dai ki zo mu je mu ga ko wane ne kuma da me ye ya zo".
"A'a Amira ni gaskiya babu inda zan je tsoro nake ji". Ta watsa mini harara kafin ta finciko ni muka yi waje muna fitowa muka hango mutum zaune a bisa babur yana latsa wayarsa.
"Amira na shiga uku! Idan Abba ya fito ya kalle ni fa?". Na furta muryata tana rawa.
"Ki nutsu mu yi abin da ya kamata mu koma gida akan lokaci. Ban da abin ki me ye zai fito da Abba yanzu kuma, ke dai kawai ki nutsu". Tana dasa aya anan ta ja hannuna muka ci gaba da tafiya duk ɗaga ƙafar da zan yi sai ƙirjina ya buga har muka isa wajen mutumin.
Sunan da ya ƙira ni da shi ya ƙara jefa ni cikin firgici.
"Tauraruwa Amatullah ba ki tsammanin gani na a ƙofar gidanku ba ko?". Jikina ya soma rawa tamkar wacce ake jonawa wutan lantarki. Da ƙyar na daidai nutsuwata.
"Mai-mai-mai aska kai ne?".
"Ƙwarai kuwa ni ne haka kawai zuciyata ta kasa nutsuwa. Na ji ko runtsawa ba zan iya yi ba idan har ban yi kwalli da kyakykyawar fuskarki ba".
"Amatullah wane shi? A ina kika san shi?". Amira ta yi magana a karo na farko.
"Amira shi ne wanda na ba ki labarin wanda muka haɗu a inda na kai talla yau". Ban jira amsarta ba na juya ina fuskantarsa da kyau na ci gaba da maganata.
"Na roƙe ka da girman wanda yake yi mana ruwa da ƙanƙara kar ka ƙara sako ƙafarka cikin layin nan, me ye kake so da ni? Don Allah kar ka ja mini masifa da bala'in da kaina ba zai iya ɗauka ba".
"Amatullah ba na nufin da masifa ko bala'in face alkhairin Allah".
"Wani irin alkhairi?".
"Ƙauna ce tafe da ni kuma ina fatan za ki amshe ƙoƙon barana".
Takaici ya mamaye zuciyata"ba na soyayya kuma ba zan fara akan ba don haka ka yi haƙuri Abbana bai ba ni damar tsayawa da ko wani ɗan namiji ba a hali yanzu". Ina gama faɗin haka na ja hannun Amira muka bar wajen muka shiga zaure ɗalibaina suka zuro mana ido. Nan take na sallame su duk suka watse muka zauna ni da Amira.
"Shi ne za ki tursasa mini fita kuma ki kasa cewa komai a gabansa. Kika bar ni ni kaɗai ina ta magana". Ta ɗan murmusa kafin ta ce"na ga ai ba cutar da ke ya zo yi ba shi yasa na yi shuru. Soyayya ce ta kawo sa kin ga kuma babu yanda za a yi na farraƙa tsakanin masoya".
Babu shiri na kai mata duka ta kauce tana ƙara ƙyalƙyale wa da dariya. Na miƙe tsaye ita ma ta miƙe na naɗe tabarma ina cewa"zan shiga ciki kar Abba ya ce na daɗe. Idan Allah ya kai mu gobe za mu tattaunawa".
"Cab! Ni kuwa kin ga yanzu ma zan je na ƙarbo awarata a fita tuya". Na taɓe baki"Allah ya ganar da ke". Ba ta amsa ba illa dariyar da ta yi muka shigo ciki tare ta yi ɗakinsu na yi namu.
[7/17, 1:21 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
___________________________________
Page 1️⃣0️⃣
Kamar ƙadangaruwar bayan murhu haka na shigo ciki ina raɓe-raɓe iwa munafuka ko kuma wacce ta yi wa Sarki ƙarya, na nema waje na zauna a falo kasancewar na jiyo Umma da Abba suna tattaunawa a cikin uwar ɗaka. Kamar ko yaushe muryar Umma ya ɗara na Abba sai hayagaga take yi kamar za ta yi aron baki.
"Manniru ni fa ba ƙaramar yarinya ba ce da za ka tisa ni a gaba ka yi min wannan zancen banza da na wofin. Da yake ni ce karkatacciyar bishiyar kuka mai daɗin hawa shi yasa kowa ya ɗebo shararsa sai ya watso min, kai da danginka kun uzura min kun sako ni a gaban akan yarinyar da babu wanda ya taya ni goyan cikinta na tsawon watanni tara balle a kawo min tallafi yayin da nake nishin naƙudanta. Kowa ya ɗebo warin bakinsa zai nufo wai ina ƙoƙarin lalata tarbiyyar yarinyar nan".
"Ni kike kallon tsabar idona ki gaya min wannan zancen?". A kaurare na tsinkayo muryarta tana mayar masa da martani kamar wacce take jira ya ce kule ta ce cas.
"An gaya maka ɗin na ce an gaya maka. Manniru ka yi duk abin da ka ga dama ga fili ga mai doki, babu wanda zai dakatar da kai balle ya hana ka wanzar da abin da zuciyarka ta yi niyyar aikatawa, ko ce maka aka yi ina tsoro ko shakkanka ne? Ai wallahi an sha ni na warke kan mage ya daɗe da wayewa".
"Ba zan taɓa iya aikata abin da zuciyata ta saƙa min akan ki ba. Allah ya sani kuma shi ne masanin abin da yake taskace a cikin tsokar zuciya kina da girma da matsayi a wajena ta yadda duk abin da kika yi zan jure shi, kuma na yi miki uzuri. Amma kin ga wannan harshen naki Hafsatu ina jiye miki zuwan ranar da zai yi silar fadawarki cikin halaka, DAFIN HARSHE ya fi dafin maciji illa da saurin nakasa sassan jikin ɗan adam".
Gama maganar da fitowarsa sun yi daidai da lokacin da ƙwallan da suka wadaci koramar idanuna samun hanyar kwaranya. Ya kafe ni da ido da hakan ya sani yin ƙasa da idanuna.
Sai da ya zauna kafin ya ba ni umarnin zama, na nema waje na zaune kusa da kujerar da yake zaune.
"Kukan me ye kike yi Amatullah?".
Na yi saurin kawar da hawaye da suka ɓata mini fuska kafin na sama sararin cewa"babu komai". Ya yi ɗan jim kafin can ya ci gaba da magana.
"Har baƙon nakin ya tafi?". Babu shiri na ɗago kaina ina dubansa mamaki da tsoro kwance luf a bisa fuskana ban ƙara shan giyan mamaki ba sai da ya ƙara jefa mini wani tambaya a karo na biyu da ya kusa sanya nokinan kaina suncewa take na soma haɗa gumi duk da sanyi da ni'iman Ubangiji da ya lulluɓe garin.
"Me kuka tattauna da shi?".
Na gyara zamana kafin na iya raba tsakanin haƙwarana da suka manne da junansu kamar mayen ƙarfe aka sanya a tsakanin su.
"Abba ba fa waje na ya zo ba. Baƙon Amira ne....". Kafin na ƙarisa ya ɗaga mini hannu alamar baya buƙatar sauraron jin ragowar bayani.
"Amatullah". Ya ƙira sunana cikin kaushashshen amon da ya ƙara sanya ni na sha jinin jikina ainun. Kamar kazar da aka jefa da ruwan gishiri na amsa da ƙyar.
"Na'am Abba".
"Me yasa kike so ki sauya daga yanda na san ku a baya? Shin zuciyar ba ta tausayina akan irin fafutukan da nake yi wajen ganin na inganta tarbiyan, na tsaya kai da fata don tabbatar da cewa ba ki sauƙa daga kan gwadaben da kika taso a kai ba. Amatullah ina sa burin ganin rayuwarki ta inganta na ƙayatar da ita sa ilmi da tarbiyya daga yanzu har izuwa lokacin da zan miƙa ragamar rayuwarki a hannun mijinki".
Take hawaye suka ɓarke mini ban iya cewa komai ba har ya ɗaura daga inda ya yi birki.
"Ke ce duk wani buri da fatan da nake da muradin wanzuwansa a bayan ƙasa kafin na koma ga mahaliccina. Ba zan hana ki soyyaya ko na katange ki ɗaga kula kowa ba don yanzu kin yi hankalin da za ki iya tantance abun da zai dace da ke ko akasin haka. Amma a duk lokacin da kika ji a ranki kin fi buƙatar aure akan karatun da kike yi, to kar ki ji nauyin sanar da ni haka. Ni kuma na yi miki alƙawarin aurar da ke a lokacin da kika buƙata domin gujewa afkuwar ɓarna da yin dana sani a gaba".
Wani irin gumjin kuka ne ya zo mini mai ƙarfin gaske, gabaɗaya falon ya ɗauki sautin kukan. Na ja jiki na ƙara matsowa dab da shi na riƙe ƙafarsa gam sannan na kwantar da kaina a jiki.
"Abba na tuna na yi nadama, ka ji tausayi na ka yafe miji wallahi ba zan ƙara aikata makamancin irin hakan ba. Na yi alƙawarin ba zan ƙara yin abun da zai ɓata maka rai ba".
Bai ba ni amsa ba har sai da na cire tsammani.
"Ko kaɗan ba ki ɓata min rai ba Amatullah. Sai dai na ji ciwon ƙaryan da kika haɗa kai da Amira kuka yi min wanda na san ba halin ki ba ne hakan. A ina kuka haɗu da shi? Tsawon wani lokaci ya ɗaura yana zuwa wajenki? Sannan me yasa Amira ta ce ita ya zo nema bayan sunanki aka ambata?".
Tagwayen ajiyan zuciya na sauƙe da ya tafiyar da kukan da nake yi na koma sauƙe ajiyar numfashi akai a kai, tamkar wacce ta fafata a gasar fidda zakaran gwajin dafi na tseren gudu.
Sai da na fizgo numfashina da yake maƙalewa a ƙirji kafin na amsa masa jerin tambayoyin da ya watsa mini a lokaci guda.
"Wallahi ban taɓa ganin sa ba sai yau, ɗazu ne muka haɗu a inda na kai talla shi ne muka sama matsala da wasu ƴan mata har suka zubar mini da kunun kuma suka neme ni da faɗa. Shi ya hana su dukana kuma ya biya ni asarar da suka yi mini ya dage akan sai ya rako ni don tabbatar da na iso lafiya saboda sun yi ikirarin tare ni a wani wajen. Abba na rantse maka har da Sarkin da ya halicci sammai da ƙassai bakwai ba tare da wani ko wata ya kawo masa taimaka ko ba wannan shi ne gaskiya yadda muka haɗu da shi. Kuma ko yanzu ma sai da na roƙe sa akan kar ya ƙara zuwa yana nemana na ƙara tabbatar masa ma ba zan ƙara kai talla inda muka haɗu da shi ba. Amira kawai ta taimake ni ne don ta ga yadda gabaɗaya na rikici na kasa magana".
"Na yarda da ke Amatullah ba ni da shakka ko kokonto akan duk abin da zai fito daga bakinki. Ba da son raina ko aminvewata kike wannan tallan ba amma da iznin Allah na kusa kawo ƙarshen abun. Ki kwantar da hankalinki ki dinga taka-tsantsan da mutane don yanzu duniyar ta lalace".
"In sha Allah zan kiyaye". Kansa kawai ya gyaɗa bayan ya tallafo kaina na tashi daga jinginar da na yi a jikin ƙafafunsa. Ya miƙe zai shige ciki na yi hanzarin riƙo gefen rigarsa.
"Abba kar ka je ka kwanta da tare da bakinka ya furta kalmar yafiya gare ni ba. Hakan zai jefa ruhina cikin ƙunci da rashin nutsuwa".
Kyakykyawar ajiyar zuciya ya sauƙe da har sai da na jiyo sautin fitarsa kafin ya ce da ni wani abun da ya sanyaya sashin ruhina da nake jin kamar ana watsa mini garwashin wuta.
"Ko ban yi amfani da kalmomin baki wajen furta kalmar yafiya a gare ki ba. Zuciya ba za ta yi dogon zango tana dakon fushi da ke ba Amatullah. Na yafe miki kuma daman ba ki ɓata mini ba".
Sakakken ajiyan zuciya na sauƙe ina jin kamar an sauƙe mini wani ajiyan da aka yi mini a ƙirjina na kasa magana sai kuka, lallashina ya yi sosai har na dawo daidai kafin na yi masa sai da safe na cike cikin ɗakin. Lokacin Umma har ta yi bacci, ta kwanta a gefenta sai dai sam bacci ya ƙi kawo mini ziyara sai da na raba dare kafin na sama na iya runtsawa.
Washe gari haka na tashi da matuƙar ciwon kai ko kaina ban son ɗagawa balle na buɗe idanuna. Ina kwance a inda na yi sallan asuba, Umma ta ɗago labulen tana ƙira na na tashi na zauna kafin ta fesar da abin da yake tafe da ita.
"To ki tashi ki zo ubanki yana ƙiranki". Na tashi na rufa mata baya muka fito tare, na zauna a ƙasa yayin da ita kuma ta zauna a kujerar da Abba yake zaune kusa da shi. Shuru ya ratsa wajen kafin Umma ta buga tsaki.
"Ka tara mu ka ce za ka yi magana, mun zo kuma ka saka mu a gaba kana kallonmu. Idan ba ka da abin da faɗa ne ka sallame mu, don ni ina da abin da ya fi wannan zaman muhimmanci wanda zan yi". Wataƙila da Umma ta sama tagomashin kasancewa cikin mata masu lura da karanta ma'anar shuru da rabe-rabensa da ta fahimci shuru da kallon da Abba ya yi mata, yana bayyanar da ɗacin da maganarta ta yi masa ne. Amma sai dai kash! Ko a jikinta wai an mintsini kakkaura ko gizau ba ta yi ba.
"Na tara ku duka ne domin na sanar da ku wani hukuncin da na yanke wannan yake kamar umarni ne a gare ku". Umma ta katse shi ba tare da ya dire zancen ba"to muna jiranka sai ka tafi kai tsaye ga saƙon da kake son isarwa ai, ba sai ka tsaya kana wani kame-kame ba".
"Ina so na sanar da ku a cikin satin nan za mu tashi daga gidan nan. Don haka tun yanzu ku duk shirin da za ku yi".
Tun kafin ya gama zancen Umma ta yi zumbur ta miƙe tamkar wacce aka yi wa alluran doki, ta yi sakeke tana kallon Abba baki sake. Ta toshe kunnuwanta tana cewa"ban gane abin da kake faɗa ba Manniru? Ka yi bayani da harshen da zan fahimta ƙwaƙwalwata ta gaza amsar sauƙon da kake ƙoƙarin isar mata. Mu bar gidan nan mu je ina? Ina muke da shi bayan nan? Ko kuma kawai so kake ka yi amfanin da ikon da kake da shi a kanmu ka tozarta mu a idon jama'a?".
"Yadda kunnuwanki suka jiyo miki haka na faɗa Hafsatu za mu tashi daga gidan nan tashi na har abada. Ki fara shirya kayanki tun yanzu".
"Wallahi ba ka isa ba. Ba zan taɓa zuba ido wannan abun ya faru ba, Manniru anya kana lafiya kuwa ƙwaƙwalwarka ba ta sama matsala ba?".
"Zan ga tsakanin ni dake waye yake auren wani. Na yi rantsu ba zan yi kaffara ba ki isa ki sauya min ra'ayi akan wannan lamarin ba, dole ne mu bar gidan nan don ba zan zuba ido ina kallo tarbiyan ƴata tana lalacewa ba. Duk gini da foundation ɗin da na yi don inganta rayuwarta yana rugujewa ba, ba zan laminta ba".
"Da an yi magana