Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : Romantic Hausa Novels
ka ce ƴa ƴa kamar ka fi kowa ƴa ko a kanka kawai aka fara haihuwa. Duk mazauna gidan nan ba su ce tarbiyyan ƴaƴansu zai lalace ba sai kai uban masu ba da tarbiyya. Wai tarbiyyan nan kai ne kake yin ta ko taimakon Allah ne? Manniru kar ka biye zuciyarka ka cutar da mu babu gaira babu dalili, ka sani na sani daga kai har ni duk ƙoƙarinmu wajen tarbiyya ba zai iya sa yarinyar nan ta kasance cikin amintattu ba, face sai Allah ya dafa mana. Iyaye nawa ne wanda suka kasance manyan malaman addini amma ƴaƴansu suka fi kowa kangarewa da lalacewa ba. Ga misali nan Manniru Allah ya buga mana akan Annabi Nuhu wanda shi annabin Allah ne ma amma iyalinsa suka kauce hanyar da yake. Shi kuma sai ya ce me ye a Ubangiji?".
Ɗan jim Abba ya yi don ta gama ɗaure sa da jijiyar jikinsa.
"Ko me ye za ki faɗa barin gidan nan wajibi ne. Saboda gujewa faruwar abubuwa da yawa don haka na gama magana, kina da zaɓi biyu ko ki haɗa kayanki mu tafi tare ko ki yi zamanki a nan ki ci gaba da ɗaukar nauyin kanki kamar yadda kike ikirarin kina yi". Yana dasa aya a nan ya fice ransa a matuƙar ɓace. Ihu Umma ta kurma kamar za ta yi hauka ta zube ta yi zaman ƴan bori.
"Shikenan na shiga uku na lalace! Ni kake yi wa kora da hali Manniru? Dole na tashi tsaye a cikin gidan nan. Na rantse ba za mu taɓa tashi daga gidan nan ba ko za ka haɗiye zuciya ka mutu dare ɗaya......".
Ba ta ƙarisa ba na yi hanzari tashi na je na rufe mata bakinta.
"Don Allah Umma ki yi haƙuri. Ki dinga yi salati zuciyarki za ta yi sanyi, ba daɗe irin wannan maganar ko kaɗan".
Ta ture hannuna kafin ta ce"Amatullah ya ya zan yi da raina? Idan muka bar gidan nan ina za mu dosa? Sanin kanki ne ba mu da wani matsugunin da ya wuce nan, a nan ne kawai asirinmu zai rufu amma ubanki ya dage sai ya tona mana asiri sai ya fallaso sirrinmu ga duniya. Wallahi ba zan taɓa barin hakan ya faru ba tashi ki ɗauko min hijabina na fita".
"Umma ina za ki je a cikin wannan halin da kike ciki?".
"Wajen Malam zan je don shi kaɗai ne zai share min hawaye nan take".
[7/18, 11:05 AM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
_______________________________________
Page 1️⃣1️⃣
Ganin tana ƙoƙarin tashi ya sani saurin cafko hannunta ina yi mata magiya"don girman Allah Umma ki rufa mana asiri kar ki je ko'ina. Da bakinki fa yanzu ki ka ce Abba yana so ya tona mana asiri amma asalin tonon silili zai faru ne daga loakcin da kika je kika baje wannan lamarin a wani can da daban da yake bakewa da malunta yake aikata abin da ba shi ne ba". Zafin marin da ta sauƙe mini a gefen kuncina na hagu shi ya sani haɗiye ragowar zancen ba tare da na furzo shi waje ba, kafin na yi aune ta ƙara sauƙe mini wani marin a karo na biyu da sai da ya tursasa mini sakin ƙara. Tsabar azaba da zogin da fatar wajen yake yi mini da nake jin tamkar ruwan tafasasshen ɗanyen dalma aka watsa mini.
"Sai yau na tabbatar har yanzu ba ki da hankali Amatullah girman jiki ne kawai da ke amma hankali kam sam babu shi a tattare da ke. Don ya wulaƙanta ni sai da ya ƙira yo ki sannan ya yi wannan ikirarin, ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba wannan duk shiri da tuggun Maman Umar ne kuma sai na nuna mata ina daidai da zamaninta. Manniru kai da ka bar gidan nan wallahi sai dai a cikin makara amma zaman daram yanzu ma aka fara sai mun ga abin da ya turewa buzu naɗi".
"Umma ki tuna fa komai ya yi zafi maganinsa Allah shi ne ya ke juya dare zuwa rana. Ya yaye ƙunci ya wanzar da farin cikin a zuciyar da cikinta babu kusuni. Me zai hana ki yi alwala ki yi salla raka'a biyu ki ba shi zaɓi ya zaɓa mana mafi alkhairi". Ba ta ce da ni komai ba illa bangaje ni da ta yi gefe guda ta shiga ɗaki ta ɗauko hijabinta ta fita, zubewa na yi a wajen na kwanta na yi luf ina sakin wani maraya kuka marar sauti.
Jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau ji nake yi kamar na tashi na ruga da gudu na je na dakatar da Umma daga abin da yake shirin aikatawa, sai dai gangar jikina ya ƙi ba ni haɗi kai wajen motsa ɗaya daga cikin gaɓoɓina. Har na ci gaba da kwanciya har izuwa lokacin da Amira ta shigo ta iske ni cikin mayuwayacin hali. Cikin tashin hankali ta iso inda nake zube ta ɗago ni sai dai na kasa tashi dole na koma na zauna na kifa kaina akan gwiyoyina ina ci gaba da kukan.
"Amatullah me ye ya faru?". Ta jefa min tambayar muryarta tana rawa, rashin samun daga gare ni bai hana ta ci gaba da tambayar duk abin da take tunanin shi ne sanadi da musabbabin kukan nawan ba.
"Ko dai mutuwa aka yi muku ne?". Na jijjiga mata kaina alamar a'a kafin na yi nasarar cira kaina ina duban ta da kumburarrun idanuna da suka rikiɗe suka sauya kala zuwa launin ja.
"Da abin da yake shirin faruwa ai gwara mutuwar ma Amira. Tun da dai shi wanda ya mutu ya huta daga rikici da fituttunun duniya sai dai ya je ya tarar da abin da ya shuka".
Ta waro idanunta tar a kaina"ke kin san zafin mutuwa kuwa? Ko don har yanzu kina ganin iyayenki biyu kuna rayuwa tare? Billahillazi mutuwa ta fi komai ciwo da raɗaɗi don har yanzu zuciyata cike take da gurbin rashin mahaifina duk da ya rasu tun kafin na mallakin hankalin kaina. Kuma alhamdulillah Baba Habu mijin Umma bai bar ni na yi kukan maraicin uba ba".
"Wani babban lamari ne yake dab da faruwa ko ina ce warhaka kam komai ya faru".
"Ki sanar da ni me ye yake faruwa don Allah, kar ki bar ni cikin duhu Amatullah".
Dogon numfashi na ja na fesar kafin na zayyana mata duk abin da ya wakana ban ɓoye mata komai haka nan ban tsallake ko da layi guda ba. Ta yi shuru kamar mai tunanin wani abu kafin can ta yi magana.
"To amma ke me ye kike tunanin ya sanya Abba yanke wannan hukuncin lokaci guda haka?".
"Ban san dalilinsa na yanke wannan hukuncin ba kuma cikinmu babu wanda ya tambaye sa".
Ta gyara zamanta kafin ta soma cewa" Samu gidan hayan a ƙurarran lokaci fa abu ne mai matuƙar wuya gwara ma ina kana da kuɗinka a hannu. Kuma ko da kuɗinka ma ba za ka sama yadda kake so ba, shi yasa gaskiya ni ban ga laifin Umma ba. Me ye amfanin a yi abun da daga baya za a zo ana dana sani?". Mamaki kwance a fuskana nake bin ta da kallo saboda dukan da zantukanta suka yi wa kwanyata.
"Kina nufin ba ki ga ma rashin dacewar abin da Umma za ta yi a addinance ba kenan?".
Ta riƙo hannuna"har ga Allah ban ga ni ba, don a tunanina haƙƙin kowacce uwa ne samar da daidaito a rayuwar gidan aurenta. Kuma Umma ta fi mu tunani ba za ta taɓa yanke hukuncin da zai cutar da ɗaya daga cikinku ba don haka kawai ki goya mata baya". Na fizge hannuna"kin manta wajen wanda na ce miki za ta je ne Amira? Wannan Malamin ba da yake fakewa da addini yana aikata alfasha. Ta inda mutum kamar ta mai ƙafafu biyu zai taimaka maka bayan shi ma mabuƙaci ne a wajen Allah?".
Taƙaitaccen murmushi ta yi tana kallona da wutsiyar idonta ta furta"amma kin san aikinsa yana tasiri akan ko waye kuma an yi ittifa'i ba a taɓa zuwa masa da kukan da ya kasa gogewa mai shi hawaye ba. Bari na sanar da ke wani sirri ko Ummata da shi ta dogara wajen kankaro mutunci, daraja har da kima a idanun Baba Habu".
"Kina nufin Ummanki tana zuwa wajensa? Tirƙashi!". Na yi mata tambayar a rikice.
Ta gyaɗa mini kanta"ƙwarai kuwa har ma tana aike na na karɓo mata saƙo daga wajensa".
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'u! Shikenan mun shiga uku!".
Na furta cikin maɗaukakin tashin hankalin gami da firgicin da yake ƙoƙarin tarwatsa zuciyar da take dashe a cikin ƙirjina. Da mamaki babu ko ɗigo mamaki balle kiɗima a tattare da Amira.
"Me ye abun cewa mun shiga uku Amatullah? Ni da wannan kalmar tsinka min zuciya take yi, zamanin ne ya lalace an daina kiwon dabba an koma na mutum. Ba ka damu da mutum ba amma shi yana can yana hana idonsa runtsawa a ƙoƙarin ganin ya ga bayanka kin ga kuwa ai dole ka tashi ka kare kanka, tun da ko Allah ma cewa ya yi sai ka tashi sannan zai taimake ka".
Takaici ya zo mini har wuya wani ɗaci ya gauraye da yawun bakina ya jirkita shi gabaɗaya ta yadda sai da na ji kamar na yi amai. Da ƙyar na haɗiye sa ta hanyar wuyana ya wuce kamar na haɗiye ƙarangiya.
"Ai ba irin wannan lamarin ake nufi ba. Ta yaya za ka je wajen wanin Allah kana neman taimakon da shi kasan in ya tsinci kansa a cikin irin halin da kake ciki ba zai iya samarwa kansa mafita ba, kina ganin akwai basira a cikin aikata hakan?". Ta taɓe baki tana jefa da wani irin kallo alamar ta soma gajiya da fahimtar da ni abin da kaina ya gaza ɗauka balle ƙwaƙwalwata ta amshe shi.
"Ni kam ban wani irin taurin kai Allah ya zuba miki ba. In da kin fito a cikin mutanen farko irin riƙaƙƙun kafiran nan zai yi wuya ki karɓi musulmci, ga zahiri nan ki na kallo amma kuma runtse ido . Amatullah ya zama dole fa mu amshi abin da zamani ya zo mana da shi, mazan ne yanzu sai da haka sai ana danganawa ga Malamai kafin a shawo kansu. Na rantse miki ba don irin wannan taimakon daga malamai ba da yanzu wani maganar ake yi ta daban mussamman Baba Habu da Allah ya yi wani irin murɗaɗɗan mutum mai wuyar sha'ani, a hakan ma yaya balle kuma an zauna haka nan".
Ni kam shuru na yi don gabaɗaya na rasa me ye zan ce da ido kawai nake bin ta har ta kai aya. Na ja wani gauron ajiyar zuciya na fesar kafin na gyara zamana, na soma ambaton Allah a cikin zuciyata.
Ina da tabbacin shurun da na yi ne ya sanya ta ta ture komai ta koma kwantar mini da hankali da kalamai masu taushi da sanyi. Har sau da na ji raina ya sanyaya, na ƙara yarda a duniya bayan iyaye da dangina ba ni da wacce take yi mini irin ƙaunar da Amira take gwada mini wanda babu sirki a cikinsa.
"Yanzu dai ki tashi mu gyara ɗakin nan. Sannan na ba ki wani daddaɗan labari".
"Fara ba ni labarin tukunnan". Na yi zancen cikin dauriya ina ƙoƙarin dasa murmushi a fuskana.
"Mansur yanzu haka yana hanya. Saura kuma in munje ki ɗaure fuska ki yi ta shan magani". Ta ƙarishe zancen tana galla mini harara.
"Allah ya kawo shi lafiya".
"Amin ta hannun dama.Don Allah ki saki ranki ke ba wani shegen kyau kike da shi ba kuma ki zo kina wani ƙara haɗe hanci da gira duk sai ki ƙara muni". Ta ƙarishe zancen tana galla mini harara.
"Ai kuwa a hakan kin san na fi ki kyau sau dubu ɗari". Ta fashe da dariya tana faɗin"kin dai fi mi auki shi ma kuma girman buredi ina gaya miki, amma ni ba ta yau ba ce". Daga haka duk muka saka dariya kamar babu wani abun da ya faru, wannan dalilin yana daga cikin muhimman dalilin da yasa nake jin Amira har ƙasan raina. Don ba ta jure ganina cikin ƙunci duk yanda zai ta yi sai ta yi ta fitar da ni daga halin da nake ciki. Tare da ita muka yi komai har na ɗumama mana ragowar abincin jiya muka ci ita ma ta amso mana waina a wajen Ummanta muka ci muka yi hani'ƙan, sai na ji duk damuwar da na tashi da shi na neme shi na rasa sa. Muna gamawa wayarta ta soma ruri ta hasko mini fuskar wayar tana faɗin"kin ga Mansur ne".
Ta ɗaga ya sanar da ita ya zo muka tashi muka fito har mun zo zaure kafin ta soma ba ta labarin yadda muka yi da Abba daren jiya. Ta ja ta tsaya riƙe da kunkuminta tana kallona.
"Kina nufin Abba ya gane gaskiyar komai? Mun shige su". Na gyaɗa mata kaina alamar e.
"Wallahi ya gane komai amma na ba shi haƙuri ya ce komai ya wuce sai dai na kiyaye gaba".
Ta murmusa kafin ta ce"Allah sarki! Abba wallahi sauƙi halinsa da yanda yake kulawa da tarbiyyanki wani lokacin yana sani kewar mahaifina sai na ji duk duniyar na yi mini zafi".
Na kai mata duka a kafaɗarta"ke dai kam ki godewa Allah don Baba Habu bai rage ki da komai ba". Ta sauƙe numfashin da har sai da na jin sautinsa kana ta ce"Amatullah ba za ki gane raɗaɗin irin ciwon nan. Babu wanda yake maye gurbin iyayen sai dai kawai a kamanta". Tana gama maganar ta yi gaba ta bar ni.
Na fita a baya muka je wajen Mansur yana tsaye a jikin motarsa tana latsa wayarsa yayin da wani abokinsa take kusa da shi, da sallama ɗauke a bakinmu muka isa wajen su suka amsa mana yayin Mansur yake tattara dukkan hankalinsa kan Amira.
"Gimbiya kin fito?".
"Ai ka san ba zan zo na bar Sarkina a tsaye ba". Ta saki murmushin jin daɗi zai yi magana na katse shi.
"Tun da na ga alama idanunka ita kaɗai yake gani, babu amfanina gwada na ja ƙafafuna na koma".
"Afuwan ranki ya daɗe. Idanuna sun ganki amma zuciyar ce gabaɗaya tana tare da ita. Ya kike ya gidan?".
"Lafiya ƙalau ka zo lafiya".
Ya amsa cike da kulawa"lafiya sai dai na tabbatar da zaran na bar nan zan zama majiyanci ne". Amira ta yi masa wani kallo da hakan ya sanya sa cewa"e mana tun da sai na shafe sati guda ban yi tozali da ke ba. Wallahi Amira ba don Alhajinmu ya matsa min akan lalle ni zan wakilce sa a wannan taron ba, babu wani dalilin da zai sa na yi nisa da ke". Jim ta yi gabaɗaya jikinta ya mutu yanayinta ya sauya ta kasa cewa komai illa kallon juna da suke yi.
Ba su dawo duniyar zahiri ba sai da abokinsa ya yi magana"ni ma tun wuri bari na san inda dare ya yi min. Don na ga alama an manta da ni ".
Mansur ya ce"Haba kai kuwa Mukhtar ni na isa na manta da kai. Kawai dai ka san an ce sawun giwa ya danne na raƙumi". Dukkan mu muka fashe da dariya sai da muka tsagaita Mukhtar ya kallo ni yana cewa"kin ga ƙawarmu waɗannan mutanen ba ta mu suke yi ba. Ya fi dacewa mu matsa mu ba su wajen".
"Ai kuwa na ga alama". Na yi maganar yayin da nake bin bayansa muka matsa gefe, mun ɗan yi hira jifa-jifa kafin Amira suka yi sallama da Mansur. Da ya buɗe bayan boot ɗin motarsa ya fara sauƙe mata manyan ledodi sai da abin ya ba ni tsoro aƙalla sun kai bakwai a ƙidayen da na yi kuma dukkannisu shaƙe suke da kaya. Har da kukanta da Mansur zai tafi shi ma duk yanayinsa ya sauya haka ya shiga mota ya tafi bayan ya yi mata alƙawarin ƙiran ta da zaran ya isa garin da zai je.
Muka kwashi ledodin wanda za mu iya muka shiga da su ragowar kuma muka saka yara suka shigo mana da shi. Ina cikin lallashina Amira a ɗakinsu Umma ta aiko ƙira na na tashi da hanzari na je.
[7/19, 7:42 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
______________________________________
Page 1️⃣2️⃣
Tana zaune a falo ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya ta kwantar da kanta a jikin kujera ta lumshe idanunta kamar mai bacci. Gaban ta wani baƙin leda ne a ajiye. Sai da na nema waje na zauna kafin na ce"sannu da dawowa". Ba tare da ta buɗe idanunta ba ta amsa mini tana ci gaba da cewa"ki haɗa wuta ki ɗaura min ruwan kunu". Na ɗan jim kafin na ce"Umma lokacin islamiyya fa ya yi". Sai a sa'ilin ta buɗe idonta tana kallona"ai tun da ba ki da safe ba to tabbas sai kin fita na rana".
"Ranan nan ma fa ban sama zuwa, da kin yi haƙuri yau ɗin na je ko da yamma inna dawo sai na fita da kunun". Ba ta ce da ni komai ba ta ta shi ta ɗauki ledar ta shige cikin ɗaki ba ni da zaɓi dole na tashi na fito na huta wuta na ɗaura ruwan da ta umarce ni na zauna na zabga tagumi sai da ruwa ya tafasa na je na sanar da ita ta fito ta dama kunun yayin da na shiga ciki na gabatar da sallan zuhr. Na fito na yi wanka na fara shirin fita idona ya raina fata lokacin da ta miƙo mini kwallin ta ce na saka a idona bayan ta gama turare bokatin kunun da hayaƙi.
Zuciyata kamar za ta tsago ƙirjina ta bayyano waje tsabar bugawan da take yi duk kuka da magiyar da nake yi wa Umma hakan bai yi tasiri ba, dole ƙanwar naƙi na karɓa kwalli na saka a idona. Na ɗaura bokatin a kaina na fita ina tafe ne kawai amma ban san inda nake cilla ƙafafuna ba mussamman da na ga duk