Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : Romantic Hausa Novels
ne?".
"Gargaɗi ta zo ta yi mini akan saurayinta Auwal".
"Cab! Ke kuma kika ce mata me ye?".
"Me ye kuwa zancen da ya wuce na ce ta yi haƙuri".
Ta tafa hannu kafin ta ce"wallahi in ni ce ba ta isa na ba ta haƙuri ba, akan wani saurayinta mai zubin ƴan daudu ga shegen kallon matan tsiya". Ta ɗago kai na yi mata kallo guda kafin na furta"ki rufawa kanki asiri ki yi shuru kafin ta ji ki wani rigimar ya kaure. Kin san ita ba tsohon ta mutu take yi ba balle ta rayu".
Ta tsirtar da tsaki"to sai me ye in ta ji? Ke dai Amatullah Allah ya ƙara miki haƙuri kawai". Taƙaitaccen murmushin gefen baki na yi na amsa da cewa"Amin ya Allah". Mun ɗan taɓa hira kafin ta miƙe tsaye na bi ta da kallo kafin na yi magana ta riga ni.
"Bari na yi shiri fita tallan dare kafin lokaci ya ƙure".
"Da kin zauna mun yi hirar mu ke da in kika fita sai mutum ya yi bacci kafin ki dawo". Ta bushe da dariya kana ta ce"dududu ƙarfe nawa nake dawowa Amatullah? Karfe sha ɗaya ne fa zuwa da rabi. Ke dai bari na wuce na san yanzu an gama dafa min awarar a gidan Tasalla".
Kasa cewa da ita komai na yi har ta wuce saboda mamakinta da nake yi na rashin tsoro komai dare ba ya hana ta fita talla haka kuma za ta ratso ta dawo gida idan ta gama soya awarar.
Sai da na kammala girkin na kwashe na tattare wajen, na ɗeba nawa na ci a wajen na kai wa Umma na ta kana na ajiye na Abba. Wanka na yi na yo alwala na yi sallan isha'i na ɗauko littattafaina na fito zaure ina nake ƙara wa yara karatu bayan sallan isha'i.
[6/14, 11:31 AM] iyammaimuna: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
______________________________________
Page 0️⃣4️⃣
Muna tsaka da karatun Abba ya shigo na miƙe zan karɓa ledar dake hannunsa bayan na yi masa sannu da zuwa.
"Zauna ku ci gaba da karatunku". Ya furta fuskarsa washe da annuri, hasken ƙwan fitillan aci bal-bal da na kunna a wajen shi yake ba ni damar kallon fuskarsa har na fahimci yanayin da yake ciki. Ƙarfe tara na sallami yaran kowa ya watse kafin na koma cikin gidan.
"Hafsatu na gargaɗe ki da ki fita daga harkan Ibrahim da kuma matarsa amma kin yi kunnen uwar shegu da zantukana. Ki sani kin fara kai ni bango fa, me ye haɗinki da mijin wata bayan kasancewarki matar aure? Da ilminki da komai amma kike takewa wane irin rayuwa ce wannan kika ɗaurawa kanki?. Saboda son zuciyarki da masifar son kuɗi ki ja wa baiwar Allah duka daga wajen mijinki kuma tsabar tsaurin ido irin na ki kika yaɓawa ƴan uwanta magana".
Zantukan Abba kenan da na fara cin karo da shi yayin da na kutsa kai cikin falon. Jikina ya yi sanyi ƙalau kamar kazar da aka jefa da ruwan gishiri, shirib na zauna akan ɗaya daga cikin kujerun da suke cikin ɗan madaidaicin falon na mu da hakan yake ba ni damar sauraron abin da suke tattaunawa daga cikin uwar ɗaka.
"Roƙansa kuɗi na yi ko kuma maula na yi? Da za ka ɗebo tsamin jikinka ka zo kana yi min hayagaga a kaina. Dare ma da ya kasance mahutan Bawa ba za ka taɓa barin mutum ya huta ba".
"Hafsatu ni kike cewa ina yi miki hayagaga?".
"Kai ɗin fa Munniru. Wani irin masifa ce wannan? Kai komai na yi a idanunka ban fita ba. Ka ƙwammace ka goyi bayan matar wani akan ka goyi bayan matarka ta sunna har kake ƙiran ta da baiwar Allah. Duka kuma ba ni na ce ya sake ta ba tashin hankalinta ne ya jaza mata, ƴan uwanta kuma da ta kwaso ba a haifi shegiyar da za ta zo har inda nake ta gaya min magana na ƙyale ta ba. Kuɗi kuwa ko sau dubu sai ɗauka ya ba ni billahillazi sai na amsa ai ba tursasa masa na yi ba shi ya yi niyya, kai ba ka ba ni ba kuma ban ga dalilin da za ka hana ni karɓa ba".
Sai mintuna suka shuɗe kafin Abba ya ce"ki kiyaye harshenki, ki dinga tauna lafazi kafin ki furta shi. Domin da zaran ya fita to ba a iya dawo da shi. Shi yasa Annabinmu da kansa ya ce kuffa alaika haza ma'ana ka kiyaye wannan a gare ka watau harshe, dafinsa ya bi na bakin maciji. Ke komai ya fito daga bakinki za ki yaɓawa mutum ba tare da tunanina ba, Hafsatu ina guje miki ranar da za ki yi dana sani".
"Babu dana sanin da zan yi Munniru, bakinka ya sari guntun gashi".
Ta yi zancen tana banko labulen ɗakin ta fito falo. Kamar wacce aka tsigara wa matsilli haka na zabura na tashi, kallon da ta tsare ni da shi ya sani saurin rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa.
"Watau kin na zaune a nan kin kasa kunne kina sauraron abin da muke tattaunawa ko?".
Na girgiza kaina"ban daɗe da shigowa ba ma". Ta doka mini tsawan da ya haifar mini da rawar jiki.
"Dalla rufe min baki munafukar banza munafukar wofi. Duk ba ke kika ce ummul abasin faruwar komai ba. Shegiya ƴar iska mai jinin tsiya". Kafin na ce wani abu tunin Abba ya fito falon cikin matsanancin ɓacin ran da ya bayyana ɓaro-ɓaro a bisa kammalalliyar fuskarsa da farin gashi su ka yi masa ƙwawanya a saman harbarsa. Ya nuna ta da ƴar manuniyar ƴatsarsa da hakan yake tabbatar da ya kai ƙololuwan ɓaci rai da faɗa wa cikin tarin takaici.
"Na hane ki da jifan Amatullah da waɗannan munanan kalaman amma kin liƙa wa kunnuwanki gayan tuwo. Shin ashe idan wani ya ce da ita shegiya ko ƴar iska abin ba zai yi miki ciwo ba kenan?. Ke uwa ce ki zama mai tausasa lafazinki akan Amatullah. Ba na son mins sa'in sa dake amma ke kike jan komai".
"Mtscheew".
Umma ta ja dogon tsaki tana yi wa kanta mazauni a kujerar da na tashi daga kanta, jinjina kansa kawai Abba ya yi kafin ya maido da duban sa gare ni yana faɗin"Amatullah ki kai min ruwan wanka".
"To Abba".
Na amsa da shi yayin da nake fita daga falon na ɗauki bokiti na cika da ruwa na kai masa bayi. Kana na zo na sanar da shi. A uwar ɗaka muke kwana tare da Umma yayin da shi kuma Abba yake kwana a falo, tun da na yi girma na yi wayo muke yin hakan wannan dalilin ya sa kullum sai na yi addu'an Ubangiji ya buɗa wa Abba ya yi gidan kansa ko da kara ya kewaye mana mu koma. Mu huta da wannan baƙin masifan takuran. Kamar a mafarki haka nake jiyo sautin maganar a tsakiyar kaina na mirgina ina murtsike idanuna tare da buɗe su kana na maida su na lumshe. Duk da haka ban daina jin sautin yana tashi ba dole ƙanwar naƙi na tashi ina yin miƙa daidai lokacin limamin masallacin kusa da gidanmu ya rangaɗa ƙiran sallan assalatun cikin zazzaƙan muryarsa mai sanyi.
Na tashi zan fita falo na jiyo Abba da Umma ne suke magana na koma na zauna, don ba na ƙaunar sauraron abin da suke tattaunawa wanda ina da tabbacin zai iya zama sirrinsu ne wanda bai dace na ji ba. Ina nan zaune Umma ta shigo tana ta bambamin da ban gane takamanmen akan abin da take yi ba, na tashi na fita domin ɗauro alwalan sallan asubahi na tarar da an haɗa wani rigimar a filin tsakar gidan.
Maman Rayyan ce take ta surfa masifa Asabe tana taya ta, a nan na tsinci kan zancen wai a daren jiya ne gandaderen ƙato ya shiga har uwar ɗakinta yana shafa jikinta, kasancewar mijinta ba mazauni ba ne ya kan yi watanni biyar zuwa shida ba ya gida.
Har hantsi ya fito masifa da bala'in bai lafa ba abu kamar wasa har ya kai gaban mai unguwa da wasu manyan unguwan, ina kwance a ɗaki ina fitan karatun islamiyya Amira ta shigo sai da na kai ayar ƙarshe da nake karantawa na cikin suratul tagabun kafin na rufe ƙur'anin ina duban ta fuskana cike da murmushi.
Kafin na yi magana ta datsi numfashina"karfe goma da rabi na dawo, na san abin da za ki tambaya kenan".
Na murmusa kafin na ce"ai ke da kan ki Amira ya kamata ki yi wa kanki faɗa, wannan daren da kike kai wa a waje ba mutuncinki ba ne a matsayinki na ɗiya mace. Ko na miji ne ai duk inda goma zuwa sha ɗaya ta yi daga lokacin ta fara neman hanyar gida balle kuma mace".
Ta yatsina fuska kafin ta ce"kin ga ni ba wannan ba ne ya kawo ni. Amshi ki buɗe ki ga". Ta ƙarishe zancen tana ajiye mini wani baƙin leda a bisa cinyata, ta bi ta da kallon mamaki.
"Mene ne a ciki?".
Na jefa mata tambayar ina juya ledar a hannuna.
"Ke kuwa ki buɗe mana idanunki su gane miki". Kamar yadda ta faɗa hakan na yi na soma ciki-cikin buɗe ledar. Kwalin waya ce sabuwa dal da ita ƴar shafai. Na kwasa ihu ta yi hanzari rufe mini baki da tafukan hannayenta na zame hannunta.
"Amira Ina kika sama wannan dalleliyar wayar nan? Ko wani ne ya ba ki ajiye? Ko aka aike ki da shi wani wajen?". Ta saki dariya har da riƙe ciki sai da ta yi mai isharta kafin ta tsagaita gami da faɗin"babu ko ɗaya nawa ce, daren jiya ta zo hannuna". Na watsa mata kallon mamaki da al'ajabi.
Cike da son tabbatar mini da sahihancin abin da ta furta ta ɗage mini idonta guda tana zarce wa da cewa"wallahi kin dai ji rantsuwa kenan ko, wayata ce". Na katse ta kafin ta ƙarisa zancen.
"Ina kika sama kuɗin sayan wannan wayar Amira? Ita wayar nan ce fa ta cikin shirin film ɗin labarina, ta hannun Baban Sumayya. Kuma na san ko riba da jarinki gabaɗaya kika haɗa ba za su sayi wannan wayar ba". Ta kuma fashewa da dariya kafin ta ce.
"Ba ko sisina a cikin kuɗin wayan nan Mansur ne ya kawo min ita jiya, tukwuicin amsar tayin soyayyarsa da na yi".
Kamar saƙaho haka na saki baki da hanci ina bin ta da kallo tamkar yau na fara tozali da ita. Sai da na tattaro jarumta na yaɓa wa kaina kafin na iya yin motsin kirki har na iya furta wani abun.
"Amira anya kuwa kina da hankali? Haka siddan daga haɗuwa da mutum ya ɗauki wannan wayar ya ba ki kuma ki sa hannu ki amsa". Ta galla mini harara tana fizge wayar daga hannu.
"Kin ga Amatullah kar ki ɓata min rai da sanyin safiyar nan, sanin kanki ne a kaf cikin gidan nan da ke kaɗai nake hira har na saki jiki na sanar da ke abubuwan da nake yi". Ganin tana ƙoƙarin ficewa ya sani riƙo hannunta.
"Kar ki ɗauka da zafi mana ke kuwa. Ki yi haƙuri".
"Ke ce ai kike ƙoƙarin ɓata min rai Amatullah". Ta koma mazauninta ta zauna ta murtuƙe fuska.
"Haba! Ke kuwa saki fuskar mana ta Mansur". Babu shiri ta ƙyalƙyale da dariya.
Ta gyara zama tana zubo mini bayanai"ban san inda yake ba amma dai a gajerin da nake kai tallar waina muka haɗu da shi ya kawo gyaran motarsa, ya saya waina ya buƙaci lambata na ce da shi ban da waya. A haka kusan kullum sai ya zo gajerin don kawai ta ganni har ya yi min tayin soyyarsa bayan na gara shi shekaran jiya na amince. Daren jiya kuwa ya same ni har ƙofar gida ina soyar awara ya ba ni ita, bayan p yi min juye".
Ƙwala mata ƙiran da mptessghaifiyarta Sahura ta yi mata shi ya hana ni furta zancen da na yunƙuro da nufin yi. Ta tattare kwalin wayar ta miƙe"bari na je na san yanzu Ummata ta kammala wainar, duk sauran ƙarin bayani inna dawo za ki ji shi". Da kallo na raka ta har ta fice na gaza cewa komai saboda giyan mamakin da ta shayar da ni, haka na zauna ina bitar zantukan Amira tare da yi musu tankaɗe da rairaya.
Ƙatuwar ajiyar zuciya na sauƙe ina tallafe kuncina lalle Amira ta kusa ta fi ƙarfina. A kwanakin baya sai da muka daina magana da ita don kawai na gaya mata gaskiya akan irin shigar banzan da take yi in za ta fita talla. Ko da na yi mata magana sai ta kaɗa baki ta ce da ni idan ba ta yi kwalliya waye zai kalle ta balle har ya sayi abin da take sayar wa. Yanzu ga halin biyewa samari da ta tsira.
"To maza malalaciya tashi gari ya waye. Ga kunu can ya kammalu".
Na tsinkayo amon Ummata da ya yi nasarar dawo da ni duniyar zahiri daga karatun wasiƙan jakin da na faɗa.
DAFIN HARSHE
©️ Maimuna Tijjani Iyam
_______________________________________
Page 0️⃣5️⃣
Zumbur na miƙe na rarumo hijabina na saka na bayyano waje, tana tsaye a baranda ta cika ta yi him da dukkan alamu ƙiris take jira ta fashe. Na durƙusa a gabanta sai dai tsoron da ya yi mini katutu a cikin ƙalbina ya hana ni furzar da zancen da ya maƙale mini a bakina.
"Uban me ye kike jira? Shegiya mai zubin aljanu".
Ta doka mini tsawan da ya tilasta mini runtse idanuna ƙirjina yana tsananta bugu. Ta rusunar da kaina ƙasa kafin na soma faɗin"daman tambaya na nawa ne zan yi". Da alama zancen nawa ya yi tasiri wajen ƙara rura wutan da yake huruwa a cikin ƙirjinta, ta yi ƙwafa tsabar takaici. Duk da idanuna suna ƙasa amma a jikina nake jin ni take kallo.
"Amatullah kina ƙure ni fa kina tuntsira ni. Ina jiye miki tsoron ranar da zan yi wasan kura da ke a cikin gidan nan. Dan ubanki na dubu ɗaya ne da ɗari biyar, idan kin ga dama ki dawo min da shi yadda na kika fita da shi. Tun da daman ke ba ki gaji abin azurki ba tsinanniya". Babu shiri na ɗago kaina"don Allah Umma ki yi haƙuri in ranki ya ɓaci ki dinga yin shuru. Kullum ana gaya mana a islamiyya cewar ba a son a dinga yi wa ƴaƴa irin waɗannan kalaman".. Kallon da ta tsare ni da shi ya sani yin shuru tare da mayar da kaina ƙasa ƙwalla suna ciko mini kurmin idaniyata.
Fahimtar abin da shurunta yake nufi ya sani tashi na naɗa gammo na ɗaura bokitin kunun a kaina, numfashi mai zafi na fesar daga bakina ina ƙarewa layin namun kallo. Don ban ma san inda zan nufa na sayar da wannan kunun ba. Amon muryar Auwal da suka yi wa ƙofofin kunnuwana sauƙan bazata.
"Amatullah kenan! Ƴan mata adon gari matar manya, irin ta gaban mota".
A tsorace na waigo ina bin sa da kallo cike da son ƙarin haske, kamar ya san abin da yake cikin raina ya ci gaba da magana kansa tsaye ba tare da tsoro ko shayin komai ba.
"Allah ya yi miki zubi da tsari uwa uba ga diri kamar ke kika zana kanki, wallahi ba namijin da za ki wulga ta gabansa bai ji wani abu a cikin ransa ba. Ni da sai yanzu ma na fahimci na yi zaɓen tumun dare, sam Ummi ba ita ce kalan matan da nake so ba sai dai ance da babu gwara ba daɗi. Amatullah na yi miki alƙawarin matuƙar kika amshi soyyayata a shirye nake da na yi watsi da Ummi daga cikin zuciyata, daman can ba shiga can ciki ta yi ba".
Sakeke na tsaya ina kallonsa raina cike fal da mamakin furucinsa da yadda yake ya wani kanne ido guda ana lashe leɓan bakinsa kamar maye.
Na gyara tsayiwata kafin na harhaɗo jarumta har na sama ƙarfin gwiwan iya furta"Auwal babu abun da ya haɗa ni da kai saurayin Ummi ne kai kowa ya shaida hakan, na roƙe ka don girman wanda yake yi mana ruwa da ƙanƙara ka fita daga harkana ko har ka manta abin da ya faru ne? Ba na son na ƙara tsoma kaina cikin wani masifan". Na ƙarisa zancen cikin sigar roƙo da magiya sai da dukkan alamu roƙon nawan bai ɗaɗa sa da ƙasa ba.
"Tun ranar da na yi ido huɗu da ke Allah ya ɗaura min sonki a cikin zuciyata, ba yin kaina ba ne ni ma Amatullah. Kuma ina mai ba ki haƙuri akan abun da ya faru, ban yi da wani manufa ba kuma ban yi tunanin lamarin zai yi ƙamari har haka ba, ki yi haƙuri ya ke Sarauniya". Yana rufe bakinsa muka yi ido huɗu da Salmanu ƙanin Ummi ya dawo daga aiken da aka yi masa, ina ganin sa na sha jinin jikina. Don na san na yi shuka ne a idon makarwa tun da ya ganni da Auwal sai ya je ya isarwa Ummi.
"Ka ga ni dai babu ruwana. Ina zaman zamana ba za ka ja mini bala'i da masifa ba, ka ga tafiyata". Ina dasa aya a nan na juya na bar ƙofar gidan da sauri har ƙafafuna suna sarƙafewa, sai da na cire daga layin gabaɗaya kana na sauƙe wani wahalallan ajiyar zuciya.
Sai da na yi tafiya mai nisa amma ko ciniki naira biyar ban yi ba na nema waje na zauna ina huta gajiyar da na kwaso. Na tallafe kuncina ina bin bokitin kunun da kallo. A ƙalla na yi zaman mintuna ashirin kafin na yi cinikin naira ɗari biyu na kuma yin naira ɗari, har hantsi ya fito ba