DAFIN HARSHE BOOK ONE BY Maimunatu Iyam.txt

Author :  Maimuna Tijjani Iyam Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   19 / 32

54K to 57K   out of 95.1K words

a yi maka ba za ka tsaya".
Furucin Anty Sawwama kenan tana kafe Yaya Alhassan da ya sadda kansa ƙasa da ido, ni kam murmushi kawai na yi na fice. Har yanzu Amira wayar take yi na je fizge na kashe muka soma gyara kayan miyan da Yaya Alhassan ya kawo kan ka ce me ye tunin har mun ɗaura miyan akan wuta. Bai ɗau lokaci ba ya kammala muka sauƙe a lokacin Umar ya dawo daga makaranta.

"Ke yarinyar nan yaushe kika zo?".

Na wurga masa harara"ban sani ba ɗan rainin yawo kawai, kuma da kake ce mini yarinya ka san dai da cewa na girme ka ko".

"Never wannan kuma zancen ne. Me ye kika jagwalgwala mana haka?". Ya ƙare zancen yana sunkuyawa ya ɗauki doyar da na sauƙe, na kai masa bugu ya zame ya yi ciki da gudu. Na kwafa na ci gaba da zubawa Yaya Alhassan abincin na kai masa ciki. Ya buɗe ya soma ci.

"Zan dawo na same ki a nan ne?".

"A'a ni kam yanzu ma tafiya zan yi, don zan je islamiyya". Ya ɗago kansa ya yi mini kallo ɗaya kafin ya mayar da idanunsa kan abincin ya ci gaba da magana.
"To yaushe za ki dawo?".

"Sai an kwana biyu".

Ya yi shuru bai ce da ni komai ba sai can ya ce"ina son zuwa gidanku ko don na dinga ganinki ina kuma gaishe da Abba. Amma ba na jin daɗi abin da Umma take yi a duk sadda na je wannan dalilin ne ya sa na ɗan ja baya da zuwa".
Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya kana na furta"halin Umma ai sai haƙuri".
"Amma dai in Sha Allah zan yi ƙoƙarin na zo kafin lokacin sauƙanku sai mu tattaunawa akan abin da ya dace a yi muku".

"To". Na amsa da shi na fito na yi alwala muka shigo tare da Amira muka yi salla, kafin mu iddar tunin Yaya Alhassan ya kammala cin abincin har ya Yaya Alhassan ya koma wajen aiki, a gurguje muka ci abincin muka fara yin haramar tafiya Anty Sawwama ta ba mu dubu ɗaya ta ce mu hau napep ina ji Yaya Alhassan muka karɓa da godiya, tare muka fito da Umar ya rako har bakin hanya hana shi ma ya wuce wajen sana'arsa ta ɗinki.
Tun muna shawo kwana muke cin karo da taron jama'a har muka iso ƙofar gidan, muka iske mutane a cike maƙil ko hanyar wucewa babu.
[10/3, 1:12 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

______________________________________

Page 2️⃣6️⃣

Mutanen ta ko'ina babu masaka tsinke, ba mu sama damar shiga cikin gidan ba muka soma jiyo jiniyar motar ƴan sanda ta nufo wajen, hakan ya sa mutanen wajen suka soma darewa. A ƙofar gidan motar ta faka wasu ƴan sanda biyu suka fito diro daga bayan motan yayin da Baban Adnan ya fito daga gaban motar.
Kai tsaye cikin gidan suka nufo hakan ya ba mu damar bin bayan su muka shiga tare, filin tsakar gidan ma ya cika da mata.
"Ina wacce aka watsawa ruwan zafin?".

Tambayar da Baban Adnan ya yi kenan da ya sani kai dubana gefen da na ka an fi cika, idanuna suka sauƙa akan Asabe da take yashe a ƙasa tana fitar da numfashi a wahale, cikinta ya yi jajir tun daga wuyanta har zuwa gadon bayanta ruwan ya ƙona ta, rigar dake jikinta ya manne a fatarta tamkar tare suka zo. Babu shiri na runtse idanuna sakamakon rawar da jikina ya soma yi tsikar jikina yana tashi.
"Duk taron yawan nakun nan a rasa wanda zai iya kai ta asibiti tun lokacin da abin ya afku, sai dai ku cika gidan ku yi cirko-cirko akan ta".
Furucin Baban Adnan kenan cikin zallar takaicin da ya cika masa birnin zuciyarsa, kafin kowa ya yi magana Maman Adnan ta yi caraf ta amshe zancen tamkar wacce take jira ya ce kulle ta ce cas.

"To kai ina ruwanka? Waye ya aike ka balle ya ga daɗewanka?. Kai ka san abin da ita Asaben ta yi ta yi mata haka?".

Ba ta ƙarisa ba sakamakon marin da Baban Adnan ya sharara mata, daman an yi masa shaida a kaf cikin unguwan nan da kewayenta babu wanda ba ya shakkan dukan matarsa fiye da shi. Ko a gaban waye ba ya shakkan kai mara bugu ko da dalili ko akasin hakan.
"Ki bar ni na yi aikina yadda ya dace wannan ba abin da ya shafe ki ba ne". Furucinsa ya sanya kowa shiga tarairayinsa, tunin ya ba da umarnin a wuce da Asabe da take kwance magashiyan rai a hannu Allah zuwa asibiti.
Ita kuwa Maman Vector da na ji an ce ita ta yi aika-aikan aka maka mata ankwa suka tisa ƙeyarta. Mutuwar tsaye na yi don har aka fice da ita na gaza motsawa daga inda nake tsaye balle na yi wani yunƙurin barin wajen ban dawo daidai ba har sai da Amira ta dafo kafaɗuna.

"Ki je ki huta. Don matsalar gidan nan ba mai ƙarewa ba ne". Kaina kawai na iya ƙarfin halin jijjiga mata kafin na soma jan ƙafafuna da nake jin su tamkar ba sa cikin sassan jikina haka na isa ɗakinmu ba tare da na san inda nake cilla ƙafata ba, na iske Umma ba ta nan ko wanka ban yi ba na sauya kayan jikina zuwa na Islamiyya don lokaci ma ya riga da ya ƙure na fito na yi wa Amira sallama na tafi, sauri nake yi tamkar zan kife akan karan hancinsa ina isa cikin islamiyyan ana fara tarar masu zuwa latti ko aji ban wuce ba na nufi wajen Malam Suleiman a makare.
Tun kafin na iso na hango Aliyu Shehu ya fito daga cikin staff room ɗin malaman muna haɗa ido da shi ya ƙara murtuƙe fuskarsa daman can ba shi da annuri ko kaɗan kullum fuskarsa a haɗe take tamkar magribar ɗinya. An yi ittifa'i a duk cikin islamiyyan babu wanda yake ji da kansa da tunƙaho da fariya da ilminsa kamar sa.

"Dalla malama ki ɗago ƙafa, kin san ai ke kaɗai ake jira amma kike wani tafiya a hankali kamar ba ki san ana jiran ki ba".

Ya yi zancen cikin ɗaga murya ta yadda zan ji, na ƙara saurin da nake yi ina sowa wajen ya juya ya koma ciki na bi shi a baya har cikin staff room ɗin, da sallama na shiga wanda ta amsawar Malam Suleiman da na Malam Aminu sai kuma Al'amin Yakubu. Sai da na zauna kana na gaishe da su suka amsa.
"Amatullah ya ya aka yi kika makara haka?".
Tambayar da Malam Aminu ya jefo mini kenan da ya tursasa mini sadda kaina ƙasa saboda tuno munin abin da wakana, sai da na aro jarumta na yafawa kaina kafin na iya faɗin"Malam a yi haƙuri".

"Ba batun haƙuri ba ne Amatullah yanzu gabaɗaya kina ƙoƙarin komawa baya akan lamarin karatunki. Ga shi kuma aski ya zo gaban goshi". Jikina ya ƙara yin sanyi ƙalau na kasa cewa komai sai Al'amin ne ya kare ni da kalamansa.
"Malam in ba za ta faɗi gaskiyar abin da ya faru ba ni zan faɗa maka". Na yi hanzarin ɗago idona ina kallonsa sai dai ya ƙi yarda ya haɗa ido da ni, maimakon hakan ma sai ci gaba da ya yi da maganarsa.

"Malam na haɗu da ita a hanya kafin na iso, wata yarinya mai talla ce abin da take sayarwa ya zube shi ne ta tsaya ta taimaka maka. Kuma ta rakata har gida gudun kar a yi wa yarinyar faɗa".

Murmusawa kawai Malam Aminu ya yi tare da cewa"to Allah ya kyauta". Duk muka haɗe baki wajen amsawa da amin kafin Malam Suleiman ya soma jawabinsa.
"Mun tara ku anan ne saboda maganar zuwan baƙonku Sheikh Dawood bikin walimarku. Bayan shi akwai sarakuna da masu muƙamai a jihar nan da za su halacci wajen don aka mu na ku nutsu ku yi karatu mai kyau, domin tabbatar da ingancin karatun da kuka samu daga islamiyyar nan. Sannan kamar yadda muka sanar da ku a tsakaninku ne za a cire gwarzon shekara, ɗalibi mafi ƙwazo da kuma wanda ya zo na ɗaya".
Tun kafin ya gama maganar Aliyu Shehu ya soma murmushi tare da cewa"Malam ai ba za mu ba ku kunya ba, kuma in sha Allah wannan shekarar ma ni zsn cinye dukkan waɗannan kambun".

Kalaman Aliyu suka sani ɗago idona na saci kallonsa, mutum ne shi ma matuƙar son ganin ya kewa kowa akan komai. Shekara uku kenan a jere shi yake lashe kambun ɗalibi mafi ƙwazo a islamiyyar gabaɗaya, a bikin yaye wasu ɗaliɓan ma ya kan yi majinta balle kuma nasa, wannan dalilin ya sanya ni cire duk wani buri a raina.

"Amatullah kasancewar ki mace ɗaya a tsakaninsu dole idanu za su dawo kanki don haka ina so ki yi karatu mai kyau kuma cikin nutsuwa".
"In Sha Allah Malam".

Dariya Aliyu ya fashe da shi da hakan ya ja hankalinmu zuwa gare shi, Malam Suleiman ya tsawatar masa.
"Dariyar me ye kake yi?".

Ya ladabtar da murya"tuba nake yi Malam, wani abun na tuna".

"Za ku iya tafiya mun sallame ku".

Godiya muka gabatar musu muka tashi za mu fita Malam Aminu ya ƙira suna na juyo ina sauraron abin da yake faɗa.
"Ki shiga aji huɗu ki karɓa haddansu. Yau Malama Khadija za ta sama zuwa ba".
Cikin girmamawa na ce"to Malam". Na juya na fita har na yi ɗan nisa na jiyo muryar Aliyu na tsaya har ya iso gabana ya tsaya har da naɗe dukkan hannayensa a ƙirjinsa.

Na bi sa da kallo tun daga ƙasa har sama, ƙal-ƙal uniform ɗinsa yake ya sha goga ga ƙamshin wani sanyayyan turare da yake tashi daga jikinsa, hularsa taɓa ni ka sha hadisi fara sol sai sheƙi take yi.

"Tunanin me ye kike yi?".

Na yi masa wani kallo guda na ɗauke kaina tare da cewa"tunanin me ye kuwa zan yi?". Ya murmusa kafin ya ce"tunanin yadda za mu fafata da ke mana, tun wuri ki sauƙaƙawa kanki yawan damuwa don ba za ki taɓa cin nasara akan Aliyu Haidar ba, tun shigowata islamiyyar ni nake yi na ɗaya kuma na lashe kambun ɗalibi mafi ƙwazo a duk shekara, na yi bajinta a shekarar wasu ma balle shekarar walimarmu. Har na bar Islamiyyar nan babu abin da zai sauya wannan tarihin don haka ma kar ki sa a ranki".

Taƙaitaccen murmushi na saka kafin na sama zarafin cewa"Aliyu kenan!. Ai kai ya fi dacewa na ba wa shawarar ka cire tunani daga cikin ranka don da dukkan alama kai hakan ya dama. Ina yi maka fatan nasara a ko yaushe ni ka ga tafiyata". Ina ƙare faɗin haka na bar wajen na nufi aji huɗu domin karɓan haddarsu kamar yadda Malam Aminu ya umarce ni, har na yi na gama raina a ƙutume na yi musu ƙari na fito lokacin har an tashi sallan asr don haka kai tsaye na wuce wajen alwala na zauna na zabga tagumi abin duniya duk ya fi ya ishe ni.
"Ke lafiyarki kuwa? Yau ki haɗuwa ba mu yi ba".

Na tsinkayo muryar Rauda a kusa da ni na zame hannayena daga tagumi da na rafza ina saki tagwayen ajiyar zuciya wani na bin wani.
"Wallahi na fara gajiya da abin da Aliyu yake yi mini a ciki islamiyyar nan".
Ta kafe ni da ido alamar son ƙarin bayani"wani Aliyu kenan?".

"Aliyu Shehu mana".

Ta taɓe baki kafin ta soma cewa"kin san Allah Amatullah wannan Aliyun sonki yake yi, matuƙar so ma kuwa. Ke in taƙaice miki bayani mazan ajinsu sun taɓa kama sa yana rubuta sunanki jikin ƙur'aninsa". Wani kallo na watsa mata da ya sanya ta haɗiye sauran zancen ba tare da furta su ba.
"Wani irin banzar magana ce haka Rauda? Sanin kanki ne babu wanda ba ya ƙaunar ci gaba na a cikin islamiyyar nan kamar Aliyu. Ko wani abun bajinta na yi sai ya ƙalubalence ni akan hakan ki na nufin wanda ma duk cikin so ne kamar yadda kika yi ikirari?".
"Ko waɗannan ba su kasance alamomin so ba to tabbas akwai soyayyarki mai ƙarfi a cikin zuciyar Aliyu. Shin ke ba ki lura da wani abu, duk yadda ƴan matan islamiyyar nan suke yi masa shishshigi baya kula su amma ke ko kina so ko ba kya so sai ya nema hanyar da zai yi magana da ke ko da kuwa baƙar magana zai faɗa miki".

Na miƙe kafin na furta"Rauda mu bar wannan maganar don hankali ba zai taɓa ɗaukarsa ba". Ban jira abin da za ta kuma cewa ba na tafi na soma yin alwala na zo na yi salla har iddar tana zaune a cewarta tana fashin salla a lokacin tare muka koma aji muka soma muraja'a cike da shauƙi da soyayyar abin da muke karantawa. Har sai da aka tashi ba mu sani ba sai da muka zo daidai inda muke son tsayawa kana muka yi addu'a kowa ya fito domin tafiya gida.

Tsaye a ƙofar fita na hango Al'amin yana tsaye muka sakarwa juna murmushi yayin da muka haɗa ido, na riƙo hannun Ammi ina cewa"raka ni na je na yi wa Bawan Allahn can godiya".
"In kuka daɗe ni kam tafiyata zan yi don yunwa nake ji". Rauda ta yi zancen tana neman waje ta zauna tana jiran mu, ba mu amsa mata ba illa darawa da muka yi dukkanmu. Da sallama muka isa wajen Al'amin ya amsa mana yana ƙara yalwata annurin fuskarsa.

"Na yi tunanin ai ɓacewa kuka yi a cikin makarantar".
Na murmusa tare da cewa"mun tsaya yi karatu ne".
"Na dai lura ajin matan nan kun dade sosai".

Na ƙara murmusawa a karo na biyu kana na ce"daman na zo na yi maka godiya ne. Tabbas ka cece ni daga tuhumar Malam Aminu".

"Ya zama dole ne hakan Amatullah babu wanda bai san tambayoyin titsiye irin na Malam Aminu ba".

"To ni dai ina godiya matuƙa".

Har yanzu fuskarsa ɗauke take da murmushi ya ce"to yanzu dai mu je na raka ku ko?".
Ammi ta amshe zancen"mu muka ce maka muna buƙata".
Ya harare ta"yau dai ba zan kula ki don masifarki sai dai ki ci kanki". Ban tsoma musu baki ba illa murmushin da na yi muka soma tafiya muka isa wajen Rauda sai dariya muke yi mata don duk ta sauya Ammi sai tsiya take ya mata wai kamar ba ta yin azumi yunwar lokaci guda ta jigata ta har haka. Har muka rabu da Ammi da Rauda, Al'amin bai daina ja na da hira ba har farkon layinmu ya raka ni, muka rabu cikin girmamawa da mutunta juna.

Ina doso ƙofar gidanmu na ji gabaɗaya raina yana ɓaci zuciyata tana tafasa sosai. Haka kawai na nema dukkan nutsuwata na rasa ƙirjina ya tsananta bugu. Sai da na tsaya a zaure na ja dogon numfashi na fesar kafin na ƙarisa cikin gidan, har yanzun Umma ba ta dawo ba don haka wanka na yi na sauya kayana na tattare wasu abubuwan kana na ɗaura mama girki tuwo na yi da miyar bushashshen kuɓuewa na juye a kula, na je wajen Amira don ba na son zama shirun.

Babban dalilin ma shi ne ina son jin haƙiƙanin abin da ya faru tsakanin Asabe da Malam Vector da ya kai su ga raunana juna, kiciɓus na yi da Ummanta za ta fito na matsa na mata hanya ina yi mata addu'ar a dawo lafiya bayan ta shaida mini za ta je wajen Sa'ade uwar adashe ta kai zubinta.
A falo na tarar da Amira tana kallo a wayanta na zauna kusa da ita tare da fizge wayar, ta bi ni da kallo"har kin dawo?".

"Har ne ma? Watau don ba ke kike zuwa ba dole ki faɗi haka. Amira na yi na yi dake mu shiga islamiyyar nan amma kin ƙi, ina guje miki ranar da wannan damar za ta kuɓuce miki".

Ta gyara zamanta tare da cewa"tun da dai na sama na salla ya ishe ni". Kaina kawai na jijjina na kawar da maganar ta hanyar cewa"wai ni kuwa me ye faru tsakanin Asabe da Maman Vector, Umma ba ta nan balle na tambaye ta".

"Kin san Baban Vector ya dawo daga Benue shi ne Maman Vector ta kama shi da Asabe a cikin ɗakinta suna hira, kin sa ta da shegen kishin tsiya tana ganin haka ba ta wata-wata ba ta ɗauko tafasasshen ruwan zafi ta shiga ta juyewa Asabe a jikinta".

Na dafe ƙirji"na shiga uku. Amma kuwa Maman Vector ba ta kyauta ba ai kamata ya yi ta fara jin dalilin shigarsa ɗakin Asabe".

"Ko ni ce fa zan yi fiye da abin da Maman Vector ta yi, wani dalilin ne zai sanya su keɓe da juna bayan su ɗin ba muharraman juna ba ne".

"Amira kenan. To ai in haka ne ma laifin Baban Vector ne tun da shi ya je har cikin ɗakinta". Ta taɓe baki"koma dai mene ne ni kam Maman Vector ta yi min daidai". Ta gyara zamana ina fuskantan da kyau kana na soma cewa"ni zuwa na yi ma na tambaye ki, ko akwai in da za ki je ne yanzu ko zuwa bayan sallan isha'i?".

Ta yi mini wani kallo kana ta ce"yau ko toyar awara ba zan fita ba amma lafiya kike tambaya?". Na yi ɗan jim kafin na ce"wallahi ba za ki gane ba ne ba na son zaman cikin gidan ne, ko Bashir za ki ƙira mini a waya to mu gaisa?". Tun kafin na rufe bakina na ga ta tsare ni da wani irin kallon mamaki da al'ajabi.
[10/4, 12:16 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️Maimuna Tijjani Iyam

__________________________________

Page 2️⃣7️⃣

Sake da baki da hanci take kallona tamkar wacce ta ga wani sabon halitta, mamakinta ya kasa ɓoyiwa har sai ta furzo shi waje.
"Bashir kuma? Yau da bakinki kike cewa na ƙira miki Bashir?". Na sauƙe sakakken ajiyar zuciya mai nauyin gaske kafin na sama zarafin faɗin"Amira ke fa ko yaushe kike nusar da ni cewar wanda ya nuna yana sonka a rayuwar nan

19 / 32