DAFIN HARSHE BOOK ONE BY Maimunatu Iyam.txt

Author :  Maimuna Tijjani Iyam Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   27 / 32

78K to 81K   out of 95.1K words

ce"zan fita kamar yadda kika buƙata, amma kafin na tafi zan ba ki wani shawarar da nake da yaƙinin cewar za ta amfane ki. Na ji an ce kina neman Mus'bahu to ba za ki taɓa samun sa don na tabbatar tun ranar da ya aikata wannan abun ya haɗa jakarsa ya bar garin nan wataƙila yanzu ba ya ƙasan nan". Tana gama faɗin haka ta fice daga cikin ɗakin ta bar ni da sakin wani gigitaccen kuka mai raunana zuciyar mai saurare. Ban gushe ina yi ba Amira ta shigo ta dinga rarrashi na, na amshi wayarta na soma karatun aƙur'ani da shi sai da dare ta raba kana na ajiye wayar na yi dogon addu'a na shafa a nan wajen bacci ya yi nasarar ɗauka ta sai dai ban yi nisa ba na farka a zabure.
"Lafiya kuwa?".
Amira ta jefa mini tambayar cikin damuwar da ya bayyana har a cikin furucinta, maimakon na ba ta amsa sai kawai na fashe da kuka.

"Amira an ya ba haukacewa zan yi ba kuwa ni kam?".

Cikin sanyin murya ta soma cewa"babu abin da zai faru da ke in Sha Allah". Ta jawo ledar kayan da Mansur ya kawo ta fito da kayan ciki kayan marmari ne sai kuma wasu manyan cakuleti masu sanyi sa'annan lemonka gora har kala biyar. Ta matsa mini akan sai na ci wani abu ba don raina ya so ba na sha lemon da wasu daga cikin kayan marmarin. Washe garin ranar a islamiyya Malam Suleiman ya aiko aka ƙira ni ya zaunar da ni ya dinga yi mini nasiha tare da ba ni wasu shawarwari, ban iya daurewa ba har sai da na zubar da ƙwalla. Ko da a fito daga wajen Malam Suleiman lokacin har an tashi ban ga su Rauda da Ammi don daman sun ce daga islamiyyar wajen ɗinki suka nufa za su je su karɓo ɗinkin ankon waliman.
A hankali nake tafiyar tamkar wacce take jin tsoron taka ƙasa na fito daga cikin islamiyyar, zan tsallaka titi na ji an ƙira sunana na waiga da sauri.

"Yaya Alhassan". Na furta kalmar cikin mamaki don ban yi tsammanin ganin sa a wannan lokacin ba.
[10/24, 10:06 AM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_______________________________________

Page 3️⃣5️⃣

Da saurina na iso inda yake tsaye a jikin mashinsa ɗin tare da wani abokinsa da tun ina tahowa idanunsa yake kaina har na iso wajen bakina ɗauke da sallama. Suka haɗe baki wajen amsawa kana na gaishe su suka amsa.
"Kun tashi kenan?". Na gyaɗa masa kaina ina zarcewa da faɗin"daman ma ina so na je gida wajenka na ba ka haƙuri akan abin da ya faru game da waɗannan kaya...". Ya yi saurin ɗaga mini hannu alamar ba ya son sauraren ragowar zancen.
"Abin da ya faru ai ya riga da ya wuce sai dai a kiyaye faruwarsa a gaba, na ji wai ba ki da lafiya tun lokacin nake so na zo na duba ki amma ina gudun abin da zai je ya dawo shi yasa ma ban zo ba, shi ne na zo islamiyya. Me yake damunki ne haka Amatullah? Duk kin rame kin faɗa tamkar ba ke ba, me ya yi zafi haka?".

Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya kafin na sama zarafin faɗin"zazzaɓi ne kawai sai kuma yanayin karatu".
"Amatullah kar ki faɗi saɓanin abin da yanayin fuskarki ya riga ya nuna. Tabbas akwai wani abun da yake faruwa ko in ce akwai abin da yake damunki". Na yi shuru ba tare da na ce komai tare rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa.
"Alhassan don Allah kar ka yi sanadin zubar hawaye daga fuskar wannan kyakykyawar halittan". Furucin abokinsa kenan ya ƙara sausauta amon muryarsa ya ci gaba da cewa"ƙanwata me yake damun ki?". Na ɗaga idona na yi masa kallo guda na janye a hankali na ce"babu komai".
Yaya Alhassan ya amshe zancen"shikenan ba zan matsa miki amma ko ma mene ne ina miki fatan samun mafita cikin gaggawa, ranar yaushe ne walimar takun".

Na yi murmushin ƙarfin hali"gobe ne da ƙarfe tara na safe". Ya jinjina kansa"me kike so na taho miki da shi, tun da Umma ta hana ni yin wancan aikin alkhairin da na yi niyya".

"Zuwanka ma kaɗai ya wadatar da ni ba sai ka zo mini da komai ba".

Ya tsuke fuskarsa"idan ba za ki faɗa ma ba ai kuwa duk abin da na yi niyya shi zan saya na kawo miki, in ya so in kin ga dama inna ba ki ki watsar ko ki kyautar wannan kuma ra'ayinki ne". Na saki taƙaitaccen murmushi"to shikenan na bar maka zaɓi duk abin ka taho mini da shi ina maraba da shi".
"Ni ma da za a yi na'am da nawa kyautar da na yi " Furucin abokinsa kenan da ya sani ɗaga idona na yi masa kallo guda na mayar da idanuna.
Na kawar da maganar ta hanya cewa"yaya Alhassan don Allah ka sanar da Anty Zulaihatu ma don ban sanar da ita ba".

Ya riƙe haɓa"ai duk dangi babu inda ban shelanta cewar ƙawata ɗaya tilo za ta yi sauƙa ba. Don haka ki kwantar da hankalinki gayya guda za ki gan ma ranar, yanzu dai ga wannan ki wuce ki hau abin hawa ki wuce gidan na ga magriba tana kawo kai". Ya ƙare zancen yana miƙo mini naira ɗari biyar ɗin da ya zaro daga cikin aljihunsa, na amsa tare da yi masa godiya sai da na tsallaka titi na shiga napep kana na ga sun tafi.
Ina sauƙa a layinmu na hango Amira tsaye da Bashir a ƙofar gida duk suka zubo mini na jiyamunsu, na sa kai zan shige cikin gida tamkar ban gan su ba Amira ta dakatar da ni.

"Amatullah ba ki ga kin yi baƙo ba ne?".

"Amira don Allah na gaji don Allah ki bar ni".

Ina ƙare zancen na shige ciki ta rufa mini baya tare da shan gabana.
"Me yasa kike haka ne Amatullah? Ai ko ba za ki ce da shi wani abu ba ya dace ki saurare shi ki ji da abin da yake tafe. Wanda ya damu da ke da halin da kake ciki da ai a tunanin ya wuce wulaƙanci a gare ka".

"Wai da wani yare kike so na yi miki bayani ki fahimta ne? Na gaya miki ba na son ganin wani alaƙa ta ƙara haɗa da wani ɗa na miji ko da kuwa ta gaisawa ce matuƙar shi ɗin ba wai ya kasance muharramina ba ne". Na yi zancen ina ƙoƙarin wuce ta riƙo hannuna gam ta riƙe.
"Kar ki manta fa ke kika ba shi dama. Kar ki zama mai ƙarya alƙawari mana". Na ɓanɓare hannunta daga jikina"ki je ki ba shi haƙuri don ba zan iya sauraren sa, ina ji a jikina ma kamar wannan ce haɗuwar mu ta ƙarshe da shi". Ban jira abin da za ta ce ba na ya wucewa ta ciki kai tsaye na nufi ɗakinmu bakina ɗauke da siririyar sallamar.

Na tsuguna har ƙasa na gaishe da Umma da na iske zaune a falon tana irga wasu kuɗaɗen masu yawa, ba ta amsa mini na har na gaji da tsayiwar na tashi zan shiga ɗaki kana ta yi magana a gajarce.

"In kin shiga ɗaki akwai saƙon ki akan katifa".

"To".

Na amsa dashi duk da kuwa ina buƙatan ƙarin bayani sai dai sam ban ga fuskar yin hakan ba. Na wuce cikin ɗakin ina shiga fige hijabina na ajiye na suri ledar da na gani akan gado na buɗe. Hijabi ne a ciki sai kuma ɗinkin doguwar rigan da aka watsawa stone ya fito ya yi ɗasar da shi, wani ihun daɗi da farin ciki na saka a lokaci guda ina faɗawa kan gadon ina tsalla tsabar murnar da na tsinci kaina a cikin sa. Na rumgume hijabin ina ta washe haƙwara tamkar wacce aka biyawa kujerar hajji, tabbas Umma ta faranta mini don na daɗe da cire tsammanin cewa zan yi ankon hijabi da atamfar walimarmu tun bayan abin da ya faru lokacin da Yaya Alhassan ya kawo mini waɗannan kayan.
Sai da na ƙarishe murnata na fito na yi wa Umma godiya bakina har kunne, rabon da na tsinci kaina cikin makamamcin irin wannan farin cikin tun kafin wannan iftila'in ya faru da ni. Sai dai kalaman da ta tare ni da su suka sanyaya mini jikina matuƙa.

"Ki dai maida hankali akan karatunki sosai da sosai. Daga ni har mahaifinki mun yarda da ke ne shi yasa muka tura ki wanga islamiyyar, Amatullah...". Kafin ta ce wani abu na tuntsire da kuka har jikina yana rawa. Ta yi sakake tana kallona kamar ba ta taɓa ganina ba.
"Kukan kuma na me ye ne? Ki tashi ki ba ni wani waje idan ba za ki rufe min baki ba". Haka na ci gaba da kukan har aka yi ƙiran sallan magriba tun Umma tana mamakina har ta tashi ta bar ni wajen. Na tashi da ƙyar na je na yi alwala na dawo na gabatar da salla tun kafin na yi iddar nake jin wani zazzaɓi mai zafi yana ƙoƙarin riƙe ni. Ina iddar da sallan na ɗauko alƙur'ani na soma karanta cike da shauƙin abin da nake karanta haɗe da sanin fassaransa, haka kawai ranar na tsinci kaina cikin wani irin matsanancin kwanciyar hankali da wanzuwar nutsuwar ruhi. Ji nake yi kamar gari ba zai waye ba balle har mu taro a filin walimar, ranar mitsitsi na kafe akan ba zan je gidan Hajiya Tasalla ba saboda shirye-shiryen walimar man gobe.

Abba ya kawo wake kwano biyu da wasu kayan miyan ya ce a yi alala na sauƙan, sannan ya ba ni naira dubu biyu ya ce na yi zoɓo. Duk yadda na so hana Amira sanar da Mansur labarin walimar sai da ta zagaya ta sanar da shi. A daren ranar ya zo shi ya yi mana siyayya sosai sannan ya ce zai halacci walimar da iznin Allah. Haka muka surfa wanken muka shanya sa muka je muka sayo kayan haɗin zoɓon, ba mu kwanta ba sai ƙarfe sha ɗaya saura na yi wanka na ɗauro alwala na zo na gabatar da salla raka'a biyu, na dinga zagba godiya ga mahaliccina a cikin sujjadata na ƙarshe. Ina ɗagowa na ɗauko alƙur'anina na buɗe na soma karanta ban dakata ba har ƙarfe biyun dare kana na rufe alƙur'anin. Duk yadda na so na runtsa bacci ya gagari idanuna haka na yi juyi har aka ƙira sallan assalatu, ladanin yana ƙwala ƙiran sallan na yi zumbur na tashi na zauna. Na fito na yi alwala ina ƙoƙarin koma ciki Amira ta fito ta dalle mini idanuna da hasken tocilan wayarta tana yi mini tsiya.

"Hafiza Amatullahi".

Na murmusa ina kare hannuna daga hasken tocilan haɗe da faɗin"in za ki yi sallan dai ki yi ki fito mu zo mu yi aiki".
"An gama ranki ya daɗe"
Ta amsa da shi ban tanka mata ba na koma ciki na yi sallan sai da na ƙara tilawar karatun da zan gabatar a wajen taron kana na fito, muka wanke waken tare da Amira muka kai niƙa muka dawo muka soma ƙulƙulawa kafin garin ya yi haske tunin ya dahu, muka ɗauko lemukan da Mansur ya kawo muka sassaka a leda muka alalen bibbiyu, sai da muka sama leda hamshin da uku.

Muka ƙula zoɓon ma, Amira ta ce tun da mun saka lemo a ledan na bar wannan na ba wa baƙina. Zoɓon kuma nawa da na ƙawayena na yarda da hakan, muna cikin aikin zoɓon Baban Adnan ya fito cikin shigar kayan aikinsa yana karkaɗe hularsa yayin da matarsa take biye da shi tamkar jela.
Amira ta taɓo ni"ga mutanan fa. Wallahi sai na ya masa magana ko don na ƙular da ita da safiyar nan".

"Ki rufawa kanki asiri dai". Ba ta ji abin da na ce da ita ba don sai da ta aikata abin da ta yi niyya. Ta lanƙwashe murya tana faɗin"Barka da fitowa Baban Adnan, har an fito ke nan? Allah dai ya saka muku da alkhairi don wannan aikin nakun ba kowa ba ne zai iya yin sa".
Take ya washe baki kamar gonar auguda" barka dai Amiratuwa ku na ta aiki ke nan da safen, biki kuke da shi ne ko suna?".

"Au! Wai daman ba ka sani ba? Amatullah ce za ta yi sauƙa yau".

"Sauƙa dai irin wacce na sani na izu sittin ko kuwa?". Ta gyaɗa kanta"ƙwarai kuwa shi fa". Zai yi magana Maman Adnan ta amshe zancen"ya dai kamata ka wuce ka tafi aikin gabanka". Ya juyo ya wurga mata wani mungun kallon da ya sanya ta saurin yi wa bakinta limzami.

Ya zaro wasu kuɗi daga cikin aljihunsa ya irgo guda biyar ya miƙawa Amira"ga wannan to ku ƙara ayi hidima, don ina da aiki da yawa ne ma da zan halatta amma yanzu ma dai bai ɓaci ba sai a yi hotuna a kawo mana mu kashe ƙwarƙwatan idonmu".
Kafin Amira ta kai ga amsar kuɗin Maman Adnan ta yi wuf ta kai hannu ta wafce.

"Wallahi ba za ku yi amfani da kuɗi nan ba, me ye haɗin kifi da kaska da har za ta ɗauki kuɗi ka ba su...". Tana rufe bakinta ya wanke ta da mari.
"Ba ta kuɗin nan tun kafin na tattaka ki a nan wajen". Babu girma babu azurki ta miƙawa Amira kuɗin ta koma ɗaki tana kuka da faɗin magauta sun shiga tsakanin ta da mijinta. Tun da aka fara dramar har aka ƙare ta ban tsoma bakina a ciki ba har sai da Baban Adnan ya fita kana na ce"yanzu me ye amfanin abin da kika yi kenan? Suna zaman zamansu ki haddasa musu rigima". Ta sheƙe da dariya kafin ta ce"ko banza dai mun sama dubu biyar a ɓagas kuma ta yi asarar hawayenta a banza". Na jinjina kaina cikin takaici ba tare da na ce da ita komai ba.

Haka Ustazu Abdulwahab ya fito ya same mu muka gaishe sa Amira ta shelanta masa cewar yau za mu yi walimar sauƙan alƙur'ani, ai kuwa ya nema waje ya zauna ya soma zubo mini ruwan addu'o'i da yi mini fatan alkhairi. Ya kuma nema da na yi masa kwantacen islamiyyar in Sha Allah amaryarsa za ta je na yi masa. Kafin ƙarfe takwas mun kama komai har na yi wanka na kimtsa cikin sabuwar atamfa da hijabina da ya amshe ni sosai. Abba ma sai da ya yaba da shigar da na yi na ɗauko niƙab na ɗaura a kai, tare muka tafi da Amira abincin kuma su Umma za su taho da shi idan za su zo.

Muna isa cikin islamiyyar Malam Suleiman ya aika aka ƙira mu ni da Al'amin da Aliyu da suka suka sha ankon faran shadda da rawani sai sheƙi da ƙamshi suke bazawa.
Sai da muka yi bitan karatun da za mu yi a wajen su, suka gyagygyara mana inda ya kamata kana muka fito lokacin waje har ya ɗau harama. Filin makarantar ya sha ado an kafa rumfuna da kujeru babban taro aka shiyar mana kasancewar an haɗe murnar waliman namun har da na bikin murnan cikar islamiyyar shekaru goma da kafuwa.
Muka zazzauna a inda aka tanada domin su masu ɗaukan hoto sai hasko muke yi, na ji kaina ya sara jikina ya ɗauki zafi tsabar zumuɗi ko abincin ban tsaya ci ba haka na taho.

Lokaci guda na ji wajen ya ɗauki kabbara ana faɗin isowan Sheikh Dawood Gaskiya dokin ƙarfe tare da shaƙiƙin ɗansa na miji ɗaya tilo. Duk yadda na so ganinsa cincirindon mutanen da suka kewaye sa sun hana ni ganinsa.
Sai da Malam Aminu ya yi magana cikin lasifika kana wajen ya nutsu, ya ƙira Rauda Salisu a matsayin ɗalibar da za ta buɗe taro da addu'a. Sai a lokacin idanuna suka sauƙa akan Sheikh Dawood take ƙirjina ya buga na ƙura masa idanuna, tabbas shi ne wanda na ga ni a tasha har ya yi mini maganar banza da ƙoƙarin taɓa jikina. Haka zalika yanzu ma shi ne zaune cikin kamala da nutsuwa, duk wanda zai gaishe shi sai ya durƙusa har ƙasa.

"Ga can Anty Sawwama da su Yaya Alhassan sun iso, Abba ma ya iso tun ɗazu. Umma ma su a hanya tare da Ummanta mun yi waya da ita ta ce sun kusa isowa". Na tsinkayo amon Amira ta yi zancen a daidai saitin kunnena, na yi kamar zan tashi na je wajen su Malam Suleiman ya yi mini ido akan na koma na zauna, babu yadda na iya haka na koma na zauna. Sai aka gabatar da jawabi sosai sarakuna da ƴan siyasa suka tashi suka yi nasu jawabin kana Malam Aminu ya fara ƙiran Aliyu a matsayin wanda zai fara gabatar da karatu.
Ya tashi ya yi karatun cikin tsantsan nutsuwa da fitar da haƙƙin ko wani harrafi, wajen ya ɗauki kabbara aka ayyana shi a matsayin wanda ya zo na uku kuma ya kasance ɗaliba mafi ƙwarzo na shekara. Aka ƙira wani basarake ya ba shi kyautarsa da makaranta ta tanada masa sannan shi ma ya ƙara masa da kyautar zunzurutun kuɗi har naira dubu ɗari tare da fatan alkhairi da addu'o'in da ya dinga yi masa.
Har na yi shiri don na sa a raina cewar ni za a ƙira a matsayin ta biyu, haka nan ma sauran ɗaliban don duk sai waigowa suke yi suna kallona. Kwatsam muka yi an ƙira sunan Al'amin jikin kowa ya yi sanyi, hatta shi Al'amin ɗin da kansa don bai fito ba har sai da aka ƙara maimata sunan a karo na biyu kana na tashi. Ya je ya yi karatun jikinsa gabaɗaya babu ƙwari, shi aka ayyana a matsayin wanda ya yi na biyu aka ƙira dan takaran kansilan yakinmu da ba shi kyautarsa da makaranta ta tanada domin shi aka yi musu hoto. Daga haka ya dawo ya zauna gabaɗaya yanayinsa ya sauya.

"Amatullah Munnir".

Malam Aminu ya ƙwala ƙiran sunana a cikin lasifika take zuffa ya keto mini ina ɗago kaina muka haɗa ido da Abbana. Fuskarsa a washe cikin tsantsan farin cikin da har sai da na hawaye a idanunsa. Na tashi na

27 / 32