LADY SAFNAH COMPLETE HAUSA NOVELS BY MAMAN AYSHA.txt

Author :  Maman Aysha Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   10 / 15

27K to 30K   out of 43.3K words

Irish. Maryam ta kalli mum tace mu zamu tafi mom Allah ya kara sauki, cikin sakin fuska tace amin Maryam, mungode sosai Allah yasaka da alkairi tace amin, mikewa safna tayi ta tafi rakasu bayan sunje bakin mota maryam tace safna kici gaba da hakuri da mom kinji insha Allah wata rana sai lbri, smiling safna tayi tace to maryam, kuma gashi nasa kinyi girki beci ba, dariya maryam tayi tace mom ta kafa ta tsare maci da daddare kawai. Sanan sukayi sallama suka tafi.

Lkcn da safna ta koma dakin mom bata nan, taje yiwa imran girki, sai shi da Fareeda ne kawai a dakin, waje safna ta samu ta zauna tana wasa da wayarta, shi kuma ogan sai waya yake da friends dinshi da suka kirashi, shiru dakin yayi kowa yana harkar gabanshi har mom ta gama girkin ta dawo, da sauri safna ta Mike zata karbar mata tray din, aikuwa ta daka mata tsawa ba shiri ta koma ta zauna, tana ajiyewa Farida ta taso cikin isa ta dauki plate din ta fara serving dinshi, bayan ta gama taje ta zauna a kusa dashi tana kokarin bashi a baki, cikin jin haushin abinda mum tayiwa safna yace bani naci da kaina ai ba ciwon hannu nake ba, wata Yar iskar dariya tayi tace oh sorry.

Zama yayi yaci abincin sosai dake mom din shi ta iya girki, kallon safna yayi yaga ta jingina da bango yasan yunwa takeji Sbd tun safe bataci abinci ba, shi besan ita dinma batyi break fast ba, kuma gashi yanzu after 6pm, Mum ce tacewa Fareeda kema ki zuba abincin mana, tace to, plate ta dauka ta zuba ta faraci a yangance, safna dake gefe itama banda hadiyar yawu ba abinda take, Sbd tun jiya rabonta da abinci kuma kamshin da abincin yake saitaji tana sha'awar taci, kmr daga sama saitaji mum tace safna, dagowa tayi tace naam, ki dauki jakarki ki tafi zamu cigaba da kula dashi nida matarsa, imran ne yayi karaf yace da wuri haka zakice ta tafi? Ko sallar magrif fa baayi ba, aida kin barta ta tafi bayan sallar isha'i, kuma naga ko abincin bataci ba itama fa tun break bata kara cin komai ba. To ubana ka gama? Banason ganin ta shiyasa nace ta tafi, abinci kuma ban girka da itaba, cikin bacin rai imran yace wallahi danasan bazaki bata ba da nima bazanci ba. Mikewa safna tayi tana kokarin tafya mum tace Dana be taba musu dani ba sai yanzu akanki to inaso ki Sani asirinku zanyi maganinku, hatsabibiyar yarinya, wa yasani ma ko ke mayya ce tunda ba wani cikekken asali ne daku ba.safna najin haka ta fice da sauri daga dakin tana kuka, nan take imran yabi bayan ta mum tana kiranshi Amma kmr ba dashi take ba. A packing space ya sameta tana kokarin bude kofar motarta, sauri yayi ya shiga gbnta cikin cool voice yace don Allah safna kiyi hakuri kinji? Murmushin da yafi kuka ciwo tayi tace karka damu hjya turai( matar baba Sharif) tasha fadamin kalaman da suka fi wadanan ma, kai kade ne zakayi min Abu na damu sbda ina sonka, cikin farin ciki yace kenan kin amince zakici gaba da zama dani a matsayin mijinki? Na Dade da amincewa dakai a matsayin mijina ya imran, sbda nima bazan iya rayuwa batare dakai ba, hugging dinta yayi sun Dade a haka sanan ya saketa dakyar ta tafi


Maman Aysha
[09:56, 9/4/2017] β€ͺ+234 803 922 1122‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady Safna






Maman Aysha
[10:01, 9/4/2017] β€ͺ+234 803 681 8427‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady SafnaπŸŽ‹πŸŽ‹

1⃣5⃣0βƒ£βž–1⃣5⃣5⃣

_By Maman Aysha_

*T W F*πŸ’¦πŸ’¦

A galabaice safna ta koma gda tana zuwa ta bude fridge tasha yoghurt, Saida ta tsirga mata sanan ta shiga kitchen ta dafa indomie, da kwai taci, sanan tayi wanka ta kira ummanta a waya ta fada mata imran bashi da lpya yana gdnsu, tace to idan munyi sallar isha'i zamuje mu dubashi.

Hakan kuwa akayi ana idar da sallar isha'i driver gdnsu Maryam ya kaisu ita da mmn Maryam, wani hadadden lace ne ajikin umman safna maroon kayan sunyi mata kyau sosai suna shiga falon gdn suka tarar da mom ita da mmn Fareeda suna hira, da fararta ta taso ta tare su, bayan sun gaisa ta rakasu part din imran wit respect imran ya gaishesu da zasu tafi Saida ya rakasu har bakin mota, Saida suka tafi ya dawo. Tun lkcn da suka shiga gdn mmn Fareeda take bin umma da kallo, suna fita tace wacece dayar naga imran yanata wani shisshige mata yana mata hira? Tabe baki mum tayi tace mmn safna ce, cikin yanayin bakin ciki tace eh lalle barewa ba tayi gudu danta yayi rarrafe ba, haka take da kyau dama? Kana ganinta kaga bafilatana, ita kuma 'yar kamar half cast, bada ita take kama ba, Kuma a hakan bata da aure ko? Mom tace eh ba aure, to kuwa wallahi karuwancinta take, ai ba yanda zaayi ace zabgegiyar mace irin wanan ace bata da masu sonta ba, mom tace gasky kam.

Washe gari sassafe Fareeda take kwarara amai kmr 'yan hanjinta zai fita, aka dauketa zuwa Asibiti bayan likita ya gama bincike yace tana dauke da ciki murna wajen imran dasu mom baa mgna su Fareeda sai wani kara narkewa take taga yana tarairaiyarta. Wuni sukayi ana kara mata ruwa, sai dare aka salleme su suka koma gda, da daddare imran yanaso ya kira safna ba dama sbda Fareeda ta dora kanta akan chinyarshi, Saida tayi bacci sanan ya dauketa yakaita daki, sanan ya dawo falo ya kira ta. Harta fara bacci taji call dinshi ya shigo, a magagin bacci ta amsa bayan sun gaisa yace INA cikin farin ciki yau my angle, meya faru? Fareeda tana da ciki, cikin tsananin murna safna tace waw masha Allah, Allah ya rabasu lpya, yace amin, wallahi a Asibiti muka wuni naga missed call dinki muna tare dasu mom shiyasa ban kiraki ba, ok ba damuwa ya jikin ka? Da sauki, ya kamata gobe kizo ki duba Fareeda sbda tana shan wahala sosai wallahi yau taban tausayi, to shekenan zanzo, sanan suka yi sallama


Washe gari imran ya kira Safna a waya yace tayi mishi abin dadi idan zatazo duba Fareeda, tace to. Shawarma, da dambun nama da kuma kunun aya me kwakwa da madara tayi mishi, saida ta gama hada komai ta shiga wanka ta shirya cikin wani tsadadden boyel brown color, zama tayi tai simple make up, tayi wanka da turare sanan ta dauki basket din abincin da key din motarta ta fice.

Tana shiga gdn taji gbnta yana faduwa amma saitayi addua ta shiga. Zaune yake akan Capet ita kuma Fareeda ta Dora kanta akan cinyar sa, mum da mmn Fareeda kuma suna kan kujera a zaune suna kallon wani Nollywood film safna tayi sallama ta shiga masha Allah kawai imran yace a zuciyarsa, suna hada ido ya sakar mata wani lallausan murmushi durkusawa tayi ta gsishe da mom, ta amsa a dakire, sanan ta gaisar da mmn Fareeda itama ta amsa ba yabo ba fallasa, sanan ta juya wajen Fareeda da imran ta gaishesu a tare, tacewa Fareeda ya jiki Allah ya sawwake tace amin. Waje ta samu ta zauna a gefe basket din abincin yana gbnta Amma ta kasa mika mishi, mum ce tace meye acikin basket din nan? Cikin fargaba tace uhm dambun nama ne da.... Wato sbda kwana biyu baya nan baki samu damar barbada mishi mgnin yaci ba shine kika biyo shi dashi har gda ko? Mmn Fareeda ce tace uhmm lalle my dota kina fama aini tunda naga makirar uwarta jiya jikina yayi sanyi idan banda makirci me zaki kawo mishi Wanda babu anan? Imran ne ya katse su da cewa ni nace ta kawo min, eh dole kace haka mana tunda ta tsafe ka, idan banda kaddara ina ita ina kai, yarinyar da ko cikakken asali bata dashi, shiyasa akeso a ringa bincike sosai idan zaayi aure, nifa ban yadda ma tanada uba ba inajin a yawon iskanci uwar ta haifeta suke fakewa da ubanta ya bata.....wata irin tsawa imran yayi yace stop it mum! Wai me safna tayi miki da take fuskantar irin wanan tsangwamar daga gareki? Haba mum kefa ba jahila bace, kinada ilimi, ai Allah ma yace ka fadi alkairi ko kayi shiru. Cikin bacin rai mum tace akan wanan marar asalin kake min rashin kunya? To idan dai nice uwarka inaso yanzu ka saketa.....muryar Abba ce ta katse su da cewa don kina mahaifaiyar sa baki da ikon sashi ya saketa tunda yana sonta, Kuma idan kika kara cewa ya saketa to wallahi kema a bakin auranki. Ita kuwa safna mikewa tayi ta fice daga gdn cikin mummunan tashin hnkli da tunani kala2 a zuciyarta, motarta ta shiga ta nufi gdn mum dinta



Safna fans kuma kun yadda Safna bata da uba?


Maman Aysha
[10:01, 9/4/2017] β€ͺ+234 803 681 8427‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady SafnaπŸŽ‹πŸŽ‹

1⃣5⃣5βƒ£βž–1⃣6⃣0⃣

_By Maman Aysha_

*Talented writers forum*

Tana shiga ta sami umma zaune tana gyaran farce bayan sun gaisa tace ya naga kmr kinyi kuka? Murmushin yake tayi tace ba kuka nayi ba, gyara zama tayi tace umma inaso muyi wata mgna ne dake, OK go ahead inajinki, wai ni a iya zamanku da abbana ko da wasa be taba fada miki garinsu ba? Da ya fadamin nakai har yanzu ban nemeshi ba safna? Kuma be taba baki lbrn koda yan uwansa ba? Wallahi be taba ba, shifa alhaji Sharif ne kadai guardian dinshi, kuma shi dinma besan komai nashi ba. Hawaye ne suka fara ambaliya a kumatun Safna, shekenan mu haka rayuwar mu zata kare kenan? Ni yanzu banida kowa a duniya sai ke, idan kika rigani mutuwa shikenan ba wani Wanda zan nuna nace jinina ne, banga lefin mom din imran ba da take kirana wulakantacciya marar asali, tabbas duk abinda ta fada hakane, sbda ban taba ganin mutun kamanni ba, babana ba asan inda yake ba, ke kuma da akasan family naki basu da wani amfani agaremu domin kuwa ban isa na tari mahaifinki nace ni jikarsa ce ba, yan uwanki duk basayi dake kuma yanzu duk Wanda yace USA a wudil ya tambayi lbrn ki ba zaa bashi lbri mekyau ba game dake, wanan waccen irin kaddara ce? Ni harna fara zargin kodai da gaske banida uba boyemin kawai kuke keda baba Shari.....dauketa tayi da mari har guda biyu cikin muryar kuka umma tace yaushe kwakwalwarki ta tabu da har kika fara zargina? Ke bakisan cewa na fiki damuwa ba? Meye ribata idan na fada miki lbrn karya? Kinsan irin kunci da radadin da nakeji na rashin mahaifinki da nayi? Duk duniya ba abinda nakeso kmr ke da mahaifinki, meyasa ba zaki taimaka wajen kwantar min da hnkli ba sedai ki dagamin? Rungume safna tayi tace wallahi safna da gaske nake ta hanyar halak na sameki, tunda nake ban taba zubar da mutunci na ba kuma insha Allah bazan taba yi ba, munyi soyayya me tsafta da babanki shiyasa na kasa kara aure, kuma kema kin fara rayuwa dashi don dai bazaki iya tunawa bane, mahaifinki yana tsananin sonmu nida ke bansan meyasa ya tafi ya barmu ba, Alhaji Sharif yana matukar so ya aureni amma sbda sonda nakewa mahaifinki naki yadda, kullum jikina yana bani be mutu ba yana nan da ransa, inaji ajikina wataran zai dawo garemu cikin loosing hope safna tace Allah yasa.

A bangaran imran kuwa safna na fita yaji gdn yayi zafi, wanka yayi ya fita wajen friends dinshi be dawo gdn ba sai dare direct part dinshi ya wuce ya dauki laptop dinshi ya nufi fakon mum, zaune ya samesu ita da Fareeda suna hira, ba tare da ya kalli Fareeda ba yace mom Saida safe, da mamaki tace INA zaka? Yau a gdn safna nake ai, na raba musu kwana ko ina zan ringa yin kwana biyu, kuka Fareeda ta saka yanzu don Allah kana ganin banida lpya amma zaka tsallake ka barni? Idan na zauna mezan miki? Ai INA ganin you can take care of your self, mom zatayi mgna yace don Allah mom karki saka kanki aciki wanan mgnar, nayiwa Abba alkawari zanyi adalci a tsakaninsu so ki tayani da addua kawai, sanan ya juya yace Saida safe. Kwantawa Fareeda tayi tana wani irin kuka dakyar mom ta rarrashe ta tace zata San matakin da zata dauka akan safna.

Sai dare Safna ta koma gda tana zuwa ta shiga wanka tayi brush sanan ta fesa turare ji tayi gbdya duniyar ta isheta, wani irin tausayin su takeji ita da umma sbda indai ba babanta aka gani ba umman ta bata isa taje gdnsu da ita ba, sbda cewa zasuyi cikin da akayi mata sharri ne ta haifi safna, kenan haka zamuci gaba da rayuwa dagani sai ita? Wani irin kuka ta fara yi me taba zuciya, kifa kanta tayi akan gado taci gaba da kukanta...batayi auni ba taji an tallafo ta, wani daddadan kamshi ne ya bugi hancin ta, cikin bedroom voice yace ya salm, safna har yanzu baki dena kuka ba? Don Allah inaso ki cire komai a ranki, kiyi hakuri da abinda mum tayi miki insha Allah wataran zata gane gskya, Inaso kisani INA tsananin sonki irin son da koda baki da uba zan zauna dake, ballatana nasan ke Yar halak ce, nayi miki alkawari zan soki har iya karshen rayuwa kuma zan zauna dake a bisa amana, goge mata hawaye yayi yace don Allah karki kara kuka safna, zatayi mgna yasa bakinsa ya fara tsotsar lips dinta kamar ya samu sweet, hugging dinta yayi ya fara aikamata sakkoni, romancing din junansu suke har sun manta a duniyar da suke, kawai sai phone dinshi ta fara ruri....



Maman Aysha
[10:02, 9/4/2017] β€ͺ+234 803 922 1122‬: πŸ‚πŸ‚



Maman Aysha
[10:03, 9/4/2017] β€ͺ+234 803 681 8427‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady SafnaπŸŽ‹πŸŽ‹

1⃣6⃣0βƒ£βž–1⃣6⃣5⃣


Dakyar ya iya dauko wayar yana dubawa yaga mum ce, a hnkli yace me mum zata fadamin da daddaren nan kuma? Yana receiving tace kazo ka kai Fareeda Asibiti yanzu, da sauri yace meya sameta? Cikinta ne yake ciwo, OK to gani nan zuwa. Duban safna yayi yace my angle don Allah kiyi hakuri zanje nakai Fareeda Asibiti, smiling din da yake kara fitar da kyaunta tayi tace ba damuwa, Allah ya sawwake yace amin. Key din motar sa ya dauka ya fice, a 360 ya karasa gdn shi dauketa yasata a mota, suka nufi hospital, bayan likita ya gama dubata yace shi ba ga komai ba, pcm kawai ya rubuta mata suka dawo gda. Kuka Fareeda take wai ita ko ina ma ajikinta ciwo yake, ita kwatakwata batajin dadin rayuwar ita komai ma ya fita akanta, ji yayi gbdya ta bashi tausayi sbda yana yawan ana cewa masu ciki suna shan wahala, rarrashin ta ya ringayi harya batayi bacci ba sai wajen 12:30am, kawai saiya kwana a gdn saidai zuciyarsa bataso hakan ba domin kuwa ya kasa manta yanayin da suka tsinci Kansu da safna dazu, daya rufe ido safna yake gani manne ajikinshi, dakyar ya samu malalacin bacci ya daukeshi

Washe gari Fareeda ta tashi garau da ita kmr ba itace tayi jinya ba, bayan sun gama break suna zaune suna hira kiran Safna ya shigo phone dinshi, tashi yayi ya fita daga wajesu cikin husky voice yace my angle gud morning, morning how are you? Yace fyn, ya me jiki? Da sauki tace Allah ya kara sauki tace ameen, cikin wani yanayi yace baki tambyeni da yaya na samu nayi bacci ba? Kmr yaya kenan? Kmr yadda nayi missing dinki mana, wallahi jiya dakyar na samu nayi bacci ba karamin missing dinki nayi ba, uhm kawai safna tace, dariya yayi yace baki yarda ba ko? Zanzo anjima, tace OK saikazo.

Suna gama waya ya nufi side din Abba ya sameshi yana shiri zai tafi abuja, yana ganin shi yace my son ya akayi ne? Akwai abinda kake bukata ne? Eh Abba, to inajinka menene? Dama Abba nayi order motoci ne guda hamsin, shine dazu aka kirani a waya wai dole da Kaina zanje nayi clearance smiling Abba yayi yace a wanne kasa ne? America, OK to kana bukatar kudi ne? Ah ah akwai kudi a hannuna kawai na fada maka ne, Sbd yau nakeson tfy, is OK my son Allah ya kiyaye yace amin, idan akwai matsala saika min mgna na tro maka kudi ko? To Abba ngde, mum ce ta shigo tace harka shirya? Yace eh. Tare suka fita rakashi hannun imran rike da brief case din abba, saida sukaje bakin mota Abba ya kalli mum yace yaronki ya fada miki zai tafi america yau? Yaushe zai fadamin? Aini yanzu gaba yake dani sbda matarsa, dariya Abba yayi yace na Sani shiyasa ni yanzu na fada miki, domin kuwa da sanina zaiyi tafyar, kenan ka daure mishi gindin yaci gaba da gabar da yake dani ko? Ke zaki gyara halnki ki kaunaci abinda yake so, Indai da gaske kina sonshi a matsayin danki. Be jira me zatace ba driver ya bude mishi kofa ya shiga suka tafi yana dagawa imran hannu. Suna fita mum marairaice tace my son wato duk irin so da caring din da nake maka fushi kake dani Sbd matarka ko? Zakayi tafya amma ni bankai matsayin ka fadamin ba ko? Shiru yayi beyi mgna ba, dataga haka saita dafashi tace INA tsananin sonka my son karka bari soyayya tasa ka ringa fushi dani kaji? To kawai yace ya shige ciki. Wanka yayi ya shirya sanan ya fadawa Fareeda zaiyi tafya, Shagwabe mishi tayi wai dole saiya tafi da ita Saida ya zauna ya rarrashe ta yace idan ya tafi da ita abinda yake cikinta zai iya samun matsala, dakyar ta barshi ya tafi.

Mom yayiwa sallama ya fita dama ya gama booking din komai yana zuwa ya sami Safna tayi wanka tayi kyau karasawa yayi yai hugging dinta ta baya ya fara kissing dinta, suna hada ido yayi mata wani lallausan smiling sanan yace muje ki shirya kayanki america zamu tafi yanzu, da mamaki tace america kuma? Shine baka fadamin nayi sallama da umma

10 / 15