LADY SAFNAH COMPLETE HAUSA NOVELS BY MAMAN AYSHA.txt

Author :  Maman Aysha Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   6 / 15

15K to 18K   out of 43.3K words

sai bayan sallar isha'i, sanan sukayi mata sallama suka tafi gdnsu Maryam suka nunawa mmn Maryam motar, itama tayi murna sosai, sanan sukaje gdn baba Sharif ma suka nuna mishi ba karamin murna yayi ba, a take ya kira Abba yayi mishi gdy, su hjy turai dasu Sakina banda habaici ba abinda sukewa safna wai Sbd tsabar miji baya sonta ko wata uku batayi a gdnshi ba zai mata kishiya, ko bi takansu safna batayi ba suka tafi.

Suna kan hanyar zuwa gdn safna salma ta kirasu tace su debo kayansu su koma gdnsu su kwana, dama ita Maryam ta debo, sai kawai ta raka safna ta Debi nata suka tafi. Part guda aka ware musu na amarya da kawayenta, friends dinta da sukeyin Oxford university tare ma sunzu hadwa sukayi anata chapter, abinci kuwa kmr banza basuyi bacci ba sai wajen 1am

Washe gari aka fara gudanar da biki, wajen 7pm kowa ya shirya zaa tafi Indian night, kowa ka kalla yayi kyau safna kuwa kmr daga kasar Indian tazo, safna ce tayiwa amarya kwalliya dake make up artist ce ita, amarya tayi kyau kmr a sace ta 7:30 aka fara fita friends din mas'ud angon salma ne suke diban yan mata, ita kuma Maryam da safna tare zasu tafi da sadi. Duk inda safna ta wulga sai friends din amarya sunbita da kallo Sbd masifar kyaun da tayi, phone dinta ce ta fara ringing tana dubawa taga imran ne, tana dauka yace tazo ta sameshi a bakin garden din gdn su, salma ta tambaya tayi mata kwatance, Sanye yake cikin wasu hadaddun kayan indya cream color, yayi dadi da wani Jan Abu idan ba Hausa yayi maka ba saika rantse Dan asalin India ne, wani irin kishi ne ya kama safna data tuna cewa taron bikin shi ake da wata, saida ta gama kare mishi kallo sanan ta karasa suna hada ido gabansu ya fadi, kallonta yayi from head to toe yace wa ya baki izinin zuwa gdn nan kuma wa kika tambaya zakije wajen program din da zaayi? A sanyaye tace ba Wanda na tambaya, to inaso ki Sani wanan kwalliyar da kikayi kinyi a banza,domin kuwa ba inda zaki, kuma wallahi idan kikaje ban yafe miki ba, wani irin bacin rai ne ya kamata nan take idonta ya kada yayi ja cikin muryar kuka tace don Allah yaya imran karkayi min haka, ni sbda salma zanje badon amaryarka ba, kuma fa duka gdn zaa tafi, ta yaya zan zauna ni kadai? Idan ba zaki iya zama ba ki tafi gdnki, amma karki sake kije na fada miki, harya fara tafya ta riko hannun shi wani irin shock yaji, cikin kuka tace don Allah yaya imran kayi hakuri ka barni naje, meyasa baka tausayina ne, why do you hate me much? Fisge hannun shi yayi cikin wani irin yanayi yace ki rungumi kaddara kawai domin kuwa wallahi bazaki ba, juyawa yayi ya tafi nan take ta durkushe a kasa tana wani irin kuka me ban tausayi, shima mota ya shiga ya dafe kanshi zuciyarsa banda zafi ba abinda take, phone din shi tana ta ringing Amma be daga ba, Fareeda ce take kiranshi sbda tun dazu ta shirya tana jira yazo ya dauketa, saida tayi wajen 12 missed call sanan ya daga yana dauka tace haba sweet heart ranar bikin namu ma saika batamin rai? Yi hkri zanzo yanzu kawai yace ya kashe wayar, Sadik da bash ya kira suka tafi tare, sauran friends din kuma su sukaje suka Debi kawayen Fareeda.

Safna kuwa saida taci kukanta ta koshi sanan ta koma dakin, duk antafi daga amarya sai Maryam da kuma wasu kawayen amarya guda biyu, da dariyar yake ta shiga falon tace kai Ashe duk an watse? Dariya sukayi sukace eh mana muma ke muke jira, still tana dariyar yake tace ok to muje ko, kallon yan matan tayi tace aunty sameeha da aunty Naila Ku tafi a motar amarya, mu kuma saimu biyoku a baya ko? Tare suka sa amarya a tsakiya suka tafi, suna fita ta kalli Maryam tace kuje kawai Maryam ni wanan azzalumin ya hanani zuwa, cikin damuwa Maryam tace to yanzu ya zaayi kenan? Kuje kawai ba komai zan shiga garden din gdn na zauna harku dawo, nasan yanzu Maman Aysha GRP members suna nan online, so zanje nayi chrtn dasu kawai, itama Maryam cewa tayi ta fasa zuwa dakyar safna ta lallaba ta suka tafi



Maman Aysha
[23:05, 9/3/2017] β€ͺ+234 803 681 8427‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady safnaπŸŽ‹πŸŽ‹

9⃣0βƒ£βž–9⃣5⃣

_written by Maman Aysha_

*Talented writers forum*✍


Budiri akasha sosai baa tashi ba sai wajen 12am, safna kuwa da tayi chtn din ta gaji saita Mike ta koma daki tasa kayan bacci tayi kwanciyarta, Maryam ce ta fara dawowa sbda Sadik ne ya dawo da ita, itama canja kaya kawai tayi ta kwanta sbda sunyi rawa sun gaji, dama su uku suke kwana a dakin ita da salma da maryam, dukansu agajiye suka dawo kowa yana zuwa ya nemi wajen bacci.

Kwana hudu akayi ana gudanar da biki, kuma duka kwana hudun ba Wanda safna taje, yau Friday aka daura auren Fareeda da imran, sanan salma da mas'ud, da daddare kuma aka kawo amarya Fareeda. Gdnta aka fara kaita yan uwanta suka gani, sanan aka taho gdn mom sbda anan zata kwana sai anyi mother's eve gobe zata koma gdnta. zumudi da murna a wajen mum abin baa mgna, part guda aka ware musu acikin gdn ita da kawayenta, karba akayi musu taban girma sai wani nan nan mom takeyi dasu, da sun bukaci Abu ake kaimusu

Washegari aka tashi da shirin yin mother's eve, acikin gdn su imran zaayi dake akwai katon fili acikin gdn kuma ko ina akwai Interlock a gdn, tun sassafe masu decoration sukazo, wajen 10am su safna suna break fast taji phone dinta tana kuka, imran ne ji tayi gbnta ya fadi, da bazata dauka ba saidai kawai tayi picking, cikin golden voice dinta tace hlo ina kwana? Lpy INA gjya, dama kira nayi na fada miki zaki iya attending program din yau tunda a cikin gda zaayi kinji ko? A hnkli tace eh, sanan ya kashe wayar. zuwa 12pm masu decoration sun gama, manyan canopy akasa aka jera kujeru gashi sunyi hadadden decoration, special kwalliya akayiwa wajen da amare da angwaye zasu zauna idan ka gani saika rantse event centre ne.

4:30 dot zaa fara bikin, tun wajen 2:30 safna ta fara yiwa salma kwalliya, ana kiran sallar laasar suka mike sukayi dake dama da alwalarsu, bayan sun idar safna ta shiga wanka tace salma ta saka gown din tunda an gama kwalliyar fuska idan ta fito daga wanka saita yi mata dauri. Tana fitowa daga wankan ko mai bata shafa ba ta karasawa amarya kwalliyar ta, wani lace amarya tasa dark purple Dan 250k, sanan aka Dora head light purple, akasa hadaddun ceremonial costume, nan take amarya tadau kyau dake itama fara ce, duk Wanda ya kalleta saiya kara kallonta, kowa na wajen zuzuta kyaun da tayi yake. Saida safna ta tabbatar amarya ta hade sanan itama ta shiga daki ta shirya


Wata hadaddiyar gown din lace safna tasa sky blue ne da ratsin silver kudinshi zaikai 150k a lefe aka sako mata shi, zama tayi tai simple make up sanan ta Mirza dauri da saika rantse gwagwaro ta Dora, silver sarka da dankunne tasa, sanan ta dakko ceremonial shoe and bag silver, gyale ma silver ta nufi dakin da amarya salma take.

Mutane ne makare a compound gdn kowa ya hallara fitowar angwaye da amare kawai ake jira, mum ce ta shigo Side din da amare suke ta shiga dakin da salma take, a tsaye ta ganta jikin madubi da niyar yi mata fada ta shigo, amma suna hada ido ta saki wani murmushin farin ciki Sbd kyaun da taga tayi godya tayi ga Allah daya bata kyakkyawar 'ya kmr salma, sbda duk events din da akayi ba Wanda kwalliyar ta batayi kyau ba, kallonta tayi tace you looks so gorgeous my dota, kuyi sauri Ku fito sbda mutane sun taru, cikin farin ciki salma tace thank you mom.....safna ce ta shigo dakin suna hada ido da mom farin cikin da yake kan fuskarta ya dauke, da hantara tace uban me kikazo yi gdn nan? Salma tace ai dama tana nan mum, ita take min kwalliya fa, cikin shan mur tace aikuwa ban yadda ta fita wajen program din nan ba, da sauri salma tace meyasa mum? Au tambayata ma kike? Kina nufin kice baki kula da Dan banzan kyaun da tayi ba? Lkcn Dana shigo dakin nan gani nayi kmr duk duniya ba Wanda ya kaiki kyau, amma tana shigowa sainaga kyaun naki ya dishashe duk da kema kinada kyau, idan har nabar safna ta fita ta jera daku to kuwa ko shakka banayi hnklin mutane kanta zai koma, ni dama ban gayyato ki ba so muje ki ficemin daga gda, kuma very soon zan dauki mataki akanki domin kuwa wanan fitinannen kyaun naki zai iya canjawa Dana ra'ayi ya dawo da sonda yake miki, ni kuma idan akwai abinda na tsana a duniya shine hada jini dake, wa ya Sani ma ko ke ba mutun bace tunda dama ba wani cikekken asali ne daku ba. Kallon safna tayi tace debi kayanki muje na bude miki kofar baya ki tafi gdnki, ke kuma salma kuyi sauri Ku fito

Sakata tayi agaba ta bude mata kofar wajen kitchen ta fita, wasu zafafan hawaye ne suka fara ambaliya a fuskar safna, packing space ta nufa, tana zuwa taga an rufe motar ta bata inda zata fita, Dora kanta tayi ajikin motar ta fara wani irin kuka me ban tausayi, wanan wanne irin aure tayi? Miji ya tsaneta, familynshi sun tsaneta Abba da salma ne kawai suke sonta, tunu ranar da aka kawota gdn tayi yanda aka karbesu a wulakance amma yanzu sai ji dasu Fareeda ake, ya zama dole su rabu da imran sbda ta gaji da wulakancin da ake mata, kuka sosai safna take ita kuwa Maryam nacan a wajen friends batasan wainar da ake toyawa ba.

Saida ya gama shirinsa tsaf ya tuna be dakko hula ba, wata gezna ce ajikinshi maroon, key din shi ya dauka ya nufi motarshi budewa yayi ya dakko hular, ya rufe zai tafi kenan yaji sheshhekar kuka, inda yaji sound din kukan ya nufa, tsaiwata kawai ya gani ya gane itace, jiyo da ita yayi suka fuskanci juna, a tsorace ta kalleshi, cikin bedroom voice yace meye sameki kike kuka? Goge hwayen tayi tace ba komai, to me kike anan? Gda zan tafi kuma na samu an rufeni, shine yasa kike kuka? Uhm kawai tace batare da ta dago ta kalleshi ba, wani smiling yayi yace safna! Kenan. Dialing din no salma ya fara yi harta kusa tsinkewa ta dauka yace meya sami safna take kuka? Wallahi ita da mum ne, korarta tayi kmr wata barauniya tace bazata je mata wajen biki ba, ji yayi ranshi ya baci wani irin tausayin safna ne ya kamashi this is d first time dayaji tausayin ta tun ranar daya gano ko ita wacece.

Hugging dinta yayi yana Dan shafa bayan ta a hnkli wani hadadden kamshi ne ya daki hancinsa, cikin low ccvoice yace iam sorry safna, kiyi hakuri kinji, sun Dade a haka sanan yace naga motar bash baa rufeta ba, bari na karbo key din shi nayi dropping dinki, karka damu kaje kawai zan jira anan, idan an gama events din na tafi, ah ah bazai yiyyu ba, ki jirani ina zuwa.

Part dinshi ya koma inda friends dinshi suke yace don Allah bash bani Aron motan ka, tsiya suka fara mishi wai Ina zaije ana dab da fara program, sharesu yayi ya karbi key din da sauri ya fito, bude motar yayi sanan ya kamo hannun safna ya bude mata kofar zata shiga kenan saiga bash kmr anjefo shi, wani mayataccen kallo yabi safna dashi cikin zafin kishi imran yace menene? Sai lkcn bash ya tuno abinda ya fito dashi, idonshi akan safna yace mantawa nayi ban fada maka inda security Motar yake ba, cikin shan mur yace oya fadamin sauri nake, yana nuna mishi imran yaja motar cikin zafin nama ya tafi yabar bash acikin tunani



Maman Aysha
[23:06, 9/3/2017] β€ͺ+234 803 681 8427‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady safnaπŸŽ‹πŸŽ‹

9⃣5βƒ£βž–1⃣0⃣0⃣

_written by Maman Aysha_


*Talented writers forum*

Tun suna hanya mum ta addabeshi da waya akan yayi sauri yazo zaa fara program, tun yana dagawa yana cewa yana zuwa harya dena picking din wayar, har cikin gdn ya shiga yanayin packing safna ta bude kofar ta fita da gudu ta shiga cikin gdn, direct dakinta ta shige ta fada kan gado taci gaba da kukanta tunani ne yayi mata yawa, wani irin son imran ne yake yawo a jinin jikinta, tunowa tayi yace mata idan ya auri Fareeda zai saketa, kuma a yanda take jin zuciyarta yanzu ya zama dole ta hakura da imran sbda bazai taba sonta ya bata kulawa irin kowanne miji yake bawa matarsa ba, gara ya saketa taje ta auri mutumin da zatayi zaman aure na yanci ba irin wanan ba.

Imran kuwa bayan safna ta shiga ciki hularsa ya dauka ya shiga part dinsa yasa hular Saida ya kalli mudubi yaga ta zauna sanan ya kara fesa turare ya fito harzai shiga dakin safna yaji mum dinshi ta kara kira kawai saiya fice.

A 360 ya karasa gdn yana zuwa yaga mum a bakin gate gabdya ta fita hayyacinta fada ta fara yi mishi sai kawai ya bata hkri ya shige, yana zuwa suka shiga cikin wajen dama shi ake jira.

Ansha shagali anyi buduri an Shana irin Wanda fada ma bata lkci ne, me kartu just imagine it, Sbd bikin hamshakin mekudi irin me sukeli dole ya zama one in town, kuma Karin burgewar ma su kadai ne 'yayyanshi a duniya dagasu ba kari, kaga kuwa dole farare bugun abuja suyi kuka. Senovias iri iri aka ringa rabawa kmr su waya android, turamen atanfofi, computer laptop, shadda laces da sauran su. Duk hadamar mutane Saida kowa ya samu varieties na abinci kuwa ni wani ma ban taba ganin irinshi ba. Daf da magrif taro ya watse kowa ya koma masaukinshi, imran ma tare suka tafi masauki da friends dinshi bayan sunyi sallar magrif da isha'i sunci abinci sai suka bude hira, Bash ne ya jashi gefe yace babah nifa iam totally loose my consciousness tunda naga babe dazu, wallahi tunanin ta ya hanani sakat, don Allah wacece ita? Wani irin kishi ne ya kama imran cikin shan mur yace matar aure ce, matar aure kuma? To waye mijinta? Wanan kuma ba damuwarka bace, juyawa yayi, zai tafi bash ya rikeshi don Allah imran ka temakeni ka fadamin gskya, wallahi INA masifar sonta na Dade INA Neman irin type din yarinyar na aura Amma ban samu ba don Allah my friend ka taimaka min tunda kai kayi aure, cikin hantara yace dalla na fada maka matar aure ce, meyasa bazaka yadda dani ba, to idan matar aurece kai meye hadinka da ita? Oh my god Bash kanada problem, Kanwata tace, kuma mijinta friend dina ne, to yanzu ina mijin nata? Bansani ba Dan iska ka dameni, idan baka yadda ba ka tsananta bincike, riko hannunshi bash yayi yace meda wukar kaifa ango ne be kamata ka ringa fushi ba, shekenan mgna ta wuce. Yana cikin friends anata chapter Fareeda ta kirashi a waya yana dauka ta wani make murya hlo sweet heart kana ina ne? Mom tace tare zamu tafi gda dakai kuma naga har yanzu bakazo ba, iam so tired inaso naje nayi wanka nayi bacci don Allah kazo yanzu mutafi, dariya abin ya bashi kawai saiyace ok INA zuwa.

Kallon friends dinshi yayi yace ni zan wuce amarya ta ta fara kirana, dariya suka sa aka danyi rudu ya tafi.

Ta suya spot yabi ya sayi gasassun kaji da ice cream ya tafi, direct gdn safna ya wuce.

A bangaran safna kuma bayan taci kukanta ta koshi mikewa tayi tahau gyaran gda dake kwana hudu bata nan gdn yayi kura, Saida ta tabbatar komai yayi neets ta shiga wanka tasa wata hadaddiyar English gown maroon color ta fesa hadaddun turare, yunwa take ji amma saita kasa dafa abincin sbda bacin ran da yake damunta, kwanciya tayi akan doguwar kujera ta kuna TV tana kallo.

Bataji bude kofa da shigowar sa ba kawai ji tayi an zauna a kusa da ita a razane ta mike ta zauna dariya yayi yace relax matsoraciya nine, komawa tayi ta zauna, shiru wajen yayi na Dan wani lkci sanan ya kalleta yace ya zaki iya kwana ke kadai kuwa? Wani bacin rai taji cikin shan mur tace ba damuwarka bace, oh god so naki naji idan ba zaki iya ba na samo wacce zatazo ta tayaki, bana bukata ta bashi amsa a takaice, ledar daya shigo da ita ya mika mata yace ga abinci nan, ni zanje na dauki Fareeda mu tafi tun dazu tana jirana, cikin tsananin bacin rai tace ka dauki abinka banaso, tafya kuma dama ban daure ka ba, Amma kafin ka tafi inaso don Allah ka temaka ka cika alkawarin daka dauka, wane alkawari ne? Kace idan ka auri Fareeda zaka sakeni, sbda haka inaso ka sakeni yanzu, wani smiling yayi yace daga tarewar amarya sai kuma a saki uwar gda? Ai se mutane su zargeni su ringa yimin kallon marar adalci, da adalcin ne dakai? Ai bakada wani adalci ko kadan zalunci ne kawai a zuciyarka, wallahi nima na tsaneka kmr yadda ka tsaneni sbda haka ka bani takarda ta idan kuma ba haka ba gobe zan bar gidan nan koda baka sakeni ba ta karasa mgnar tana kuka. Ji yayi zuciyarsa tayi zafi wani irin radadi yakeji rasa abinda zaice mata yayi kawai saiya juya ya fice daga gdn





Maman Aysha
[23:06, 9/3/2017] β€ͺ+234 803 681 8427‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady safnaπŸŽ‹πŸŽ‹

1⃣0⃣0βƒ£βž–1⃣0⃣5⃣


Sai wajen 10:30pm imran yaje ya dauki Fareeda mum tana tayi mishi fada wai yaje ya Dade tana ta jiranshi, suna zuwa gda kowa ya wuce dakinshi, imran na

6 / 15