Author : Maman Aysha Category : Romantic Hausa Novels
kowa, daga ita sai mahaifiyar ta ko ta taba nuna maka wani Dan uwansu na jini? Na tabbata bata taba ba, sbda haka ni ban amince na hada jini dasu ba idan har kanaso naci gaba da daukar ka a matsayin dana to ya zama dole ka rabu da ita, idan kuma ba haka ba to bani bakai koda hakan zai zama sanadiyar mutuwar aurena da mahaifinka. Durkusawa imran yayi yana wani irin kuka, kama kafafuwan mom yayi yace don Allah ki sassauta min, haba mum, yakamata ki tausaya min wallahi Inason safna rabuwa da ita barazana ne ga rayuwata, don Allah mom ki temaki rayuwata. Shiru mom tayi for some seconds, tausayin Dan nata ne ya kamata, ita kanta batasan irin son da takewa Dan nata ba, kenan yafi son safna akaina? Wanan wacce irin kaddara ce? Kallon shi tayi tace is OK, zan amince kaci gaba da zama da safna a matsayin matarka amma a bisa sharadi, cikin rawar murya yace wanne sharadi ne? Saita nemo asalinta, kuma 1month na bata ta nemo duk inda mahaifinta ko yan uwan mahaifinta suke, idan kuma ba haka ba to ya zama dole ka rabu da ita ko kanaso ko bakaso. Sanan ta tashi ta fice daga gdn
Maman Ayshaβ
[10:49, 9/4/2017] βͺ+234 803 681 8427β¬: ππ
Swanky lady safnaππ
1β£9β£5β£β2β£0β£0β£
Bin bayan ta imran yayi Saida ya rakata har bakin mota kafin driver ya bude shiya bude mata, sanan ta shiga ya rufe kofar, saukar da glass mum tayi tace nasan fitinannan kyaun safna ne yake rudar ka, amma duk da haka ya kamata kayi tunani domin asali ba karamin Abu bane, bata jira mezai ce ba driver yaja suka tafi. Yana komawa ya sami safna durkushe a kasa tanata kuka, zuwa yayi ya dagata ya rungume ta tsam ajikinshi cikin loosing hope safna tace dama ka biyewa kudirin mum ka sakeni sbda bazaa taba ganin mahaigina ba, ni na Riga na fitar darai dashi, gara ka sakeni kawai kowa ya huta.....shitss bazan taba sakinki ba safna INA sonki, I Luv you wit all my heart ni kaina bansan irin sonda nake miki ba, so bazan iya rabuwa dake ba, kuma don Allah ki dena cewa kin fitar da ran ganin mahaifinki, kidai kawai mu dage da addua, me rai baya fitar da rai daga rahamar Allah, so muci gaba da addua Allah ya tallafa mana, cikin kuka tace amin.
Lallaba ta ya ringayi har Saida ta ware, bayan sunyi sallar isha'i suna zaune suna hira tace waini me talaka sukayi muku ne kuka tsanesu kaida mom? Smiling yayi ya lakaci hancinta sanan yace "akwai wata me aiki da muka taba yi a gdnmu, ita take yimana girki a wancan lkcn, ba karamin girmamata mom take ba, ta dauki amana ta bata tashi daya tayiwa Abba asiri ta aura mishi jikarta, suka gaje gdnmu, Abba ya tsanemu muka dawo abin tausayi sai gdnsu mom muka koma da zama, Saida aka dage da rokon Allah sanan Abba ya dawo hayyacinsa yayi musu korar kare sanan ya dawo ya bawa mom hakuri muka koma, sai reason na biyu kuma, akwai wani driver Abba shima Abba ya amince dashi 100%, wata rana Abba zaiyi tafya zuwa kasar Egypt saro kaya sai abokan hamayya suka hada baki da wanan amintaccen driver nashi suka bashi cocaine yasawa Abba a brief case dinshi, wani abin mamaki ba gane a 9ja ba Saida yaje airport din Cairo sai suka gane, aka daure Abba ba karamar wahala mukasha ba kafin a sakeshi, daga baya sai muka gane wanan driver ne yasa mishi, tun daga lkcn nida mom muka tsani talaka, ni haduwata dake ne yasa na dena, amma mom har yanzu akwai abin a zuciyarta. Jinjina abin safna tayi tace Allah yasa mufi karfin zuciyarmu yace amin, sanan suka mike suka kwanta. Wajen karfe 2:30 na dare suka tashi suka fara jera nafila Saida sukayi rakaa 8 har shafa'i da wutri 11 sanan sukayi addua akan Allah ya bayyana musu mahaifin safna indai yana raye, idan kuma baya Raye Allah ya hadasu da yan uwanshi, sanan Allah ya dorasu akan mum ta fara son safna kmr yadda takeson salma yarta. Sun Dade suna addua safna kam akan sallaya bacci ya dauketa sai imran ne ya mayar da ita daki.
Washe gari around 10am Abba ya kira imran da no 9ja da mamaki imran yace abba yaushe ka dawo? Tun jiya jirginmu ya sauka a Lagos, yanzu zan shigo wani zuwa Kano, kazo wajen 12 ka dauke ni a air port, yace to Abba, ai nayi zaton sai next WK zaka dawo? Eh da haka na tsara, Kasan daurin auran Bilkisu Yar gdn me martaba Sarki upper WK ne ko? Eh Abba na sani, to shine shekaranjiya yayi min waya ya dawo dashi wanan satin, kuma His royal highness Alhaji abdulwahab ne walin amarya, munyi waya dashi dazu da safe yace yau zai shigo kano, wani ihun murna imran yayi da har Saida ya tsorata safna sanan yace Abii zai zo 9ja dole ka taho Abba, lalle munada babban bako, Allah ya kawo Ku lpy Abba yace amin.
Suna gama waya ya kalli safna cikin tsananin farin ciki yace INA ganin Allah ya amshi adduarmu domin kuwa Hero din Abba da mummy zai shigo 9ja yau, sbda haka zanje nakai mishi karar mum na tabbata idan yayi mata magana bazata kara cewa na sakeki ba koda kuwa baaga babanki ba sabd mom ba karamin ganin mutunci shi take ba, da mamaki safna tace shi kuwa waye wanan? Kuma meye hadinku dashi da kuke mugun sonshi haka?
Sunan sa his royal Highness alhaji abdulwahab Nasir, shine babban sarkin Alexandria ta kasar Cairo, wato abinda ya hadamu dashi shine" idan zaki tuna jiya na baki lbri cewa an kama Abba da cocaine a kasar Egypt amma ban fada miki yadda akayi ya zama free ba ko? Eh kawai dai kace kunsha wahala kafin a sake shi, yawwa to abinda ya faru shine daurin life in prison gwamnatin Egypt ta daurewa Abba, ba karamin tashin hankli muka shiga ba, manyan abokan Abba ne suka ringa kaiwa da komowa cikin su harda sarkin garin nan, dakyar muka samu sukace zasu bamu belin shi Amma sai munzu da me babban mukami kmr minister ko kuma babban Sarki Dan asalin garin Egypt ya saka hannu da 100 million dollars sanan, nan take murnar da muke ta koma ciki, muka kara shiga sabon tashin hnkli, gashi an rufe account din Abba gabadaya ana cikin haka sai me martaba sarkin garin nan ya tunu da his Royal Highness abdulwahab, class mate dinshi ne tare sukayi kartu dashi, ba shiru muka tafi tafkeken gdnsa dake garin Alexandria, muna zuwa akayi mana iso mukaje muka kwashi gaisuwa, sanan me girma sarkin garin nan yayi mishi bayanin abinda ya kawo mu, Sbd tsananin kirkinshi yace ba damuwa, ko kinsan haka bawan Allah nan yaje yayi signing ya bada zunzurutun kudi har 100 million dollars yayi belin abba, sanan ya wuce damu gdnshi muka kwana ya hada mana sha Tara na arziki muka dawo, da aka kwana biyu sai muka koma harsu mom da kakarmu lkcn tana dare mukaje muka kara yi mishi gdya, sanan Abba ya mayar mishi da kudin sa, kinsan wani Abu? Safna tace ah ah, cewa yayi bazai karba ba bisabillilla ya bayar, tun daga wanan lkcn mom da Abba suke tsananin sonshi duk da Abba ya girmeshi, kuma time to time suna zuwa kasar su su gaishe shi. Safna tace uhmm lalle ba zaku manta dashi ba, yayi kokari sosai, gasky nima he is my hero domin kuwa samun irinshi da wahala, kiran daya shigo wayarsa ne ya katse musu hirar yana dauka Abba yace yaje air port ya dauko shi yace to.
Sai wajen karfe 4pm me girma sarkin Alexandria ya shigo Kano, me martaba Sarki da kansa yaje ya taro shi ya kaishi masauki shida jamaarsa, bayan sunci abinci sun huta ya kira Abba yace ya shigo.
Ana idar da sallar magrif su safna sukayi shiri, wata Arabian gown ta saka pink color me duwatsu tun daga sama har kasa, sanan tayi rolling da gyalen rigar nan take tadau wani kyau, shima imran wata maroon gezna ya saka suka tafi gdnsu suka fara zuwa, gbn safna sai faduwa yake Sbd tsoron mum da take, amma ga mamakinta sai taga mom acikin farin ciki take kobi ta kanta ma batayi ba.
A wata makekiyar range rover din Abba suka tafi, imran ne yake driving fadar me girma San Kano suka fara zuwa suka kwashi gaisuwa, yanata tsokanar imran yace bashida kirki baya zuwa ya gaisheshi, aka danyi dariya, sanan yasa aka rakasu special part din daya sauke shi. Suna shiga suka sameshi a zaune cikin shiga ta alfarma dogarawanshi kuma suna tsaye sun zagaye shi, zubewa sukayi suka kwashi gaisuwa har Abba ya amsa da faraarsa, fuskarshi dauke da murmushi yace my son imran zo ka zauna a kusa dani, ya nuna mishi gefensa ya zauna, kallon shi yayi yace kayi hakuri ban samu nazo daurin auran ka ba, wallahi lkcn ummina ce bata da lpya mukace follow up america, cikin sunkuyar dakai imran yace ah ba komai Abii, sanan yace to ya amaryar taka? Lpya kalau, gata canma tare muke da ita, cikin sanyi murya safna tace INA wuni? Meda hnklin shi yayi kanta, suna hada ido gabansu ya fadi lkci guda, kamannin mahaifiyar shi ya gani exactly a fuskarta, da zaa kawo pic din Ummin shi tana yarinya da kowa na wajen ze rantse safna ce, a zabure ya mike yana nuna ta da hannu, dafe kanshi yayi yana kokarin ya tuno wani Abu Amma ya Kasa, busy brain din shi ta zama a lkci guda kuma kanshi yadau zafi, nan take ya tafi zai fadi cikin zafin nama fadawanshi suka taro shi.....
Maman Ayshaβ
[10:50, 9/4/2017] βͺ+234 803 681 8427β¬: ππ
Swanky lady safnaππ
2β£0β£0β£β2β£0β£5β£
Ruwa suka dauko a fridge aka fara yayyafa mishi, amma duk da haka be farfado ba, mum ce ta kalli safna tace anya kuwa bake kika kamshi ba? Daga hada ido dake saiya suma, waike wacce irin annuba ce safna? Abba ne yace su fita su koma daya falon. Suna fita aka kara kwara mishi ruwan da yawa, sai yayi wata ajiyar zuciya sanan ya bude idon sa a hnkli, da Abba ya fara hada ido, cikin sanyin murya yace mafarki nake ko? Abba yace ah ah ba mafarki kake ba your Highness, to idan ba mafarki nayi ba tana ina? Wa kenan ranka ya Dade? Safna, koba safna nagani ba? Cikin zumudi imran yace itace Abii, Dana Kasan safna? Idan dai har da gaske na dawo hayyacina safna 'yata ce, mikewa yayi yace Ku kira min ita don Allah, da gudu imran yaje ya kamo hannunta suka shigo tare har mum, yana daga zaune ya ware hannunshi alamun taje wajenshi, rarraba ido safna ta farayi a razane, cikin sansanyar murya yace come to me my dota, iam your father, nine mahaifinki rarraba ido safna ta fara yi kmr wata sokuwa, imran ne yayi mata alama data je, kawai saita tafi da gudu ta fada jikinshi tana wani irin kuka, rungumeta yayi tsam sun Dade a haka sanan ya saketa ya tashi yayi sujadda yayi gdya ga Allah sanan ya kalli safna yace ina Jidda? Tace tana gda, cikin loosing hope yace tayi aure ko? Tace ah ah, har yanzu bata kara aure ba, cikin farin ciki yace alhamdulilla yau Allah ya cikamin burina, tabbas me rai baya fitar da rai ga rahamar Allah, Allah ngde maka. Ku tashi mu tafi wajen Jidda, me girma San Kano ya kira a waya yayi mishi bayani, aikuwa yace shima harda shi zaa je.
Umma na zaune afalo tana kallon sunna TV sai taji sallama, safna ce ta fara shiga sanan mum da imran, sai Abba, jitai gabnta ya fadi a zuciyarta tace Allah yasa dai lpy......ganin Wanda ya shigo ne ya katse mata tunani, cikin sassarkewar murya tace Nasi........tfy tayi zata fadi Abii ya tafi da sauri ya riketa ta fada ajikinshi, ruwa ya samu ya shafa mata a idonta, Kasa bude idon tayi, a hnkli ta fara cewa ya Allah wanan mafarki da nake yawan yi idan har da gaske nasiru yanada rai Allah ka tabbatar min da mafarkin nan, idan kuma baya Raye Allah ka bamu hakurin jure rashin sa ya Allah, ta karasa mgnar tana wani irin kuka, shi ya katseta da cewa wanan karan ba mafarki kike ba Jidda, ki bude idonki ki kalleni nidin ne dai, bude idon ta farayi ganin sun hada ido tayi saurin mikewa ta zauna binshi tayi da kallo San an ta juya ta kalli su Abba da imran tace da gaske kuma kuna ganin shi? Murmushin farin ciki imran yayi yace da gaskene umma, sedai muyiwa Allah godiya kawai, faduwa tayi tai sujadda sanan tace alhamdulilla ala kulli halin, rungumeta abi ya karayi yana kuka, safna ma ta fada jikin su Saida sukayi kuka me isarsu sanan sukayi shiru. Bayan waje ya lafa yace mata ina alhaji Sharif? Tace yana nan, cikin kankanin lkci aka kirasu shida iyayen maryam, sanan safna ma ta kira sadik da Maryam suma sukazo.
Saida kowa ya hallara sanan umma ta bashi lbrn yanda rayywarsu ta kasance bayan tfyar shi, sanan ta fada mishi halin hallaci da kuma rikon amanar da alhaji Sharif da kuma Yar uwarshi mmn Maryam sukayi musu, sanan ta fada mishi halin dattako da kirki irin na alhaji kabeer mesikeli daya amince danshi ya auri safna ba tare da yasan cikekken asalin su ba, kuma dedai da rana daya be taba nuna kyama agareta ba, datazo kan imran kuwa murmushi tayi tace shi kuma sirikinka katt kenan domin kuwa shine farin cikin safna, shine walwalar ta, shine jin dadin rayuwar ta, shine ya sayamana wanan gdn da nake ciki, ba abinda zamu cewa wadanan bayin Allah se addua Allah ya hadamu a aljannar Fiddausi kmr yadda ya hadamu anan, duk aka amsa da amin. Mum din imran kuwa banda gumi ba abinda take, gabadaya ta jige tayi jagab tunda sukaje gdn ta Kasa dagowa kanta sbda borin kunya.
Godiya his Royal Highness yayi musu sosai irin godiyar da besan ma da wanne kalami zai musu ba, sanan ya kallesu yace nasan dukanku zakuyi mamaki ya akayi INA matsayin yaron wani anan 9ja kuma na koma Sarki? Sanan meyasa na tafi nabar iyalina ban nemesu ba for d past 16yrs, bayan kuma duk duniya ba Wanda nakeso kmr su? Gyara zama yayi yaceWato abinda ya faru shine........
Maman Aysha
[10:50, 9/4/2017] βͺ+234 803 681 8427β¬: ππ
Swanky lady safnaππ
2β£0β£5β£β2β£1β£0β£
Mahaifina shine me girma sarkin Alexandria, matanshi biyu ne hajja safiyya itace wife dinshi ta farko yaranta uku, yaya shuraim ne babba sai aunty juwaira sai kuma naila itace abokiyar haihuwa ta.
Ita kuma Ummin mu Yar sarautar India ce, acan babanmu ya auro ta kuma itace fulanin shi, kyakkyawa ce sosai idan ka kalleta sai kace ita ta haifi safna sbda mugun kmr da suke. Mu biyu ne a wajen Ummin mu, nine babba sai kuma kanwata jalila. Familyn mahaifiyata manyan yan kasuwa ne, kuma a wajen su nayi kartu, wanan dalilin ne yasa na koyi business tun INA Dan karami. A Business admin nayi degree da masters Dina, bayan na kammala sainaci gaba da kasuwanci na, INA 25yrs na mallaki many an shaguna na saida gold wajen kuda goma, sanan na bude manyan mall kusan guda shida acikin garin Cairo, guda biyu kuma a Alexandria, banda kamfanoni Dana mallaka. Tun INA Dan karamina ni mutun ne meson kyautatawa mutane, ko kadan abin hannuna be rufe min ido ba, wanan hali nawa ne yasa Mutanen garin suke mugun sona domin kuwa ba karamin gudun mawa nake bawa Mutanen garin ba, ana cikin haka sai mahaifina ya yanke hukunci zaiyi murabus daga kan mulki ya bawa daya daga cikin mu, saboda rashin lpyar hawan jini data dameshi. Meeting ya kira suka zauna da kings makers na masauratar daga karshe shawara ta kare akan ni zaa bawa sarautar, sbda a cewar su ni nake da duk wasu halayya masu kyau da ake bukata Sarki ya samu, kuma uwa uba inada hankli, nayi ilimin boko da arabi kuma INA kaunar talakawan garin. Lkcn da labari yaje wajen hajja safiyya da 'yayyanta ko kadan basu nuna damuwarsu ba, saima farin ciki da sukayi.
Ana saura wata uku ayi bikin dadi hajja safiyya taje wajen boka tayimin kurciya, dagowa yayi ya kalli Alhaji Sharif yace wanan shine dalilin haduwata dakai alhaji, domin kuwa na shigo Nigeria ba tare da nasan inda kaina yake ba.
Ba karamin tashin hnkli iyayena suka shiga ba, tsananin damuwar bata na ne yasa zuciyar mahaifina ta buga ya rasu, bayan anyi sadakar arba'in sai patron din sarakuna na kasar Egypt yace a saurara da nadi harsai an ganni, idan yaso a Nada wakili kawai tunda nine burin mahaifina. Ummina ta dage da rokon Allah akan duk a inda nake Allah ya nuna mata ni.
Cikin ikon Allah ranar daka aikemu Lagos alhaji itace ranar da Allah ya amshi adduar Ummina domin kuwa INA bakin wani shago zan sayi recharge card, kawai sainaji kaina yana juyawa, nan take na zube a Kasa sumamme, Mutanen wajen ne suka temaka aka kaini Asibiti bayan na dauki gud 2 hour unconsciousness, saina farfado, rayuwata ta Egypt ce ta dawomin memory dina sbda haka na manta da rayuwar da nayi a 9ja, cikin mamaki na tambayi nurse din a INA nake? Tace Lagos, ba karamin mamaki nayi ba nan take na fara tunanin me nazo yi Lagos? Sanan zuciyata tanason tuno min wani Abu amma na Kasa tuna ko meye.
Babban likitan me Asibitin ne ya shigo, kallo daya nayi mishi na ganeshi, domin kuwa a kasar mu yayi kartu lkcn INA Dan sec, kuma yana zuwa gdnmu. Wani irin ihu naji yasa dake baye rabe ne, nan take yace na tashi mu tafi zai kaini kasarmu ayau din nan, sbda dama yaji lbrn batana.
Bamu sha wahala wajen samun ticket ba kasancewa ta Dan babbar