Author : Maman Aysha Category : Romantic Hausa Novels
kan dining din, saidai safna najin kamshin abincin ta tafi ta fara amai, amma duk da haka gogan be gane abinda yake damun ta ba. Komowa tayi ta kwanta tace bazan iya ci ba, cikin matseneciyar damuwa yace to me kike so? Tace kunun gyada, aikuwa tuni ya dauki waya ya kira mom din shi yace bakinshi ba appetite ta temaka mishi da kunun gyada, tace to ba matsala idan ta gama zata bayar akawo mishi. Haka yasa safna agaba duk tausayin ta ya kamashi har aka kawo kunun, Allah ya temaketa tasha ta koshi harta boye guntun zatasha da daddare.
*2:15am*
Fareeda ta farka da wani azababben ciwon Mara, mararta taji tana ciwo kmr zata balle gda biyu, phone din imran ta fara dialing to her own surprise saitaji switch off, faduwa tayi tana murkususu, dakyar ta samu ta rarrafo falo ta fara kiran larai daya daga cikin masu aikinta, da gudu larai tazo, tana ganin yanayin data ke ciki tahau salati, kiran mmn Fareeda tayi ta fada mata, mama tace ina mijinta? Baya nan kuma an kira no sa akashe, OK to ganin nan zuwa. A Daren ta tashi driver suka nufi gdn Fareeda, kafin su karaso jini ya balle kmr fanfo, suna zuwa suka sameta a sheme a Kasa, ciki sauri aka dauketa akasata a mota direct standard Hosp suka nufa.
Suna zuwa likitoci sukayi rubdugu akanta Saida suka tabbatar komai ya zama normal sanan sukayi pcv su kaga 19% dole sai anyi blood transfusion, likita yana fadawa mama ta fara kiran no imran amma still akashe, kawai saita kira mom din shi ta fada mata, tare suka tafi asibitin da Abba, ajikin abban imran aka Debi jinin aka kara mata dake dukansu o+tive ne. Saida su Abba suka tabbatar she is stable sanan sukace zasu je su dawo
Imran kuwa be bude waya ba sai wajen 11am aikuwa yana budewa call din mom yana shigowa, yana dauka tace my son meya faru ka kashe wayar ka? Kuskunda ya fara, dataga zai bata mata lkci tace kaje standard Hosp yanzu Fareeda tanacan bata da lpya, muma acan muka kwana sbda saida aka debi jinin abbanka aka kara mata, inaso kaje yanzu sbda mu mun dawo gda zanyi musu abincin break fast. Ji yayi gabanshi ya fadi, Allah yasa ba wani Abu ne ya sami babynshi ba.
[10:12, 9/4/2017] βͺ+234 803 681 8427β¬: ππ
Swanky lady safnaππ
1β£8β£0β£β1β£8β£5β£
Yana shiga dakin da aka kwantar da ita ya samu tayi wanka tana zaune kmr ba marar lpya ba, kusa da ita yaje ya zauna cikin tausayawa yace sannu Fareeda ya jikin? Tana wani basarwa tace da sauki, mmn Fareeda ce ta shigo dakin, aikuwa tana ganinshi tahau shi da fada sai yanzu kaga damar zuwa? Sbd tsabar iskanci ka tashi ka wani rufe waya bayan Kasan ba cikekkiyar lpy ne da ita ba, yanzu da ace banzo da wuri ba ai zata iya rasa ranta, sbda acikin jini naje na sameta, to wallahi bari kaji na gaji da wulakancin da kake mata, ya zama dole a raba auran sbda ita ba kmr marar galihun matarka take ba, ita tanada gata. Haka tayi ta masifa shi kuma imran bece mata komai ba, saidai ya kulu da fadan datake mishi. mom din imran ce ta shigo hannun ta dauke da basket din abinci, Amma duk da taganta bata dena fadan ba, da mom taga abin yayi yawa sai tace kiyi hakuri hjya zinatu akasi aka samu Amma wallahi baya kashe waya idan ze kwanta.....dakata dalla, dole kice haka mana sbda ba yarki bace, aini wallahi anyi angama ya saketa kawai kowa yahuta, Mom tace haba hjy zinatu abin ai bekai haka ba, kiyi hakuri don Allah cikin jin haushi imran yace ki rabu da ita don Allah mum, idan sakin takeso ai saina saketa, shigowar Abba dakin ne tasa kowa yayi shiru.
Abincin aka zuba mata ta fara ci, imran ya kalli su Abba da mom yace Ku koma gda Ku huta tunda Nazo, sukace to Allah ya kara lpy yace amin. Mmn Fareeda sukayuwa sallama suka tafi, ta amsa tana wani basarwa. Likitan daya duba tane ya shigo sunanshi Dr james, bayan sun gaisa yace wa imran is she your wife? Yes iam d husband, OK iam very sorry, you lost d baby as a result of criminal abortion, be jira abinda imran zaice ba ya fice daga dakin, cikin tashin hnkli imran yace what? Criminal abortion? Innalillahi wa inna ilaihir rajuun, Fareeda why criminal? Wanne irin lefi nayi miki da har kika zabi ki zubar min da gudan jinina? Kinsan yanda na kwallafa raina akanshi kuwa? Haba Fareeda, duk wahar hanani bacci da risking kaina da nake nakaiki Asibiti acikin tsakiyar dare abinda zaki sakamin dashi kenan? Ya karasa mgnar yana kuka, zatayi mgna yace yimin shiru bana bukatar jin komai daga gareki, abinda kika aikata ya tabbatar min da cewa bakya sona, sbda haka kije na sakeki saki uku, wata mahaukaciyar kara tasa wadda ta razana su, amma imran bebi ta kanta ba ya fice daga dakin yana kuka. kuwa mmn Fareeda tunda taji likita ya ambaci criminal abortion tayi mutuwar tsaye, jin karar da yarta ta saka ne yasa tayi kanta da gudu, wani irin kuka Fareeda take tana cewa Allah yasa mafarki nake, idan da gaske imran ya sakeni to wallahi mutuwa zanyi, cikin tsananin bacin rai mamanta tace kinsan kina sonshi kika zubar da cikin? Ba kanki kadai kika cuta ba nima kin cuceni sbda gbdaya kin karya min budget, duk Wanda ya baki wanan grguwar shawarar ya cuce ki
Maman Aysha
[10:21, 9/4/2017] βͺ+234 803 681 8427β¬: ππ
Swanky lady safnaππ
1β£8β£5β£β1β£9β£0β£
Imran na fita daga Asibiti gdnsu ya wuce a falo ya sami su Abba da mom suna hira, ko sallama beyi musu ba ya shiga ya zauna, cikin fargaba Abba yace me kuma ya faru my son? Badai wani Abu ne ya sami Fareeda ba ko? Ba abinda ya sameta Abba, saidai iam sorry to say, na saki Fareeda saki uku, dauke shi da mari mom tayi, cikin masifa tace baka da hnkli ne? Yarinyar tana cikin rashin lpya zaka tashi ka saketa? Ambi an tsafe ka yanzu safna ce kawai me mutunci a idonka, ai dama nasan safna annoba ce a garemu to wallahi.... Abba ne ya katseta da cewa dakata da Allah, sanan ya kalli imran yace my son meya faru zakayiwa matarka saki har uku lkci guda, kuma akan gadon Asibiti? Sunkuyar dakai imran yayi yace Abba Fareeda criminal abortion tayi, kuma ni a iya sanina INA kokarin naga nayi mata duk abinda takeso, wallahi Abba ko shekaranjiya a Asibiti muka karasa kwana da ita, amma duk da haka ta zubar da cikin, mom ce tace sbda wanan Dan dalilin naka ne yasa kayi mata har saki uku? Abba ne yace you make a big mistake my son, ya kamata ace kayi shawara damu kafin ka yanke hukunci, annabi Muhammad SWA ya hanemu da yanke hukunci cikin fushi sbda haka karka sake ka kara irin wanan, cikin girmamawa yace insha Allah Abba, sanan Abba ya kalli mum yace ke kuma karna karaji kin sako safna ackin zancen, kuskure ne ya Riga ya tafka shi, saidai kiyi mishi addua Allah yasa haka shi yafi alkairi suka amsa da amin.
A ranar aka sallami Fareeda suka tafi gda, saidai tunda ta koma gda take kuka, yau kwana uku kenan ko abincin kirki bata ci, kullum acikin kwantar mata da hnkli mum din ta take, hnklin ta be kara tashi bama Saida Mimi ta kirata a waya tace gadar zare ta hada mata sbda tana bakin cikin ganin ta da imran a matsayin mijinta, bayan itama ta Dade tana sonshi, sabda haka tace gara duk su rasa
A bangaran imran kuwa wani nishadi yake ji sbda ya rabu da alakakai, wani irin so yake nunawa safna kamar zai cinyeta, Amma fa har yanzu be fada mata ya saki Fareeda ba, karya yayi mata yace sun tafi medical check up London. Matsalarsa daya yanzu rashin kuzarin safna, kusan kullum a kwance take yini kuma ba komai take ci ba, gashi taki yarda suje Asibiti, wani lkcn sai maryam ce take aiko musu da abinci, yauma kmr kullum a gajiye ya dawo daga office gashi kwanan baya cikin hayyacinsa sbda mum din shi ta matsa mishi ya saki safna, tace karya kara zuwan gdnta Saida takardar safna, gashi abbanshi baya nan yayi tafya zuwa chaina. yana shiga gdn ya sameta a kwance gefenta kuma basket din abincin da Maryam ta aiko mata ne ko bude shi batayi ba, dagota yayi ya kwantar akan cinyarsa cikin damuwa yace my angle meya faru naga bakici abincin ba? Cikin shagwaba tace inajin kamshin abincin naji bazan iya ci ba, ka samomin zogalai shi nake sha'awa, binta yayi da kallon tausayi yace yau kuma zugalai kike so? Tace eh, OK INA zuwa. Gdn umman ta yaje yace ta samo mishi zogalai, ya kaiwa safna, wani irin farin ciki ne ya kamata ta, godiya tayiwa Allah sosai, sedai bata bari imran ya fuskanci murnar da take ba. A makota tasa aka yago mata ta wanke ta dafa, Saida ta kwadanta mata sanan ta bashi yakai mata.
Yana kaimata ta faraci kmr mayya, ci tayi har yayi mata yawa tana gamaci taji amai ya taso mata, ta kofar kitchen ta fita bayan gda ta fara kwara shi, Saida duk abinda da taci ya zube, lkci guda ta zama restlessness mikewa tayi zata tafi wani mahaukacin jiri ya debeta, ta tafi luuuu zata fadi imran ya riketa da sauri, daukar ta yayi yasa a mota sai Asibitin get well, bayan lab investigation aka tabbatar mishi she is pregnant, faduwa yayi yai sujadda sbda tsabar farin ciki. Umman ta ya fara yiwa albishir, sanan ya kira abbanshi duk da baya gari ba karamin farin ciki yayi ba, sanan yayi addua sosai yace ayi mata sannu kafin ya dawo, Amma be fadawa mum ba sbda yasan ba zatayi farin ciki ba. Kafin kace me su umma dasu Maryam sun cika dakin duk an zagaye ta, Saida ta shanye ruwa Leda goma sbda yawan aman da take yasa ta zama dehydrated, kwanan su biyu a Asibiti aka sallame su, tun daga lkcn imran ya ninka caring da sonda yake ma safna, ji yake kmr ya hadiye ta sbda masifar so, ko wajen aiki ya dena zuwa sanan yasa an samo mata yara guda biyu masu yi mata shara da wanke kwanuka
1 month later
Ba lefi safna ta fara murmurewa domin kuwa yanzu da kanta take girki. Su Fareeda sunje sun kwashe kayan su, sai yasa aka sakewa gdn sbon fenti, sanan yayi order furniture's daga America, ya nemo interior decorators suka gyare mishi gdan to his own test, komai da kuka Sani na amfanin gda sabo akasa har kayan kitchen, wato me kartu fadin kyau da tsaruwar da gdn yayi abin baa mgna, gashi dai kayan millions of naira aka jerawa Fareeda, Amma ko quarter din yanda gdn ya koma yanzu bekai ba.
Da daddare yaje Gdansu yana zuwa yaji gdn shiru sai kanwar mom aunty badia da yaranta kadai ya samu a zaune, suna kallo, cikin murna yace aunty na yaushe a gari? Dake a Italy suke zaune da mijinta, wallahi dazu mukazo my son, haneef ne yaje da gudu ya rungumeshi, aikuwa imran ya dagashi sama ya manna mishi kiss, yana dariya yace nayi fushi gsky, yanzu da banzo ba shekenan sai gobe zan San kunzo kenan? Dariya tayi tace surprise dinka naso nayi ai, OK ina mom? Tana daki tana salla.
Zama yayi sunata hira da aunty badia, har dare ya fara mom bata fito ba, mikewa yayi ya nufi dakin saiyaji kofar a rufe, dawowa falon yayi yace wa aunty badia inajin fa tayi bacci, kai batayi bacci ba gskya sbda tasa lami ta dafa mata ruwan zafi zatasha green tea, OK to bari na kirata a waya, kiran na shiga ta dauka cikin fushi tace indai ba takardar safna ka kawo minba ka tafi bana bukatar ganin ka, zaiyi mata bayani ta kashe wayarta, Saida yayi mata kusan 12missed call amma bata dauka ba, ji yayi zuciyarsa ba dadi, idonsa ya kada yayi ja, kallon aunty badia yayi yace nizan tafi gud nyt, yasa kai ya fice daga gdn
Maman Aysha
[10:48, 9/4/2017] βͺ+234 803 681 8427β¬: ππ
Swanky lady safnaππ
1β£9β£0β£β1β£9β£5β£
Tuki imran yake amma Sam hnklin shi baya jikinshi tunani ne ya cika zuciyarsa meyasa mum ta tsani safna much, yasan talakawa sunyi betraying dinta, Amma kuma ai kowanne mutun da irin halin shi, bazai yiyyu ace duk wani talaka halin su daya ba akwai masu wadatar zuci kuma akwai masu rikon amana, to yanzu ya zaiyi kenan? Safna ce rayuwata, itace komai nawa gsky bazan iya sakinta ba, to amma ya zanyi da mum kenan? Dole ne kabi umarnin mum indai kanason ka gama da duniya lpya, zuciyarsa ta bashi amsa, innalillahi wa inna ilaihir rajuun, ya Allah kafi kowa sanin halin da nake ciki, idan har Baban safna yana nan da ranshi Allah kayi gaggawar bayyana mana shi daidai nan yayi packing ya fita. Safna na kwance akan 3seater sanye cikin wata red armless sleeping dress tana jiran dawowar imran, sai taji ya bude kofar ya shigo, ba tare da ya kalli inda take ba ya wuce part din shi, mikewa tayi tabi bayan shi da sauri, tana zuwa ta sameshi a kwance akan gado ya Dora hannunshi a kanasa. Gadon tahau ta dauke hannun, ga mamakinta saita ga hawaye yana zuba a idonshi, janye filon tayi ta mayar da kanshi bisa cinyarta, cikin cool voice tace sweet man meya faru? Beyi mgna ba saita tallafo fuskarshi ta fara shafa gashin kansa a hnkli, cikin wata golden voice tace nasan be zama dole ka fadamin abinda yake damun ka ba, amma don Allah koma meye kayi hakuri ka mikashi ga Allah, kayi adduar Neman zabin Allah nasan insha Allah zai yaye maka koma meye, so don Allah stop crying ta karasa mgnar tana lashe hawayen da harshen ta, romancing din shi take a hnkli tun yana basarwa har ya biye mata, nan take ya nemi baci ran da yake ya daina.
Washe gari bayan sunyi break yace yau zamu tashi daga gdn nan, Saida ta fara ido sanan tace ina zamu koma? Gdana na GRA, tro baki tayi ni gskya bazan iya zama gda daya da aunty Fareeda ba, zamana anan yafimin kwanciyar hnkli, wa ya fada miki da Fareeda zaku zauna? Ke kadai zaki zauna sai masu aiki dazan karo miki, to ita aunty Fareeda Ina zata koma? Saida ya sassauta murya sanan yace na saki Fareeda fa, harta kwashe kayanta, salati safna ta saki, cikin rashin jin dadi tace meyasa? Kai lalle na yarda maza basu da adalci, duk irin son da aunty Fareeda take maka? Kama hannunta yayi yace relax safna, zauna na baki lbrn abinda tayi min, from A to Z ya bata lbri ammafa duk da haka safna bata goyi bayan shi ba domin kuwa taji abin har cikin zuciyarta.
A ranar ya tayata suka hada duk abinda suke bukata daga wanan gdn ya debesu ita da masu aikinta marwa da zawaira suka tare a sabon gda da zamu iya kira da aljannar duniya.
2 days later
Labari ya jewa mum cewa imran ya tare da safna a sabon gda, ai kuwa da yamma ta shirya takai musu surprise visit, tana shiga gdn taji shiru, masu aiki sun gama sharar yamma sun koma side din su, an saka turare gidan sai buga kamshi yake, karewa gdn kallo tayi taga ko ina neets ga wasu hadaddun furniture's gdn kmr a turai, a zuciyarta tace lalle yarinya ta sami duniya dole ta kara daura belt wajen tsafe min da, Amma zataci ubanta domin kuwa ya zama dole yau tabar gdn nan.
Steps tahau ta nufi part din imran, tana bude kofar falon kamshi da sanyin A/c ya daketa, ita kanta mum tasan the different is very cleared btwn safna and Fareeda, take gskiya kawai take. Imran yana kwance akan Capet ya jingina da wasu hadaddun toror pillows, yana sanye cikin wani hadadden tissue yard cream color, ita kuma safna ta fito daga kitchen din falon hannunta dauke da tray din shawarma, paper chicken da kuma jug din kunun aya me kwakwa da madara zata kaiwa imran kawai suka ga mum ta shigo, zumbur imran yayi ya mike, cikin faduwar gaba yace sannu da zuwa mom, bismilla ga waje zoki zauna, binshi tayi da kallon so irin na da da mahaifi, gani tayi ya kara kyau ya kara haske, yau kusan 2wks kenan batasashi a idonta ba, tanacan ko baccin kirki bata iyayi sbda tunanin shi, Amma shi yana nan yana rayuwarsa hnkli kwance, cikin kakkausar murya tace ba zama nazo yi ba, kallon kwayar idonshi tayi tace my son Ashe dama akwai ranar da zaka gujeni? Ashe akwai ranar da zan baka umarni kaki bi? Kenan ka tabbatar min kafi son wanan tsinanniyar matar taka akaina ko? Ta karasa mgnar tana kuka, zuwa yayi ya riketa ya zaunar akan kujera, sanan ya fara goge mata hawaye, wallahi mum ba haka bane duk duniya ba wacce nakeso kmr ke kum.......dakata, idan har da gaske kake inaso ka saki safna yanzu nan? Saida ya hadiye wani yawu me daci sanan yace shikenan mum na amince zan saketa amma ki fadamin meyasa kika tsaneta? Sbda talaka ce, kuma talakan ma Yar masu aikin wani gdn, kafi kowa sanin ha'incin da masu aiki sukayi min. Na Sani mom, Amma ai ba safna ce tayi miki ba, kuma suma Wanda sukayi mikin sun rokeki gafara kin yafe musu, itama ya kamata ki sassauta mata, idan na sassauta mata asali fa, ko Kasan asalinta ne? Nayi bincike akan mahaifiyar safna ita kanta bata da kowa, domin kuwa mahaifinta korarta yayi sbda abin kunyar data jawo mishi, Abu ne me wahala idan safna tanada uba, a yanzu haka zancen da nake maka basu da