LADY SAFNAH COMPLETE HAUSA NOVELS BY MAMAN AYSHA.txt

Author :  Maman Aysha Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   4 / 15

9K to 12K   out of 43.3K words

9/3/2017] β€ͺ+234 803 681 8427‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady SafnaπŸŽ‹πŸŽ‹

5⃣5βƒ£βž–6⃣0⃣

4pm kowa ya shirya, matar da aka dauko daga Sudan ce tayiwa safna make up, wata hadaddiyar gown din material tasa Dan wajen 150k red and golden, ta Dora golden head, ceremonial shoe and bag ma golden, da wasu hadaddun costume suma golden, wato me kartu duk Wanda ya kalli safna saiyaji ya kara kallonta koda kuwa makiyinta ne sbda kyaun da tayi bana wasa bane, kowa yayi imagining kawai.

Friends din safna da sukayi excel college dukansu sukazo, suma Wanda suke BUK tare su wato su Bilkisu duk sunxo, sunsha ankon lace blue and silver, su kuma salma da Maryam ankonsu sukayi su biyu na wani lace pink and blue, suma ba karamin kyau sukayi ba. Manyan motoci aka kawo suka ringa diban mutane zuwa wajen events din dake mmn Maryam tayi gayyata sosai.

Tun wajen 5pm amarya taje cikin venue din wato Meenat events centre, saidai har yanzu ango bezo ba, kuma ba alamar zaizo domin kuwa salma tanata kiran phone dinshi yaki dauka, shima sadik yanata kiranshi yaki dauka, ita kuma safna tana zaune a motar sadik dake tinted glass ce kuma A/c a kunne take.

Can na hango umma Jidda wato mmn amarya tasha wani lace Dan 50k ta Dora head tayi kyau saikace safna kanwarta ce Sbd tanada kyaun jiki, saidai kallo daya zakayi mata ka gane tana cikin damuwa sbda sun Tara jama'a gashi har yanzu amarya da ango basu shiga hall din ba, mmn Maryam ce tazo Maryam ya ake ciki ne Maryam? Kaddai Dan iskan yaron nan bazaizo ba? Maryam tace wallahi tun dazu muke kiranshi amma yaki picking, ni mama INA ganin kawai mu shigar da safna ita kadai muyi bikinmu, amma kuma Maryam ya zaayi ace muyi biki ba ango? Gasky abin yayi wani iri, kudai kara kiranshi amma wanan Yaro bashida mutunci.

Bude motar Maryam tayi tana shiga ta samu safna tayi kuka harta gaji gabadaya kwalliyar ta baci, cikin shessheka tace Maryam meyasa kuka fadawa mutane da ango zaayi program din? Da kunyi shawara dani da bakuyi ba, sbda nasan kiyayyar da imran yake min bazata bari yazo nan ba, INA ganin kawai a hakura da auran nan Maryam, inaso kuje Ku sallami kowa Ku fada musu cewa anfasa auran idan kuma Baku fada ba zanje na tarwatsa taron da kaina, cikin daga murya tace Maryam kuje mana, riketa Maryam tayi tace kar bacin rai yasa mu zama mahaukata mana, idan mukayi haka ai mun wulakanta kanmu, tunda bezo ba kawai bari na kira hjyn Sudan tazo ta kara gyara miki kwalliyarki saimu maze ki shiga kawai, rike hannunta safna tayi tace kiyi yadda nace kawai Maryam, ai dama ni wulakantacciya ce, ki duba fa ki gani duk yawan Mutanen da suke wajen nan ba dangin mahaifina, kuma ba yan uwan umma ko daya anan sbda ta aika musu sunki zuwa, wacce irin rayuwa ce wanan? Amma kinsan idan ummanki ta fuskanci akwai wani Abu zaa samu matsala ko? Ai gara a samu matsar, gara dagani har ita mu mutu mu huta, duk duniya kuda baba Sharif ne kawai kuke sonmu, wanan wacce irin kaddara ce? Wallahi Maryam na gaji da rayuwar duniya...... Sauri Maryam tayi ta rufe mata baki karki yi sabo safna idan kika fadi haka kina jayayya da hukuncin Allah kenan, don Allah ki nutsu Ku dena kuka INA zuwa, fita tayi daga motar ta kira hjyn Sudan dakyar safna ta hadiye kukanta aka kara yimata kwalluyar suna shirin fito da ita daga mota kenan saiga wasu hadaddun motoci guda biyar sun shigo ajire, da gudu securities sukazo suka bude mishi mota wani shegen boyel ne ajikinshi maroon kudinshi zaikai 200k ya Dora wata shegiyar zanna bukar, sanan ya manna farin glass a idonsa, hannunshi kuma daure yake da wani hadadden agogon axurfa da Ku dinshi zaikai 300k, yana fitowa daga mota gabadaya hnklin yan matan da suke tsaye a gefe yayi kanshi, da sunata gulma amma suna ganin shi suka firgice, wata daga cikin friends dinta na excel college ne tace shegiya safna wato kyau da gayunta be tafi a banza ba domin kuwa ta samo Mijin daya dace da ita.

Body guards dinsa ne suka sashi a tsakiya yana wani tafiya ta takama idan ka ganshi saikace sultan of sokoto ne, bakin motar da safna take suka nufa suna karasowa su Maryam suka fito da ita suna hada ido zuciyarsu ta buga a lkci guda, saurin kawar dakai dukansu sukayi, sanan friends din amarya suka shige gaba su kuma body guards dinsu suka Mara musu baya suna shiga kowa ya mike aka saki wata waka me dadi har saida amarya da ango suka zauna a mazaunin su, sanan kowa ya koma ya zauna.

Wato me kartu ko makiyi idan ya kallesu yasan sun dace, saidai hassada tasa suki fada.

Ba bata lkci aka fara program, an fara bude taro da addua sanan mom din Maryam tazo tayi well coming mutane, sanan aka bukaci familyn amarya dana ango su fito ayi kamu, 200k kanan mum din imran suka bayar sanan akayi kamu. Daga nan aka kira amarya da ango su fito fili su tsaya nanfa mutane suka ringa zubar da kudi Nura M inuwa ne yake cashewa a wakarshi ta amarya Yar amana, yana ganin ruwan kudi ya kara gigicewa bayan sun koma sun zauna aka kira kawayen amarya ma suka cashe, haka aka ringa casu maikatan Meenat ne suka fara raba hadadden varieties na abincin da akayi dake su aka bawa contract din sukayi, kuma duk taron ba Wanda be ci ya basshi ba nama kuwa kmr banza, su Kansu Aunties din imran abin ya burgesu ba sbda basu taba zaton zasu ga haka ba dake an riga ance musu Yar talakawa ce.

Sai wajen magrif taro ya watse, cikin farin ciki , domin kuwa inba Wanda suka Sani ba bame cewa akwai matsala. Mota daya amarya da ango suka shiga, su suna sit din baya shi kuma Sadik Sadik da Maryam suna gaba.

Tunda suka shiga ba wanda ya kula wani, su kuma su Sadik suna gaba suna hirar su ta soyayya. Fareeda ce ta kira imran a waya nan take ya sassauta unique voice dinshi yake mata mgna rarrashinta yake yana bata hakuri sbda da yace bazai je wajen bikin ba kuma yaje, lovingly yace haba Fareeda in banda abinki meye na damuwa, ni wanan ai ba aure na dauke shi ba, kinsan bikin Yar tsanada yara sukeyi? To wanan auran bashi da banbanci da irinsa, nabi umarni Abba ne kawai amma a yanzu ba digon son safna a zuciyata kuma nayi miki alkawari very soon zan saketa so nake kawai kurar ta lafa, INA auran ki zan saketa. Tunda ya fara rashin mutuncinsa safna tana jinshi Amma ko kallon iskar data deboshi batayi ba ana zuwa kofar gdnsu Maryam ta bude mota ta fita, ko sallama batayi wa Sadik ba, Maryam na ganin haka tabi bayanta da sauri, shi kuma imran ya koma gaba suka tafi





Maman Aysha
[23:03, 9/3/2017] β€ͺ+234 803 681 8427‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady SafnaπŸŽ‹πŸŽ‹

6⃣0βƒ£βž–6⃣5⃣

Tana shiga compound din gdn ta durkushe akasa tana wani irin kuka me ban tausayi Maryam ce tazo ta dagota part din kaninta Faruk suka shiga dake bayanan, suna shiga safna ta fada kan gado taci gaba da kuka zama Maryam tayi ta fara bata hakuri tana mata nasiha har saida ta ware ta dawo normal sanan suka koma part dinta inda sauran friends dinsu suke gasassun kaji da drinks Sadik ya saya ya kawo musu anaci ana harka safna kuwa yake kawai take, dakyar Maryam ta takurata taci naman kadan, sai iskanci sukewa safna wai tunanin imran ya hanata sakat gobe de zaa kaiki kowa ya huta, wasu daga ciki sukace karku takura mata ai ita tayi kokari ma idan nice na samu miji kmr imran ai nizan kai kaina, ai gsky safna mijinki yayi muma Allah ya samu a danshinki murmushi kawai safna take amma a Kasan zuciyarta ita kadai tasan abinda yake damunta. Da wuri safna ta kwanta su kuwa su Maryam saida suka kai wajen karfe daya suna hira sanan suka kwanta.

Washe gari wajen 11am aka daura auren safna da imran akan sadaki naira dubu dari, daurin auran ya tara jamaa da yawa shi kansa imran ba karamin mamaki yayi ba, be taba zaton anyi inviting mutane haka ba.

Tunda gari ya waye safna taji gabnta yana faduwa, ji tayi tana bukatar kebewa waje daya, saita karbi key din dakin Faruk ta koma can ta kulle kanta ta kunna A/c ta kwanta, tana cikin bacci taji anata busa algaita da kade kade a gdn daidai nan Maryam ta knocking safna taje ta bude mata wata matace ta rangada guda tace an daura, nan take bugun zuciyar safna ya karu sulale wa tayi ta fadi sumammiya A gigice Maryam ta dagata ta kwantar a tsakiyar falo, sanan ta bude fridge ta dauko ruwa ta yayyafa mata wata ajiyar zuciya safna tayi sai kuma ta fashe da wani irin kuka shekenan Maryam na jefa kaina acikin matsala, najefa kaina acikin masifa wuni tayi ranar tana kuka cikin kankanin lkci zazzabi ya rufeta salma Maryam tayiwa waya tazo tayi mata allura da magunguna nan take bacci me dadi ya dauketa, bata farka ba sai wajen azahar toilet ta shiga tayi wanka ta shirya cikin wani purple lace yayi mata kyau sosai. Da yamma dad din Maryam da baba Sharif da kuma umman safna da mmn Maryam suka kira safna sukayi mata nasiha me ratsa jiki.

Karfe takwas salma da aunties dinta sukazo daukar amarya, haka aka fito da safna tana kuka tana komai aka tafi da ita gdnsu imran aka fara kaita abban imran yayi mata nasiha da addua sosai sanan aka dunguma zuwa gdnta dake badawa lay out, bayan yan kawo amarya sun gama ganin gdn aka debesu aka mayar dasu gda. Kawayen amarya ne suka ki tafya sukace sai ango ya basu kudin budar baki.

Suna zaune suna hira sai gasu sun shigo shida su Sadik bayan sun Dan taba hira anyi barkwanci imran ya basu 200k na budar bakin amarya sanan friends dinshi suka daukesu suka tafi dasu gdjensu, dakin ya zama daga safna sai imran

Kallon ta yayi yace tunda sun tafi ai seki bude fuskar ko? Budewa tayi tana dagowa suka hada ido cikin unique voice dinshi yace burinki ya cika an daura mana aure saidai inaso kisani kin tafka babban kuskure a rayuwar ki, kin karyamin budget dina kuma wallahi saina fanshe bacin ran da kika samin, 'Yar me da bakin nacin tsiya, kallon kwayar idonshi tayi tace idan kana tunanin har yanzu INA sonka to kayi kuskure, mugayen halayen ka sunsa nima na tsaneka, Sbd baka da kirki, baka da tausayi kuma baka yafiya, Allah ma muna mishi lefi ya yafe mana, meyasa kai bazaka yafemin ba? Meyasa ko kadan baka tausayina? Dama sonda ka nuna min na karya ne ko? Ta karasa mgnar tana wani irin kuka ji yayi hnklin shi ya tashi gabadaya zuciyarsa ta karaya, wani mugun sonta yaji ya dawo mishi sabo, kawai saiya juya ya fice daga gdn. Yana fita gdnsu ya wuce ya kira salma a waya yace taje ta taya safna kwana shi kuma ya wuce wajen sadik




Maman Aysha
[23:03, 9/3/2017] β€ͺ+234 803 681 8427‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady SafnaπŸŽ‹πŸŽ‹

6⃣5βƒ£βž–7⃣0⃣

Yana dab da zuwa kofar gdnsu Sadik sai salma ta kirashi tace hlo yaya Abba ya hanani yace sbda banida hnkli zanje gdnka na kwana, cikin jin haushi yace meyasa kika tambayeshi zaki fita? Ba tambayar sa nayi ba, harna shiga mota zan tafi ya hangoni ya tsaidani, is OK gud nyt, tace OK nyt.

Zama yayi yana tunani a mota, kenan dole saina koma na kwana acan? Ko kuma kawai na kyaleta ta kwanta ita kadai ba, ai ya zama dole ma ta koyi kwana ita kanne domin kuwa duk ranar Dana auri Fareeda nayi sallama da gdnta, harzai yi horn megadi ya bude mishi sai kuma ya tunu yanayin daya barta, kawai sai yayi ribas ya koma megadi yayiwa mgna ya bude mishi yashiga, sanan yasa key ya bude kofar falon corridor dazai sadashi da part dinshi na gdn yabi ya shiga.

A bangaran safna kuwa ta Dade tana kuka bayan imran ya tafi, saida tayi me isarta sanan ta mike ta shiga toilet tayi alwala ta fito, sallar isha'i tayi sanan ta Dora da nafila raka'a 8, tayi shafa'i da wutri, ta Dade tana addua tana fadawa Allah kukanta, akan Allah ya bayyana mata mahaifinta duk inda yake, sanan Allah yayi mata zabin abinda yafi alkairi a zamanta da imran haka tai tayin addua tana kuka, akan sallayar bacci me nauyi ya dauketa bata farka ba sai asuba ta tashi tayi sallar asuba sanan ta koma kan gado ta kwanta. Sai wajen 9am ta tashi, ji tayi tanajin wata masifaffiyar yunwa cincin dasu dublan din gara ta diba ta faraci bayan ta gama ta dauki tsintsiya ta fara Shara, saida ta share ko ina tayi moping har corridor din part din imran, saidai data taba kofar falon saitaji a rufe, tunani ta shiga yi to nan din inane? Sbd su Maryam ma dasukazo Jere sunce a kulle suka samu kofar, kuma basu gane meye awajen ba sbda basu jera komai acikin wajen ba, tabe baki tayi tabar gun. Turaren wutar ta me kamshin gaske Dan Sudan ta dakko ta kunna, nan take gda ya dauki wani irin kamshin dadi, toilet ta shiga tayi wanka ta shirya cikin wata yellow java Holland Riga da siket, zama tayi ta tsantsara kwaliyya tayi dauri mekyau, tasa sarka da dankunne masu kyau, sanan tayi wanka da turare. Kitchen ta shiga ko zata samu abinda zata dafa taci, amma saita ga ba komai sai kayan garar ta da aka jera wato buhunhunan shinkafa, semovita, cartons din taliya, macaroni da maggi, da indomie da crate's din kwai da sauran su kato ne store din amma saida aka makareshi da kaya, addua tayiwa baba Sharif da kuma mmn Maryam da Allah ya sadasu da gdn aljanna domin kuwa abinda sukayi mata ko Maryam iyakaci kenan.

Daki ta koma ta kwanta banda jiri ba abinda take ji sbda tunda aka fara hidimar biki bata samu taci abinci ba.


Imran kuwa bayan ya dawo daga sallar asuba komawa yayi ya kwanta be farka ba sai 9:30, waya yayiwa mom din shi yace ta aiko mishi da break fast, sanan shima ya shiga toilet yayi wanka ya shirya cikin wata gezna me tsada coffee color yayi wanka da turare sanan ya bude laptop dinshi yana wani aiki acikin

Har bacci ya fara daukarta saitaji alamun ana buga kofar falo, mikewa tayi ta dauki key din ta nufi kofar, tana budewa taga mutun da basket din food flaks din abinci a hannunshi, saida ya rusuna ya gaisheta sanan yace hajya ce tace a kawo muku wanan, ya mika mata basket din karba tayi tace to kace angode, maida kofar tayi ta rufe sanan ta nufi dakinta da abincin, ta juya ta fara tafiya kenan saitaji daga bayanta ance dalla tsaya ....wani irin firgita tayi, a razane ta juyo sbda bata taba tunanin akwai mutun a gdn ba ajiyar zuciya tayi cikin yanayin shagwaba tace harka bani tsoro wallahi, binta yayi da wani mayataccen kallo sanan yace, is true bakisan INA nan ba, amma kuma kunsan bakida matsayin da zaa aiko miki abinci daga gdnmu ko ? So yakamata ki tambayeshi abincin waye for d first time daya miko miki, sbda kunsan mom dina bazata bata lkcnta a aiko miki abinci ba, ko kin manta cewa kema kuku ce? Mgnar ta bata mata rai amma saita basar tace meyasa kake ganin bazata aikomin abinci ba? Ai ko kwasar kashi nake karewar kuku yanzu a matsayin matar danta nake, kuma Dan tayiwa matar danta abinci taci ai ba lefi bane ko? Ta karasa mgnar tana wanu shu'umin smiling, dauketa yayi da mari har guda biyu, sanan yace idan kika kara kiran kanki a matsayin matata saina karya ki stupid girl kawai, kallon kwayar idan shi tayi tace baa canjawa tuwo suna ko kaso ko kaki ni matarka ce, so tunda kana ganin hakan a matsayin abin kunya ka bani takardata yanzu nan kaga sai hnklin kowa ya kwanta, ai basai kin fada ba idan lkcn yayi zan sakeki, yanzu zanci gaba da zaman kaddara dake har zuwa lkcn da zan auri muradin raina kuma class dina, sanan ya dauki basket din ya shige part dinshi kujera ya samu ya zauna zuciyarsa banda zafi ba abinda take, dafe kanshi yayi, ya Dade a zaune yana tunani anya safna mutun ce kuwa? Wanan wane irin bala'i ne? Kullum kokarin yakice ta nake a zuciyata amma abin yaki, meyasa na kasa cireta a zuciyata? Anya kuwa ba asiri take min ba? Ya zama dole na dage da azkar, kuma zansa asamomin mgnin karya suhiri, dayar zuciyar ce tace kumafa da gamida kana zaune gda daya da ita, idan kayi aure ka dauke kafarka a gdn nan da wuri zaka manta da ita, smiling yayi sanan ya bude abincin ya faraci. Dayaci ya koshi memakon ya bawa safna kawai saiya dauka ya kaiwa baba megadi.

Safna kuwa daki ta shiga ta fara kuka me tsuma zuciya, ji take kmr ta kira abban imran a waya tace ya fadawa imran ya saketa, sai kuma tayi tunanin yin haka zaisa Abba ya ringayi mata kallon marar tarbiya. Haka taci gaba da kuka aikuwa ta farajin sanyi, bargo ta dakko ta lulluba wajen azahar salma da Maryam sukazo gdn suna ta buga kofa shiru acikin bacci safna ta jiyo bugun kofar ta mike dakyar ta bude musu dakyar ta karasa kan kujera ta kwanta hada ido sukayi suna zargin ko wani abu ya faru ne sbda sunga yanda yake ta wani nuna mata caring agabansu jiya, su duk tunanin su ko ya janye mummunar akidarshi basu San haryanzu yana nan akan bakanshi ba. A tare sukace safna lpya? Wallahi banida

4 / 15