LADY SAFNAH COMPLETE HAUSA NOVELS BY MAMAN AYSHA.txt

Author :  Maman Aysha Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   14 / 15

39K to 42K   out of 43.3K words

masauratar Alexandria, kuma Sarki me jiran gado.

Ba karamin farin ciki Ummina, da yan uwa da abokan arziki sukayi ba, ita kuwa hajja safiyya muna hada ido da ita ta haukace, kuma har yau bata sami lpya ba. Bayan na koma gda da wata biyu aka tabbatar dani a matsayin me girma sarkin Alexandria, a inda na Dora da halin kirki da kuma tausayin talakawa akan na mahaifina.

Wani Abu da yake daure min kai shine inaji ajikina nayi rayuwa a wani waje, nayi aure na haifi 'ya me kama da mahaifiyata amma na Kasa tuna a wanne gari ne, INA kokarin na takurawa brain dina kozan tuna, Dana fara sai kaina ya dauki zafi saina fara wani irin ciwon kai kmr zai fado Kasa,kuma a haka na ringa rayuwa. Da abin ya isheni saina bawa Ummi lbri tasa aka ringa yimin taimako amma INA, koda wasa na Kasa tunawa, wanan dalilin ne yasa Ummina ta hadu da hawan jini, domin kuwa bata da wani buri a duniya daya wuce taga matar da nace na aura da kuma Yar da muka Haifa me kmr ta, kuma gashi na Kasa tunawa.

Dakyar aka Sani nayi aure sedai a haihuwa matar ta rasu, kuma tun daga ita ban kara aure ba. Kamannin da safna take da mahaifiya shine ya dawo min da memory na daya gushe 16yrs ago. Kallon Mutanen falon yayi yace kunji abinda ya faru



Maman Aysha
[10:50, 9/4/2017] β€ͺ+234 803 681 8427‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady safnaπŸŽ‹πŸŽ‹

2⃣1⃣0βƒ£βž–2⃣1⃣5⃣

*T *W * F*

Umma ce ta sauke ajiyar zuciya tace Allah me iko, Ashe kai jinin sarauta ne shiyasa 'yarka ta ringa bani wahala, INA kokari na nemi kudi domin mu rufawa kanmu asiri, amma Dana bata saita kashe su, alhaji Sharif ma duk wata 50k yake bata kudin motar zuwa sch, amma ko sati biyu ba yayi take kashe su, tun tana yarinya bata da aiki sai Neman gwaninta, jiji dakai dason nunawa jamaa ita Yar wani ce, bayan kuma mu ba kowa bane idan nayi mata fada sai tace wai itama batasan tanayi ba, kawai dai tana tsintar kanta a hakane, Ashe kuwa da gaske take jinin sarauta ne yake aiki a jikinta. Dariya suka sa gabadaya har me girma sarkin Kano, sanan Abii yace yanzu kowa saiyaje ya huta, idan Allah ya kaimu gobe ana daura aure zamu tafi Alexandria gabdayanmu, suka amsa da Allah ya kaimu, kallon me girma San Kano yayi yace ranka ya Dade kaje kawai niyau anan zan kwana, dariya sosai San Kano yayi, sanan suka fita har bakin mota suka raka me martaba Sarki ya tafi, sanan Abba da alhaji Sharif sukce your Highness muma zamu tafi, smiling Abii yayi yace to shikenan Allah ya tashemu lpy sukace amin gaban imran sai dukan Tara Tara yake yana tsoro kar Abii yace mishi ya bar safna ta kwana
a wajen su, domin kuwa ya riga ya sangarce baya iya bacci ba tare da safna tana jikinshi ba.

Kowa ya watse gdn ya rage daga safna da imran sai umma da Abii, Ummi Abii ya kira a waya bayan sun gaisa ya fada mata yaga matarsa da yarsa, rasa inda zata tsoma ranta tayi don murna, sanan ya hadasu suka gaisa har imran, amma da harshen turanci domin kuwa batajin Hausa, sanan ya fada mata gobe suna nan zuwa. Sabuwar hira suka bude, safna tana kwance ajikinshi da imran yaga abin nasu bana kare bane saiya mike jiki a sanyaye yace Abii nima zan tafi Saida safe cikin rashin daukar haske Abii yace ok my son Allah huta gjya, umma ce tayi saurin cewa safna tashi kibi mijinki Ku tafi, Abii ne yace nayi zaton ya barta ne ta kwana, tunda gobe zamu tafi gda, umma tace ah ah ya tafi da matarsa gobe sa dawo, shagwabe fuska safna tayi tace nifa anan zan kwana, umma tace idan baki tashi kun tafi ba ranki zai baci, rarrashinta abii yayi ba tare da ransa yaso ba yace my dota gud nyt, Sbd shima yana son kasancewa da yarsa dande ba yanda zaiyi da umma ne, sanan yayi kissing dinta a kunci suka tafi. Suna fita umma tace me zakaci yanzu na dafa maka, janyota jikinshi yayi yai hugging dinta yace ke kadai nakeso yanzu, I miss you alot jiddat, ban taba zaton zan kara haduwa dake a gdn duniya ba, smiling umma tayi tace I miss you too your Highness, shafa kanta ya fara yi a hnkli, INA ganin haka saina fice daga gdn nabi su imran

Har suka karasa gda ba Wanda yayiwa wani mgna, cool music ne yake tashi a motar suna shiga kowa ya wuce dakinshi yayi wanka imran ne ya fara fitowa falo ya zauna sanan safna ma ta fito tana zuwa ta Dora kanta akan cinyarsa cikin muryar shagwaba tace iam so happy today, tunda nake a duniya ban taba shiga farin ciki irin nayau ba, yana shafa gefen fuskarta yace yah ai naga alama, Sbd murnar ganin Abii har ana Neman a guje min, bayan kuma kinsan bana iya bacci ba tare dake ba, dariya tayi tace 'Yar kara nayiwa Abii sbda naga bayaso na tafi, amma wallahi da bamu taho tare ba bazan iya bacci ba, tashi tayi ta zauna ta kafeshi da kyawawan idanuwanta tace INA sonka yaya imran, da ace ka sakeni da bansan inda zan saka raina ba, kaga shikenan yanzu mutuwa ce kadai zata rabani dakai, ba wani sauran fargabar zamu rabu, Allah yasa ni zan rigaka mutuwa, toshe mata baki yayi da hannunshi yace stop it, ya muna cikin farin ciki kina min zancen mutuwa, zatayi magana ya fara romancing dinta, dakyar suka mike suka nufi dakinta, tsayawa safna tayi cikin shagwaba tace ni gaskiya sedai ka dauke ni bazan iya tafya ba, kuma a dakinka nakeso na kwana, smiling din da yake kara mishi kyau yayi yace angama my princess, turo baki tayi tace princess kuma? Daga mata gira yayi at d same time yana murmushi yace yes princess, kinsaan sarauta ba karya bace, sanan ya dauketa kmr Yar babe ya haura da ita part dinshi



Maman Aysha
[10:51, 9/4/2017] β€ͺ+234 803 681 8427‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady SafnaπŸŽ‹πŸŽ‹


2⃣1⃣5βƒ£βž–2⃣2⃣0⃣


*T *W *F*

Washe gari bayan his Royal Highness yayi break suna zaune suna hirar soyayya da umma yace ni kuwa kun shirya da mahaifinki? Cikin sanyin jiki tace aa, aidama kai kace zamuje, kuma sai kazo ka bata, ni kuma INA tsoron komawa garin da safna sabda zasu iya cewa da gaske cikin shege nayi, shiyasa kawai naci gaba da zamana anan, shiru ya danyi sanan yace ki shirya INA dawowa daga daurin aure sai muje wudil din tace to.

Imran ne yazo ya dauke shi suka tafi, ana gama daurin aure ko reception his Royal Highness be tsaya ba suka taho gda mota biyu sukayi suka nufi wudil, dakyar umma ta gane gdnsu sbda gabadaya unguwar ta sauya kuma gdnsu ma an rushe anyi ginin zamani mekyau, ita da Safna ne suka fara shiga ciki wata mata ta gani a zaune tana tsifar kayi, bayan sun gaisa tace don Allah ina inna tabawa? Wai tabawa ai ta Dade da rasuwa cikin faduwar gaba tace to INA baba? Wata matace ta leko daga wani daku suna hada ido tace wa nake gani kmr Jidda? Nice inna mero, INA baba? Alhamdulilla shikenan yau rashin lpyar yaya ta warke, Jidda dama kina nan da ranki? Ina kika shiga akayi cikiyarki har aka gaji? Wani daki ta shiga da sauri tace yaya tashi Allah ya amshi adduar mu yau ga Jidda a gdn nan, rarrafo wa yake kokarin yi umma ta tafi da gudu ta rungumeshi, kuka suke sosai safna na ganin haka ta fita ta shigo dasu Abii a falo suka zauna sanan Jidda ta kamo baba ya fito dakyar, cikin kuka yace Jidda ki yafemin sbda nayi miki mummunan hukunci akan abinda baki aikata ba, ko kadan banyi miki adalci ba ya kamata ace nayi bincike tun lkcn da abin ya faru, amma saina gagara yin hakan na yanke hukunci acikin fushi bayan kuma manzon Allah SAW ya hanemu da yin hakan, kuma koda ace da gaskene kin aikata ya kamata na zama me yadda da kaddara, amma saina kasa yin haka, nayi nadama a rayuwata sosai, cikin farin ciki tace yanzu kana nufin ka gano cewa ban aikata abinda kuke zargina dashi ba? Kwarai kuwa, Jidda tace alhamdulilla Allah nagode maka, amma ya akayi kuka gane? Tun bayan tfyarki na shiga tashin hnkli marar misaltuwa, kullum acikin kuka da nadama nake, dakyar na gano cewa sunan matar data tafi dake da naje nemanta sai aka fadamin Allah yayi mata rasuwa, ba karamin bakin ciki naji ba Dana tambayi yaranta ko sun Sanki sai sukace sun taba jin lbrnki a wajen ta Amma yanzu basu San inda zasu sameki ba, haka na dawo gda naci gaba da jinyar rashinki.


Shekaru uku da suka wuce hatsarin mota ya rutsa da tabawa kafafuwan ta suka dagargaje, sai yanke mata su akayi, ba adade ba ta hadu da ciwon ido muna zuwa Asibiti sukace glaucoma ne, ana mgni kmr baayi ido daya ne ya fara mutuwa, daga karshe dayan ma ya mutu, tun daga lkcn take kuka tana cewa a nemo mata ke ta rokeki gafara domin kuwa hakkin ki ne yake bibiyarta, nan de ta kwashe komai ta fadamin, tsabar bakin ciki yasa nayi mata saki uku na koreta daga gdana, kuma na auri wanan besar Allah me suna Adama, yanzu itace iyali na kuma inajin dadin zama da ita. Bayan na koreta ba a Dade ba Allah yayi mata rasuwa, sedai kafin ta rasu ta rokeni na yafe mata, kuma tace duk ranar da Allah ya hadani dake na rokeki ki yafe mata.

Umma tace na yafe mata Allah ya yafe mana baki daya, dagowa baba yayi yace nima kin yafemin? Tana goge mishi hawayen fuskarsa tace na yafewa inna tabawa ma ballantana kai, kallon his Royal Highness tayi tace wanan mijina ne, shine me girma sarkin Alexandria, wanan 'yata ce safna, wanan kuma.....haka duk dabi kowa tayi mishi bayani, sanan ta bashi lbrin rayurta bayan ya koreta in a note shell, sun Dade suna hira daga nan sukayi musu sallama suka tafi da sharadin zasu dawo gobe su daukesu zuwa Egypt sbda his Royal Highness zai hada shi da babban likita acan.


Maman Aysha
[10:51, 9/4/2017] β€ͺ+234 803 681 8427‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky laday safnaπŸŽ‹πŸŽ‹

2⃣2⃣0βƒ£βž–2⃣2⃣5⃣

Suna shiga Kano direct gdn me martaba Sarki suka wuce, lkci guda har Queen umma sun saba da fulanin San Kano, sai bayan sallar laasr suka tafi, gdn safna suka wuce Abii yaga gdn 'yarsa, zama sukayi sunata hira, saida sukayi sallar magrif safna ta shirya musu varieties na abinci sukaci, sanan suka dunguma zuwa gdn alhaji kabeer mesikeli. Nan ma ba karamin tarba akayi musu ba Amma kadan sukaci sbda sunci abinci a gdn safna, Saida sukayi sallar isha'i sanan umma da Abii suka tafi, a gdn suka bar safna.

Mum kuwa tunda Abii da umma sukaje gdn ta rasa inda zata sa kanta don kunya, duk se wani Dari dari take, Abba ne ya fada mata ta shirya gobe har ita zaa tafi Egypt, saita marairaice tace wai batajin dadi bazata iya zuwa ba, imran da safna suna zaune a falo Abba yazo yake fada mishi cewa mummyn ka tace bazata iya zuwa Egypt ba sbda batajin dadi, safna naji tadau haske, mikewa tayi ta shiga dakin mum, zaune ta sameta akan sallaya sai kawai ta karasa kusa da ita ta zauna, cikin nutsuwa tace mummy naji Abba yace bazaki bimu gobe ba, indai sbda abinda ya faru a tsakaninmu ne to ki cire komai a ranki, Sbd na Dade da yafe miki, kuma ki saki jikinki da iyayena domin kuwa ban taba fadawa umma abinda yake faruwa ba, duk abinda kikayi min INA kokarin na danne shi a zuciyata, ummana bata taba sanin bakya sona ba, sbda idan ta Sani zata tsaneki, kuma inaji ajikina zaki dawo ki soni.

Ban taba jin haushin ki akan abubuwan da kike min ba sbda imran ya bani lbrn duk abinda ya faru, kuma ya fadamin duk duniya ba Wanda kika tsana kmr driver da me aiki, so kinga kenan akasi aka samu, me girkin gdan nan ta taba ha'intar ki, kuma saiya kasance mahaifiyata me girki ce a wani gdn, da driver gdn nan aka hada baki aka sa Abba acikin bala'i kuma se kikaji lbri mahaifina driver ne, wanan shine abinda yasa kika tsaneni sbda kina tsoro karna cutar da danki, sedai abinda nakeso ki gane mum ba duka mutane suka taru suka zama daya ba, kowa da irin zuciyarsa, don me girki da driver sun cuceki bazai yiyyu ace duk wani driver dame aiki halin su daya ba, sunan sana'arsu ne kawai daya amma zuciya kowa da irin tashi, INA fata zakiyi musu uxuri ko nan gaba? Kai mum ta daga tace insha Allah safna, don allah kema kiyafe min abinda nayi miki ban kyauta ba, shiyasa bakyau wulakanta mutun sbda kowa da irin bewar da allah yayi mishi, kuma naji dadi da kikace baki taba sanar da mahaifiyar ki irin wulakancin danayi miki ba, wanan shiya tabbatar min ke me tarbiya ce, sbda Fareeda ba wani takura mata ake ba, Amma duk abinda ya faru saita fadawa mum dinta. Inama kowacce matar aure zatayi koyi da halinki, tabbas ba komai ya kamata mu ringa fadawa iyayenmu ba more especially abinda ya shafi tsakaninki da mijinki ko uwar miji, idan mijinki yayi miki lefi ke zaki iya mantawa Ku dawo Ku shirya, amma iyaye bazasu taba mantawa ba, kullum zasu ringa ganin shi da abin. Na gode sosai safna Allah yayi miki albarka tace amin, smiling safna tayi tace to yanzu kin amince zaki bimu? Dariya mum tayi tace zanje safna Allah ya kaimu goben tace amin, imran ne ya shigo ganin mum da safna cikin nishadi ba karamin dadi yaji ba, kallon safna yayi yace me kuke diskantawa ne da mum naga kun kule a daki, kuma lkci guda mood din mum ya canja daga yanda na barta? Mum ce tace ba abinda ya shafe ka bane tsakanina ne da yata, dariya yayi yace to idan kun gama ki fito mu tafi na fara jin bacci, cikin shagwaba safna tace kaje kawai ni yau a wajen mum zan kwana, dariya mum tayi tace to kaji saika je ka tafi, da ido yakewa safna alama ta taso su tafi, kawai se sukayi sukayi 4 eyes da mum, dariya mum tayi tace mijinki bashi da kunya safna tashi kije Ku tafi kinji. Har bakin mota mum ta rakasu suka tafi.

Suna shiga gdan kowa ya shiga part dinshi yayi wanka, cikin wata Yar karamar Riga purple safna ta shirya tayi wanka da turare, kulle ko ina na part din ta tayi, sanan ta haura upstairs part din imran, a kwance ta sameshi akan gado harya fara bacci, a hankli tahau gadon ta kwanta a kusa dashi tana mishi tafiyar tsutsa a kafar shi, cikin muryar bacci yace safna stop it, dariyar mugunta tayi taci gaba, matsawa yayi daga kusa da ita ya koma karshen gado yace ni dama na kyaleki kinyi zaman ki, Sbd zanfi sakewa nayi bacci, Amma yanzu duk kin wani takura min, cikin fushi safna tace oh hakama kace ko? Shekenan bari na koma dakina, sauka tayi daga kan gadon ta nufi kofa, cikin zafin nama ya fisgota ta fado jikinshi, kan gadon suka koma suka kwanta da bedroom voice yace sarkin fushi har kinji haushi ko? Iam joking, Sbd da baki biyoni ba da nayi wahalallen bacci yau, banason abinda ze nisantani dake my princess, kuma kema nasan bazaki iya bacci ba tare dani ba, amma Dan gulma hada wani ke a wajen mum zaki kwana, cikin shagwaba tace oh nice ma nake gulmar ko? To bari kaga na tafi dakina, kuma wallahi bacci na zanyi comfortably, matseta yayi sosai ajikinshi yace safna let us sleep, kinga akwai tafiya agaban gobe, smiling safna tayi sanan ta kwanta luf ajikinshi



Maman Aysha
[10:51, 9/4/2017] β€ͺ+234 803 681 8427‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady safnaπŸŽ‹πŸŽ‹


2⃣2⃣5βƒ£βž–2⃣3⃣0⃣

Washe gari da wuri aka tura driver ya dakko baba da inna Laraba, sanan kowa ya shirya aka rankaya zuwa air port, harsu Maryam da iyayenta zaa tafi, sanan alhaji Sharif da kuma su Abba. Har airport me girma San Kano ya rakashi, a daya daga cikin jiragen Abii zaa tafi Sbd dama shiya kawosu, seda sukaje air port akace sedai a canja mishi driver domin kuwa yau driver shi ya tashi da ciwon ido, Abii yace subahanalla yanzu ya zamuyi kenan? Kuma ni gaskiya mu kadai mukeso mu tafi, da se mubi jirgin da zeyi Lodi anjima mu tafi, Sbd na Riga na sanarwa da Ummi zuwanmu yau, imran yace tunda flight dinka ne muje kawai na tuka, murmushin farin ciki yayi yace aina manta my son pilot ne, Amma are you practicing it? Eh ko last week naje London, masha Allah, Allah ya temaka yace amin. Safna ce ta tro baki tace Tabb indai kai zaka tuka bazan shiga ba gsky, wani lallausan kallo ya watsa mata yace saiki hakura da tafiyar, dariya su Abba suka sa sanan suka nufi wajen jirgin.


Bayan komai ya zama ready imran ya shiga ya tuka suka nufi kasar Egypt✈

A Alexandria kuwa shiri suke sosai na tarar babban sarkin su da family shi, domin kuwa tun tuni lbri yaje musu cewa his Royal Highness abdulwahab yaga familyn shi da yayi missing 16yrs ago, duk jaridu da gdn television abinda suke magana akai kenan, jin lbrn yau ze koma ne yasa governor garin da sauran sarakuna suka shirya mishi lafiyayyar walima ta gani ta fada.

Suna sauka a airport suka tarar da daruruwan Mutanen da sukazo taryarsu duk wani gdn televisions da gdn magazine's ba Wanda basu tura wakilansu ba, suna fitowa waje aka fara haska su da camera, manyan Mutanen da suka zo tarar sune suka nufo wajensu Ummi ce ta fara zuwa wajensu, cikin nutsuwa taje

14 / 15