LADY SAFNAH COMPLETE HAUSA NOVELS BY MAMAN AYSHA.txt

Author :  Maman Aysha Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   8 / 15

21K to 24K   out of 43.3K words

bace ka sakeni mana, haba dalla wanan wanne irin zalunci ne? Ta karasa mgnar tana kuka, cikin firgici yace relax Safna, don Allah inaso ki nutsu ki saurareni wallahi INA sonki, duk duniya ba abinda nakeso kmr ke, in fact tsananin kishinki da nake ne yasa banaso kije dubai. Da mamaki tace So? Kishina? Bakaji kunyar fadin wadanan kalmomin ba? Kana sona amma ka kasa sauke hakkina na aure da yake kanka? Na fuskanci akwai renin hnkli a al amarinka, sbda haka inaso ka Sani na gaji da zaluncin da kake min, kuma tunda ka rabani da duk guardians dina duka basa ganin lefinka ni zan dauki mataki da kaina, idan har baka barni naje Dubai din nan ba ko, to wallahi suna tafya nima zan bar garin na shiga duniya, duk lkcn daka shirya sakina ka bawa umma takardar......cikin firgita yace hold on safna, don Allah karki wanan danyen aikin iam begging you pissπŸ™πŸ», na amince Ki bisu Ku tafi sauran mgnar kuma idan na dawo zamu karasa bcos nasan yanzu be zama dole ki yadda dani ba, saidai don Allah INA Neman wata alfarma idan zaku shiga kasuwa ki ringa saka hijab da nikaf, don Allah badan ni ba. Katse wayar safna tayi ba tare da ta bashi amsa ba.

Suna gama waya yaji gbdya hnklin shi ya dawo 9ja, ba abinda yakeson gani kmr safna, Maryam ya kira a waya yace idan sunje Dubai din karsu kama hotel, akwai gdn dad din shi a garin yasa a gyara musu, kuma ayi musu girki dake akwai masu hidima da gdn, sanan ya bata no daya daga cikin driver mall din babansu na Dubai yace idan sun shiga garin suyi mishi waya yazo ya daukesu.

Hakan kuwa akayi a gdnsu imran suka sauka shiyasa aka ringa dawainiya dasu kwanansu hudu suka dawo, fadin sayayyar da sukayi bata lkci ne, bayan sun dawo da kwana biyu sukaje akayi Jere a dankareren gdn Maryam dake hotoro tsamiyar boka.

Matar da tazo ta yiwa safna gyara Yar Sudan aka kara kira tazo ta yiwa maryam ma, wani sabon gyaran aka kara yiwa safna gdn umma suka koma da zama ita da maryam Saida sukayi 1wk basa fita ko ina, wani irin kyau sukayi suka kara haske skin dinsu ta koma kmr ta jarirai sbda tsabar laushi da taushin da tayi, ana gobe kamu su imran suka dura a Nigeria



Maman Aysha
[23:07, 9/3/2017] β€ͺ+234 803 681 8427‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady SafnaπŸŽ‹πŸŽ‹

1⃣2⃣0βƒ£βž–1⃣2⃣5⃣


An fara gudanar da biki sosai, jiya akayi kamu saidai imran be samu damar zuwa ba yana can yana organising wajen da zasu ajiye friends dinsu da sukazo daga nesa da kuma abincin da zasu ci har akayi aka gama, Washe gari kuma zaayi dinner, tun safe imran ya fita sbda shine ya dauki nauyin hada dinner din da kudinsa, a rose flower sweet and bakery za ayi, kuma har abincin da zaa ci su zasuyi, saida ya tabbatar an gama organising komai ba matsala sanan ya koma gda, yana zuwa wanka ya shiha ya shirya cikin wani dankareren boyel skye blue color din ba karamin daukarsa tayi ba dake fari ne shi. Yana cikin fesa turare fareeda ta shigo cikin shiri tayi kwalliya sai wani iyayi take, kallonta yayi yace ke kuma ina zaki? Binka zanyi mana, wa ya fada miki dake zani? Ba inda zaki bini gara ma ki fitar da rai, kukan shagwaba ta fara mishi tana kunkuni, ji yayi ta bashi haushi yamutse fuska yayi yace wai ni kikewa shgwaba? Aikuwa gara ki dena, ke ai ba yarinya bace, shagwaba tafi yiwa yara kyau ko kin manta 3yrs kawai na baki? Kallon takaici ta bishi dashi a zuciyarta tace Imran bashida mutunci, idan yana rashin M saikace wanda akewa wahayi....wayar da yake ne ta katse mata tunani, da taga da gaske yake bazashi da ita ba sai kawai ta kira mum ta fada mata aikuwa mum ta tilasta shi dole saida ya tafi da ita.

A bangaran safna kuwa suma duk sun zama busy, gdnsu safna ne wajen zaman amare ita kuma umma ta koma gdnsu Maryam wanka da bacci ne kawai yake shigo da ita gda.

Da yamma wajen 4:30 kowa ya shirya amarya Maryam shigar orange tayi, safna kuma tayi shigar pusher pink. Friends din ango ne sukazo suna ta diban kawayen amarya suna kaisu wajen events din, dake program din na iya matasa ne. Safna ce last din tafiya sbda Saida kowa ya tafi ta rufe gdn sanan ta tafi.

Su imran ma direct wajen bikin suka nufa, lkcn da sukaje wasu daga cikin friends dinshi suna tsaye a bakin wajen dake baa fara shiga ba, wasu daga cikin su tare suke da matansu, dake dama yan gari ne, tunda sukaje wajen Fareeda take cika tana batsewa tana ganin matan friends din imran amma ba wacce tayiwa mgna, sai su sukayi mata mgna, sanan ta amsa tana wani iyayi tana basarwa wai ita Yar masu kudi, su bash ne da al ameen abokan su imran da sukazo daga abja sukace au Ashe amaryar tamu ce, anan ko sbda bigboy be inviting dinmu munje mun kwashi girkin amarya bane yasa muka kasa ganeki, dariya tayi tace to ai saikuje gobe kuci, bash yace ai kuma gobe ana daura aure zamu tafi, to kuzo kuyi break fast, kallon imran sukayi sukace to kaji big boy amarya tayi inviting dinmu, dariyar yake imran yayi yace Allah ya kaimu sukace amin.

Zuwan amarya da ango ne yasa kowa ya koma wajen zaman shi ya zauna, Saida waje ya nutsu an fara program safna ta shigo cikin wajen cikin tafiyar kasaita da saika rantse Yar Sarki ce, hnklin jamaar wajen gabady kanta yayi more especially oga imran da kusan 2months kenan be sata a idonshi ba, shi kuwa bash tunani ya shiga yi akan mgnar da imran ya taba fada mishi wai safna marar aure ce, har ta karasa wajen zamanta idon mutane a kanta yake sai kace itace amaryar, wani irin kishi ne ya kama imran ji yake kmr yaje ya tsolewa masu kallon safna ido.

Abubuwa na kayatarwa akayi a wajen sanan bayan kowa yaci abinci ya koshi aka fara shiga rawa, amarya da ango aka fara fitarwa fili safna ce ta fara shiga yi musu liki da raper 100 sabbi fil, tana cikin yi musu liki bash ma ya shiga ya fara yiwa safna da raper 200, mamaki ne ya kama Mutanen wajen, cikin firgita da fargaba safna ta juya zata fice daga filin, kawai saiya sha gabanta,cikin sigar Jan hnkli yace ya zaki fita ban gama yi miki likin ba? Ta bude baki zatayi mgna kenan taji an fisgi hannun ta da karfi an fitar da ita daga wajen, cikin bacin rai bash yacewa mas'ud Mijin salma wai meke damun sirikinka ne? Yaki ya barni nayi soyayya da yarinyar nan, kuma wallahi I really Luv d girl, wai me yake faruwa ne? Ko shima sonta yake? Dariya mas'ud yayi yace first wife dinshi ce fa, da mamaki bash yace wife dinshi? Yaushe akayi auran? Secretly akayi auran ba Wanda ya gayyata saimu da muka Santa kawai, dafe kai bash yayi yace oh my god

Fareeda dake gefe a zaune batayi auni ba ta hango imran rike da hannun safna suna kokarin fita, aikuwa da sauri tabi bayan su saidai kash kafin ta karasa wajen harya jefa safna a motar yayi mata key ya tafi, kurar motar shi kawai Fareeda ta tarar


Maman Aysha
[23:08, 9/3/2017] β€ͺ+234 803 681 8427‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady safnaπŸŽ‹πŸŽ‹

1⃣2⃣5βƒ£βž–1⃣3⃣0⃣

Direct gdnta ya wuce da ita yana packing ya kama hannun ta suka shiga ciki key yasa ya kulle kofar sanan ya zauna akan kujera ya dafe kanshi shiru wajen yayi for some minutes, safna ce ta katse shirun da cewa me kake nufi da dawo dani gda bayan Kasan nice me masaukin baki, kuma ko ba biki ni nagama zaman gdn nan dama jira nake a gama biki muyita ta kare na gaji da zaman ukubar gdnka, kuma inaso ka bude min kofa na tafi Sbd I have alot to do, dagowa yayi ya kalleta da jajayen idanuwanshi yace duk irin sunan da kika kirani dashi I deserved it safna, tabbas banyi miki aldalci ba, ba tausayi a al amurana ko kadan, saidai inaso ki Sani wallahi safna INA sonki, inayi miki sonda ban taba yiwa wani irin shi a duniya ba, duk abinda nake miki taurin Kaine kawai yasa nake, amma daidai da second daya ban taba jin bana sonki ba, kneel down yayi agabanta cikin muryar nadama yace I have totally change safna don Allah ki temaki rayuwata ki yafemin, wallahi ban taba zaton a rayuwata zanyi Hulda da talaka ba, amma sonki ya canja min rayuwata gbdya. Don Allah ki yafemin plissπŸ™πŸ», kasa hada ido dashi safna tayi sbda lkci guda ya zama abin tausayi, dake zuciyarta tayi tace ni yanzu indai ba magnar saki zakayi min ba bana son jin komai daga bakinka, sbda haka tashi ka maidani gda, mikewa yayi yace muje, yana gaba tana binshi a baya, har sukaje bakin kofa bayan ya bude zata fita kenan ya janyota jikinshi cikin bedroom voice yace kina ganin zan iya sakinki? Don Allah karki kara cemin na sake ki kinji? Ya kafeta da sexy eyes dinshi, ya salm kawai safna tace a zuciyarta, wato imran hatsabibi ne, Allah yayi mishi bewar da duk fushin da kake dashi kallo daya zaiyi maka kaji ka dena jin haushinsa. Da kyar ta daure tace cikani, sanan ya saketa suka tafi. Mas'ud ya tambaya yace an tashi daga taron har an fara mayar da mutane ma, kawai sai ya wuce gdn umma.

Yana yin packing safna ta bude kofar zata fita sai taji a rufe, juyowa tayi ta kalleshi, marairaicewa yayi yace jikina ne ya bani INA yin packing zaki fita, kuma inason mgna dake, san kunu tayi tace inajinka, so nake don Allah idan kun rage abinci a gdn ki bani wallahi tun break fast ban kara cin komai ba, cikin wata irin kasaita dashi kansa mamakin yanda take yake tace muje, bude kofar yayi suka shiga a tare, 'yan mata ne su wajen goma a zaune a falon, su safna suna shiga suka bisu da kallo, ba wacece imran ya kalla acikinsu, wit respect suka gaisheshi ya amsa dakyar, daya daga cikin su ce ta daure tace imran mesikeli ko? Basarwa yayi kmr bada ita yake ba, Amma duk da haka taci gaba da cewa iam sorry naga kmr ranka ya baci Kasan kai celebrity ne, na Dade inaso na zama friend dinka a Instagram Amma ba halin hkn, kuma sai gashi yau Allah ya hadani dakai a sauka ke shiyasa na kasa daurewa nayi maka mgna, ok kawai imran yace ba tare da ya kalleta ba ballantana yaga fuskarta. Safna ce ta fito da food wormers din abincin tace gashi nan kaje dashi kawai, mayaudarin murmushin da yake kashe mata dashi yayi mata yace ai anan zanci Sbd indai na tafi dashi bazan sami time din ci ba, cikin wani irin salo yace muje ki kaimin guest parlour. Saida yaci ya koshi sanan ya tafi


A bangaran Fareeda kuwa imran yana fita ta kira mum dinta ta fada mata abinda ya faru, aikuwa tahau fada, da kanta tazo wajen ta dauketa, gda ta wuce da ita sanan ta kira mum din imran ta fada mata, kuma tace yarta ba zata koma gdnshi ba tunda wulakanci ne abin. Hakuri sosai mum ta basu, kuma tace zata kirashi. Suna gama wayar mum ta kirashi, daidai lkcn yana gdnsu safna kuma ya manta phone din shi a mota. Saida tayi mishi 10missed call baa dauka ba, ranta ba karamin baci yayi ba.

Imran yana shiga mota yaga wajen 30missed call, 10 na mamanshi, 20 kuma na friends dinshi, mum din shi ya fara kira cikin bacin rai tahaushi da fada kuma tace duk abinda yake ya bari yaje gdn su Fareeda ya basu hkri, to kawai yace mata.

Suna gama waya ya kira Fareeda yace kinje kin kai karata gun su mom ko? To inaso kisani na fara gjya da hadani da mom dina da kike, idan naga damar sakinki ba Wanda zai hanani sbda ni nake zaune dake, sbda haka zanzo gdnku anjima idan nazo inaso kicewa mom dinki bazaki dawo gdana ba sai nan da 1wk, idan kuma ba haka ba wallahi saina sakeki , kuma kinsan hlina, cikin tsananin damuwa tace meyasa kake son kauracemin harna sati guda bayan Kasan zuciyata bazata iya jure hakan ba? Kashe wayarsa ya kashe ba tare da ya bata amsa ba, kwanciya Fareeda tayi tana wani irin kuka sbda ba krmn son imran take ba.

Hakan kuwa akayi imran yaje gdnsu Fareeda ya bada hkri amma Fareeda tanaji tana gani tace bazata koma ba, ita kuma mom da batasan komai ba tace ya tafi saita nemeshi



Maman Aysha
[23:08, 9/3/2017] β€ͺ+234 803 681 8427‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady safnaπŸŽ‹πŸŽ‹

1⃣3⃣0βƒ£βž–1⃣3⃣5⃣


_By Maman Aysha_

*Talented writers forum*

Washe gari aka daura auren Maryam da sadik around 11am, da yamma akayi hadadden mother's eve mom din imran ma taje dake mmn Maryam kawarta ce, da daddare kuma aka kai amarya Maryam gdnta dake hotoro. Bayan yan kai amarya sun watse safna da salma suka gyara gdn Tass suka kunna turaren wuta. Falo suka dawo suka zauna har amarya, suna zaune saiga ango sun shigo shida imran da mas'ud, Imran ne yayi dariya yace to best friends din amarya ai saiku tashi mutafi ango ya fara gyangyadi, dariya suka sa dukansu Amma banda safna, sallama sukayi wa Maryam da sadik sanan suka fito salma da mas'ud suka shiga motarsu suka tafi suma, sai imran da safna kawai aka bari a tsaye kallonta yayi yace oya let's go mana safna, shanmur tayi tace nifa bazan koma gdnka ba, wai har yanzu baki hkra ba? Eh kawai tace a takaice, to shekenan shigo muje mayi mgnar a gda ko, sanan ta shiga suka tafi.

Suna zuwa daki ta wuce tayi wanka, tasa sleeping dress, shima imran wanka yayi ya shirya tana ta gama shafe jikinta da hadaddun humran ta kenan ya shigo dakin, kamshi da sanyin A/c ne ya bugeshi at d same time, rike hannun ta yayi yace taso muje kici abinci, tro baki tayi tace na koshi, Uhm uhm safna, kar Fushin da kike dani yasa ki janyo mana matsala, nasan bakici abinci ba yi hakuri kizo kici kinji? Idan na shiga matsala ma ai ni ta shafa....nima ta shafeni, safna INA sonki da yawa fa, ya kamata ki ringa saussauta min, sassauci? Ni lkcn Dana ringa rokon kayimin sassaucin kayimin ne? Basar da zancen yayi da cewa yi hkri muje kici to, ya dagota suka fita. Kayan motsa baki ne iri2, safna tana cikin cin nama bata karasa ba ta bingere awajen ta fara bacci Sbd gajiyar biki, imran ne ya debe kayan yakai kitchen, Sanan ya dawo ya zubawa kyakkyawar fuskarta ido, ya Dade yana kallonta sanan ya dauketa ya nufi dakinshi da ita ya kwantar ta akan gado, fitilar dakin ya kashe yayi addua sanan ya jawo safna jikinshi suka kwanta.

Da asuba datayi juyi tajita ajikin mutun, ga wani daddadan kamshi da yake bugar ta, ko acikin mafarki zata gane kamshin turaren imran, a razane ta mike ta zauna a hnkli tace imran? Kenan a gdn nan yau ya kwana? Lalumen inda zata kunna wutar dakin take saita ga Ashe ba room dinta bane, Dan tabashi tayi tace tashi ka kunna fitila asuba tayi, janyota yayi ta fado jikinshi yayi hugging dinta sosai Cikin shagwaba tace ni ka sakeni Dalla salla zanyi, smiling yayi yace OK go and pray. Shima mikewa yayi yaje yayi alwala ya tafi masallaci, ita kuma safna bayan ta idar da salla zama tayi tai kartu as usual, sanan tayi addua ta fita ta fara aikin gyaran gda dake dama gdn yayi kura kwana biyu bata nan, shi kuwa imran yana dawowa daga masallaci bacci ya koma.

Safna yau har part din imran ta gyara, dakinshi ne kawai bata gyara ba sbda yana ciki yana bacci bayan ko Ina na gdn yayi kalkal ta shiga kitchen ta Dora abinci, pizza da burger tayi, ta dafa ruwan zafi ta zuba a flaks, ta soya doya da kwai sanan tayi paper soup din ostel, Saida ta gama jera komai a dining sanan ta kunna turaren wuta sbda gdn kamshin abinci yake, dakinta ta koma ta shiga wanka ta shirya cikin wani wandon jeans black da orange top 3quarter, kara gyara gashinta tayi ta daure da katon orange ribom, Dakin imran ta nufa ta tarar ya shiga wanka, kawai saita fara gyaran dakin ta cire bedsheet din ta shimfina sabo sanan ta share tayi moping tana cikin fesa freshener ya fito daga toilet suna hada ido ya sakar mata wani lallausan murmushi yace gud morning my Angle, morning tace a dakile, sanan ta fita daga dakin.

Fitowa yayi cikin yellow jeans da red shirt hannunshi daure da wani hadadden agogon azurfa me tsada, ji yayi gdan banda kamshi ba abinda yake, ji yayi zuciyar sa tayi mishi dadi, be karajin farin ciki ba Saida kamshin abinci ya daki hancinsa, a hnkli ya furta the different is very cleared, comfortably yaci abincin sabanin abincin Fareeda da tun kafin ya fara ci zuciyarsa take tashi. Saida yaci ya koshi sanan ya mike yace bari naje gda na gaisa dasu mom



Maman Aysha
[02:45, 9/4/2017] β€ͺ+234 803 681 8427‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady safnaπŸŽ‹πŸŽ‹

1⃣3⃣5βƒ£βž–1⃣4⃣0⃣


Haka zaman ya Kasan ce tsakanin safna da imran kullum zatayi mishi girki me dadi kuma su kwanta daki daya Amma Sam safna taki yadda ya tabata, gashi wani irin sonta da Sha'awar ta ne yake addabarshi, yauma kmr kullum bayan sun gama break fast sai imran ya Debi plates din yakai kitchen, sanan ya nade hannun rigar shi zai fara wankesu sai safna ta kalleshi tace me zakayi? Tayaki aikin zanyi naga kmr agajiye kike, ka barshi kawai wanke abina, bakyaso nima na sami ladan? Wai don Allah safna meyasa kike min haka ne? Ba komai so nake kawai ka sakeni,

8 / 15