Author : Maman Aysha Category : Romantic Hausa Novels
tayi hugging din his Royal Highness tayi mishi kiss, kallo daya tayiwa safna ta ganeta, hannu ta ware mata ba tare da bata lkci ba safna ta tafi da gudu ta rungumeta, zuciyarsu ce take bugawa a lkci guda, sanan ta rungume umma ma tace you are highly well come to kingdom of Alexandria my dota, cikin tsananin farin ciki umma tace thank you my Queen. Itama sis dinshi jalila da yaranta zuwa sukayi sukai hugging dinsu one by one, sanan suka nufi inda aka jera manyan Motoci sunfi guda Dari kowa ya zabi wacce ze shiga, his Royal Highness da umma kuwa Royal car ta wajen 50 billion suka shiga, sanan akayi convey zuwa gdn me martaba Sarki.
Wato me kartu gate goma sha biyu ne agdn, amma tun daga gate din farko jama'a suka jeru suna kwasar gaisuwa har akaje gate na karshe Wanda shine ba kowanne mutun ake bari ya shiga ba.
Jalila ce tayi musu jagaba zuwa wani hadadden part da fadin tsaruwa da kyaun shi ma bata lkci ne, bayan kowa ya zauna sanan tace umma da safna subi bayanta, wani part din ta shiga dasu ta dakko musu wasu hadaddun alkyabba masu tsadar gaske da hadaddun set din sarkar gold da bangles kowa da kalar nashi tace Susa, cikin few minutes suka shirya suka fito, kallon mamaki su mom da maryam da mamnta suka bisu dashi domin kuwa da basu sansu ba se suce basu bane sbda canjawar da sukayi lkci guda, domin kuwa har wani Chen din gold aka daura musu a kafa. Suma su Maryam hadaddun alkyabar aka basu suka shirya sanan suka nufi wajen walima, imran sakin baki yayi yana kallon safna sbda mugun kyaun da taga tayi.
Bayan anyiwa his Royal Highness barka da dawowa da kuma murnar ganin family shi, se aka fara presenting gifts, safna seda ta karfi kyautar many an motoci, hadaddun alkyabba da kuma gwalagwale, itama mum haka. Bayan his Royal Highness yayiwa Mutanen da suka yiwa iyalinshi godiya shima ya bada gift me tsoka ga alhaji Sharif da abban Maryam, kuma yayiwa son in-law dinshi imran kyatar jirgi daya acikin jiragensa nan take waje yadau tafi da ihu. Shima governor garin su alhaji Sharif da Baban Maryam ya bawa nashi gift din sbda yanda suka rike su safna amana. Ita kuma Ummi tayiwa maryam kyatar sarkar gold da kudinta zekai 10 million, sanan aka rufe taro da addua kowa ya watse
[10:52, 9/4/2017] βͺ+234 803 681 8427β¬: ππ
Swanky lady safnaππ
2β£3β£0β£β2β£3β£5β£
Daddare bayan kowa yayi wanka aka fito dining cin abinci, dukansu suka hallara dake dining table din irin mecin mutun ashirin din nan ne, kowanne sako da lungun falon hause maids ne zagaye a wajen bayan sun gama aka zauna aka taba hira sanan kowa ya mike suka fara shirin tafya dakin da aka saukesu dake kowanne mata da mijinta aka hadata, alhaji Sharif ne kawai beje da familynshi ba. Safna da imran suna shirin tafya dakinsu Ummi tace my grand dota yau aitare zamu kwana dake, Juyawa tayi suka hada ido da imran, sanan ta buga dariyar yake tace to ummi, shima imran dariyar yake yayi yace eyee yau yarinya zata kwana da kakarta, duka Mutanen wajen suka bushe da dariya sanan kowa ya nufi room dinshi.
Imran tunda ya shiga daki ya Kasa bacci, juyi kawai yake akan gado, pillow ya dauka ya rungume ko zaiji relief amma a banza. Har kusan 12mid night ya Kasa bacci, kawai saiya dauki phone dinshi ya ya fara dialing no ta
Itama a bangaran ta d same things domin kuwa rashin jin dumin jikin imran ya hana ta bacci, wata zuciyar ce tace ko zaki lallaba ki tafi tunda tayi bacci, kai aikuwa da nayi rashin kunya, hmm INA nan INA tunanin shi amma shi ko ajikinshi, nasanma yayi nisa a bacci....karar phone dinta ce ta katse ta, cikin bedroom voice yace safna kema bakiyi bacci ba? Wallahi nima na Kasa bacci, banda missing dinki ba abinda nake, haka kawai don rigima tsohuwar nan ta tashi ta janye min ke, ita batasan bama iya rabuwa bane? Wallahi yau daya na shiga wani hali, INA sonki da yawa my princess, Murmushi tayi da har seda yaji sautinshi, sanan tace I love you too my Prince, wata lallausar dariya yayi kmr tana kallon shi sanan yace prince kuma safna? Eh mana tunda na zama princess ai kaima ka zama prince, so you're are now d prince of Alexandria, dariya yayi yace ki rufamin asiri karsu baffanki shuraim su kadani wata kasar, dariya safna tayi sosai, imran yace irin wanan dariya haka safna karfa ki tashi tsohuwa, dariya ta karayi tace ai tsuhuwa ta Lula tun tuni, tsaki yayi yace ai kaji matsar ta hanamu mu sake, kuma tayi dumping dinki a gefe tana baccinta, sekace wani Abu zata baki idan kin kwanta a dakin nata, safna tace tsananin so da murnar ganina ne yasa, yace gsky kam don naga tayi murnar ganin ki sosai. Haka sukai ta hira har seda suka fara gyangyadi sanan suka kashe suka kwanta.
Washe gari da safe kowa ya hadu a dining zaayi break amma banda imran, Abii yace safna taje ta kirashi, tana shiga ta sameshi yayi wanka ya shirya cikin wani hadadden boyel sky blue yana kwance akan gado banda buga kamshi ba abinda yake, gefen gadon taje ta zauna cikin rada tace you looks so handsome my sweet man, wani shu'umin smiling yayi ya jawota jikinshi yace thank you, cikin nuna caring tace ka tashi muje muyi break kowa ya hadu kai ake jira, ba inda zani, kawai ki debo mana muci anan idan sun tambaya kice banida lpya, da ido tayi mishi tambaya meyasa? Smiling yayi yace kiyi yanda nace kawai. Dakyar ya saketa ta fita, tana zuwa kuwa ta fada musu, cikin damuwa suka tmbyi abinda yake damun shi? Tace ciwon kai ne. Kasa cin abincin sukayi har seda sukaje suka gano shi su kaga jikin da sauki sanan sukaci.
Bayan sun gama imran da sadik da safna da maryam suka tafi Yawo cikin gari basu dawo ba sai bayan laasar, shi kuma Abii yasa ankai baba surikinshi Asibiti sunyi admitting dinshi.
Tunda suka dawo daga yawo imran ya shiga daki ya kwanta be fito ba har dare, su duk azatonsu jikin ne, dakyar Abii ya lallaba shi ya fito sukaci abinci, yana gama ci yayi musu sallama ya tafi, ba yanda basuyi dashi aje Asibiti ba Amma yaki yace wai yasha mgni. Sun Dade suna hira daga karshe kowa ya mike ya nufi makwancinsa, da akazo tafiya Abii yace safna ki tafi wajen mijinki tunda bashi da lpya, tace to.
A kwance ta sameshi yayi shirin bacci, kusa dashi taje ta kwanta tana shafa gashin kansa tace wai me yake damun ka ne? Hugging dinta yayi yace missing dinki ne matsalata, naga tsohuwa na kokarin kwace min mata shiyasa nayi hysteria, kinga ai yanzu an dawomin dake ko? Zatayi mgana ya fara tsotsar lips dinta.
Satinsu daya a Alexandria suka dawo gda 9ja, safna da umma ba karamin kukan rabuwa sukayi ba, dakyar aka banbare safna daga jikin umma, sunbar Baban umma acan sbda baayi discharge dinshi ba.
Tunda suka dawo mum take nunawa safna so kmr ta cinyeta, cikinta ya fara tsufa Sbd yanzu kallo daya zakayi mata ka gane tanada ciki, wani irin caring mum da imran suke nuna mata domin kuwa ko girki ta dena sedai a aiko musu daga gdn mum
*6 months later*
Safna ta haifo twins din yayan ta kyawawa mace da namiji, sabda girman su se c/s akayi mata, bayan an sallamota daga Asibiti da sati biyu akasha bikin sunan da fada ma bata lkci ne, Mutanan Alexandria ma sunzo, yara sunci sunan Fatima da kabeer sunan mom da Abba
*Alhamdulilla, anan na kawo karashen wanan novel, kuskuren Dana fada aciki Allah ya yafe min, sai kunji ni a sabon novel dina me suna* _Gadar zare_
Maman Aysha