LADY SAFNAH COMPLETE HAUSA NOVELS BY MAMAN AYSHA.txt

Author :  Maman Aysha Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   7 / 15

18K to 21K   out of 43.3K words

shiga ya fada toilet yin wanka, Fareeda kin yin wankan tayi kawai ta dauki rigar bacci tasa, ta fesa turare ta nufi dakinshi yana fitowa daga wanka tana shiga dakin da mamaki yace har kinyi me? Cikin kissa tace aini bana dadewa a wanka, towel din hannun shi ta karba ta goge mishi jikin, tunda taga skin dinshi hnklin ta ya tashi, jallabiya ya dauka yasa sanan ya fesa designer turaren shi ledar kajin dayazo da ita ya dauka yace mu koma dakin ki ko? Tace toh. Baje musu yayi sukaci suka koshi, sanan ya fita yayi strolling ya Dade yana exercises sanan ya dawo, da mamakinshi Fareeda na zaune kallonta yayi yace bakiyi bacci ba? Cikin kissa tace INA jiran na kwanta ajikin lallausan mijina, da mamaki yace first night din ki nefa Fareeda, kina nufin bakya tsorona? Tsoro kuma? Hmm Kasan dadewar da nayi INA jiran wanan ranar kuwa? Ina masifar sonka da baka aureni ba iam very sure da zuciyata bugawa zatayi, matsowa kusa dashi tayi ta fara shafashi, wato me kartu kowanne namiji yana zumudi a first night Amma a gdn imran abin ba haka yake ba domin kuwa tun yana Jan class yana basarwa Saida tayi galaba akanshi suka murji amarci, basuyi bacci sai wajen 1am, a Daren imran yayi wanka Amma Fareeda kam kinyi tayi. Da asuba ya tasheta tayi wanka shi kuma ya tafi masallaci amma har ya dawo bata tashi ba, komawa yayi ya kwanta sai wajen 9am ya tashi yayi wanka ya shirya cikin wani tsadadden yadi ash and black, ya fesa turare ya fita, direct gdnsu ya wuce part din abbanshi yaje ya gaishe shi sun Dade suna hira Abba yanata yi mishi nasiha akan yayi adalci a tsakanin matan shi, yace insha Allah zaiyi.

Mum ce ta shigo da tray din break fast din Abba a hannun ta, da sauri imran ya karbeta sanan ya gaisheta da faraa ta amsa mishi, tace me kake a gdn nan sassafe ana shirin kai muku abinci yanzu, langwabe fuska yayi yace har kun fara cire mu a 'yayan gdn nan? Dariya sukayi har Abba sanan imran yace ki bayar akai mata ni zanci a wajen Abba. Tare sukaci abincin da Abba, sanan ya Debi kwanikan yakai kitchen sbda masu aiki basa shiga part din abbansu. Daga nan side din sallama yaje suyi sallama, sun Dade suna hira yayi mata fada akan tabi mijinta, bayan sun gama Maryam ma tazo suka gaisa da faraar shi ya amsa yace ina sadik tace yana gda, shirin tafya abj suke tayi a gdn, yana fita ya nufi gdn safna.

A bangaran safna kuwa bayan fitar imran kobi takan kajin daya kawo batayi ba, daki ta koma ta kwanta bata farka ba sai asuba bayan tayi salla ta zauna tayi krtn kur'ani har Saida gari ya waye, sanan ta mike ta fara aikin gda Saida ta kalkale ko ina ta kunna turaren wuta sanan ta shiga wanka ta shirya cikin wata atamfa Hilton red and white, zama tayi ta Mirza dauri tayi simple make up sanan tayi wanka da turare, kitchen ta shiga ta soya plantain tai toasting bread sanan ta dafa ruwan zafi, baba megadi ta kaiwa nashi sanan ta dawo tana cin nata.

Key din shi yasa ya bude kofar falon yana shigowa sanyi A/c hade da daddadan kamshi ya bugeshi, ya Dade a bakin kofar yana kallonta komai nata burgeshi yake, meyasa safna ta fito a poor family? Inama safna ce ta fito a familyn su Fareeda da bashi da wani matsala a rayuwar shi, Saida yaje dab da ita yayi sallama dagowa tayi suka hada ido, wani irin kyau taga yayi, saurin kawar da kanta tayi, zama yayi a daya daga cikin kujerun dining din yace ni bazaa ayimin tayin abincin ba? Basarwa tayi kmr bataji ba, zuba mata ido yayi harta gama cin abincin, diban plates din tayi takai kitchen ta wanke, harta gama ta fito still yana zaune, binta yayi da wani mayataccen kallo sanan yace jeki shirya kayanki Ku tafi abj rakiyar salma, tro karamin bakinta tayi tace ni bazanje ba, dama ba raayinki nakeso ba umarni nake baki, meyasa kake son naje bayan mom din ka bataso? Ni gskya ba inda zanje nida nake jiranka kazo ka bani takar......mugun kallon daya watsa mata ne yasa ta kasa karasawa, Saida ya tabbatar ta tsorata dashi sanan yayi wani mayaudarin murmushi yace INA jiran ki a mota, karki batamin lkci


Maman Aysha
[23:06, 9/3/2017] β€ͺ+234 803 681 8427‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady safnaπŸŽ‹πŸŽ‹

1⃣0⃣5βƒ£βž–1⃣1⃣0⃣


Kaya kala daya kawai ta dauka ta fita suka tafi, bayan yayi packing suka fito a tare zuwa cikin gdn, Saida ya rakata har part din salma sanan ya fito, da gudu Maryam ta tare ta cikin rada tace ya barki a sanyaye safna tace ya barni Amma INA tsoron mum, sbda abune me wahala ta barni naje, Maryam tace karki damu tunda ogan ya barki ai shekenan, bazata gane ma dake zaayi tafiyar ba yaya sadik ne zai kaimu safna tace da nasan zaije ma da banzo gdn nan ba, kinga kawai da sukuje gda Ku dauke ni tunda bada mum zaayi tafiyar ba, Maryam tace yanzu ma ba damuwa

Bayan an raka amarya tayi sallama da Abba aka fito da ita dake dama tun tuni motoci sunzo, ta kofar baya su safna da Maryam suka fita, Suna dab da zuwa inda Sadik ya aje motar kmr daga sama sukaji ance ke kuma me kikazo yi gdn nan? Badai abjn zaki ba ko? Tsuru tsuru sukayi suna kallonta, idan dai shirin abja kikayi to ki koma domin kuwa ba inda zaki, idan kuma naji lbrn kunje wallahi saina.....mum ni nace ta shirya taje, muryar imran ta katseta karasowa wajen yayi yace oya kuje motocin sun fara tafya, ga mamakinsu sai suka ga mum tayi shiru bata kara mgna ba, karbar traveling bag din safna yayi ya rakata har bakin mota, Maryam ce a gaba sai safna da wata causing din su imran Sadiya a baya, zagayawa wajen sadik yayi yace ka kular min da wife dina don Allah, kuma banda gudu, hararar shi sadik yayi yace ai basai ka fada ba, sanan yayiwa mota key suka tafi.

Imran na fita daga gdnsu gdn alhaji Sharif yaje bayan sun gaisa yayi mishi bayani cewa ya sayawa umman safna gda, kuma ya zuba komai aciki idan ba damuwa yanaso yau ta tare a gdn, cikin farin ciki yace a wacce unguwa ne? Yace a gadon kaya kusa da gdnsu Maryam, sbda naga yanzu sun zama kamar ya da kanwa ita da Maman Maryam, so kaga idan suna kusa sai zumunci ya karu, gidaje uku ne kawai a tsakaninsu. Alhaji Sharif yayi murna sosai sanan yace muje gdn nata kayi mata bayani.

A tare sukaje gdn, tun daga waje suke jin kamshin turare dake tsaftar ta safna ta dakko, Saida sukayi sallama tayi musu izini sanan suka shiga, tayi kwalliyar ta idan ka ganta saikace batafi 25yrs ba, nan kuwa shekararta 40 tsabar kyaun jiki ne da ita, kuma yanzu ta kwantar da hnklin ta Sbd tun tana tsammanin dawowar mijinta har ta hakra, bayan sun gaisa ta tambayi alhaji Sharif iyali yace suna nan kalau, sanan tace wa imran ya amarya da safna yace suna nan kalau, Safna sun tafi Abja, tace eh ta kirani dazu, shiru wajen yayi na Dan lkci, sanan alhaji Sharif yayi mata bayanin abinda ya kawo su, dagowa tayi ta kalli imran tace kabar gdnka wallahi ngde, ni wanan gdn ya isheni rayuwar duniya, ai dawainiyar tayi yawa ngde Allah ya saka da alkairi, alhaji Sharif ne yayi mata nasiha akan baa mayar da hannun kyauta baya, kuma ya fada mata dalilin imran na son zamanta a kusa da gdnsu Maryam.

Dakyar suka shawo kanta ta amince, sanan ya dauketa ya nuna mata gdn, kuma ya hadata da yaran da zasu dibar mata yan abubuwan da zata bukata na tsohon gdn, kuma ya basu motar kamfaninshi na aluminium zaa Debi kayan aciki.

Maman Maryam ba karamin murna tayi ba, gdn drive in ne me masifar kyau, kuma furniture's din da imran yasa masu kyau ne a kamfaninshi na furniture's yasa akayi, idan kaga gdn saika rantse na amarya ne. Masu aikin gdnsu Maryam akasa suka kara gyara gdn, Saida komai ya zama neets mmn Maryam ta kawo musu abinci sukaci suka baje a falo suka kunna A/c sanan suka kira Safna tana dauka umma tace Safna ya hanya? Alhamdulilla ai mun isa tun dazu, masha allah nima kin ganni a baje a sabon gda sai A/c nake sha, da mamaki safna tace sbn gda kuma umma? Eh mana, gdn da mijinki ya sayamin mana, ai matsamin yayi Saida na koma yau, kin ganmu ma tare da mamanku. Cikin rudani safna tace nifa umma ban gane abinda kike fada ba, wai waye ya saya miki gda? Lbri umma ta bata from AtoZ, daga karshe tace ki kirashi yanzu kiyi mishi gdya, jiki a mace tace to umma, tana kashewa ta fara kuka me imran yake nufi dani ne? Maryam tace meya faru? Wato sbda nace ko be sakeni ba zanbar mishi gdnshi shine yaje ya sayawa umma gda a kusa dasu kuma ya sata ta koma ayau, kenan abinda yasa ya matsa saina taho garin nan kenan, na tabbata yanzu umma da baba Sharif ba zasu taba yadda cewa imran yana cutar dani ba, wane irin lefi nayi mishi daya zabi ya ringa hukuntani ta wanan hanyar? Wallahi Maryam na tsani imran ta karashe mgnar tana kuka, rufe mata baki Maryam tayi tace kiyi hakuri safna, nan ba wajen da zamu tattauna irin wanan mgnar bane, kiyi hakuri muje gda kinji.

A bangaran imran kuwa yana barin gdn umma gdnshi ya tafi a falo ya sami Fareeda tayi wanka tana harde akan kujera da remote a hannun ta sai wani cin magani take wai ya fita ya dade, shima basar da ita yayi ya wuce ciki, tashi tayi tabi bayan shi yanda yabar dakin haka ya dawo ya sameshi kallonta yayi yace yanzu don Allah bakiji kunya ba? Ki duba dakin nan fa ki gani ko gado kin kasa gyarwa, kunkuni ta farayi to ba kaine ka wahalar dani jiya ba, shine dalilin dayasa kika kasa gyara gadon da kika kwana akai? Tsuka yayi ya fice daga gdn sbda ba abinda ya tsana a rayuwar sa irin kazanta, yanason yaga komai neets, Sbd shi mugun Dan gayu ne, kuma yanada masifar tsafta idan kaga kafarshi sai kace ta mace Sbd is very smooth


Maman Aysha
[23:07, 9/3/2017] β€ͺ+234 803 681 8427‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady SafnaπŸŽ‹πŸŽ‹

1⃣1⃣0βƒ£βž–1⃣1⃣5⃣

_written by Maman Aysha_

*Talented writers forum*✍

Kwanan su safna daya a abja suka dawo, direct sbn gdn ummanta ta wuce, ginin gdn har yafi nata kyau, dakyar taci abinci sbda bacin rai, ita kuwa umma banda murna ba abinda take, kusa da Safna umma tazo ta zauna tace mun yanke shawara da hjy Kubra(mmn Maryam) zan sayar da tsohon gdnmu na fara business da kudin, zan fara zuwa Dubai saro kaya, shiru safna tayi, ta kara cewa bakice komai ba? Murmushin yake safna tayi tace Allah yasa albarka aciki, umma tace amin, kuma yaushe zaki fara zuwa? Tace next WK. Sai dare safna ta koma gdnta.

Haka rayuwa taci gaba da tafya, safna sun koma school yanzu a last semister dinsu suke, tunda ta dawo daga abj beje gdn ta ba, 2wks kenan rabonta da taganshi kuma duk lkcn da sukayi waya da umma sai tace mata yaje ya gaisheta ko tace yanzu mijinki ya fita daga gdn nan, wani lkcn ma a gdn ummanta yake cin abinci, ta rasa dalilin shi na yin hakan, tun abin yana damunta harya daina ta fita sabgarsa gabadaya yanzu krtun ta ne agabanta Sbd very soon zasu fara exams, kuma anyi fixing date din bikin Maryam nan da 1month


A gdn Fareeda kuwa kazanta sai abinda ya karu, imran zaman maleji kawai yake Amma Sam bayajin dadin zaman gdn sbda ko abincin gdn baya iya ci, kuma gashi 'yan aiki har mutun shida amma ya rasa aikin da suke a gdn. Dakin Farida banda zarni ba abinda yake, ayaga haka saiya daina kwanciya a dakin ya koma bacci dakinshi, kuma dakin nashi ma saidai shi ya gyara da kanshi sbda ta sangarce komai masu aiki ne suke mata

Yauma kmr kullum imran yana farkawa daga bacci yaji gdn ya kaure da wani irin karni, toilet ya shiga yayi wanka ya sakko kasa cikin shirinshi banda kamshi ba abinda yake. dakinta ya duba be ganta ba, yana sakkowa falon kasa yaji karnin yayi yawa, a zaune ya ganta tana cin break fast taci uban kwalliya, kallonta yayi da mamaki yace kinajin karnin da gdn yake kuwa? Cikin rashin damuwa tace eh wallahi moping din gdn akayi yanzu kuma moper a jike take shiyasa take karni, Amma zai daina bismilla zo kaci abinci, cikin bacin rai yace wai ke wacce irin dabba ce mahaukaciya? Kinada masu aiki har mutun shida amma kin kasa maintaining gdn nan, yanzu dana leka dakin ki ba shiri na fito Sbd toilet banda zarni ba abinda yake, gadonki kuwa zan iya rubuta sunana da kurar da take jikinsa, haba Fareeda ke ko kunya bakyaji? Kefa macece, shagwabe fuska tayi haba yaya don Allah ni ya kakeso nayi ne? Kasan ni ban saba da wahala ba, kuma su indo yanzu suka fara aikin a hnkli zasu iya komai.....shut up, useless girl kawai, banda ke banza ce ta yaya zasu iya baki koya musu ba? Daukar Dan aiki ba lefi bane, Amma ya kamata kisa ido a aikin da suke ya zamana duk abinda zasuyi kina tsaye kina directing dinsu idan sunyi shirme ki gyara musu, Amma baki da aiki sai kwanciya ko chtn duk badakalar da sukayi ba ruwanki, to wallahi bari kiji na fara gjya da kazantar ki idan kin bata kayan ki ni bazan yadda ki batamin gda ba, sabda haka ki gyara idan kuma ba haka ba zanyi maganinki, ko bi ta kan abinci beyi ba ya fice cikin bacin rai, ita kuwa Fareeda ko ajikinta sbda ita bataga wani kazanta a gdn ba neets take kallon gdnta.

Tafiyr 3wks ce ta taso mishi zuwa London, yanaso su tafi da safna koya samu su shirya acan domin kuwa yanzu tsoron safna yake sbda yayi mata alkawari duk ranar da suka hadu zai saketa, kuma a yanzu bazai iya cika alkawarin ba domin kuwa yanzu duk duniya ba abinda yakeso kmr safna, zama da Fareeda yasa ya fuskanci cewa auren 'yayan masu kudi ko yiwa mutun jeren kaya masu tsada a gda ba shine aure ba, ka auri me tarbiya da wacce tasan menene rayuwar duniya da abinda yake ciki shine aure, domin kuwa irinsu Fareeda gata da sangarta kawai suka iya, basu San me duniya take ciki ba. Sadik ya kira ya fada mishi zai tafi da safna london, sai sadik yace aikuwa next WK zasu fara final exams dinsu saidai idan daga tafyr zakayi, yace ai bazai yiyyu na daga ba sbda meeting zanje akan oxford university, mtss kai amma exams ta kofsa min, dariya sadik yayi yace to ka tafi da fareedan taka mana, basar dashi yayi kmr beji me yace ba

Ba yanda fareeda batayi ba akan zata bishi amma yaki, kawai saita kira mum ta fada mata ita kuma mum ta kirashi tace idan har yana son farin cikinta to ya zama dole ya tafi da Fareeda. Haka Fareeda ta shirya suka tafi bada son ran imran ba.

A bangaran safna kuwa, sun gama exams dinsu sai jiran fitowar result da suke, mum dinta kuma ta fara zuwa sarin kaya Dubai, alhaji Sharif ya hadata da wasu manyan yan kasuwa a kantin kwari tana order kaya suke Sara su bata kudin ta, sbda haka yanzu a wata sau biyu take zuwa Dubai.

Yau satin su imran biyu kenan a London nan da 1wk zasu dawo sbda fara shirin bikin Maryam da amininshi sadik, a bangaran su safna yanzu gbdaya sun zama busy domin kuwa shirin biki suke sosai, tafya dad din Maryam ya shirya musu zuwa Dubai har umma zaaje sbda yanzu Dubai ta zame mata kmr gda, safna ce tace itama zata, sai umma tace saiki yi waya ki tambayi mijinki, a zuciyarta tace dankari, ni yanzu INA zan samu no shi? Kmr umma tasan tunanin da take saita katse ta cewa dazu ma kuwa ya kirani munyi waya dashi, smiling safna tayi tace Allah Sarki, nima idan ya kirani anjima zan tambayeshi



Maman Aysha
[23:07, 9/3/2017] β€ͺ+234 803 681 8427‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady safnaπŸŽ‹πŸŽ‹

1⃣1⃣5βƒ£βž–1⃣2⃣0⃣

_written by Maman Aysha_

*Talented writers forum*

Phone din umma safna ta dauka ta duba no imran ta London, sanan ta fice bayan gda ta fara kira bugu biyu ya dauka wit respect yace ummanmu ina yini? Cikin isa da kasaita tace ba ita bace, ya salm yanajin muryarta gbdya ya rikice, sassauta murya yayi yace my angle how are you? A zuciyarta tace kaji wai my angle, Dan renin hnkli kawai. Ba tare da ta bashi amsa ba tace, dama na kira ne na fada maka inaso zanbi su umma Dubai, zamuje sayayyar kayan Maryam, ban amince ba kawai yace a takaice, cikin bacin rai tace wai kai meyasa baka da adalci ne? Meyasa bakason farin cikina kullum saidai ka bakanta min? Yau wata biyar kenan da auran mu amma ji nake kmr mun shekara dubu Sbd kunci da rashin kwanciyar hnklin da yake cikin auran, kafin ka tabi London Saida kayi 2wks baka leko inda nake ba, sanan don rashin adalci ka dauki matarka kuka tafi ko sallama bakayi min ba, kuma Sbd zalunci ka shiga jikin duk Wanda Kasan zai share min hawayena ka nuna musu cewar kai mutumin kirki ne, sunyi maka yardar da duk abinda na fada akanka ba zasu yadda dani ba, haba yaya imran don Allah kaifa musulmi ne, baka tsoron cewa Allah zai kamaka da hakkina? Baka tunanin zuciyana zata iya tarwatsewa sbda bakin cikin ka? Meyasa ka zabi da ka cutar dani fiye da kowa a duniya? Tunda kace ni ba type din ka

7 / 15