LADY SAFNAH COMPLETE HAUSA NOVELS BY MAMAN AYSHA.txt

Author :  Maman Aysha Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   2 / 15

3K to 6K   out of 43.3K words

bayan ya zama cikakken pilot sai suka daukeshi aiki agarin, lkcn da dad din shi ya bude Nigerian Oxford university saiya nemi daya dawo gda 9ja kuma ya nadashi chairman management committee na sch din, wanan shine dalilin dayasa manyan yara na garin suka San imran, kuma yayi popular sosai.

Imran su biyu ne a wajen iyayenshi shine babba, sai kuma kanwarshi salma itace aminiyar Maryam friend din safna.

Imran kyakkyawa ne irin kyaun da zama ringa ganin kamar shi yayi kansa, kallo daya zakayi mishi kaji ya shiga ranka saidai miskiline, bashida mutunci, yanada girman kai da izza kuma sanan ya tsani talaka, ko kadan imran baya tausayin talaka, tsakaninshi da talaka kawai yayi mishi aiki ya biyashi. Wanan mummunar dabi'ar tashi ba karamin damun mahaifinshi take ba, kullum addua yakewa danshi akan Allah ya cire mishi tsanar talaka a zuciyarsa, duk lkcn da suka zauna suna hira saiya tayi mishi nasiha amma dake Wanda yayi nisa bayajin kira ko kadan baya dauka. A yanzu haka salma tana kartu a NOU panshekara, medicine take krnta kuma a level 6 take, shekararta 23, ita kuma Maryam babanta ne vice chancellor na bayero university Kano itama 23yrs take kuma tare suke karantar law da safna, ita kuma safna shekararta 20 so 3yrs Maryam ta bata, amma kuma bata da aminiyar da tafi Maryam.

Shi kuma imran bashi da friends din dayakai Sadik da mas'ud, Sbd tare sukayi kartu dasu, kuma dad din mas'ud shine ambassador na kasar Holland kuma family friends ne suda gdn su imran, shi kuma Sadik babanshi ne minister of finance kuma lecture ne a BUk, sanan suma family friends ne da gdnsu Maryam. Sadik shi yakeso ya auri Maryam, shi kuma mas'ud shizai auri salma.

Kafin imran ya hadu da safna saida yayi soyayya da yan mata har guda uku kuma 'yayyan manyan mutane domin kuwa harda yar President, sai anzo mgnar aure yace ya fasa, dake dad din shi yana mugun soshi sai yake ta biye mishi. Daga karshe dayaga yana Neman mayar dashi krmin mutun saiya yanke hukuncin hadashi da Yar amininshi senator ma'azzam doguwa, me suna Fareeda yanzu haka tana final year dinta a Oxford university kuma shekararta 25, da imran ya amince Sbd babbar yarinya ce, amma tun ranar daya fara ganin safna yaji bayason kowa sai ita.

Cigaban labari


Maman Aysha


Maman Aysha
[22:34, 9/3/2017] β€ͺ+234 803 922 1122‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady safnaπŸŽ‹πŸŽ‹

2⃣0βƒ£βž–2⃣5⃣

Yauma kmr kullum imran suna zaune suna hira shida Sadik ya kalli Sadik cikin bacin rai yace zuciyata ta fara bani shawara na rabu da safna, cikin kidima Sadik yace meyasa zska rabu da ita? Sbda tana Neman renamin hnkli, kuma sbda batasan halina ba shiyasa takemin haka, Kasan ni a kankanin lkcn nake cire mace a zuciyata, mata basa renamin hnkli, tuntuni nake binta takaini gdnsu amma taki, kuma ni so nake na aureta, bazai yiyyu ace kullum saidai mu hadu a school ba, idan bata canja ba very soon zan rabu da ita. Sadik yace yi hakuri abokina, zanje nayi mata mgna, Amma don Allah karkace zaka hakura da ita.

Yau lecture 9to11 ne dasu safna bayan sun fito ta samu waje a gefen faculty su ta zauna taba tunani yanda zata tafi gda sbda yau Maryam bata shigo ba, kuma ta kira wayarta switch off. Sadik ne yayi mata waya yace tazo yanzu ta sameshi a office dinshi tace to.

Da hanzari taje, bayan sun gaisa yace dama imran ne yace na tambayeki meyasa bakya so yaje gdnku? Wit confidence tace problem din shine dad dina yayi min warning sosai akan kula samari kafin yabarni naxo kartu nan, kuma yana yawan kawomin unexpected visit, so INA tsoron kar wataran asamu akasi kuma iam very sure duk ranar daya kamani INA zance to confirmed zan koma USA ne, kuma dakyar zai yarda na aureshi Sbd dad dina mafadaci ne, kuma yanada tsauri. Yanzu haka yasa an nemomin body guards suna kula dani tare muke zuwa school din nan dasu, window office din shi ta kalla ta nuno masa wasu mutane sunsha bakaken suit a tsaye a bakin office din VC tace kaga irinsu can ma, ba inda basa tsayawa a sch din nan. juyawa yayi ya kallesu kawai saiya kwashe da wata 'yar iskar dariya, dariya yayi sosai har yana Dora kanshi akan table, cikin isa da kasaita safna tace meya baka dariya? Dagowa Sadik yayi yace gani nayi sai wani muxurai suke, gskya dole kiji tsoron kai samari gdnku, Amma ba matsala yanzu nagano reason dinki kuma I will explain to him insha Allah ya karashe mgnar yanata dariya, jikinta ba karmn sanyi yayi ba Amma saita basar. Sallama tayi mishi ta tafi har taje bakin kofa ta dawo tace yau Maryam kalau kuwa? Naga batazo sch ba, kuma na kira layinta baya shiga. Eh wallahi batajin dadi ne, eyya Allah sarki my sis, aikuwa zanje yanzu na dubata, cikin kallon zargi yace body guards din naki zasu yarda ki biya kuwa? Cikin basarwa tace ba matsala, smiling Sadik yayi yace kinga sallami body guards din naki muje na kaiki, har zatace aa sai kuma ta tuna cewa a adaidaita sahu zata tafi, sai kawai tace toh zan jiraka a waje yace to.

A tare suka jera zuwa wajen da yayi packing imran ne ya kirashi a waya, saiyace kazo packing space INA jiranka. Suna tsaye a wajen saiga shi ya fito daga office din VC yana wata tafya ta takama hnklin safna be tashi ba saida ta hangi Mutanen dazu da ta cewa Sadik body guards dinta ne suna takewa imran baya, gabanta ne yayi mugun faduwa shekenan asirina ya tonu, dama ba securities din VC bane? Ya salm to ko shiyasa Sadik yake ta yimin dariya? Yanzu ya zanyi idan Sadik ya fadawa imran? Shi kenan yau karyata ta kare kenan...... Imran ne ya katse mata tunani da cewa my princess what's wrong? Tunanin me kike harna karaso baki Sani ba? Sadik ne yayi karaf yace Kasan twin sis dinta Maryam batajin dadi ko skul batazo ba, shiyasa ta shiga damuwa, dagowa tayi suka hada ido da Sadik kawai saitaga ya daga mata gira.

Imran yace eyya Allah ya bata lpya suka amsa da amin, kusa da ita imran ya matso cikin rada yace mata yanzu INA zaki? Jiki ba kwari tace zamuje mu dubota ne nida Yaya Sadik, cikin wata irin voice yace kyale Sadik muje na kaiki, Sadik ne yayi karaf yace rufa mata asiri nima saida na nemi izini a wajen body guards dinta da sukazo daukarta, kuma nayi musu alkawari zan mayar da ita gda sanan suka kyaleta, so INA ganin ka tafi kawai zanzo muyi discussing anjima. Wani kallon so imran yayiwa safna yace wai haka my princess? Diriricewa safna tayi ta rasa abinda yake mata dadi, ji take dama ta nutse a wajen sbda kunya amma saita daure ta daga mishi kai kawai, cikin so da kulawa imran yace to ni zan wuce, don Allah kiyi mata sannu kafin Nazo, a hnkli tace to, ya shiga mota suka tafi da securities din shi, shima Sadik ya bude mota yace safna ta shiga su tafi. Suna fara tfy ya kalleta yace Aron body guards din naki kika bawa imran ne? Kasa dagowa tayi ta kalleshi ballantana ta bashi amsa.

Har sukaje gdnsu Maryam safna bata dago ba, yana faka mota safna ta bude ta shiga cikin gdn da sauri, a falo ta sami mama suka gaisa sanan ta shige dakin Maryam a zaune ta sameta tana kallo a laptop dinta, tana shiga dakin ta fada kan gado ta fashe da wani irin kuka, a rikice Maryam tace kawata meya faru? Komai ma ya faru Maryam, yau asirina ya tonu nayiwa Sadik karya kuma da alama ya gane ni, cikin zumudi Maryam tace iya Sadik ne ya ganeki ko harda imran? Cikin kuka tace Sadik ne ya gano ni, amma nasan zai fada mishi, dafata Maryam tayi tace indai Sadik ne karki damu yasan komai



Maman Aysha
[22:35, 9/3/2017] β€ͺ+234 803 922 1122‬: πŸ‚πŸ‚βœ



Maman Aysha
[22:38, 9/3/2017] β€ͺ+234 803 922 1122‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady safnaπŸŽ‹πŸŽ‹

2⃣5βƒ£βž–3⃣0⃣

Kallon mamaki safna tayi wa Maryam tace ban gane yasan komai ba? Eh yaya Sadik yasan lbrn ki safna, in fact shine ma ya kara mana caurage akan kici gaba da nuna ke Yar masu kudi ce har lkcn da imran zai fada tarkonki sbda shima girman kan imran da tsanar da yake nunawa talaka tana damunshi, sunaji ajikinsu kmr kice zakiya magance matsalar imran, dariyar da yayi miki dazu tsokanar ki kawai yake, Amma yasan komai. Ajiyar zuciya safna tayi sanan tace gasky na fara tsorata da al amarin imran Maryam, sbda na fuskanci tsanar da yayiwa talaka ba karama bace, INA tsoron ranar dazai gane ni ba 'Yar wani bace, yanzu zancen da nake miki imran yana nan ya Gina gda na tro billions of naira, kuma yana nan yana sa ran iyayena su hade mishi gdn da kaya masu tsada, kuma shi bashi da wani buri daya wuce ace ya auri kyakkyawar mace, big girl kuma 'Yar masu kudi, yanada burin aurar yarinyar da tayi suna ita da iyayenta, ya kike tunanin zaiji duk ranar daya gane koni wacece? Ina ganin lkci yayi dazan fadawa imran gskiyar lbrina.

Uhm uhm safna wallahi karki soma, ko kina nufin kice min baki kamu da sonshi ba? Iam very sure kina son imran so me tsanani, kuma wallahi idan kika sake yasan lbrnki bazai taba auranki ba, ni INA ganin kawai kice ya tro parents din shi su sami baba Sharif ayi magana a zuwan shine uncle dinki, ya zama koda zai ganeki sai bayan an daura muku aure.

Anya wanan shawarar tayi kuwa? A yanzu nafiki sanin halin imran Maryam, bashi da mutunci kuma wulakanta mutun awajenshi ba wani Abu bane, gara na mutu da sonshi akan wulakancin dazan fuskanta a wajen shi

Dafata Maryam tayi tace karki damu my friend, kinsan INA tsananin sonki bazan taba yin abinda zai cutar dake ba, munyi mgna da salma kanwar shi insha Allah ba abinda zai faru, jiki ba kwari safna tace to shekenan Allah ya zabar min abinda yafi alkairi tace amin.


Tare suka fita wajen Sadik bayan sunsha hira da dariya sukayi sallama ya dauki safna ya kaita gda, tana shiga dakinta dake boys quarter gdn ko ajiye bag dinta batayi ba taji hjy turai tana kwala mata kira, jikinta yana kyarma taje cikin tsawa tace mata don uwarki sai yanzu kika ga damar komowa? Tunda lecture safe ne dake ai kinsan ke zakizo kiyi abincin rana yau Amma shine kika wuce yawon iskancinki ko? Zatayi mgna hjy turai ta dauke ta da mari har guda biyu, sanan tace wuce ki Dora mana girki Dan ubanki. Hawaye na zuba a idonta tace me zaa dafa? Yi mana jallop din taliya da salad, sai paper chiken kuma, da sauri safna ta shiga kitchen ta fara girki, sai kusan 3pm ta gama daki ta dawo ta shiga wanka tayi sallar azhar ko abinci bataci ba ta kwanta, saida tayi kuka me isarta sanan sanan wahalallen bacci ya dauke ta

A bangaran imran kuwa, Sadik yaje ya tsarashi akan abinda safna tace mishi na cewa dad din ta ne yake yawan kawo mata surprise visit shiyasa bataso takaishi gdnsu, kuma ya gamsu Sbd shi koda wasa be taba zargin cewa safna ba Yar masu kudi bace, sanan Sadik ya bashi shawara akan ya tura parents din shi kawai ayi mgnar aure kuma ya yarda da shawarar saidai yana tsoron yanda zai tunkari dad din shi ya fada mishi ya fasa auran Fareeda yanzu safna yakeso, saidai kuma yanda yake jin wutar son safna ba abinda bazai iyaba domin yaga ya mallake ta


Wai me kartu wacece safna ne?


Swanky lady safnaπŸŽ‹
[22:37, 9/3/2017] β€ͺ+234 803 922 1122‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady safnaπŸŽ‹πŸŽ‹

3⃣0βƒ£βž–3⃣5⃣

Mahaifiyar safna Yar asalin garin wudil ce a wata unguwa me suna Unguwar Sarkin Aska(USA) wanan shine dalilin dayasa safna take cewa iyayenta suna USA.

Mahaifiyar safna wato Jidda takasance marainiya ce, domin kuwa a haihuwarta babarta ta rasu, sai ya zamana ta taso a wajen kakarta, zaman jin dadi da annushuwa tayi a wajen kakarta, kuma ansata a makarntar boko da arabiya bayan ta gama primary sai aka Samar mata admission a WTC dala taci gaba. lkcn data shiga ss 2 Allah yayiwa kaka rasuwa daga nan saita koma gdn babanta da zama, ba karamin so yake nuna mata ba Sbd ita kadai ce yarshi a duniya, ganin haka sai inna kande ta fara kulla makircin da zata shiga tsakaninsu da babanta, kuma tun daga lkcn sai rayuwarta ta canja domin kuwa matar uban irn mugayen matan nan ne, daga karshe ma saitayi asiri ta rabata uban ya dena yi mata komai, da haka dai a daddafe ta samu ta gama secondary school, bayan ta gama sai samari suka fara kawo Kansu dake muguwar kyakkawa ce, kuma dake tayi kartu ta samu exposure sosai, da zataci gaba da kartu amma sai mahaifinta yaki yace wai ya tsani ganin ta agabashi sbda inna kande ta riga ta rabasu dashi Wani Dan me kudi ne yazo zai aureta aikuwa inna kande tace auren nan bazai taba yiyyuwa ba saidai idan bata raye, haka ta ringa bin malamai da bokaye ana asiri, daga karshe saita karbo wani mgni agun boka tasa mata a abinci tunda taci maganin kullum saitayi amai, cikin kankanin lkci ta rame tayi baki idonta sukayi fari Tass, inna marka ta dauketa suka tafi Asibiti ta hada baki da wani likita yana gwadata yace ciki ne da ita, ba irin kuka da rantsuwar da Jidda batayi ba akan ita bata taba tarraya da wani da namiji ba, amma sbda akwai asiri akan babanta fur yaki yarda, haka ya rufe ido ya tsine mata kuma yace tabarmishi gda bashi ba ita, wai dama kakarta ta gama bata ta, tun tana Yar karamar ta take bin maza.

Kuka take kmr ranta zai fita haka ta dauko kayanta ta fito yaje Mutanen unguwa suka cika suna kallonta kowa yana fadin albarkacin bakinsa, daidai nan wata hajya tazo wucewa tana ganin cincirindon mutane tace driver ta ya tsaya, fita tayi ta tambayi abinda yake faruwa aikuwa mutane suka bata lbri, karewa Jidda kallo tayi ta kanta kyakkyawa ce, kawai. saita kama hannun ta tace zaki yadda na tafi dake ki ringayi min aikin abincin sayarwa? Da sauri tace eh, janta tayi ta sata a mota suka tafi, amma wani abin mamaki ko darr mahaifin Jidda beji ba duk da besan matar data tafi mishi da tilon yarsa ba, Allah ya rabamu da sharrin asiri.

Kano ta tafi da ita suka sauka a unguwar sharada kwanar ganduje, gdn matar katon gidane ba laifi, kuma ajikin gdn hadadden restaurant din yake me suna hjy marka restaurant, abinci kala2 ake awajen harda su paper soup iri iri, daki guda hjya marka ta ware wa Jidda ta ajiye kayanta sanan tace zata sakata a wata catering skul 6month ake, tanaso ta kuyi abincin zamani da kuma snacks, hakan kuwa akayi cikin wata shidan nan ba abinda Jidda bata iya ba na nau'in abinci, kuma dake matar Nada kirki tanajin dadin zama da ita.



Ana cikin haka ne soyayya me karfi ta shiga tsakanin Jidda da wani saurayi me suna Nasir. Kyakkyawan saurayi ne da kallo daya zakayi mishi ka gane ba Dan kasar nan bane, amma kuma bafilatani ne domin kuwa farkon zuwanshi garin bayajin Hausa sosai sai filatanci. Nasir driver motar company alhaji Sharif ne, a boys quarter gdn alhaji Sharif yake da zama, dake uban gdnsa ne, sun shaku sosai dashi saidai shi kanshi alhaji Sharif besan asalin nasiru ba. Lkcn da maganar auren nasiru da Jidda ta taso da hjy marka taso taki Sbd ance baasan asalinshi ba amma sai Jidda tace zata aureshi a haka sbda a yanzu da ita dashi din ba bambanci tunda itama mahaifinta ya koreta.

Alhaji Sharif da hajya marka su suka tsaya akayi biki na gani na fada, amarya ta tare a boys quarter gdn alhaji Sharif, bayan sun gama cin amarci sai Nasir ya cewa alhaji matarsa zata ringa taimakawa da me dakinshi girki tunda taba zaune ba abinda take, ba karamin dadi alhaji yaji ba, amma ita hajiya turai Sam bataso hakan ba, sbda haka kawai taji ta tsani Jidda. Haka Jidda taci gaba da yin girki me dadi a gdn alhaji ba tare da ana biyanta ko sisi ba, ana cikin haka ta sami ciki murna a wajen Nasir baa mgna, bayan wasu wattani ta haifo kyakkawar yarta wacce saika rantse half cast ce, ranar suna aka sa mata suna safna.

Nasir da Jidda sun dauki son duniya sun dorawa safna lkcn data cika shekara 4 akasata a wata privt sch dake tanada mugun wayo ga surutu. Haka rayuwa taci gaba a tsakaninsu

Da alhaji Sharif ya fuskanci Nasir yanada ilimi, saiya nadashi marketers na company shi na Flour ya zama shiyake rabawa manyan yan kasuwa akan sari, kuma Yawo yakeyi gari gari, ana cikin haka ne tafyr sati guda ta tasowa Nasir zuwa Lagos, tunda sukaje kullum sai sunyi communicating da alhaji, ana saura kwana biyu alhaji yayi ta gwada layinshi yaji akashe, tun yana daukar abin kmr wasa har yazo ya zama babba, ba irin Neman da abokan tafiyarsa basuyi mishi ba amma baa ganshi ba, har Lagos alhaji yaje dakanshi Amma ko lbrnshi babu. Lkcn da Jidda taji lbri ba karamin tashin hnkli ta shiga ba, Sbd tsabar kuka da tunani saida ta hadu da hypertension. Daga karshe alhaji Sharif ya bata hakuri kuma yace taci gaba da zama a gdn shi zai cigaba da daukar nauyin safna, sanan ya bata mukullin gda a ja'een yace da mijinta yayi niyar bawa Amma tunda baa ganshi ba yabar mata.


Haka sukaci gaba da zama a gdn bayan safna ta gama primary alhaji ya nema mata admission a excel college taci gaba, a lkcn ne kuma Jidda ta fara koyawa safna varieties na girki, cikin kankanin lkci ta iya komai. saidai abinda

2 / 15