LADY SAFNAH COMPLETE HAUSA NOVELS BY MAMAN AYSHA.txt

Author :  Maman Aysha Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   3 / 15

6K to 9K   out of 43.3K words

yake damun Jidda shine ta fuskanci safna Yar karya ce, tanada jinkai kuma tanason nuna isa da nuna ita wata ce, tun tana karama ta lura da haka sai ta dauka ko yarinta ne, amma data girma saita ga abin nata karuwa ma yake. Tana yawan yi mata nasiha akan ta ringa tsayawa a matsayin da Allah ya ajiye ta, amma saita ringa cewa itama batasan tanayi ba kawai tsintar kanta take a haka, Amma itama ba ason ranta take ba, kuma bazata iya denawa ba.

Alhaji Sharif yayan Maman Maryam ne uwa daya uba daya, tun su Maryam suna kanan ake kaisu Hutu gdn, a dalilin haka ne suka shaku da safna sosai bayan sun gama secondary school sai Maryam tayiwa babanta mgna ya samarwa safna admission a BUK, a lkcn ne kuma alhaji ya tare a katon gdn shi dake nasarawa GRA, tare da safna suka tare sbda alhaji Sharif ya roki ummanta ta basu ita, saidai Sbd rashin kirkin Haj turai a boys quarter ta bata daki, ita kuma umma Jidda ta ta tare a gdn da alhaji ya basu na ja'een. su kuma yayyan alhaji Sharif Sakina da Rabi dis year suka gama Oxford university Kano

Cigaban labari.....

Maman Aysha
[22:40, 9/3/2017] β€ͺ+234 803 922 1122‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady safnπŸŽ‹πŸŽ‹

4⃣0βƒ£βž–4⃣5⃣

Waya alhaji kabeer ya dauka ya kira alhaji Sharif, wit respect alhaji Sharif ya gaisheshi, bayan sun gaisa yace kana gari ne? Yace eh INA nan, to don Allah idan ba damuwa zanzo anjima da yamma akwai mgnar da nakeso muyi, to shekenan alhaji, sanan ya kashe wayar.

Su hudu sukaje shida yayunsa guda biyu da kuma amininsa guda daya, cikin karramawa alhaji Sharif ya karbe su, bayan sun gaisa sukayi mishi bayanin abinda ya kawosu, ba karamin farin ciki alhaji Sharif yayi ba, ba tare da wani bata lkci ba aka yanke date din biki nan da 1month. Sun bayar kudin gaisuwa da kuma kayan sa rana 2 million naira, sanan sukayi sallama suka tafi. Bakin na tafya alhaji Sharif ya shiga mota ya nufi gdn UMMA Jidda mahaifiyar safna yayi mata bayanin komai, itama ba karamin farin ciki tayi ba, sanan tace ta bashi wuka da nama duk abinda ya yanke daidai ne.

Sai bayan sallar magrif alhaji Sharif ya koma gda, yana cin abinci hjy turai tace alhaji dazu wanne manyan bakin kayi ne naga kunata kaiwa da komowa gaida alhaji salmanu? Cikin farin ciki yace abin alkairi ni ya samu, alhaji kabeer mesikeli ne yazo, washe baki tayi tace alhaji kabeer a gdn nan? Lalle zaayi ruwa da kankara babban mutun irin wanan ai dole Ku gigice, me yazo yi wajen ka? Dansa yazo nemawa aure, wata guda ta saki cikin farin ciki tace Allah na godema, dama shakuwarku dashi har takai yayi sha'awar hada jini dakai amma baka taba kainin gdansa ba? Dariya alhaji yayi yace ba haka bane, su yaran ne suka hada Kansu, Allah me iko, kaga kuwa basu fadamin ba, wa yakeso acikin su? SAFNA, nan take faraar fuskarta ta dauke, safna kuma? Ita kuma a INA tasanshi? Wallahi nima bansani ba, an yanke date din biki nan da wata daya, cikin kololon bakin ciki tace Allah ya kaimu, tashi tayi ta nufi dakin 'yayan ta, tana shiga tace kunada labrn Dan gdn mesikelin naira ne zai auri tsinanniyar yarinyar nan safna? A zabure suka mike, cikin kidima sakina tace wa ya fadana miki mum? Babanku mana, iyayenshi sun zo har an saka date din biki, bura uba, shi yanzu imran duk izza da girman kan nashi akan safna ya kare? Ya rasa wacce zai aura sai me aiki, marar asali? To a inama ya Santa har ya fara sonta? Rabi tace duk yanda akai karya tayi mishi, ke baki kula da irin dressing din da take ba, kayan da take sawa ko mu bama sa irinsu, Tabb aikuwa yanzu zan kirashi dama na Dade da karbar no shi Dan banzan kwarjininshi da waulakancinsa ne ya hanani kiransa, dialing no imran ta fara......

A bangaran imran kuwa bayan abbanshi ya koma gida sawa yayi aka kirashi yayi mishi albishir da cewa angama magana zaayi biki nan da wata daya, cikin tsananin farin ciki yace alhamdulilla Abba nagode Allah ya kara girma, dariya Abba yayi yace amin my son. Dakinshi ya koma yayi wanka ya shirya cikin wasu orange shirt da black jeans ya fesa designer turare sanan ya dauki key din motarshi ya nufi gdnsu Sadik, daidai nan kiran Sakina ya shigo wayarsa saida tayi mishi 10missed Call be dauka ba, Da taga HK saita tura mishi text kmr haka

_salm ya jin dadi, wani lbri naji daya bani mamaki, kai yanzu duk wulakancin daka ringa yi mana a auran me aiki marar asali ka kare_

Saida ya karnta text din yakai sau biyar sanan ya fara dialing no, bugu daya ta dauka cikin kasaita yace wacece ke? Sunana Sakina Sharif murabus, a wajen mahaifina aka nema maka auran safna, kuma inaso kasani safna kuku din gdn mu ce, nasan be zama dole ka yadda dani ba sbda ta riga ta sharara maka karya, Amma idan kana doubting kaje ka samu safna zatayi maka bayani.

Tunda Sakina ta fara mgna yaji wani irin zafi a zuciyarsa sbda mugun bacin rai jikinshi har rawa yake, saidai har yanzu a Kasan zuciyarsa be yadda ba, cikin izza yace mata idan naje nayi bincike na gano kazafi kikayi mata wallahi saina daureki, be jira me zatace ba ya kashe wayarsa.

Maman Aysha
[22:42, 9/3/2017] β€ͺ+234 803 922 1122‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady SafnaπŸŽ‹πŸŽ‹

5⃣0βƒ£βž–5⃣5⃣

Kuka sosai safna take cike da tausayin kanta, kirane ya shigo wayarta tana dubawa taga Maryam ce saida ta sassauta kukan sanan ta dauka, cikin firgita Maryam tace safna meya faru? Komai ma ya faru Maryam, domin kuwa imran ya gano koni wacece, kuma ba wacce ya tsana a duniya yanzu kmr ni, lkci guda ya canja kmr be taba sona ba, na jefa kaina a bala'i Maryam ta karashe mgnar tana kuka, Maryam ce ta katseta da cewa yanzu kina ina? Ina hotoro, OK bari nazo na daukeki.

A daki suka sami mmn Maryam kallo daya tayiwa safna ta gane tana cikin wani hali, cikin kulawa tace safna meya sameki? Bata lbrn abinda ya faru sukayi tun daga farko har karshe, ai kuwa nan take tahau yimusu fada, tace kunyi kuskure ba kadan ba, ai duk abinda zakayi a rayuwa ka zamo me gsky duk rintsi Sbd baa taba cewa gskyr mutun ta kare ba saidai ace karyashi ta kare. Kama hanun safna tayi tace ke kuma safna dole ne kiyi hakuri ki rungumi kaddara sbda kinsan ummanki tanada hawan jini, kuma idan taji lbrn nan zata iya tada hnklin ta, dole ki guji duk abinda zai daga mata hnkli inaso kisa wanan abinda ya faru a matsayin jarabawa ce kiyi hakuri kinji? Cikin sanyi jiki safna tace to nagode mama, karki damu safna ai dake da Maryam duk daya awajena, zanyiwa yaya Sharif mgna yabarmin ke awajena na shiryaki sosai, sbda wanan matar tashi bazata iya yin abinda ya dace ba, phone dinta ta dauko ta kira alhaji Sharif tayi mishi bayani yace ba matsala shawara tayi zaizo ya sameta a gda su tattauna akan yanda bikin zai kasance. Tun daga ranar safna ta koma gdnsu Maryam da zama

A bangaran imran kuwa yana fita daga falon abbanshi dakinshi ya shiga zuciyarsa banda zafi ba abinda take more especially idan ya tuna cewa Baban safna driver ne, ummanta kuma kuku, meyasa safna ta munafurceshi? Yayi dana sanin sanin safna a rayuwarshi, ta cuceshi ta karya mishi duk wani budget dinshi, gashi ya tashi ya gina gda na billions of naira, ta ina zasu samu kudin da zasu yi mishi Jere mekyau a gdn? Ji yayi an dafashi yana juyowa suka hada ido da mum dinshi, a gefenshi ta zauna tace nasan kana cikin tashin hnkli, amma inaso ka kwantar da hnklin ka ka dena nunawa abbanka cewa ka daina son safna, idan ba haka ba zai iya halaka auran Fareeda, so ka lallabashi ana gama biki sai ayi mgna kuma inaso a kullum ka ringa nuna mishi kana son safna sbda duk ranar daka saketa bazaiga lefinka ba, so duk wanan bacin ran da kake daka auri Fareeda zaka denashi, kuma yanzu ba wani taro zamuyi ba, domin kuwa ni ko gayyata baxanyi ba, Dora kansa yayi akan cinyarta yace shiyasa nake sonki mum, sbda kinason duk abinda nakeso.

2wks later

Yau saura sati guda kenan ayi bikin safna da imran, saidai rabonda safna taga imran tun ranar da yayi mata rashin mutunci, sun kawo lefe Dan ubansu suma kuma sun hada musu abin arziki.

Shiri mmn Maryam take sosai, tunda ga Sudan ta dauki me gyara saida safna tayi 2wks bata fita, tayi wani irin kyau ta kara fari, sanan alhaji Sharif ya biyawa umma Jidda da mmn Maryam kudin jirgi sukaje Dubai suka sayo furniture's hadaddu,

Ana saura sati daya biki sukaje sukayi Jere a gdn imran dake badawa lay out sbda yace bazai kaita gdn shi na lodge R'd ba sbda Fareeda zaisa a gdn.

Jire akayi mata Dan ubansu, gdn safe content ne me 3bedroom da falo, sai kitchen, store da kuma dining area. Komai na falon orange and lemon green akayi, master room dinta kuma peach color, daya dakin red and cream color, daya dakin kuma brown. Gdn ba karamin kyau yayi ba sbda Maman Maryam muguwar Yar gayu ce.

Ranar Friday itace ranar da aka ware zaayi bikin dake rana daya zaayi komai agama, Saturday kuma a daura aure.

Maman Aysha
[22:43, 9/3/2017] β€ͺ+234 803 922 1122‬: πŸ‚πŸ‚
Swanky lady safnaπŸŽ‹πŸŽ‹

4⃣5βƒ£βž–5⃣0⃣

Phone dinshi ya dauko ya fara dialing no safna....

A bangaran safna kuwa yau lecture 4to6 ce lecture su ta karshe, suna fitowa suka shiga library sukayi assignment ana kiran sallar magrif suka fito daga library din. Motar Maryam suka shiga suka nufi gdn umman safna, da murna ta taresu a gdn sukayi sallar magrif sukaci abincin, umma tace safna dazu alhaji sharif yake fadamin ansaka rana, nayi matukar farin ciki Allah ya tabbatar da alkairi, kuma Allah yayi miki albarka, ji tayi gabanta ya fadi hada ido sukayi da Maryam saitayi mata alama da ido, dariyar yake tayi tace amin UMMA, sanan sukayi mata sallama suka tafi. Suna fita ta kira alhaji Sharif tace mishi don Allah yayi mata uzuri ta kwana agdn su Maryam, yace ba matsala duk daya ne.

Suna shiga gdnsu Maryam ko fitowa daga mota basu yi ba phone din ta ta fara ruru, tana dubawa taga imran ne cikin wata muguwar fargaba ta dauka, da dakekkiyar murya yace kina ina? Jiki ba kwari tace gdnsu Maryam, OK zanzo yanzu.

A 360 ya karaso gdn yana zuwa yayi yace ta fito waje, tana fita ya bude mata kofa yace ta shiga, ba musu ta bude ta shiga ko karasa rufe motar batayi ba ya figi motar suka tafi, wani gda ya wuce da ita yana faka motar yace ta fito da fargaba da komai tabi bayanshi, suna shiga falo ya kunna A/c sbda ya jike jagab da gumi, kallonta yayi da jajayen idanuwanshi yace zanyi miki tambaya, karki sake ki fadamin karya.

Ina ne gaskiyar inda parents dinki suke? Sanan kuma menene gaskiyar dangantakar Ku da alhaji Sharif? Kasa mgna safna tayi sai wasu zafafan hawaye da suke fita daga idonta, daka mata wata mahaukaciyar tsawa yayi, da har saida hanjin cikinta sukayi rawa, cikin shesshekar kuka safna ta fara bashi labarinta.......har saida taje karshe.

Ji yayi ya nemi yawun bakinsa ya rasa, tunda uwarsa ta haifeshi be taba shiga rudani irin nayau ba, cikin dashasshiyar muryarsa da dakyar take fita yace meyasa kikayi min karya? tun farkon haduwa ta dake nake fada miki cewa a duniya ba abinda nafi tsana irin talaka, meyasa tun a lkcn baki fadamin gskya ba har kika bari zuciyata ta fara sonki? Safna meyasa kika yaudareni ya karasa mgnar cikin daga murya, a zaune take a kujera amma batasan lkcn data zame ta zauna a kasa ba, wani irin kuka take da duk Wanda yaji saiya tausaya mata amma imran ko ajikinshi cikin sheshekar kukan tace lkcn Dana fara soyayya dakai bansan cewa baka kaunar talaka ba, sai bayan nayi zurfi a sonka sanan na gane, nayi kokarin na hakura dakai tun a lkcn amma saina kasa, sbda zuciyata ta riga ta kamu da matsainacin sonka, irin son da bazan iya rayuwa batare dakai.......shut up, son banza son wofi, sonda zai jawomin zubar da mutunci da kima a gari? Kina gani tun yanzu an fara fadamin bakar mgana, kamar ni ace na auri Yar driver da kukun gdn daya daga cikin yaran mahaifina? God forbid Allah ya kiyaye, kin cuceni safna, wallahi kin cuceni sbda koba komai kin barni da abin kunyar soyayyar da nayi dake domin kuwa soyayya dake abin kunya ne agareni, kuma inaso ki sani yin hakan shine kuskure mafi muni da kika tafka a rayuwar ki, na tsaneki safna ko son ganinki banayi, kallonta yayi da jajayen idanuwanshi yace tashi ki fita. Mikewa tayi jiri yana dibanta ta fice daga gdn dakyar, bakin wata bishiya ta samu ta zauna tana wani irin kuka me tsuma zuciya.

Imran yana fita gdnsu ya wuce, a sukwane yana zuwa ya wuce falon abbanshi, zubewa yayi agabansa yace don Allah Abba kayi min afuwa, na fasa auran yarinyar daka nemomin aurenta dazu, Ashe bata da tarbiya, yawon karuwancinta kawai take, d worst thing ma Abba bata da asali, ni gskya na fasa aurant....shut up Abba ya daka mishi tsawa ya kake Neman ka mayar dani karamin mutum bayan inada kima da mutunci? Da Kasan bakayi binciken ba kace a nemo maka auranta? To bari kaji na fada mana aure ba fashi dakai da ita, idan kaga baka aureta ba saidai idan bana Raye, Sbd haka fita ka bani waje, yana kokarin yin mgna Abba yace I say walk out from here, mikewa yayi ya fita zuciyarsa a dagule

Maman Aysha
[23:03, 9/3/2017] β€ͺ+234 803 681 8427‬: πŸ‚πŸ‚

[23:03,

3 / 15