L U'U L U'U BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY HUGUMA.txt

Author :  Safiyya Abdullahi Huguma Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   10 / 21

27K to 30K   out of 62.7K words

ta fada zuwa hannun yaran gidan baffanninsa.....yasan komai na Allah ne.....muddin kuma akwai yiwuwar zaman sarautar hannunsu ba wanda ya isa ya karba,ballantana ma shi bai dauki gadon da wani zafi ba.... Don ko a baya zamanin kakanninsu ta taba barin hannun kakansa sai daga baya ta dawo musu.

"Ranka ya dade.....bawai zakayi sabbin amare ba fa kuma a juya mana baya" Ta fada cikin sigar tsokanar data sakashi murmusawa har kyakkyawar wushiryarsa ta fito.

★★★★

Qarfe shida da rabi na yammacin ranar motar qirar Lamborghini ta ajiyeta a sashen ajiyar motoci na musamman dake gidan.

Bude murfin motar akayi,daga gaba wani kakkauran matashi dake da komai baqi ya fito yana bude seat din baya.

Iska ta furzar daga bakinta tana jefo qafafunta waje.......gaba daya jikinta yayi laushi saboda dadewar da tayi a zaune a office.

Yau din harta gota lokacin tashinta saboda alwashin da taci tabbas sati me zuwa sabbin design na kamfaninsu zai fara zaga kasuwannin duniya.

Duk da a jigace take,amma hakan bai hana bayyanuwar kwantaccen kyan da take dashi ba. Jikinta yana busa lallausan qamshin nan nata a kowanne motsi da zatayi,iska kuma na dada zaqulo qamshin nata sanda take kada tattausar lafayar data nade jikinta da ita,lafayar data yafata iyakar kafada,kanta zaune das da daurin dankwalin wani veil baqi me taushi daya zauna mata kamar hula.

"Birra" Ta kira sunanta a gajiye..... Gajiyar data sake zame mata ado,don sai suka qara adadin yauqin halitta da yangar data zame mata ta asalin halittarta. Sign kawai tayi mata na ta karbi tarkacen office dinta dake hannun saaleem ta fara takawa zuwa gaba tana furta.

"Wash Allah na". Gami da yarfar da hannu.

Taku goma kacal tayi idanunta suka sauka kan Shehinaz ita da baqonta dake zaune suna facing juna..... Da alama magana ne sukayi me matuqar muhimmancin da har basa sanin meke faruwa daura dasu.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*MY NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*


PAGE 14


Idanu akhnan ta fiddo tana kuma rage dan saurin data aro daaa don isa ciki ta watsar da gajiyarta. Mamaki da tsoro suna cikata tana kuma sake ware idanunta akan baqon Shehinaz din,wanda bata sani ba,kaifin idanunta ne suka sanya yaji kallon a jikinsa ya maido dubansa sashen da take?,abinda ya dauko hankalin Shehinaz kenan itama ta maido dubanta inda taga yana kalla.

Hannu ta dagawa akhnan cikin sakin murmushi,tashin farko taji ba zata iya maida mata koda da daga hannun ba bare murmushi ballantana akai ga takawarta zuwa inda suke,sai kawai ta dauke kai ta maida hankalinta zuwa hanyar da zata sadata da ainihin gidan zuciyarta na wani irin bugawa,bugawar da batasan meye dalilinta ba.....bacin rai ne?,ko kuma mamaki ne?,ba zata iya tantancewa ba.

Da kallo dukkansu sukabi bayanta har ta bacewa ganinsu,sai Shehinaz ta dauke dubanta ta mayar kan Jamaal tana maye mamakin dake saman fuskarta da murmushi.

Duk yadda taso wucewa daki kamar yadda ta tsara kafin ta iso gidan amma sai ta yada zango a parlor,abinda kusan ya bawa duka hadimanta mamaki. Saboda wani baqon abune da bata saba yinsa ba. Lokuta da dama ma idan ta dawo ta wuce ciki ba lallai bane ka sake ganinta ba sai washegari.

Hannatou keda hidima da ita tana kai kawon bata abunsha da tasan takan sha idan ta dawo gidan. Buhaina na qoqarin tattare kayan office din data cire a nan,takalminta laffayarta dan kwalinta da jewelry dinta duka data zare. Ta saba komai tana ajjiyeshi ne a inda yayi mata,akwai masu kula da komai din su tattalashi. Xasu kwashe jewelry dinta a gogeshi kowanne a maidashi cikin box dinsa. A sake goge takalmanta ayi musu feshi a maidasu cikin qawatacciyar ma'ajiyar takalman dake cikin dressing room dinta. Wannan ya sanya komai nata idan ka kalla zakace ba'a sakashi ko ba'a taba sakashi ba,don hatta da qasan takalmanta babu wani datti da zai alamta maka haka. Tana da mugun qyanqyami.......sai Allah ya hadata da hadimai na amana dake iyayi mata komai kamar ko fiye ma da yadda takeso. Ganin hankalinta ba'a gurin yake ba sai Hannatou ta janye hirar da take dan sako mata.

Agogo ta kalla dake bango don tuni ta cire na hannunta an wuce mata dashi. Ta soma gajiya da zaman jiran shigowar Shehinaz,kuma alamu sun nuna bata da niyya ko yunqurin shigowa a yanzu,dole ta miqe don wucewa ciki ranta na sake sosuwa. Taso qwarai Shehinaz ta shigo da zafi zafinta kafin ta sauya ra'ayin yi mata magana.

Dab da zata wuce hanyar da zata sadaka da dakunan baccinsu taji shigowar aisa. Ta biya ta wani guri ne bayan sun tashi daga office,don haka yau tafiyar tasu daban daban take.

"Kinga Shehinaz?" Ta tambayeta da muryarta a sanyaye. Bude idanu aisa tayi tana kallonta.

"Eh na ganta ita da jamaal.......so masha Allah wallahi......Il a une maturité étonnante,II a une apparence trés religieuse(akwai alamun kamala sosai tare dashi,da alamun addini sosai tare dashi)" Ta fada kanta tsaye fuskarta na gasgata abinda ta fada har cikin zuciyarta yake fitowa.

Baki da idanu kawai akhnan ta saki tana duban aisa,maqogoranta taji kamar ya bushe duk da bata jima da shan ruwa ba.......ta tattaro ragowar yawun bakinta ta hadiya sannan tace.

"Aisa.....Êtes-vouse conscient de ce que vous dites(kina sane da abinda kike fada?)......kina tunanin mace irin Shehinaz ta dace da kidahuman mazan da babu wayewa a tare dasu?"

"Qidahumai?" Aisa na maimaita kalmar cike da mamaki.

"Biftu?.....wai me kika dauki ma'anar KIDAHUMIN NAMIJI?.....Namijin da baiyi karatun boko ba?......namijin da ilimin arabiyya kawai yake dashi?,shine kidahumi?.....kinsan kura kuren dake cikin wannan tunanika naki guda biyu?".

"Ehnnnn........ki gayamin,Vouse lui lavez le cerveau(ke kike wanke mata tunani).......wannan mummunar hanya ce......hanya ce mara bullewa.......a ajin da darajar rayuwarta?........namiji me wannan suffar II n'était pas qualifié(bai cancanci) ya zama mijinta ba.......ba wani guri da mataki na rayuwa da zai iya tsaya miki........ba wani abu me muhimmanci da zai iya tunkararsa saidai ya tsaya a bayanki ki zame masa garkuwa.......banason irin wannan namijin......koda yaushe nafison NAMIJI ZAKI NAMIJI GARKUWA.......wayewarsa da iliminsa basu isa su tsaya a kowanne mataki da me ilimin boko zai tsaya ba.......mu gaya ma kanmu gaskiya kuma itama ki gaya mata gaskiya...." Ta qarashe maganan cikin fada da bacin ran da aisa ta jima bata ga ta yishi ba,sai kuma tayi gaba fuuuu da dan guntun saurinta ta wuce dakinta har aisa na jiyo qarar rufe qofar duk da qofofine da sam saika qaraci zamanka dasu bakaji qarar koda motsinsu ba.

"Mon dieu du ciel(oh Allah na)" Aisa ta fada tana komawa ta zauna saman kujerar dake daura da ita. Ba zafi abun yayi mata ba......mamakin dauka zafin da akhnan din tayi ne yake daure mata kai. Tabbas a dukka su ukun suna iya shawara akan rayuwar daya su tsaida matsaya ko si zartar. Tun asali tasan burace buracen akhnan akan iri mijin da ya cancanci ta aureshi masu yawan gaske ne.......tun asali tasan akhnan din burinta babba a wajen namiji ya zama me cikakkiyar wayewa.......me zuzzurfan matakin karatu a duniya gaba daya.......namiji me zarra sosai......tsayayye jarumi maras tsoro ko shakka......bata da burin namiji me ilimin addini muddin yana da ilimin da zai kiyaye ibadarsa daidai........abu na qarshe data tsana tafi kuma raina ajawalinsa shine.......namijin da zaiyu karatun arabiyya. Takan fadi wani lokaci idan magana ta tashi.

"Banga hikima ba......banga basira da wayo a karanta arabic ba.......a matsayinka na namiji da aka sani da zallar gwagwarmaya.......ina wani gwagwarmaya a karatun da iyakacinsa ka zama malami me koyarwa ko karantarwa?.

A sannan zata iya cewa bata fiya ganin aibu ko rashin dabara a maganganun akhnan nan ba.......amma sannu a hankali da girma ya ratsasu.......rayuwa ta rarrabasu zuwa wasu qasashe......cikin jinsina da yare sai dukka wannan tunanin yabar jikinsu.....Musamman su din da karatu ya cilla aisa Egypt yakai Shehinaz madeena.........akhnan tata qaddarar ta kaita French. Kusan kowanne ya dawo ne da sabon tunani......sabuwar rayuwa da sabbin mutane cikin rayuwar tashi.

Tsaye kawai tayi gaban babban madubin dake toilet dinta tana duban kanta da kanta. Iska take zuqa tana fesarwa tanason saisaita yanayinta,tsahon wasu mintuna zuciyarta ta fara magana da ita.

"Ki nutsu akhnan......ki nutsu.......baki isa ki sauya qaddarar kowa ba.......baki isa ki tsarawa su aisa qaddararsu ba.......taki qaddarar ce kadai a hannunki......kina iya lanqwasata ta sigar da kikaga dama(a nata tunanin kenan)......karki bata wannan relation
Amitié din(dangantaka da qawance),damuwa da damuwar wani ba dabi'arki bace.....ki concentration akan abinda yake gabanki".

"Mais(amma) Shehinaz ce fa?" Ta fadi a fili da siririyar muryarta tana jin abun yana tsaye mata a wuya,tasan ta damu ne kawai saboda Shehinaz dince.......su din kamar wani sashe ne na tata rayuwar.

"Idan Shehinaz ce zuciya da tunaninku ba daya bane......dole a samu banbanci cikin rayuwarku" Wani sashe na zuciyarta ya sake tunasar da ita.

Dole ta tattare komai tayi wani watsin tsiya dashi,duk da tana ji abun yana ci mata zuciya,tayi wanka ta fito har sannan bata sake jin motsin kowa ba,sai ta zauna a nutse ta shirya cikin wani budadden wando da blouse data lafe ta fidda shape din jikinta.

Sanda Shehinaz ta shigo aisa ta saukewa complain din abinda akhnan din tayi mata,ta diba da zummar binta daki ta gaya mata dalilin mata hakan,don bata taba ganin jamaal ido da ido ba hakan ba yana nufin baqo bane ko bare. Riqota aisa tayi,don tasan rigimarsu bata qarewa. Akhnan shariya......Shehinaz mita da gaza yin shuru akan komai indai ya shafesu.

"Jamaal bai yiwa akhnan ba.....saboda II semble trés religieux(yayi zubin masu addini)......har yanzu wannan tsohon tunanin yana tare da ita......mais(amma) idan kin yarda dani.....wannan lokacin kiyi mata irin abinda takeyi mana?" Aisa ta shawarci shehinaz,dan fidda ido shehinaz tayi tunda aisa ta fara maganar

"Me kenan?"

"Ki koyi shariya da basarwa.....karkiyi qorafi akan abinda tayi,Arrête de te plaindre d'elle(ki daina qorafi a kanta)indai akan Jamaal ne,Laisse-la vivre comme elle veut(ki barta tayi rayuwarta yadda takeso)yadda kuma ta tsara......kin fahimta?". A nutse shehinaz ta gyada kanta,ta fahimci abinda aisa ke fadi,wanda dama wasu lokutan idan ta cakude a tsakaninsu aisa din kadai tunaninta ke zama a jikinta ta ajiye mafita guda daya.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*

PAGE 15



*_ETHOPIA🇪🇹_*

*_oromia region_*
*_jimma_*



K'abilar oromo daya daga cikin manyan qabilu ne da qasar Ethiopia ke dasu. Qabila ce data kasance ta musamman kuma ta biyu da yarenta yafi yawa a qasar Ethiopia din(afaan oromo),idan ka cire yaren Amharic yaren oromo shine na biyu da sukafi yawa cikin qasar Ethiopia din.

Qabila ce da take da mawadata sosai,suna da qarfin arziqin,hakanan mafi akasarin al'adunsu suna nuna irin qarfin arziqin da suke dashi. Al'adun yaren oromo na dabanne,wasu irin al'adu na musamman girmama manya.....girmama yanayi gaskiya dayin adalci kyautata mu'amala tsakaninka da jama'a.

Yanki na musamman suke dashi......da yawansu kuma sunfi yawa a jimma......wani babban gari dake dauke da wani irin yanayi(weather)me matuqar kyau dadi da kuma nutsuwa. Saidai hakan bai hanasu rayuwa cikin garuruwa da dama a qasar Ethiopia din ba.....kamar addis ababa capital na Ethiopia din da sauran garuruwa.

Duk da kyau irin na al'ummae Ethiopia,amma qabilar oromo kyansu na dabanne. Wata irin launin fata garesu......da wani irin hanci da launin baki(lips) da yake sake bambanta da kowacce qabila cikin qasar ta habasha.



*_irreechaa festival day_*


*ABA JIFAR PALACE (Aba jifar mosque national mosque jimma)*


Ba abinda ke fita daga ilahirin manyan sifikun dake da dogon zangon cimma kunnuwan al'umma na nesa da kusa.....saboda ingancinsu da yadda aka zamanantar dasu face daddan sautin karatun al_qur'ani me girma da qira'ar fitaccen makarancin alqur'anin nan dan asalin qasar habasha Ethiopia wato sheik afif muhammad taj. Sak da sak muryar ke fita da wani irin kwantaccen karatu da muryar dake qara nutsuwa cikin zukatan masallatan dama wadanda ke nesa da masallacin ba sallar suke bi ba.

Wata muryar da ta zame wa al'ummar yankin ta daban kuma ta musamman.......duk da cewa salon karatun sheik afif taj ne.......amma kuma sautin muryar ba tashi bace sam sam. Akwai wani irin taushi da amo daya sake banbanta muryar data sheik afif taj.

Duk da ta kasance yau din ranar juma'a ce.......amma cikar masallacin ta zama ta daban da kowanne lokaci saboda dalilai guda biyu. Dalili na farko yau din tazo musu a watan October ne......daidai da ranar da suke gabatar da bikin al'ada na irreechaa......biki ne ko ace festival da ya jima cikin qabila da yaren oromo ana gabatar dashi shekaru masu yawan gaske.....bikine da kafin musulunci ya mamayi qasar sukeyinsa don godewa abun bautarsu a shekaru daruruwa da suka shude,saidai bayan zuwan musulunci tun daga zamanin king Solomon da queen sheeba sai aka musuluntar dashi ya zamana daidai da tsarin da bai sabawa addini ba.

Abun yaci gaba da kasancewa a haka har kawo yanzu da moti(sarki a yaren oromo)abba jifar abba yake kan tashi sarautar. Sarautar da a wasu fuskokin iya tsari tafi da mulki da kuma shigo da zallar wayewa a cikinta yaso yayi kamaceceniya da tsarin sultane muhammas hammud.

Ya maida tsarin ya sakeyin daidai da yadda zai dace da addini. Festival din ya sanyashi ya zamana ranar ciyarwa ga marasa qarfin da dukka ya kasance daga yaren oromo dama yankin oromo gaba daya,ba iya jimma kadai ba. Ranar ya sake maidata ta zama ranar kyauta sadaka da miqa kayan abinci wa mabuqata marayu da marasa qarfi. Abun zuwa yanzu yayi girma da fadadar da bawai yankin oromo kadai ba......ana fidda abinci daga taskarsa da kuma masarautarsa a irin wannan rana da yayi yawan da ake fita dasu wasu garuruwan dake cikin qasar habasha gaba daya.

Bayan kammala taron akwai zaman addu'a da saukar qur'ani da akeyi na musamman don sake samun wanzuwar zaman lafiya da yauqaqar arziqi da albarkar rayuwa ga kowa. Saidai wannan sashen,an qirqireshi ne qarqashin jagorancin d'ansa *Prinsii(yarima)SHEIK MUHAMMAD HAISAM ABBA JIFAR*.

Shi yake kula da wannan sashen,shine kuma yake dauke da nauyinsa da dukka iyawarsa. Jajirtaccen d'a guda daya daya zamewa mooti abba jifar daya tamkar da dubu. Duk da bashi daya ya haifa din ba........amma ya zame masa na daban da samun irinsa ba nan kusa ba.

Bashi kadai ba.......hatta da masarautar oromo dama yankin gaba daya sun shaida da hakan,wannan ya sanya ko a yau cikar masallacin SHEIK HAISAM na daga cikin dalilin sabbaba shi.

Yariman da kaf tarihin yankin oromo ba'a taba haifar irinsa ba........yana da wasu irin personality daya jawo masa farinjinin da yake bawa mahaifiyarsa tsoro.......farinjinin daya sanya a dole ta tsaya tsaiwar daka da dukka qafafunta wajen nema masa kariya ta kowacce fuska,ta kuma kowacce halastacciyar hanya.

Cikin nutsuwa da kamala ya sallame sallar,kafin sauran daruruwan mutanen dake binsa jam'i a babban masallacin suma su sallame,ciki kuwa harda mahaifinsa mooti abba jifar.

Shuru masallacin ya dauka na wasu mintuna,sanda yake sadda kansa qasa yana karanta.

"Astagfirullah astagfirullah astagfirullah,Allahumma antassalam,wa minkassalam,tabarakta ya zaljalali walikram,la'ilaha illallah,wahdahu la sharikalahu,lahul mulk wa lahul hamd wa huwa ala kulli shai'een qadir,Allahumma la mani'a lima a'a daita.....wala mu'udiya lima mana'ata wala yanfa'u zaljaddi minkaljadd". Can qasan ranshi,ya dora da gajerun azkar da akanyi bayan sallamewa daga sallah,sannan ya motsa cikin cikakkiyar nutsuwarsa yana fuskantar al'ummar dake bayansa cikin sahu.

Dukkaninsu sa'annine na mahaifinsa sarki abba jifar dama wadanda suka girmeshi,idan ka cire mutum biyun da suka kasance sa'anninsa ne wato omari da taarik.

10 / 21