L U'U L U'U BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY HUGUMA.txt

Author :  Safiyya Abdullahi Huguma Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   8 / 21

21K to 24K   out of 62.7K words

a fili yana qarewa fuskarta kallo. Baisan kallonta daga nesa ya rage mata kyau ba sai daya matso kusa da ita.

"Sunana ruslan........" Katsewa maganarsa tayi saboda wani lumshe ido da tayi gami da budesu lokaci daya,wanda suke gaya masa

"Sai me?.....me ya shafeni?".

"Bala'i" Ya fada cikin ransa yana jin yadda wani gumi ya fara yanko masa. Yasha ji cikin abokansa suna firar nau'ikan mata masu tsananin aji.......yadda wasu matan suka qware wajen baiwa namiji amsa da iya qwayar idanuwansu,bai taba dauka da gaske bane......bai kuma taba dauka magana da idanu kawai zata saka ka fahimci me mace ke nufi ba sai yanzu.

"Ammmm.......kiyi haquri......ban nema izini ba ko?......duk da naga kamar daga daya daga cikin masarautunmu kika fito ko?". Wani abu ne yazo ya tsaye mata iya wuya,bata taba tsammanin saqon data aike masa bai isheshi haka ba.......

"Baka fahimta ne?" Ta fara tana juya hannunta gamida da ware yatsun hannun.

"Subhanallahi" Bakinsa ya motsa ya furta can qasan maqoshinsa yana jin maqogoronsa yana bushewa. Komai nata me burgewa ne.....me kuma daukan hankali ne.......komai nata daga kusa yafi kyau da qayatarwa.......tabbas idan yace a kowanne qarni irinta kadan Allah ke halitta cikin mata baiyi kuskure ba.

Sanda yakai qarshen wannan tunanin tuni harta cusa earpiece a kunnenta,ta lullube idanunta ta kuma ja blanket dinta ta rufa har kanta ruf zuciyarta na mata suya.

Bayan first class a flight batasan kuma wanne guri zata shiga ta boyewa idanuwa ba.......ashe har first class dinma an fara samun mutane marasa aji irin wannan mutumin da ko sunansa ma bata gama fahimta ba ballantana ta riqe.

Ya fahimci zamansa a wajen bazai amfana masa komai ba,bazai kuma maganta masa komai ba,don haka ya miqe tsam daga gurin,zuciyarsa tana bashi shawarar ya tunkari aisa,don ya fahimci kamar ta fita sauqin kai da iya mu'amala,wataqila ta samo masa kanta.

Bata ko sake bude fuskarta ba bare tasan yabar wajen ko baibar wajen ba. Har suka gama awannin da zasuyi,jirgi kuma ya saukesu a Diory hamani international airport.

A nan ta taras da driver dinta da kuma security dinta mutum uku suna jiranta,wadanda suka kasance tsaffin sojoji da suka samu horo me kyau suka kuma goge ta fannin tsaro da kuma bada tsaron.

Tayi zaton a motar aisa zata sake ce mata wani abu,amna sai taga bata qara cewa da ita komai ba,hasalima Mac book ne a hannunta take wani sabgar daban,sannu a hankali har suka isa unguwar tasu.

Commune I,unguwa ce data kasance mazaunin al'ummar dake da sukunin rayuwa sosai koda cikin Niamey din ma. Area ce data qunshi manyan gurare,kamar ofishin jakadancin qasar amurka manyan makarantu masu tsada da daraja na 'ya'yan masu hannu da shuni da sauransu.

Avenue dinsu suka shiga wanda ke cike da security dake kula da motsi da kuma kai kawo na avenue din gaba daya. Tun daga gate na farko security din dake tsaron gurin ke saluting motar. Motar masarautar agadez fitacciyar mota ce,daba wani guri da zata ratsa ba tare da ta fita daban ba.

Gida me number shida anan motocin sukaci burki,basu ko danna horn ba babbar qofar da zata sadaka da farfajiyar harabar gidan me wani irin adon qarafuna masu daukan hankali dake nuna sarauta a jikinsu suka bude motocin suka shige ciki.

Kusan kowanne ma'aikaci dake cikin gidan tsaye yake yana jiran isowarta,isowar data sanya kowa sake shiga nutsuwarsa har zuwa sanda birra ta bude mata motar ta sanyo qafafunta waje.

"Barka da sauka.......maraba da isowa........Bienvenue chez nous(barka da dawowa gida)..........Content de vous revior(muna farinciki da dawowarki gida)". Hannu ta daga musu sannan ta juya zuwa cikin gidan hankalinta yana kan hannatou. Wani lokaci irin wannan yanayin yana kasancewa takura a tare da ita,duk da kasancewarta mutum me tsananin jin girman da take dashi.......amma yanzun bataga dalilim taruwrasu ba dukka haka suna marabtarta. Inda kowa yayi zamansa zata nemeshi idan buqatar hakan ta taso.

Wata dabi'a ce a cikin jininta,sam bataso bata kuma qaunar a dinga shiga al'amuranta muddin ba itace ta gayyatoka ba. Ita dinma tana da dabi'ar yin halin ko in kula da al'amuran wasu,koda ya shafeta ballantana bai shafeta ba.

Hannatou ita ta kasance kamar wata idanu na me martaba a nam Niamey gidan da akhnan ke rayuwa......hadima ce itama da asalin kakanninta suka kasance bayi ne ga kakan akhnan sarki muhammad agg bin muhammad agg abba.

Tana da wani matsayi daya sha banbam dana sauran dukka hadimai da bayi,don hatta iyayenta basu mutu a mazaunin bayi ba,sun samu 'yancin kansu tun zamanin sarki muhammad agg din.

Tana iya yiwa akhnan gyara,tana iya nusasheta kan wasu abubuwan ta sigar shawara da hikima da dabaru da Allah ya hore mata a shekarunta da Allah ya bata.

Akwai sabo tsakaninta da akhnan din a yawancin lokuta,duk da sabon bai hanata aiwatar da duk abinda take ganin yayi daidai da tsafinta da rayuwarta ba,koda kuwa a hangen hannatou hakan ba daidai bane. Tun tana da shekaru goma a duniya hannatou ke tare da ita,kebantacciyar hadimar da ta dauki nauyi da dawainiyar wahalarta tun kafin tasan kanta,wannan dalilin ya sanya da wasu abubuwan akhan din take sauraren hannatou din,ta kuma sake da ita har sama da yadda take sakewa dasu birra kuwa,duk da yadda suke 'yan kusa kusa da al'amuranta.

Ajiyar zuciya ta saki me nauyi sanda ta zauna sosai saman gadon nata gana kuma sheqar daddara iskar da dakin nata ke bayarwa. Tana matuqar qaunar dakin qwarai da gaske,dakin yana da wani irin yanayi na musamman da kuma tsarin ginin da ya dace da zabin akhnan din. Ba dakin kawai ba,gidan gaba daya na musamman ne a wajenta,saboda yadda take samun sakewa sosai da kalar yanayin da tafi buqata a rayuwarta. Ba gidan bama,ita kanta Niamey na daya daga cikin garuruwan da take so sosai,saboda tana bata irin yanayi da nutsuwar da take buqata a yawancin lokuta fiye da agadez.

"Mun dauka zaki kai zuwa wani satinne biftu" Hannatou dake maida luggage din akhnan inda ya kamata ace suna zaune ta fada,da sunan da banda hannatou din ba wani cikin hadimai dake kiranta dashi sai ahalinta kawai.

"Na gama abinda ya kaini hannatou.........dama kawai rigima ce irin ta sultane" Murmushi hannatou ta saki kawai,ta sani indai biftu din ta fadi haka sultane din yayi wani da baiyi daidai da tsarinta ko abinda takeso ba kenan.

"Ran sarki ya dade......kullum hangensa shine yadda biftu zata zama mutum ta musamman......"

"Banda a nan hannatou.......na taba ganin inda aka tursasawa mace tayi aure bisa dole?" Ta fadi da alama maganar har yanzun bai qare ba a ranta. Abinda hannatou keyi ta bari,ta dawo gefan akhanan tana taimaka mata wajen fidda takalmin qafarta da take cirewa da qyar,tabbacin hidimta mata a komai nata da zatayi ya zame mata jiki.......bata iya yin komai da komai wa kanta a karan kanta kenan inaga hidimar da ba ta jikinta ba.

"Koda yaushe sultane me gaskiya ne.......sultane me hangen nesa ne.....zai kuma ci gaba da kasancewa hakan har abada koda akan kanki ne biftu........a ganina da zaki bude zuciyarki ki fahimci maganganunsu da zaifi alkhairi da alfanu......aure cikar diya mace da qarin darajarta ne......."

"Wacce daraja hannatou?......ina daraja wajen zama qarqashin wani bisa dokokinsa da umarninsa........ina daraja wajen rayuwa cikin mafarkin wani ba naka mafarkin na qashin kanka ba?" Tayi maganar tana waro manyan idanunta wane kamar waddda taga wani abun tsoro daban.

Kai hannatou ta girgiza tana murmurshi,ba shakka sai yau ta gasgata akwai tarin tasirin quruciya akan akhanan ba 'yar kadan ba.......ta sani da dadewa cewa duk abinda yazo bakinta tana fadi muddin iya gaskiyarta kenan,sai a yau ta sake yadda da hakan. Ta manta su din suna rayuwa ne qarqashin umarnin wasu mafarkin wasu kuma rayuwar wasu?,amma hakan bai rage musu komai ba saima daraja da suka samu ta silar hakan da ingantacciya kuma amintacciyar rayuwa.

Tana can tana laluben ta yadda zata fahimtar da akhanan din ta tsinceta har ta miqe tana fadin.

"Zanyi sallar azahar.......bayan nan inaso na kwanta na huta........banaso a tasheni sai zuwa sanda na farka"

"An gama zuciyar sarki zinariyarsa.........a huta lafiya" Ta fadi tana miqewa da takalman akhanan din,tayi musu mazauni sannan ta fice tana rufe mata qofar.

Hankali kwance ta dauro alwala sannan ta fito,tana jinta a sake kamar dan prison din da ya samu 'yanci. Kayan jikinta ta sauya zuwa Palazzo pant da wata cross front blouse data fidda qirarta. Wani irin shape gareta da tasha jin aisa da Shehinaz na maganar muddin zata saka kayan da zasu lafe a jikinta ko yaya ne. Boobs dinta ne kawai basu fiya girma ba,don aisa tace inda sunfi haka girma tabbas fitinar sai tayi yawa Kuma. A dole a sannan ta saka akhanan din dariya,duk da ba'a cikin mode na dariyan take ba,don suna tsaka da fidda lissafin shekara ne na kamfani,abubuwan duka tana jin sun cabe mata.

After dress ta dora saman kayan,tayi Rolling da babban mayafinta tayi sallah. Dogayen riguna ne daban da ita wanda aka ware mata don yin salla,a gida ko a office,don bata da wani hijabi guda daya da zatace ta mallaka.

Taci bashin bacci jiya,don bata kwanta da wuri ba,wannan ya sanya tana kammala sallar ta zare dogon rigar da mayafin ta watsar a nan kamar yadda ta saba don tana da masu killace mata ta haye gadonta. Kusan dabi'arta ce haka,ba wani abu da takeyi bayan sallah daya wuce tashi daga gurin. Sau tari kafin takai haka suna sallah tare da sultane,tana mamakin yadda bayan sun gama sallar yakan dade saman dardumarsa kafin ya tashi,koda ta tambayeshi murmushi ya saki,ya kuma gaya mata alfanun hakan.





zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer πŸ‡³πŸ‡ͺ*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITAπŸ‘‘*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
πŸ’Ž *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*πŸ’Ž


*H U G U M A*


PAGE 12



"Akwai azkar masu yawa da akeso baya mutum ya kammala sallah ya yisu kafin yabar gurin......bugu da qari kuma zama a inda mutum ya idar da sallah ba tare daya tashi ba ko yayi magana,yana samun ribar nema masa gafara daga wajen mala'ikun Allah har sai ya tashi daga gurin,to kinga inda bawa zai dawwama a wajen zaiyita samun gafarar Allah ne ba yankewa,wannan ya sanya zakiga wasu mutanen sun lazumci zaman masallaci.....sallah bayan sallah". Kai kawai ya gyadawa sultane,ita sam irin mutanen nan ma basa burgeta,tana musu kallon mutanen da suka takura rayuwarsu ne kawai,bayan ba haka ubangiji yake ba,basai ka tsananta ko zurfafa akan komai,indai zaka kiyaye haram da halak shikenan. Da tanayi subhanallahi walhamdulillah wa la'ilaha illallahu wallahu akhbar kowanne talatin da uku......to amma daga baya da rayuwa ta miqa,abubuwa sukayi yawa saita watsar,sai lokaci bayan lokaci.

Akwai malaminta da sultane ya dauko musamman don koyar da ita karatun addini,saidai sam rakiyar batayi nisa ba tace sam malamin baiyi mata ba. Ta kuma dora masa wata muguwar tsana da har takai kafin ya iso gidan zaa nemeta a rasa,ko zaiyi awa nawa kuma babu me sakin ganinta har sai ya tafi. Sam sam bata jin dadin karatunsa.......yana cikin mutanen da basu iya koyarwa ba sam sam,ta wani bangaren kuma a hankali ta fahimci mutum ne shi meson zuciya sosai,kamar irin mutanen nan da ake kira 'YAN CI DA ADDINI,ko ita yana iya roqo,duk da a sannan sultane yasa an tsaya masa da komai,albashi me kyau ci da sha na iyalinsa gaba daya. Baiyi karatun Boko ba ko kadan...... Hakanan karatun addinin nasa bai azashi daidai da yadda yazo daga asali da tushensa ba,asalin daya kasance salsala kuma tushiya ga dukka wani ilimi da wayewa da bature ko me jan kunne ke taqamar yana da ita.......wannan ya sanya duk wata wayewa sukayi hannun riga da ita,sai zallar gidadanci.......rashin wayewa da kuma qauyanci zalama da son abun duniya. Wannan shine abu na farko daya DASA mata wata irin MUMMUNAR AQIDA DA MUMMUNAN ZATO a ranta......muguwar tsana qiyayya da kuma qyama.

Ko meye zakayi masa muddin akan abun duniya ne ba komai bane a wajensa,uwa uba ma sam jininta da nashi baizo daya ba.......tun daga wannan lokacin take wa duk wani mutum irinsa wani irin kallo......wani irin mummunan fassara da kuma nesanta kanta da duk abinda ya shafesu.

Har tsakiyar kanta taji knocking din yana ratsata duk kuwa da nannauyan baccin da tayi nisa a cikin sa. A hankali ta bude idanunta tare da wani irin bacin rai daya sauko mata.

Batasan wanne me gangancin bane yake tashinta,bayan kowa ya sani doka ce......ba'a tashinta muddin tana bacci har sai sanda ta tashi don kanta. Wannan dalilin yasa kowanne time na sallah take saka masa alarm muddin zata kwanta,don sallar na cikin abu qwaya dayan data yiwa riqo me kyau......bata kuma yarda ita ko lokacinta su kufce mata komai girma ko muhimmancin abinda takeyi.

Hannu tasa ta dafe kanta jin ana ci gaba da knocking din kamar ba'a san dakinta ake qwanqwasawa ba. Ta miqe a fusace tana wantsalowa daga saman gadon,cikin ranta takejin ko waye wannan yau yake mata wannan gangancin ya kade a wajen ta.

Mutum biyun data gani a tsaye a gabanta sun kaure da magana a tsakaninsu,wanda maganar da sukeyi ma ta sanya basuga ta bude qofar ba. Bataji hayaniyarsu ta ciki ba don qofar irin qofofinnan ne da ba zakaji hayaniya daga waje ba,hakanan daga cikin ma kaima ba za'a jika ba.

Aisa da Shehinaz........sashenta.......'yan uwanta kuma aminanta. Idanunta da suka qara girma saboda bacci ta zuba musu,ganin bilhaqqi hira suke kaman wadanda suka shekara basuga juna ba tare da sun kula da fitowarta ba.

Ta shiga uku.....ciwon kanta guda dayar ta dawo,wadda wani lokaci har tafi aisa daga mata hankali. Baqar buzuwar da kalar fatarta tasha bamban da tasu fatar ita da aisa,saidai akwai wani sirrantaccen kyau itama da take dashi qasan chocolate colour skin dinta.

Shehinaz dince ta fara lura da an bude qofar

"Elle a ouvert la Porte(ta bude qofar)" Ta fada tana fincikar hannun aisa. Matsawa gefe tayi tana basu hanya sanda suke wucewa ciki abinsu suna mita

"Tu pionces comme un mort(kina bacci kamar gawa)" Still Shehinaz ta sake fadi tana yin ciki abinda. Goshinta ta dafe kawai tana ci gaba da jin hargaginsu sanda suka isa dakin. Wannan me shegen faransancin tasan ta kade a hannun ta itama,don ta tabbatar aisa ta gaya mata abinda tace data bata labarin abinda ya hadosu da Jamaal.

Daidaita kanta tayi sannan ta juya tana komawa dakin.

"Wai don Allah bakiji toc toc namu ba?". Scarf dinta kawai ta dauka dake ajiye saman dressing mirror ta daure sassalkan gashinta.

"Biftuuuuuuu" Shehinaz ta sake qwala mata kiran da sai data dakata daga shiga toilet din ta waiwayo ta ware mata blue eyes dinta

"Ban bude bane Shehinaz?......Fiche-moi la paix(ki qyaleni don Allah)" Ta qarasa fadi kaman zata saki kuka. Bata doguwar magana ko hayaniya me yawan idan ta tashi a barci,dukkansu sun sani haka yanayinta yake,amma yanzun gasu sun sakata a gaba zasu addabeta,kuma ta fahimci plan ne.

Samu tayi ta wuce bandakin ta barsu a nan,a gurguje tayi tsarki ta daura alwala,tana mamakin baccin da tayi haka,har yayi nauyin da ko alarm dinta ma har yayi kuwwarsa ya gama bata ji ba,na qarshenne ma ta jishi kamar cikin mafarki,kuma ta miqa hannu ta kashe taci gaba da baccinta. Muddin ta gaji da yawa ko kuma ranta a bace yake to takanyi nauyin bacci,don haka ba kowanne guri take sakin jiki tayi bacci sosai ba.

Har ta fito ta shimfida abun sallah Shehinaz da aisa basa jin kawunan juna. A nutse ta bada faralin sallarta,wanda tana dab da idarwa kira ya shigo wayar Shehinaz din ta dauka,abinda ya kawo ragin karadinsu cikin dakin.

8 / 21