L U'U L U'U BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY HUGUMA.txt

Author :  Safiyya Abdullahi Huguma Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   17 / 21

48K to 51K   out of 62.7K words

tazo karba kona girmamawa ba. Girma dashi dama suka ganta,yabo kuwa iya na bakin mammina da sultane sun isheta. Ta shiga gasar ne kawai don rad'in kanta,ta shiga ne kawai don farincikinta,ta kuma shiga ne don haka takeso haka kuma take sha'awa.

Cikin Lamborghini din da tazo musamman saboda daukarta suke ta barsu da kururuwar kiran sunanta. Ita da aisa sai shehnaz. A nutse take cire helmet din kanta ta miqawa birran. Karba tayi sannan ta matso tana zare mata boot din qafarta. Barratu ta miqa mata tataccen ruwan cranberry juice me matsaikaicin sanyin da bazai cutar da haqora ba.

"Biftu wannan wasan bai cika ba......Vouse avez fait un mauvais choix(kinyi yanke hukunci mara kyau),IIs te réclament toujours au micro(har yanzu kiranki sukeyi ta mic)".

Ajjiye cup din tayi a saman tafi hannun birra dake duqe gabanta tana jira ta gama,ta karba cup din ta matsa can wajen wani madanni daban dake jikin motar ta latsashi tana maida komai saman dan tray din daya fito.

Lallausan handkerchief dinta ta sanya yana goge dogayen yatsunta farare sol da babu digon komai koda saman farcenta,daidai sannan aisa itama ta tanka.

"Ki gaya mata dai.......wannan wasan bai kamata ya tafi a banza ba........Tu as joué un bon match(kin buga wasa me kyau.....ni kaina nayi mamaki". Shigowar kira wayarta da number mammina yaja hankalinta fiye da qorafinsu,sai kawai ta yiwa birra alamu,da hanzari ta ciro mata Bluetooth dinta ta miqa mata ta maqala a kunnenta tana relaxing sosai cikin kujerar

"Ba abinda ya kaini kenan ba......ba yabo nake buqata ba bare na karbi nombre(number).....me so a cikin ku tana iya komawa ta karba daga baya" Ta qarasa maganar tana daidaita Bluetooth din a kunnenta cike da dokin son yin magana da mammina din da take jin kewarta har zuciyarta.

Aisa ce ta watsa mata harara tana dora qafarta daya saman daya.

"Eh ga gantalallu ba". Bata ma ji abinda take cewa ba saboda hankalinta ya tafi ga wayar.

"Bonjour mammina" Ta fada a shagwabe kaman yadda ta saba yin waya da ita. A duk sanda take gaban mammina......ko take waya da ita,tana jin kanta kamar qaramar yarinya. Wani girma da izza takeji sosai a duk sanda take tare da mammina din. Itace mutum ta farko data dasa sarauta da kuma izza sosai a tattare da ita......ta sanar da ita wacece ita a aikace......ta sanadin mammina tasan irin daukakar da Allah ya bata. Nisan tazara da banbancin dake tsakaninta da sauran yaran masarautar dama qasar agadez gaba daya.

"Me kikayi haka AKHNAN?". taji saukar tambayar daga bakin mammina ba tare da tabi takan welcoming nata da tayi ba.

Gabanta ya fadi......saboda taqi jinin dukka wani abu da zata yiwa mammina din har ya kawo motsuwar ranta ko rashin jin dadi a tattaare da ita,harma kuma hakan ya nuna ga fuskarta.

"Kinason ki manta ke wacece akhnan?.......kinaso ki manta tsada da darajarki?.......me kaiki shiga tseren doki?.......har kina yin kamar zaki fadi bayan kinsan tsada da darajarki?......bakisan kin wuce ajin irin wadannan abubuwan ba?......me kike nema?". Boyayyar ajiyar zuciya ta saki kafin ta narke murya,har cikin ranta tana jin ba dadi da yadda tasa ran mammina din ya baci har taji ba dadi har irin haka a kanta.

"S'il vouse plaît mammina.......nayi hakanne kawai don nishadi na fa?" Ta fadi kaman zata saka kuka. Ta fadi da wannan narkakkiyar shagwabar da mammina din da kuma sultane kadai takejin kanta a hakan a gabansu.......batasan ko akwai wata halitta a doron qasa data cancanci wannan zubin yanayin da kuma tsarin ba.

"Amma idan sultane ya gani yace me?,kina zaton ranshi zaiyi dadi?".

"Excusez-moi(sorry)mammina........Je suis vraiment désolé(am really sorry),don Allah karki fadawa sultane mana mammina". Shuru mammina din tayi,kaman ba zata sake cewa komai ba kafin tace.

"Shikenan,kada hakan ya qara faruwa"

"Je ferai preuve de diligence(zanyi qoqarin hakan sosai)" Ta amsawa mammina tana sauke boyayyar ajiyar zuciya na samun sukuni.

"Kika ce?"

"Mammina zanyi qoqari sosai akan hakannnn" Ta sake fada kama zata saki kuka,saita dora da

"Salut......À plus tard(sai anjima)" Tana dan boye sirrintaccen murmushin nan nata.

A nutse ta yiwa yalwa alamun ta gimtse kiran. Cikin cika umarni yalwa din ta janye kiran ta kashe kiran ta dora wayar daga saman wani tattausan tuntum.

"Murmushi.......kulawa......nuna qauna.......damuwa da dukkan lamurannan.......bansan daga ina kike iya zaqulosu daya bayan daya ba" Muryar yalwa ta maye gurbin shirun da parlor din ya dauka,kafin a hankali yalwan ta waiwayo tana zube idanunta cikin na mammina,kamar ba itace a dazun kanta yake qasa da inuwar mammina din ba.




zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*


PAGE 27
____________________________
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mutanen Zuzeam ventures
Ga wani sabon promo na bullo muku dashi don farin cikinku dajin dadinku
Kunsan promo na na dabanne namu ba irin nasu bane hajiya ta mai kike jira da 7500 dinki ki kwashi kayan 19k
1. Rabin kazar mallaka 4500
2. ⁠married femfresh wash 2k
3. ⁠garuka 7in1 masu wata 7 ajiki 2k
4. ⁠Gumbarmadaradanonon rakumi 1500
5. ⁠Tsimin mallaka 2500
6. ⁠maganin infection 1500
7. ⁠matsin mallaka ba aba mai kishiya 5k
Duka kayan 19k za a baki akan 7500
Kuma mutun 20 na farko sunada kyautar kayan 4k
Matsin maida tsohuwa yarinya 1k
Gumbar emergency 1k
Turaren mallaka 2k
Allah yaba mai rabo sa a Zuzeam ventures takuce 🥰👍🏼
Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi https://wa.link/l1gcz8 gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye ta WhatsApp 08144015291 muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
😁😁😁 https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
____________________________



Itama nata shimfidaddun idanuwan mammina ta zubawa yalwa. Kamar masu gasar tantace qurewa juna kallo. Tsahon wasu qayyadaddun sakanni,mammina ta miqe a hankali ta soma takawa.

"Bansan daga ina suke tahowa ba......bansan daga inda suke gina kansu kuma su bayyana a maganata da fuskata ba......abu guda daya na sani......mutuwa kawai nakeyi yalwa a kowanne bullowar rana da faduwarta......mutuwa nakeyi ina kuma sake mutuwa tsahon shekaru ashirin dinnan.......ki aika saqo zuwa ga *SAHEL COUTURE* Na Niamey........lokaci yayi da kowa zai motsa........inason kowanne dan makunni ya kunna kansa.......ina buqatar kowanne gini ya motsa......ina buqatar kayan aiki su wasa kansa.......su kuma fara abinda aka haliccesu saboda shi!" Ta qarasa msganar daidai sanda ta isa qofar da zata fiddata daga parlor din.

"Ayi musu bita......ayi musu tilawa.....sannan kuma a maimaita musu......dukkan kuskure qwaya daya tal......daidai yake da bugun numfashin zuwa guda daya.......dukkan sakaci guda daya kuwa.......daidai yake da rage adadin yawan fitar numfashi da maidashi zuwa ga mashaqa iska"

"An gama ranki ya dade" Yalwa ta fada da wani irin biyayya me zurfi tana sauke kanta qasa,wutar dake ci a tata zuciyar tana soma rura kanta.

Cikin izzarta ta isa inda ta tashi dazun idanunta akan tamim da wani irin nazartaccen kallo.

"Me kake fadi dazu?" Ta jefa masa tambayar da yanayi na izgili. Sautin daya tabbatar masa ya fadi wani abu ba daidai ba.......ya fadi wani abu da bai dace da ra'ayinta ba.......bai kuma dace da abinda takeso taji ba. Saidai a ransa yana jin dole ya maimaita mata......don baya fatan ta jawo wani kuskure da zai zama almakashin gintse jira da haqurinsu na shekaru kusan GOMA!.

"Ba wani gurbi da sauri yake dashi a!"

"Tamim!" Ta kirashi a zafafe tana sake jin cewa haqurinta da gaske yazo qarshe.

"Kodai baka shirya ba?......" Ta masa tambayar me tarin ma'anoni da yawa. Dubanta kadan yayi,kafin murmushi ya subuce masa,ya danyi qasa da kansa kafin ya dagashi zuwa gareta.

"Inda TAMIM ba shiryayyen bawa bane......na tabbatar a yanzun labarin shekaru goma da abubuwan da suka shude da ita a ciki BASHI AKE MAIMAITAWA A YANZU BA!". Ya fada yana cika idanunsa da yaqinin da yakeso ta cikashi a zuciyarta,ta kuma sanya hakan har can qasan ranta. Idanu ta kafeshi dashi sosai cikin salon nazarta da karantar mutum kamar yadda ta saba. A nutse saidai da wani irin sauti me tarin ma'anoni tace masa.

"Wannan jarumtar.......wannna zarrar.......ita na gani......ita ta sakani zabarka na sakoka cikin wani sha kundum din sirri da ya shafi rayuwar zaituna gaba daya........zaituna bata jiran banza.......bata taba jiran wani abu a rayuwarta har haka ba.......dole ya wannan abun dake binne a tonoshi!.......dole wannan damar da muke ganin qyallinta take mana b'aton dabo ta ruskemu.......koda mu bamukai ga takawa izuwa muhallinta ba........har zuwa yaushe komai zai qare?!......ya kamata ya fahimta.......ya fahimci akwai mafarauta.......akwai masu tarin buqata.......ya kamata a sanyashi ya waiwaya.......ya kuma yiwa kansa da kansa karatun da bai buqatar me fassara!"

"Biyan buqatarki itace muradina........amma har yanzu inason tuna miki cewa............ZAKI NE dake qarqashin kulawar DAMISA!!". Tamim yayi maganar kowacce gaba ta jikinsa tana motsawa.

Kamar daukewar ruwan sama bayan shafewar dogon zango yana zuba haka shuru ya gifta a dakin. Sosai maganar ta daki zuciyar mammina da wani irin qarfi daya tilasta tsaiwar bugawar jini zuwa ga sassan jikinta na wasu qananun daqiqu.

"Tamim......." Ta kira sunansa,saidai kafin takai ga cewa komai ya rigata dora maganarsa akai.

"Za'ayi........za'ayi......za'ayi.....bansan meye zai dakatar dani daga qarasa wannan aikin ba!"

"Haka nakeso naji!" Ta fada cikin wani qwarin gwiwa daya lullubeta gaba daya.

"Ban miki alqawarin komai zai kasance kamar yadda ya kasance a baya ba......saboda komai din a yanzun ba yadda yake bane a baya!"

"Na baka wannan amannar.......na kuma baka wannan yardar" Ta fada tana bude tafukan hannayanta kamar wadda kewa qasa daquwa.

Idanunta a kansa har ya fice gaba daya. Dauke kallonta tayi tana qoqarin maida dukkan qwarin gwiwarta gangar jikinta.......taja wata sassanyar iska da garin ya fara saki sakamakon hadarin da ya kammala haduwa ya kuma hade jikinsa guri guda.

Miqewa tayi ta fara takawa,tana jinta a wata sabuwar zaituna......wata sabuwar mammina......wata zaituna ta daban ba wadda take jinta a yanzu ba.


★K'arfe bakwai da rabi ne na dare a garin addis ababa dama Ethiopia gaba daya. A daidai wannan awannin wasu sirrintattun awanni ne da suka kammale abba muhammad dawud......omari.......da haisam guri guda cikin wani kebantaccen office dake da wani irin tsaro da sirri.

Abba muhammad dawud din yana zaune ne cikin kujerarsa swivel chair,yana jinsa yana sake narkewa a cikinta saboda maganganun da suka kammala yi a yanzu.

Daga can saman wasu swivel chair din omari ne.......wanda ya soke yatsunsa guda goma cikin na juna.......yana jin wani abu yana masa amsa kuwwa cikin kunnuwansa shima tun bayan daukewar kalamai daga bakin kowannensu. Haisam din,wanda ke zaune sosai saman wani table dake ajjiye musamman saboda karatu,a maimakon cikin kujerar,ya nannade hannun kurta pyjamas din jikinsa,yatsunsa dauke da biro yana kadashi a hankali,manyan idanunsa da suka lumshe kadan suna saman allon dake gabansu da suka gama rubuce rubuce mintuna kadan da suka rage.

Daga muhammad dawud har omari hankulansu suna kan haisam ne. Omari cike yake da fatan yaji haisam yace ya janye zuwa NIGER ya janye shiga birnin AGADEZ. Tarin hadurran suna da yawa......tarin sharuddan sunyi nauyi da girman da yake ganin haquri da tafiyar yafi alkhairi.

"Na shirya......zanje!" Haisam din ya shammaci ji da ganinsu dukka ya furta yana ajiye abun rubutun hannunsa,sannan yayi qaramin tsalle yana dira daga saman table din yana ware hannun kurta dinsa daya nade.

Dukkansu idanu suka zuba masa,zallar mamakin qarfin halin haisam da jarumtarsa tana kad'a Muhammad dawud. Yanzun nan......da kansa ya sakeyin wadansu binciken........da kansa ya duba komai,ba wani bane ya duba ba......ba wani bane ya bincika ballantana yayi tunanin bai fahimci abun daidai ba ta sigar bayanin da sukayi masa.

"Ka tabbatar ka shirya muhammad haisam?" Muhammad dawud ya fada a ransa yana fatan ko yaya ne haisam yace ya janye.

Da wannan qasaitar tasa ya tako a hankali,ya qaraso gaban table din muhammad dawud,ya janyo kujera qwaya daya ya aje a gaban nasa sannan ya zauna.

"Karanto komai kawai......ka karanto yadda komai zai kasance" Ya fada yana cire murfin biron dake hannunsa ya rufe biron ya ajiye gaban Muhammad hammud......abinda me gaya masa haisam din baida buqatar rubuta komai......kwanyarsa ta shiga yanayin da zai iya riqe komai da basirarsa kamar yadda ya saba a yawancin lokuttan da ya dauki abubuwa serious da gasken gaske.

_TOFA_


★★★★

Awa guda cur suka shafe suna tsarawa da tattaunawa gami da shirya yadda komai zai kasance kafin su kammala. Tsam ya miqe,ba wani rauni daya bayyana a gangar jikinsa bare kuzarinsa ko kadan,daya daga cikin abubuwan dake burge abba dawud kenan matuqa tattare da haisam din. Yasha fada yana kuma maimaitawa

"Tabbas haisam halastaccen jinin abba jifar ne.......da gaske shi din sarauta cikin jininsa take......gado ce ta tun usul......irin wadda idan ta ratsa mutum take maidashi jarumi na gasken gasken. Jarumtarsa tafi kama da jarumtar kakanninsa da suka shude a yawancin lokuta,wadanda suka tsayawa qasar Ethiopia......tsaiwar data sanya aka gagara yi mata irin mulkin fyadiya da aka dinga yiwa qasashen africa a wancan lokacin.

Hannu abba muhammad dawud ya miqawa omari dake tsaye a gefan haisam din yana sauke numfashi. Dariya ta kufcewa abba muhammad yana finciko omari din da shima dariyar ta qwace masa.

"Omarul farouq fa kake........me wannan sunan jarumi ne da baisan tsoro ba ko kadan.......jarumtar data sanya hatta da shaidan baya iya hada hanya dashi ka manta?". Murmushi ya sake kubcewa omari yana girgiza kansa.

"Muhammad ya fini jarumta......kuma ya fini son kasada da rayuwarsa......abba bakaji me yake fada ba?,so samu muje har niger a mota......me yayi zafi?,kawai don zuciyar dutse gareshi?" Ya qarashe maganar yana zube kallonsa akan haisam dake hada kayayyakinsa cikin wata jaka ta musamman. Baiko waiwayo ya kalli omari ba......saboda shi ko sau daya ko alama baiji wani fargaba ko shakka akan komai ba. Hankalinsa kwance yake,bayajin akwai abinda zai sanyashi ya janye.

Ya sani......gagarumin abune shiga wata qasar ba tare da izinin qasar ba......shiga wata qasar da zummar aiwatar da aikin da ya shafi tsaro bincike da samo bayanai daga wasu ahalin qasar.......to amma hadarin dake fuskantarsa.......hadarin dake fuskantar masarautar jimma ya kere dukka wadancan hadurran a ransa.

"Karka damu......na yadda da muhammad.......bani da tsoro ko fargaba a kansa.......amma nasan halinka.......indai baka yiwa mootii bayanin aikinnan da kyau ba ni da kaina zan masa.......don kada ka tafi ka barshi da tsammanin dawowa kwanaki kadan a nan kusa" Abba Muhammad ya fada yana qoqarin boye tashi fargabar.

"Alfarma daya abba". Haisam ya fada yana goya backpack dinsa a baya gami da gyara zamanta.

"Uhummmm.......fadi muhammad" Abban ya fadi yana dubansa.

"Ba yadda zaa canzamin wannan b'eran?" Dariya taso kama muhammad dawud. Daga ganin idanun haisam da gaske yake fadi,ba tun yau ba ya sani,duk wani aiki da zai shiga ko zai jagoranta to ba shakka sai ya zabi mafiya nagarta wajen jarumta da qwarewa sannan yake aiwatar da aikin.

"Kasan dokar aikin mu haisam.......indai kasan wani abu a ciki ko akai......to ka shiga cikin aikin ko ka shirya ko baka shirya ba". Muhammad dawud ya fada yana danne dariyarsa ganin kallon da haisam ke jifan omari dashi. Idanun nasa ya dauke daga kan omari din,ya fara takawa zuwa qofar fita daga office din,yayi scanning card dinsa qofar ta bude masa,ya saka qafarsa daya a waje sannan yayi magana ba tare daya waiwayo ba.

"Kaja masa kunne.......ka sake karanta masa komai,bazan dauki sakaci ko ganganci ko wani tsoro ba.......mu ba mata bane......an haifemu don mu fita muyi farauta......an haifemu don mu zama garkuwa......bango majingina" Ya qarasa fada yana qarasa ficewa ya maida qofar.

Sanda yake saukowa daga escalator yayi mamakin hango abdii sosai. Tsaye yake a lobby din shi daya,cikin shigar qananun kaya. Hannayensa zube a aljihun wandonsa yana duba wayarsa.

"Abdi" Ya fada qasa qasa yana motsa labbansa idanunsa a kanshi. Baisan wanne irin qauna yaron yake masa ba......wannan qaunar ita ta sanya ya gutsira abdii kadan daga sirrinsa da ko nanay bata sani ba.

Boyayyen murmushi ya saki da bai bayyana akan fuskarsa ba. Ya sani zai wahala abdii ya iya zama sai ranar daya tsara zai dawo din,ya tabbatar tunda ya taho shima hankalinsa yayo addis ababa,yanzun kuma da zai tuhumeshi me yasa ya yanke hutunsa tun yana da ragowar lokaci zaice wani uzuri ne ya taso daga makaranta.

Kamar a jikinsa yaji haisam din yana wajen,sai

17 / 21