L U'U L U'U BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY HUGUMA.txt

Author :  Safiyya Abdullahi Huguma Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   12 / 21

33K to 36K   out of 62.7K words

mallaki hankalin kansa ya kuma fahimci irin halittarsa sai ya zamana ya dauki matakin kame ganinsa.......sake nesanta kansa daga dukkan wani jinsi da ba nasa jinsin ba......bai sha wahala ba,don dama dabi'arsa daban take.......tun asali kuma shi din mutum ne me kiyaye hakan,sai komai yazo masa da sauqi,har wani lokacin suna tsokanarsa da MR LOWERING GAZE. Wani lokaci su fada da turancin da dukkan su sun iyashi......wani lokaci kuma da yaren oromo din *Mr ilaalcha gadi buusuun*

Qasa tayi da kanta,hakan kuma bai hanata takowa zuwa inda suke din ba,saidai ta rage saurinta sosai.

Ta sanshi,sannan ta karanci abubuwa da yawa daga halayensa......wannan ya sanya dab da zasu isa ga junansu ta buda bakinta cikin nutsuwa.

"Assalamu alaikum" Ta fada da cikakkiyar sallama.

"Wa'alaikumussalam" Omari ya amsa yana niyyar wucewa,saidai tuni haisam ya riqe yatsunsa ya kuma dawo dashi baya.

"Barka da warhaka" Saami din ta fada tana dan duban sashen da omari yake. Fuska yadan sake mata,a iya shigowarsa gidan yasan saami.......da fari bai dauki wani abu game da samee din ba da yadda take girmama haisam da damuwa da lamuransa ba.......sannu a hankali ya fahimci akwai wani babban al'amari a game da haisam din a zuciyar yarinyar.

Tana da wata irin nutsuwa da kuma kamun kai..... Irin wadda ya jima bai ganta game da wata yarinya matashiyar budurwa me irin shekarunta ba.....wannan ya sanya shi kansa yake girmamata da kalar girmamawar da yaga haisam din yanayi mata.

"Barka da dare" Ta fada tana dan rusunawa haisam din ba tare data iya kallon fuskarsa ba.

"Barka.......ina zaki haka da daren nan a hanyar da ba jama'a?". Har tsakiyar zuciyarta taji tambayar da yayi matan.......yanayin yadda yayi tambayar da mamaki cikin muryarsa dake nuna da gaske baisan me ha fiddota zuwa ga hanyar ba a irin wannan lokacin.......bai fahimci ta fito bane kawai don ta samu ta ganshi ko yaya.......ta fito ne don ta kebanta dashi koda na daqiqa ashirinne.

Bata iya ce masa komai ba,saita miqa masa kwalin hannunta,duk kuwa da yadda kunya ke dawainiya da ita. Kwalin yabi da kallo a nutse kafin ya maida dubanshi ga fuskarsa. Yanaso yayi tambaya ne game da kwalin amma sai omari yayi masa riga malam masallaci ta hanyar sanya hannu ya dauke kwalin daga tafukan hannayenta.......hakan ya bata damar juyawa ta basu baya sannan tace.

"Saqo ne daga wata baiwar Allah" Daga haka ta soma takawa da hanzari tana bacewa ganinsu ta tsakanin wasu qananun bishiyoyi.

"Wani lokacin sai naga kamar ta bangaren aikinka da karatunka kawai kanka yake kawo wuta..... Kamar ta fanninsu kawai kake gane komai". Fararen manyan idanunsa dake tsakiyar rawaninsa ya zubawa omari.........kamar zaice wani abu sai kuma ya fasa.

"Tana buqatar ke kebe ne da ita fa.......kai kuma kayi kaman baka fahimta ba?......."

"Na fahimta mana omari.....na fahimta" Ya amsa masa yana soma takawa yana yin gaba ba tare daya damu da sanin meye a kwalin ba.

"Ba inda musulunci ya bamu daman kebewa nida ita irin hakan......ka manta ne omari?" Kai ya jinjina yana takowa don cin masa,duk da cewa hankalinsa yana kan kwalin daya dan budashi kadan yana leqa cikinsa.

"Amma ya kamata ka fahimta.......ya kamata ka gane me yarinyar nan ke nufi......ko baka fahimta ba har yanzu sai anyi maka fashin baqi?". Kansa ya girgiza yana kafe hanya da ido kamar meson gano wani abu.

" Na fahimta omari.......sameera sona takeyi.......so takemin irin na aure.....amma ni kuma........"

"Karka soma cemin samee batayi ba......zanyi abinda ban taba yi maka ba wato qaryataka......kamar yadda nasan kaima kayi abinda baka taba yi ba wato qarya" Miskilin murmushin nan nasa ya saki,yana ci gaba da takawa ba tare daya dubi omari ba. Sai da yaja fasali sosai sannan ya maida masa amsa.

"Tako ina samee tayi.......kamilar mace ma'abociyar addini.......mahaddaciya sittin da tafsir......wadda ta haddace litattafan addini masu tarin yawa,ba inda ta sani,daga gidansu sai makaranta.......sai nan gidan.......idanma akwai wani abu da samee bata cikashi ba......saidai cikar nan da ake cewa duk dan adam tara yake bai cika goma ba.......matsalar kawai ni dinne". Ya fada calmly har hakan na bayyana cikin maganarsa.

Dakatawa omari yayi cikin mamakinsa. Ya dauka dukka daya jero wadannan maganganun zai gaya masa cewa ya jima shima da fara son samee ko accepting nata.

"Kai din me?".

" Ban shirya soyayya ba......ban kuma taba jin son samee a zuciyata ba so irin na soyayya......donme zan bata mata lokacinta?" Ya qarashe maganar da sigar tambaya yana kuma waiwayowa gaba dayansa hannayensa zube a aljihunsa yana zubewa omari su.

Kallon kallo suka fara yi a tsakaninsu. Mamaki yana kashe omari.......yayin da haisam ke jiran ko zaiji wani qwaqwaran dalili da zai sanyashi bawa samee lokacinsa ko hankalinsa.

Gaba daya ya gama gogewa omari hadda,sai yaja jikinsa kadan ya zauna saman kujerun concrete dake kusa dashi.

"Sai yaushe kenan zaka shirya yin soyayyar......ka shirya kuma accepting wata?". Wannan boyayyen murmushin nasa dake cikin rawaninsa ya saki,ya kuma yi qas da kansa yana zubawa qananun fararen duwatsun da aka qawata wajen dasu idanu kamar yanason qididdige lokacin da zai jarrabawa wata macen ko ya bata dama a rayuwarsa.

"Not now omari......ba yanzu ba,ina da sauren abubuwa masu muhimmanci daya kamata na gama dasu omari".

"Haisam....." Omari ya kirashi a sanyaye yana aza dukka hannayensa saman kwalin..

"Ina jiye maka haqqin 'dubban 'yammatan da wannan shu'umin murmushin naka kadai ya jefa zuciyarsu kogin soyayya......ka kasa kuma taimaka musu da komai". Dole wannan karon murmushinsa ya fito da wani irin sauti.

" Laifina ne omari?......" Kasa bashi amsa omari yayi......dondai da gaske kai tsaye bazaice laifin haisam bane.......hasalima dukka cikinsu yafi kowa takatsantsan da lamarin mata,banda jaruma kuma tsayayyar zuciyar da sukasan yana da ita tabbas ba abinda zai hanashi soma kiransa da ME TSORON MATA.

Wani irin magnet ne cikin halittarsa dake fusgar hankalin 'yammata a kanshi........kusan dukkansu suna da irin wannan baiwar,amma nasa kaman yafi nasu zafi da yawa.

"Karkayi kwantai ko kayi zaben tumun dare fa?......" Omari ya fada yana fidda idanunsa waje. Kai kawai haisam keta girgizawa kaman dariya nason qwace masa,fararen jerarrun haqoransa da haskensu ya fita harta qyallen bakinsa suka bayyana.......a wannan karon sai da yakai hannun nasa ya zame qyallen zuwa wuyansa don ya bawa dariyarsa damar fitowa sosai.......wannan ya sanya qarashen cikamakin kaykkyawar fuskarsa damar bayyana gaba dayanta.

Wani lafiyayyen ajiyayyar baqa sidik din suma ce ta bayyana data gewaye habarsa da kumatunsa da wani iri qawataccen shape da zai gaya maka zallar qwarewa da sanin haqqin qasumba name askinsa. Kyawawan jajayen lips dinsa dake qyalli kamar an shafa musu man labba suka bayyana suna kuma sake zama ado ga jerarrun fararen haqoransa.

"Ba damuwa.......sai na jira sanda d'iyarka ta farko zata isa aure saika bani ita". Wani harara omari ya watsa masa.

"Ina ma ace akwai wani lafiyayyen abun bugu a nan?".

"Kana da hannu fa omari?......abun bugun me kake nema?" Ya tambayeshi yana dage masa girarsa dukka biyun,amsar bayarwa omari ya rasa,daya tabbatar da haka sai ya zare hannayensa daga aljihunsa ya hardesu a qirjinsa yaci gaba da tafiya zuwa ciki hankali kwance.

"Ko haka na zauna ba aure......Allah bazai tambayeni dalili ba.........muddin zan kare dokokinsa zan kuma tsare kaina......"

"Ba zaka iya ba.......na rantse da girman Allah kana cikin sahun mutanen da aure ya zame musu wajibi" Omari daya miqe da sauri ya fada yana kuma bin sahunsa. Dariyar mamaki ta sake kama haisam,amma saidai bai juyo ba.

"Zakayi kaffara omari......ka manta akwai manyan malaman da har suka rasu basuyi aure ba?......manya manyan malaman musulunci........ciki harda malamin mazhabar malikiyya imamu maalik?".

"Na sani......inajin kusan lokaci guda muka karanta littafin daya kawo sunayensu gaba daya......malaman da suka fifita karatu akan aure........amma sam baka sahunsu fa" Dif haisam din yayi masa ganin suna dab da fara shiga gurin jama'a,kuma zuwa sannan haisam yana jin bazai iya ci gaba da musayar magana da omari din ba.......don yana cikin abinda ke burge omari dama can suyita musayar ra'ayi.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*


PAGE 18



★★★Idan kaga yadda take shawagi cikin dokunan zaka rantse harda Allah ba diya mace bace,ba wasu alamu da zai nuna maka shakka ko d'ari d'ari game dasu......

Daya bayan daya take zagayawa tana duba lafiyar dawakan nata guda uku cikin dokunan hawa shida da take dasu.

Uku a agadez tare da raqumma uku da takan hau lokaci bayan lokaci,sai wadannan guda ukun da take dasu a nan Niamey.

Wasu irin qosassun fararen dawakai da take matuqar sonsu........ba ita kadai ba......duk wanda yasan sirrin kyan doki bazai kallesu sau daya tak yaji basu burgeshi ba.

Sanye take da yalwataccen wandon palazzo data dora masa wata blouse a sama long sleeve,sai ta kawo top data sauka har saman cinyoyinta me gajeran hannu ta dora a sama. Lallausan scarf ne a kanta data nannadeshi kamar tufkar igiya tayi wani irin dauri dashi daya bawa doguwar sumarta dake kwance a bayanta daman fitowa sosai,saidai ba zaka samu daman ganin tsahon sumar daya bazu a gadon bayanta ba sosai saboda wannan top din data dora a saman gashin nata.

Wani takalmi ne a qafarta,samansa kaman socks yake,qasansa ne takalmi. Jikinta a kowanne motsi idan tayi lallausan qamshinta ne yake kadawa.

Miqewa tayi daga tsugunnon da tayi tana duba qafar daya daga cikin dawakan nata,ta juya a nutse tana duban gabjejen mutumin dake tsaye a bayanta cikin son cika umarninta.

"Thunder zan hau(sunan daya daga cikin dawakan nata)"

"An gama ranki ya dade" Ya furta cikin rusunawa yana sakin murmushi. Da ita za'ayi wasan tseren dawakan.......amma ya fita qaguwa ranar tazo. Karon farko kenan data taba yin register kuma zata shiga wasan,duk da irin qwarewarta a sarrafa doki da kuma raqumi. Akwai kyakkyawar alaqa tsakaninta da dabbobin nan guda biyu,ta taso a cikinsu sosai,ta kuma koyi hawansu da sarrafasu. Tana da tarin raquma da ake kiwata mata,amma a ciki guda uku kacal take hawa da aka waresu musamman suka kuma saba da juna. Hakanan dawakanta guda shidan nan na Niamey da wadanda suke a agadez tana bala'in ji dasu. Sam sam yadda ta damu dasu bata damu da motocinta ba.....bata muhimmanci ba kamar nasu.

Wayarta ce dake cikin aljihun wandonta tayi qara,ta zura hannunta ta dauko tana duba me kiran,abinda ya saka murmushi subucewa daga fuskarta kenan,ta fara takawa tana fita a wajen hadi da sanya wayar a kunnenta.

Daga yadda take amsa wayar kawai zai shaida maka da wani me muhimmanci take magana.......hankalinta kwance take barin sashen dawakan zuwa parlor din gidan da wayar a kunnenta.

A nutse ta murza handle din parlor din ta wuce ciki,daga baki bakin qofa ta zare takalmin qafarta ta sauyashi da wani,sannan taci gaba da shigewa zuwa main parlor na farko.

Shehnaz kadai ta gani saman dining da alama lunch take. Don yau tun safe bataga gilmawarta ba,duk da kwana biyun nan ma ba wani magana sukeyi sosai ba. Haushinta takeji akan Jamaal shi yasa take shareta......tana ganin sam bai dace shehnaz ta ragi rayuwarta damarta kimarta da martabarta ba wajen auren jamaal din ba.....wayayyen namiji tafi dacewa dashi......wayayyen namiji take da buqata ba jamaal ba. Sai ita kuma shehnaz din tayi kamar bata gane abinda yake faruwa ba......sam taqi ta nuna wata alama na ta fahimci akwai wani abu.

"Munyi magana da mommonki morsa safiyya......." Daga daya bangaren wayar mata da suke kira da Nannie ta furta da muryarta me cike da nutsuwa. Lumshe idanunta akhnan tayi tana dawo da tunaninta kan wayar da sukeyi da Nannie din. Kiran sunan morsa safiyya kadai kuma ya dawo da nutsuwarta jikinta.

"Me matar nan taje ta fadawa Nannie a kaina ne?" Akhnan ta raya a ranta kafin ta sake jin maganar Nannie din.

"Na bawa shehnaz saqo......ina fatan ta gaya miki ko?". Sai data aza idanunta akan shehnaz dake kai abinci bakinta tana kuma danna waya da daya hannun kafin ta dauke idanun tana ansawa Nannie

" Aah Nannie.......batace komai dani ba".

"Don qaniyarta ban gaya mata ta gaya miki ba?" Nannie ta fada da alamun daukan zafi kadan a muryarta. Kai akhnan ta karyar gefe jin Nannie din zata dauki zafi da shehnaz,duk yadda sukakai ga fada da junansu basason wani yaga laifin dan uwansa,don haka a shagwabe tace.

"Fada mukayi Nannie.......batason kulani shi yasa bata gayamin ba......"

"Yoni ina ruwana da wannan shashancin naku da zata saka maganata a ciki?....."

"Nannieeeeee.....bada gangan bane ba" Akhnan ta sake fada a narke kaman zata sakewa Nannie din kuka.

"Sannu me 'yar uwa........ni naga gyada ma sarkin goyo" Nannie ta fadi tana jin haushin yadda ko laifi akayi tsakanin su ukun ake rasa gane waye me laifin waye me gaskiya.

"To abinda na gaya mata ta gaya muku......naji fes abinda ya faru zuwan yaroncan na garin tahoua........wannan shashancin ya ishemu hakanan......kuma tabbas don bana agadez wasu abubuwan ke faruwa,nace ta gaya miki keda aisa din gaba daya......Ku maida hankulanku jikinku......lokaci yayi da zamu miqaku dakunan aure.....don ba zamu zuba idanu ku dinga rayuwarku yadda duk kukaso ba". Duk wani walwala da nishadi da ta tashi dashi a yau Nannie ta warware mata shi tas,sai kawai tayi shuru tana sauraren sababin da Nannie din takeyi harta gama.

"Sai anjima" Nannie ta rufe da fada tana katse kiran.

Ba yau ko jiya ki shekaran jiya tasan Nannie ba.......tsayayyar mutum ce me wani irin kafaffen ra'ayi.......tana tsananin sonsu da qaunarsu.......to amma a hakan fa idan abunta ya motsa kowa ma bi take ta kanshi. Qanwa ce guda daya tal data ragewa sultane muhamma hamud a duniya,kuma itace mahaifiyar aisa.......mahaifiyar shehnaz ke bin Nannie,kuma shehnaz kawai ta Haifa ta rasu,don haka shehnaz Nannie kawai ta sani a mazaunin mahaifiya.

Sunan Nannie na asali bilkissou......Nannie ya samo asali ne daga bakunan shehnaz da aisa.

"Soni masoyi......soni ka sani ranka.....domin so da yardaaaaaa" Muryar aisa da akhnan batasan da zamanta a gefe ba ta soma motsawa cikin baitocin waqoqin fitacciyar mawaqiyar qasarsu.

A nutse ta juya tana duban aisa din,ta tabbatar da ita take......kuma da biyu tasan takeyi. Rasa me zatayi mata tayi,kawai saita jefeta da wayar hannunta.

Dukka idanunta aisa ta fidda bayan wayar tadan sameta a qafa kadan tana bin wayar da kallo kafin ta kalli akhnan.

"Vous ne savez pas à quel point elle est coûteuse(bana tunanin kinsan tsadarta),kike jifa da ita haka?". Manyan almond shape eyes dinta ta ware ta watsawa aisa din,saidai kafin suce komai shehnaz dake can a zaune ta fara magana a nutse


"Vous êtes tous invités aux courses de chevaux spéciales, présentation du nouveau cavalier de la famille royale, Akhnan Muhammad Hammud".

Yadda tayi shuru bayan ta kammala karantawa haka falon ya dauki shuru,kowa a cikinsu ya rasa me zai fada. Tsam akhnan din ta miqe,don batason kowa a cikinsu ya maido mata tunaninta baya,da nutsatsiyar muryar nan tana da ta dace da innocent fuskarta da sam bata dace da attitude nata ba taurin kanta da kuma kafiyarta ba tace.

"Tous sont invités(eh.....dukkaninku ana gayyatarku" Sai ta fara wucewa hankali kwance.

"Biftu.......sanarwa ne fa na gasar tseren doki fa aka karanta miki.....da sunanki da na sultane a mazaunin babbar baquwa 'yar tsere......what if me martaba yaji?". Zagayayyun idanunta ta juyo ta zube musu.

"Idan ke kika gaya masa ba......ba wani gurin bane.....cikin Niamey ne......cikin Niamey din ma cikin hippodrome.....ba wani bangon duniya ba".

"Tare da maza ne fa biftu" Aisa ta sake fada fargaba na bayyana saman fuskarta.

"Et puis?(sai me?).....C'est mon rêve(mafarkina ne),zan kuma cikashi ko sau daya ne". Ta fadi hankalinta kwance,bata kuma qara ba taci gaba da takawa tana tafiya abinta.

"Laissez-la(ki qyaleta).....ki barmu muga wasannan s'ilvous plaît(please)" Shehnaz ta fada tana murmushi,don har ga Allah ita abun ya mata dadi. Tana ganin ba wani abu bane me muni tunda na dan lokaci ne,kuma tafi kowa sanin yadda akhnan ke mugun son tseren doki da yadda ta qware akai.

"Na qyaleku" Abinda aisa kawai ta fada kenan ta koma tana zama ba tare data sake cewa komai ba.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*

PAGE 19



Sanye yake da Moroccon jallabiyya ta maza,wadda

12 / 21