L U'U L U'U BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY HUGUMA.txt

Author :  Safiyya Abdullahi Huguma Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   20 / 21

57K to 60K   out of 62.7K words

dake gabansa,yayi relaxing sosai cikin kujerar sannan ya fara mata bayani.

Batace komai dashi ba harya kammala. Shurun nata har yayi yawan da sai daya kira sunanta.

"Nanay?"

"Tunani nake muhammadu".

" Karkiyi tunanin komai Nanay.....Allah shine me rayuwa.....shi yake tsarewa".

"Muna fata kuma yaci gaba da tsarewar.......wacce qasa ce muhammadu?" Ta tambayeshi a karye.

"Niger agadez". Wani siririyar faduwar gaba ta saukar mata. Kiran sunan qasar hade da garin ya zame mata tamkar wani tuni akayi mata.....tuni a KANTA.....fuskar da har yanzu taqi bacewa cikin idanunta.....kaman yadda sautin muryarta taqi bacewa daga kunnuwanta.

"Agadez muhammadu?"

"Eh nanay......da wani abu ne?" Kai ta girgiza a hankali,saita zarce da jan hankalinsa kamar yadda ta saba,da rufewa da tarin addu'o'i.

"Kada kace zaka rufemin komai bayan tafiyarka......ina da buqatar sanin kowanne hali kake ciki......inaso a wannan karan na zama qawarka kuma abokiyar shawararka fiye da ko yaushe.....Allah ya albarkaci rayuwarku gaba daya".

" Ameen nanay " Ya amsa yana lumshe idanunsa. Haka kawai yaji zuciyarsa kamar tayi rauni kadan,ya sani a yanzun idan aka zubewa nanay zabin ya tafi ko ya zauna.....tabbas da gudu zata zabi ya zauna din,saidai wannan tafiyar nada tarin muhimmanci a rayuwarsu gaba daya.....amma yana sanya ran tafiyar ta zama ta qarshe da zata kasa samar da gamsuwa cikin zuciyar nanay kamar yanzun.

Yana shirin ajiye wayar tasa ya fahimci da shigowar sabon saqon email. Budeta yayi ya kuma wuce kai tsaye zuwa gmail dinsa.

Da sauri ya aje qafafunsa qasa yana bude lumsassun idanunshi da dukka girmansu.

"Welcome to NIAMEY horse race........you're successful registered to the special horse race batch 2 and final.....muhammad ja'afar". Sau uku yana maimaita karanta email din da baisan daga inda ya fado ba......saidai a iliminsa na karatun na'ura me qwaqwalwa,bata yadda za'ayi saqon haka kawai ya fado email address dinsa saida wani dalili.

Omari na ya fado a ransa,sai ya sauka da dukkan nutsuwarsa ya sanya lallausan bedroom slippers dinsa ya fara takawa a hankali ya nufi balcony din da ya baro Omari din dazu a zaune yana qoqarin tattara bayanai.

Sama sama yake jiyo muryar omarin,da alama waya yakeyi,kuma wayar ta masa dadi da gaske,don kuwa yana iya jin fitar sautin dariyarsa.

Yana dab da shiga balcony din ya fahimci conference call yakeyi shi dasu mutallab naseeb khadeem da Amjad,muryar maleek ne kawai bai samu jiyowa ba.
(08187255862 lu'u lu'u novel paying)

"Yauwa......gashinan ma" Omari ya fada yana karkato da fuskar system din saitinsa sanda yake qoqarin zama saman bean bag din dake gefan omari. Zama yayi Normal zama a wajensa......amma a idanun me kallonshi zama ne dake nuna zallar qasaita da sarauta dake yawo a jininsa.

Murmushi Amjad ya saki daga allon system din yana duban haisam.

"Ya zame maka jiki.....yabi jikinka da kyau......yanzun idan nace wani qasaitaccen zama kayi fa ba zaka yarda ba" Dukkaninsu dariya suka sanya,abinda ya sanya haisam fidda wani siririn miskilin murmushi yana kuma gyara zaman nasa daga yadda yake a dazun.

"A'aha......an kuma dai" Mutallab ya fada yana duban haisam din. A wannan karon dole suka sanya ainihin murmushi subuce masa,wanda har sai da jerarrun fararen haqoransa suka bayyana.

"Ba zaku canza hali bane?" Haisam din ya fadi da wani irin nutsuwa wadda tun asali tasa ta bambanta da tasu.

"Indai akan fadin gaskiya ne ba zamu canza ba......ina aka kwana ne?......ba wani labari?" Mutallab ya tambaya yana karbar cup daga hannun matarsa wanda iya hannunsa ne kawai daya miqa ya karba cup din ya bayyana.

Hannu haisam ya aza saman sumarshi yana shafata a nutse,yasan me haisam ke nufi,indai yace ba wani labari?.....to da gaske yake,yana son yaji labarin yayi budurwa......ko ya samu matar aure.

"Akwai labarai" Omari ya fada da sauri sannan ya dawo da fuskar system din saitinsa. Idanu haisam ya zube ma omari,wanda sosai yaji a jikinsa haisam din ya kafeshi ne da wadannan mayatattun idanuwan nasa,shi kuma a yanzun bayajin akwai abinda zai dakatar dashi daga bawa su Amjad wannan labarin,musamman da signal ya harba ya nuna amsa maleek ma ya iso online.

Hannu kawai haisam ya miqe ya bame fuskar system din ya hadeta da juna yana tsare omari da ido bayan ya danne mic din.

"Me kakeson gaya musu?,labarin qanzon kurege?" Yayi maganar yana dage masa dukka girarsa biyun ba yare daya dauke hannunsa daga system din ba. Shima girar ya dage masa masa dariya tana kubce masa.

"Idan kai baka sonsu su suna sonka ai......ya kamata a nema musu tallafin masu yi musu campaign ko zaa dace daya a cikin su suyi wuf dakai.....ko duka biyun ma"

"Biyu.....waye da waye."

"Saami da Menelik". Sosai ya tsaya yana duban omari.

"Wato har qwaqwafinka yakai can omari?" Dariya sosai omari din ya saki ganin yadda haisam din ya hade rai da gasken gaske. Dariyar omarin ta fara isarsa,ya kuma tabbatar a yanzu haka sunbar su maleek akan layi,sai ya saki siririn tsaki ya dauki system din yana riqeta a hannunsa,sannan ya bude screen din yan zarcewa zuwa wani parlor din daban.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA๐Ÿ‘‘*

*HUGUMANKU CE*โœ๐Ÿฝ
๐Ÿ’Ž *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐Ÿ’Ž


*H U G U M A*


PAGE 31



*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX



Saman ottoman ya zauna,ya jawo wani ya dora system din akai yana goye hannuwansa a qirjinsa sanda fuskokinsu dukkaninsu suka fito tarwai cikin screen din.

Har hada baki sukeyi wajen tambayarsa wanne labarin omari zai basu?. Hannuwansa ya watsa yana cin serious.

"Bani nace xan baku labari ba......saiku jira parrot din yazo ya baku" Dariya suka saki kafin maleek yace.

"Ranar Saturday din zaka sauka agadez din?.....qarfe nawa race din zai fara?.......ya zama dole muje mu nuna solidarity". Idanu waje haisam ke kallonsu ganin yadda suka barke da maganar da zancan tseren dawakan.

"Hi guys" Ya fada da Sassanyar muryarnan tasa da yakanyi amfani da ita wani lokaci yana daga fararen hannuwansa. Dukka hankalinsu suka bashi.

"Wanne race kuma?" Ya kuma tambaya yana baza idanunshi a tsakaninsu.

"Look man......wannan wani abune na daban a qasar daba tamu ba.......ba kuma haramun bane bare ka haramta mana zuwa......so please bama buqatar wani sharhinka okay?" Khadeem ya fada yana dage dukka girarsa,kafin kuma ya sake cewa wani abu khadeem yayi off,sai dukka yaga kowannensu yayi off,alamun zuwa kenan ba gudu ba ja da baya.

Shuru yayi ya zubawa system din da kowa yayi off ido yana dubanta. Yana jin kamar hadin bai dace ba,bai kamata Omari yayi wannan hadin a qasar da suke da gagarumin aiki a cikinta ba,sai yayi shutting down na system din ya dauketa cak ya nufi dakin da omari yake sauka.

A nutse ya tura ya shiga,sai ya sameshi saman abun sallah yana raka'ar qarshe,da alama wuturi yakeyi(sallar wuturi nada matuqar muhimmanci sosai.......Allah yana sonta,koda baki da daman sallar dare,kiyi wuturi kafin ki kwanta).

Koda ya sallame sai ya juyo yana duban haisam din.

"Wanne irin ganganci ne wannan omari?,wanne irin kuskure ne haka?". Zama yayi sosai saman abun sallar bayan ya juyo yana duban haisam din.

"Hanya muke nema a sauqaqe ta shiga garin agadez cikin yanayin da zai badda hankulan mutane......ba wata hanya mafi sauqi sai wannan.....sassauqar hanyar da zata bamu daman sajewa da 'yan garin a cikin sauqi". Shuru haisam yayi yana juya maganar taren da jefata nisan nisan hankali da kuma mizanin da zaiyi daidai da ita.

Shurun da haisam yayi bai sanya omari katse shurun ko katse masa tunani ba. Don ya tabbatar a dukka shurun haisam din akwai dogon nazari da hangen nesa .

"Wannan action din naka zai iya calling attention na wadanda bai kamata ba......ka gane mana omari" Duban haisam ya sakeyi kafin yayi qasa da kansa yana dafe hannunsa guda daya da kan nasa. Sai a yanzu da haisam yayi maganar da wannan yanayin ya tuna da abinda ya kamata ace ya tuna dashi din kafin wannan lokacin.

Tun suna da qananun shekaru mooti ya hana haisam shiga kowacce gasar tseren doki,saboda wani irin maita da yake dashi gurin qurewa doki gudu. Ya qware sosai irin qwarewar data sanya nanay ta yiwa mooti magana akan BAKI.

"Ina tsoron baki akan muhammad......baki gaskiya ne Allah ya taimakeka,a duk sanda zai shiga wata gasa shike zama na daya,kada baki ya kassara mana shi". Sosai mooti ya fahimceta,ya kuma fahimci inda ta sanya gaba,take kuma ya hana haisam shiga kowanne gasa bama ta doki kawai ba.
(Wannan din wani kariya ce data kamata kowanne iyaye su bawa yaransu,bawai kayita murna yarona ta daya yake zuwa ba....yarona ya iya kaza,ai yarona yayi mugun iya kaza.......baki baki masifa ne akan 'ya'yanmu,baiwar da Allah ya yiwa yaronka boyeta kakeyi,har sai sanda ya isa munzalin da duniya zata gani,baki gaskiya ne.....wani baisan kuma yana dashi ba,koda yaronka ne ka rage tankashi,don akwai da dama iyayen da suka cinye yaransu da bakinsu suka gusar da wata baiwa ta kyau yawan gashi ko farinjinin jama'a da yake dashi,dake da ubansa kansa ku rage tanka yaranki,Allah ya bamu kariya da tsari irin nasa ameen summa ameen).

"Na riga na shigar da komai.....sunyi approving kuma......yanzu mene abunyi?" Omari ya fada yana bawa haisam dukka hankalinsa.

Ajiyar zuciya ya sauke yana sauke hannayensa qasa

"Zan gani......zanyi dukkan qoqari wajen ganin komai ya tafi daidai ba tare da wata matsala ba" Ya fada yana miqewa hadi da zube hannayensa a aljihun wandonsa.

"Me gaminka da English ne?" Omari ya tambayi haisam din yana cire hular kanshi ya aza saman abun sallar da yake kai. Juyawa haisam din yayi a nutse,kaman bazai tanka masa ba,har sai da ya kai dab da qofa

"Idan baka da siffofi mabanbanta ka sani baka cika mizanin zama ma'aikacin NISS ba...........dole ka zama a duniyarka,dole kuma ka zama a wata duniya ta daban da taka". Shuru omari yayi yana bin hanyar da haisam ya fita da kallo,murmushi na fita kadan kadan daga fuskarsa.

Shi din shaida ne......kyakkyawar shaida kuma me cike da tabbacin muhammad haisam ya banbanta da mutane masu tarin yawa........idan maganar intelligence akeyi nashi na dabanne......komai nasa tamkar an zabar masa ne.....kamar haka yaso ya kasance.


โ˜…โ˜…*NANAY*

Boyayyar ajiyar zuciya ta sauke tana gyara zamanta idanunta suna kan saami.

"Saamirah" Ta kira sunanta a tausashe,abinda ya sauke saukar da nauyi ga jiki da zuciyar sameera din kenan.

"Na'aam nanay" Ta amsa ba tare data iya daga idanu ta kalleta ba.

"Saamee......kada ki saka rai me yawa......kada kuma ki saka buri da yawa,amma kuma kada ki sare,kada kice kin gaza,kada kuma kice zaki daina har sai kin cimma burinki......". Wani faduwar gaba dukka maganganun nanay suka saukar mata dashi. Kunya da nauyi suka wani irin dabaibayeta,tana jin kamar ba zata iya motsawa daga inda take ba. Kada dai ace hatta da nanay ta fuskanci abinda ke zuciyarta?,dama kallonta kawai nanay keyi?.

Yanayin yadda saami din ta takura cikin tsangwamar kanta ya sanya nanay sakin boyayyen murmushi.

"Koda ban haifeki ba saame ina iya fuskantar wasu al'amura daga yaran da suma ba nice na haifesu ba,ke din amana ce a hannunmu saami,dole mu sanya idanu a duk wani motsi naki kaman yadda zamu sanya akan na yaranmu........haisam......yaro ne da ban taba hasashen samun kyautar Allah kamarshi ba,yana da wasu nagartattun halaye da nayi imanin ba zaki wulaqanta ba,ba kuma zai wulaqantaki ba saboda kina sonshi.......amma yana da kebantattun halaye da suka sha banbam dana sauran abokan rayuwarsa.....yana da zabi.......yana da kuma irin nashi yanayin.....ko bayan haka ma gaba daya,zanso ko wacece zata shiga rayuwar haisam ta fara samun soyayyarsa tukunna......ta nemi soyayyarsa da kanta kafin ta kutsa kai cikin rayuwarsa,wannan ne kadai zai sanya ta fahimceshi,ta bashi uzuri,ta bashi cikakkiyar kariya a kowanne irin yanayi,irin kariya da nutsuwar da kowacce mace ta gari take bawa mijinta......" Sai tayi shuru tana maida numfashi,tana ganin yadda maganar ke samun kyakkyawan matsugunni a zuciya da kuma hankalin saame din.

"Zanso a sanda zaki shiga rayuwar haisam ki shiga da dukkan daraja da martabarki ta diya mace,kaman yadda zan sowa yaran da na haifesu a ciki na.....zanso ki samu wannan martabar da mutuntawar.......kin cancanta saami,kina da kowanne irin quality da namiji ke buqata a gurin mace,bana haufin watan watarana zaki samu wannan gurbin......zaki samu wannan muhallin......za kuma ki samu wannan darajar......wannan matsayin da kuma wannan matakin". Har tsakiyar zuciyarta takejin wani abu me sanyi yana kwarara mata da kalaman nanay,bata tana zaton haka abun zaizo da sauqi ba daga bangaren Nanay,duk da ita din me sauqi ce.......sai gashi yazo mata da sauqin fiye da yadda ta zata ko tayi hasashe ma.

"Na gode nanay.....na gode" Ta fada cikin matsananciyar kunyar data sanya takejin ba zata iya tashi tayi tafiya a gaban nanay ba.


โ˜…banda Dim light din da dakin yake bayarwa,ba wani sauran haske ko fitila data rage idan ka cire ta system din dake gabanta.

Su ukune cikin dakin,tsakanin qarfe goma zuwa goma da rabi na daren ranar.

Aisa akhnan da kuma shehinaz......kusan dukkansu su ukun,duk da suna zaune ne a mabanbamtan kujeru amma hankulansu yana kan system din dake gabansu wadda ta nuna maballai biyu. ACCEPT da kuma REJECT.

A yadda suke zaunen da yadda dakin ya dauki wani irin shuru saika rantse da Allah suna tsoron suyi qwaqwaran motsi kada wani abu me matuqar firgici ya dirar musu.

Blue eyes dinta da hasken system din ya qarawa wani irin haske me qyalli kawai take rabawa tsakanin fuskokin aisa da shehinaz wadanda suma junansu take kallo.

Tashi tayi ta zauna sosai tana sake fuskantar system din,sannan ta miqa hannu a nutse ta dannan maballin ACCEPT din,abinda ya sanya aisa fidda dukka idanunta waje tana dubanta.

"Biftu......kinsan me kikayi kuwa?" Zagayayyun idanunta ta daga a nutse hankali kwance ta zubewa aisa su,ta lumshesu sannan ta budesu,wanda iya hakan ya sanarwa da aisa tana nufin eh......nasan me nayi.

"Akhnan........wancan lokacin fa.......alfarma....."

"Alfarma?" Akhnan ta fada a nutse tana dauke hannunta daga saman system din tana zubewa aisa su a karo na biyu.

"Alfarma aisa?......" Ta sake maimaitawa tana maida bayanta jikin kujerar tayi relaxing tana fidda manyan idanunta waje.

"Akwai wani abu dama da za'a yiwa akhnan alfarmarsa a duk duniyar nan?" Ta qarashe maganar da sigar mamaki cikin muryarta. Duban juna suke ita da aisa na wasu sakanni,kafin aisa din ta dauke kallonta daga kanta

"Alfarma ko ba alfarma ba.....koma meye biftu,last time nayi kawaici ne kawai,kina tunanin idan sultane yaji kina shiga irin wadannan abubuwan ko mu zamu kubuta daga laifi a gurinsa?" Ta qarashe maganar tana dubanta sosai itama.

Yatsunta kawai akhnan take muzawa,ko meye aisa zata fada....ko meye aisa zata ce ta fadi din......daidai da ita ne,amma ta janye kalmar alfarma a maganarta,shine kadai abinda zai sanya ta fahimceta.

"Alfarma aisa....." Ta sake fada tana duban tafin hannunta da rashin hasken dakin yasa bata iya ganinsa sosai.

"Yes" Aisa ta fada kanta tsaye. Shuru ya kuma wanzuwa tsakaninsu,cikin qasa da minti daya ta yunquro da wani irin zafi zafi a muryarta.

"Yayi daidai.....kici gaba da alfarma din ko kada kici gaba.....ki zabi duk abinda kika zaba......koda wannan shine tsere na qarshe da zanyi sai na yishi" Akhnan ta fada tana soma sarrafa system din da zafi zafi tana cike duk wani abu daya kamata ta cike tayi submitting.
(08187255862 lu'u lu'u paying)

Ita kanta tasan cikin murna da alfaharin sake amsar gayyatarta suke,saboda ta tabbatar wani abu ne da bazasu taba tunanin zai yuwu ba.

"Haka kika ce?" Aisa ta fada ranta a bace sosai.

"Haba aisa mana......mubi komai a hankali don Allah" Shehinaz ta fada karon farko tana duban aisa din.

Tsam Aisa ta miqe tana dubansu,kafin ta ajiye kallonta na qarshe akan shehinaz.

"Ko meye zai faru......kada sunana ya fito a ciki gurin sultane ko nannie......babu Aisa a ciki sam". Daga haka tayi gaba abinta ba tare data ko waiwaye su ba.

Shehinaz ta wannan bangaren,duk da irin sabaninsu a abubuwa da dama ita da akhnan.......amma ta wasu fannonin a ra'ayinsu da kawunansu yafi zuwa daya. Kamar a wannan bangaren......shehinaz mutum ce mesonh abubuwan da zasu bata nishadi gami da sakata walwala,don haka tseren ke nishadantar da ita itama,to amma ita kanta ba zataso sunanta ya fita wajen

20 / 21