Author : Safiyya Abdullahi Huguma Category : New Hausa Novels 2026
Sosai momma ta sake zuqar wani numfashin da ya cakuda da nannauyar ajiyar zuciya. Akhnan itace BARAZANARTA ta farko a rayuwa duk da ta kasance wani ruhi me tsananin daraja a wajenta fiye da diyoyin da suka fito a cikin ta. Akhnan itace barazanarta ta wani bangaren kuma itace kwanciyar hankalinta......akhnan itace matsalarta ta wata fuskar kuma nutsuwarta da kwanciyar hankalinta........shin ta yaya zata maida komai ya zamana akan saiti?,tambayar da ita kanta bata san amsarta ba.
Daya daga cikin kebantattun lambunan gidanne wanda ya zama na musamman koda a cikin masarautar. Waje ne da yake da sassa biyu masu matuqar dadin zama saboda shuke shuke na musamnan dake gurin. Kusan kowanne tsiro da aka dasashi a wajen ya fito daidai da girmansa asalin irinsa daga qasar France da Germany aka kawoshi,wannan ne ya sanya zaka ci karo da tarin tsirrai wadanda sam sam baka sansu ba baka kuma sama dasu ba. Ya zama na musamman ne saboda irin wannan tsirran da yake qunshe dasu,sai ya sake zama na daban saboda tarin nutsuwa da rashin hayaniya da gurin yake dashi.
Tun gabanin ka qarasa kaiwa ga lambun zakayi amannar cewa wani isashe ne a wajen......wani basaraken ko kuma wanda sarauta ke zagayawa a duniyarsa. Tarin dogarai dake tsaitsaye a kowanne dagin qafa da zakayi da kuma saukewa,cikin shiga da suturar masarautar TAHUO. Ba wanda ke motsi a cikinsu,suna tsaye ne qyam cikin son bawa yarimansu kariya. A nutse take karantar yanayinsu da yanayin da gurin ya sauya izuwashi cikin kowanne taku nata da zatayi,ta sani masarautar TAHUO din babbar masarauta ce kaman yadda tasu take.........girma dadewa da kuma yawan al'umma,saidai batajin ta kamo tasu ta fannin IZZA da QARFIN IKON da suke dashi.
"Eh........ Lallai ne,da gaske ne abinda ake fada game da yarima altaab" Aisa dake takawa tare da akhnan ta furta qasa qasa daidai yadda sautin zai isa ga kunnen akhnan. Da gaske take,tsarin da yanayin ya burgeta,yanayin da ya sanya cikin jikinta takejin kamar akhnan tayi miji........kamar altaab din zai dace zaiyi kuma daidai da tsarin akhnan.
Baki kadan akhnan ta tabe,saidai bata ko motsa labbanta ba ballanta tace komai da aisa. Bata jinta cikin yanayin magana,koda kuwa tana da jin cewa wani abu tasan wannan banbancin dake a tsakanin tunaninta hangenta dana sauran al'umma ya zama babbar katanga kuma hijabi daga fahimtar ma'anoninta motsinta da maganganunta.
Kamar a cikin jikinsa yake jin tahowarta......kamar a cikin jikinsa yake jin alamun fuskantowarta zuwa muhallin da akayi masa mazauni,saiya daga kansa a hankali daga duban Mac book din da yakeyi,yayi kyakkyawan gani kuwa ta hanyar zube idanunsa a kanta lokacin da take takowa d'ai d'ai da qasaitaccen takunnan nata.
Wani irin abu ne me qarfin gaske ya harba daga tsakiyar qirjinsa zuwa zuciyarsa........wata mummunar faduwa gabansa yayi,sai ya lumshe idanunsa can qasan zuciyarsa yana gayawa kansa.
"Ka nutsu altaab". Tsahon second biyar sannan ya sake bude idanunsa yana maidawa kanta da wani irin qwarin gwiwar daya samu ya arota da qarfin cin tuwo.
Ba sau daya ba,ba kuma sau biyu ba yakejin labarin kwarjinin da take dashi. Sau da dama......sau tari kuma siririyar dariya yake saki,shine fa altaab........altaab nu'uman sirreen?,har akwai dama wata halittar diya mace da zatayi masa tasiri da girma?,har akwai wata qwayar halittar KWARJINI da zata sanyashi ya gaza fuskantar diya mace ko wacece ita?,komai girma da izzarta......komai qarfin ikon masarautarsu?......kai koda hurul'eeni ce.
Daga sanda girma ya ruskeshi.......shekaru suka cillashi zuwa matakin samartaka baisan adadin matan da suka soshi ba.......baisan adadin matan da yayi soyayya dasu ba.........baisan adadin matan da ya sanya kuka a kansa ba.......sai a yanzun 'yar sarkin AGADEZ zata gagareshi?.
Bai santa ba,......bai kuma taba katarin ganin koda gilmawarta ba bare akai ga ganin hotonta.....wani abu daya fuskanci yana wahala shine.......sanin ainihin fuskarta da kuma kamanninta,duk kuwa da cewa SHUGABA ce kuma CEO ta babban kamfanin da kaf nijer babu na biyunsa. Babban kamfanin da ida kace baka taba sanin sunansa ba ko bakasan da zamansa ba kayi gawurtacciyar qarya.
Tana da wani irin dogon tsinkaye.......iya nazari da kuma karantar komai da wani irin kaifin basira dana idanu. A yanzun da take takowa tana sake fuskantarsa kwata kwata hankalinta bai tare da aisa dake fasalta mata altaab din da yadda take tsammanin samun dukka wani quality da take buqata tattare dashi.
Inda a yanayin nishadi take tabbas zata yiwa aisa murmushi ne,a yau ta yarda ta kuma sake yarda da gasken gaske ita din tasha bamban da kowa.......kamar yadda take diyar MUHAMMAD HAMMUD tallin tal! Haka dabi'unta dama zabubbukan rayuwarta sukayi nesa dana kowacce mace dama kowanne mutum.
A abinda baifi taku goma ta riskeshi ba ta gama tantance altaab.......ta kuma tabbatar cewa YA FADI bazaici ba ba kuma zai tsallake sharuddan da take neman ya cikesu kafin ya samu nasarar mallakarta ba.
Duk da cewa tana qare masa kallo ne amma koshi da ake kalla din bai fahimci shi take kalla ba......tsaiwarta a gabansa ya sanya wani abu tsarga masa tun daga qasan tafin qafarsa har zuwa tsakiyar kansa. Hakanan ya samu kansa da miqewa da dan hanzari,ya miqa hannu yana jifanta da murmushi,ya dawo da daya daga cikin kujerun dake wajen daura da tasa yana fadin.
"Barka da fitowa......marhab". Har yanzu idanunsa na a kanta yana jifanta da wani irin murmushi hadi da sanya hannunsa ya sauke nadin rawanin daya rage bayyanar fuskarsa gaba daya zuwa qasan habarsa......murmushi da ya jima da sanin cewa,yana daya daga cikin abinda yake narkar da zuciyar 'yammata.......yana daya daga cikin abinda yake qara masa kyau tare da fidda zatinsa.
Wani irin abu na daban yakeji a kanta,wani irin yanayi da bai taba tsintar kansa a ciki ba game da kowacce d'iya mace ba.......tabbas inda yasan yadda AKHANAN take.......da ya jima da nemawa kansa ita. Sai yakejin kamar daya daga cikin matan dake aljanna ce aka sauko da ita gidan duniya.
"Na tsani yawan kallo" Kalamanta suka shiga kunnensa da wani irin kaifi da sautin muryar da yanayin amonta ya tilasta masa kubcewar ajiyar zuciya.
A nutse ta taka zuwa wata kujerar ta daban da wadda ya ajiye mata,har qasan ranta tana jin tambayoyinsa shikam masu sauqi ne idan har zai iya amsasun,don bata jin kwata kwata zai iya shallake sharuddanta. Inda zata iya,zata zabi tsaiwa akan zama harta sallameshi,saidai bata jin hakan ya dace da darajarta da ikonta.......baqo ya shigo cikin masarautarta ya kuma zama dalilin tsaiwarta saman qafafunta.
"Waye kai?" Ta jefa masa tambayar bayan ta zauna sosai cikin kujerar,ta kuma aza qafarta daya saman daya da wani irin salon zama dake sake tabbatar da izza da qasaitarta.
Sauke idanunsa ya somayi akan qafafun nata,duk da ko farcenta bai samu daman gani ba amma salon zaman nata sai yaji gaba daya ya tafi dashi. Karon farko da yaji ya soma d'ari d'ari,ya kuma soma raina qarfin nasu ikon da a baya yakejin ba wata masarauta ko sultane da yakai mahaifinsa,ballantana azo Maganar 'yan'yan iko irin na nasu masarautar.
Tambayar tata ta bashi mamaki sosai,ya maida dubansa saman fuskarta yana son karantar gaskiyar tambayar tata. Abu na farko da yayi tsammanin fara ji daga bakinta shine tarba........ban gajiya sannu da hanya bisa tattakin da yayi har zuwa gareta,koda ace babu gaisuwa cikin tsarinta. To amma duka ba wannan ba........shi ALTAAB ne bata sani ba?.
"Da gaske bakisan waye altaab ba?.......altaab nu'......" Daga masa hannu tayi tana alamta dakatar dashi.
"Ka fadi matakin farko........waye kai?" Ta sake jefa masa tambayar tana ware manyan idanunta saman fuskarsa,idanun da suka sanya gabansa sake tsananta faduwa.
Yasha ganin blue eyes iri daban daban amma ba irin nata ba........yasha ganin idanuwa masu shape da launi daban daban amma banda irin nata.....natanne da gaske ko itama tana amfani da qwayar canza launin idanu?.
"Na tsani kallon qurilla" Ta furta a hankali tana ware yatsunta suka zama guda biyu.......
Motsin da tayi da yatsunta guda biyu kadai suka baiwa birra dake zaune daga qasa a gefanta alamar mataki daya ya ragewa altaab ya rasa damar ganawa da akhnan din.
Wani abu ya hadiye fargabarsa taba qaruwa,fargabar rasata,fargabar rasa damarsa. A baya bai zurfafa da yawa haka a kanta ba,don baisan yanayinta ba baisan kuma yadda take ba,amma a yanzun da idanunshi suka gauraya a kanta sai yakejin dukka burinsa na duniya ya ta'allaqa a kanta,duk burinsa na duniya ya rataya ne akan son ta zama MALLAKINSA,don haka ya hadiye dukka mamakin da take bashi hade da wani yawu daya zarce zuwa maqogoronsa ya fara magana.
"Sunana altaab dan sarkin tahoa sarki nu'uman......nine d'ansa na farko daya haifa kuma magajinsa da zai maye gurbinsa nan ba da jimawa ba in sha Allah........" Yatsunta na hagu ta kada masa,abinda ya fahimtar dashi dakatar dashi takeyi.
"Ba wannan nake nema ba.......waye kai A DUNIYA........wacce daraja gareka bayan SARAUTA?.......da wanne abu kake jin zaka iya mallakar AKHNAN?" Cak komai yaso tsaya masa,saboda tambayar tazo masa a sanda bai shirya mata ba,tazo masa ne a sanda baiyi zaton akwaita ba.
Dukka jarumatar da yakeji yana da ita ya tattaro guri guda,wani sashe na zuciyarsa na qarfafashi ta hanyar tuna masa.
"Kaine fa wannan altaab din da mata ke kuka a kanshi.....kada ka bada maza mana altaab......kada ka bari 'yar sarkin AGADEZ tayi nasara a kanka......ka kafa tarihi.......a kuma kafa tarihi a kanka,kayi nasarar da maza da yawa da suka nemi mallakarta suka kasa kafashi.
Wannan qwarin gwiwar daya samu ya sakashi sakin murmushi.
"Wannan ai tambaya ce me sauqi........ko waye kuma kika tambaya koda bani ba zaki samu amsarta.........sanin kowa ne mahaifinmu babban attajiri ne daya tara mana dukiyar da bana tunanin ko dan jika a zuri'armu zaiyi wahala a rayuwa.......komai da muke da buqata an tanadeshi tun kafin haihuwarmu.......bama buqatar karatu me zurfi don mun mallaki abinda takardar zata bamu tun kafin samuwarta..........idan kika auri altaab zaki san cewa kin samu kalar mijin da yakewa mata wahala........kin taki babbar sa'ar da ba kowacce mace keda irinta ba.....". Yatsunta ta sake motsa masa,tana jin kalamansa gaba daya sun mata banbarakwai.
Ita akhnan ce zata taki sa'ar mallakar altaab?.......ba altaab za'a yiwa murna ba idan har tsananin rabo ya ratso da sa'arsa cikin rayuwarta?.
A iya wannan gabar taji ta kowanne fanni altaab ya gama rikitowa.....
"Zaki nake nema ba kura ba.......me fita yayi farauta ba wanda ake farutowa ba.......ILIMI ina buqatar mijin da iliminsa ya kasance shine matakin qarshe na ilimi a DUNIYA......SA'A kuma tana ga wanda yayi nasarar mallakar diyar sarkin agadez.......bazan wahalar da lafuzza na ba wajen yi maka sauran tambayoyi ba.....don ka fadi tun a nan......abu na qarshe....." Ta furta da kalaman dake fita a jejjere kamar wadda ke irga adadin haruffan da zatayi amfani dasu a wajen...........
Abu na qarshen da bata fadeshi ba kenan saita miqe a qasaice,tana jin kamar iya haka ya kamata ya gama jin sautinta,kamar tayi masa alfarma me yawa idan ta qara bari yaci gaba da jin sautin nata........abu na qarshen data qi gaya masa ta kuma kalmashe magananta a cikinta ta fara takawa dashi,ya bita da wani irin razanannen kallo me cike da mamaki,saidai ita dinma tana jin ya kamata maganar ta fits a cikinta.........yadda aka halicceta kenan......yadda ta dabi'anci kanta kenan.....muddin tana ji a zuciyarta ya kamata magana ta fita tana barinta ta fita,bata ajiyar maganganun da takeji sun cancanci su fita din.
"Bakayimin ba......baka dace da irin tsarina ba".
"Wanne tsarinne irin naki?,a shirye nake na dabi'anci kaina zuwa ga wannan yanayi da tsarin" Altaab da ya kasa zama ya miqe da wani irin sauri ya furta yana duban akhnan da bayanta kawai yake iya gani wanda ke lullube da babban mayafin dake sharar qasa wanda yazo hade da rigar.
"Ka makara........kafin ka shigo da'irata ya kamata kasan wannan" Abinda ta fada kenan a taqaice,sai taci gaba da takawa tana motsa yatsarta,abinda ya bawa birra daman matsowa dab da bayanta a rusune tana biye da ita.
"A fitar da kyauta mafi girma da nauyi wadda zata taba zuciyar masarutar tahou a hadashi da ita........akwai abota tsakanin mahaifinsa da sultane........ina buqatar tarin karamcin agadasawa yayi masa rakiya zuwa gida". Ta fada tana jin kamar a yau lambun yayi mata tsaho da yawa,don bata da burin da ya wuce ta kammala ficewa daga cikinsa.
"An gama Allah shi taya miki" Birran ta furta cikin tsananin girmamawa.
Haka kawai takejin wani nishadi yana ratsata sanda take takawa tana komawa zuwa cikin gida.......tunda ta samu ta kori altaab sai taji kamar ta zare wata qaya. Wannan nishadin nata ne ita kadai,kuma wani yanayi ne da bazai boyu a fuskarta ba,bata kuma buqatar tayi wani abu da zai sanya hadimai na gidan da nata hadiman sassauta matsayinta da izzarta,don haka ta sallami kowa ta soma takawa ita kadai zuwa nata sassan ta wata sirrintacciyar hanya data haramta kowa ya bita idan ba sultane ita ko su mammina ba.
Shukokine suka lullube hanyar suka zame mata tamkar sune rufin gurin,wasu irin shukoki dake sarqafe da junansu,wannan ya bawa tsintsaye da yawa daman baje kolin samar da guraren zama gurin. Wasu irin tsintsaye da dare da rana basa gajiya da raira waqoqi da wani irin kuka me sanyi. Duk da cewa nishadi ne qasan ranta amma sam bai nuna saman fuskarta ba. Tsaki taja karo na hudu kenan,tanaso ta kawo dakatar da zuwan da maza sukeyi neman aure gurinta. Ta fara gajiya,tana kuma hangen raguwar martaba ne kawai a gurinta. Batasan rana ko lokacin da wani namiji zai samu yarjewarta a aure ba......to meye duka na batawa kai lokaci irin haka?. Sam ita bata shirya rabo kowa cikin rayuwarta ba,bata sha'awar hakan sam,don bataga abinda zasu bata ba.
Hankalinta kwance ta isa ga qofar data sadata da sassanta,bata kuma tsaya ako ina ba ta zarce zuwa bedroom dinta.
*_Uhmmmm........tofa😊_*
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*LAST FREE PAGE 05*
_____________________________
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mutanen Zuzeam ventures
Ga wani sabon promo na bullo muku dashi don farin cikinku dajin dadinku
Kunsan promo na na dabanne namu ba irin nasu bane hajiya ta mai kike jira da 7500 dinki ki kwashi kayan 19k
1. Rabin kazar mallaka 4500
2. married femfresh wash 2k
3. garuka 7in1 masu wata 7 ajiki 2k
4. Gumbarmadaradanonon rakumi 1500
5. Tsimin mallaka 2500
6. maganin infection 1500
7. matsin mallaka ba aba mai kishiya 5k
Duka kayan 19k za a baki akan 7500
Kuma mutun 20 na farko sunada kyautar kayan 4k
Matsin maida tsohuwa yarinya 1k
Gumbar emergency 1k
Turaren mallaka 2k
Allah yaba mai rabo sa a Zuzeam ventures takuce 🥰👍🏼
Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi https://wa.link/l1gcz8 gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye ta WhatsApp 08144015291 muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
😁😁😁 https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
____________________________
★Yadda Armelle da take zaune a gabanta ta sadda kai cikin wani irin taushi da rashin son su hada idanu kadai ya darsa qaqqarfan zargi a ranta. Tun kafin Armelle ta bude bakinta tace komai ta soma hasashe iri daban daban,hasashen daya soma haifar da motsuwar zuciyarta da kuma soma taruwar gangamin tawagar fushi a qasan zuciyarta.
Ta sani......wannan din dabi'arta ce,tana da zafi,tana da fada tana kuma fushi,saidai dukka wadannan dabi'un nata akan gaskiyar ta suke faruwa. Ba ita ta yiwa kanta wannan shaidar ba......kusan shaida ce data sameta