L U'U L U'U BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY HUGUMA.txt

Author :  Safiyya Abdullahi Huguma Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   3 / 21

6K to 9K   out of 62.7K words

dauki halittarsu wata aba me muhimmanci ba da zanyi komai don na burgesu ba.........kawai darajarsu guda daya ce........da abaat(sultane muhammad hammud)ya fito a cikinsu" Tayi maganar sanda take sanya qafafunta don fita a dakin.

Cikin kwarjinita take takawa tana ratsa sassanninta zuwa sassan mammina. Wani kwarjini da kusan gadonshi tayi daga wajen abaat dinta wato sultane muhammad hammud,anyi ittifaqi a tarihin qasar agadez ba'a taba sarkin da yake da kwarjini irinsa ba. Da yawan sukan fadi maganganu akan irin kwarjininsa,wasu sukance nema yayi......wasu kuma suce dabbar daji yake ci wadda take da irin wannan tasirin a jikinta,yayin da wasu ke alaqanta hakan da yawan ibada da yake da ita da riqe dokoki da shari'ar Allah daidai gwargwado,wannan ya sanya wani haske na musamman da kwarjini ya wanzu a fuskarsa.

(Tabbas.....ga duk mutumin daya riqi ibada zaka sameshi da wani irin kwarjini.......zaka samu wani haske na musamman akan fuskarsa darajar wannan ibadar,Allah ya bamu dacewa ya sanyamu daga cikinsu ameen).

Birra buhaina bushira da barra'u,suna cikin amintattu kuma hadimanta makusanta. Cikin tarin hadiman da take dasu su kadaine mafi kusanci da ita. Zababbun hadimai da aka mallaka mata su,wadanda asali iyayensu da kakanninsu suma amintattu ne ga sarki muhammad hammud dama iyayensa. Wata qarin daraja ce me yawan gaske samun damar zama hidimi ga ZUCIYAR SULTANE wato AKHNAN,wata dama ce da mutane da yawa sukaso ta kasance dasu,saidai su din suka samu saboda aminci da nutsuwa da kuma nagartar halayensu dana mahaifansu.

Suke take mata baya cikin kula da kowanne taku nata da kuma inda suturarta dake sharar qasa take sauka. Aisa na gefanta tana amsa wayar da akhnan batasan ta waye ba,don hankalinta ya tafi kan yadda zirga zirga ta ragu a sassan mammina din cikin qanqanin lokaci. Tasan wannan aiki ne da kuma umarnin mammina........ba yau ta fara yin baqi makamantan altaab ba,a duk lokaci irin hakan kuma takan hana yawaitar zirga zirga a cewarta kada a rabawa diyarta hankali,har sai ta gama ganawa dasu sun wuce.

"Barka da fitowa ado kuma zinariyar SULTANE" Abinda bakunan da yawa daga cikin hadiman sassan mammina ke fada kenan cikin girmamawa da yin qasa da kawunansu. Su birra ke amsa mata,suna kuma biye da ita,sukaci gaba da wuce faluka har suka kai bakin wata pivot door da akayi mata zubin masarauta sosai.

Sakin mata rigar sukayi suka kuma ja baya,don tasu iyakar kenan,saita sanya kai zuwa parlor din bayan ta tura qofar,ita da aisa suka sanya kai.

Tana tsaye gaban wani kyakkyawan madubi da zakayi zaton fuskarta take kallo,saidai kuma ba haka bane,qaramin kaskon turaren wutane a hannunta wanda qamshin turaren ya gama zama a parlor din tun wani lokaci me tsaho daya shude.

Duk da bata waiwayo ba amma ko a iya haka zaka iya gane tsahon da take dashi. Giant ce wadda ke sanye da wata irin riga da laushinta kawai zai saka ka kasa kiranta da alkyabba. Ba komai a jikin rigar sai wani irin zanen adon dawisu ruwan bula(blue color) da yarfin ruwan dorawa cikin zanen jelarsa.

"Assalamu alaikum" Aisa data ajiye kiran da take amsawa tayi sallamar,abinda ya sanya matar amsawa kafin daga bisani ta waiwayo fuskarta fadade da murmushi.

Da dan sassarfa akhnan ta soma takawa,ta isa ga matar ta rungumeta sosai gami da shigewa jikinta,sai ka rantse qaramar yarinya ce da duka shekarunta basu haura uku zuwa biyar ba.

Da madaukakin murmushin nan ta maida hannuwanta ta lullubeta da kyau,sannan ta jata kujerar kusa dasu ta zauna tana zaunar da ita a gefanta.

"Kyau gadon gidanku ne diyata......kinyi kyau matuqar kyau.......amma me yasa su birra suka baki suturar da ba ita na basu ba?" Mammina ta qarasa maganar idanunta akan fuskar aisa.

Dukka girarta isa ta dage tana qarasowa ta zauna saman hannun luntsuma luntsuman Royal sofas din dake parlorn.

"Duk cikinsu kowa yayi aikinsa yadda ya dace yayi.......matsalar daga gurinta ne,c'est une fille têtue(she's a stubborn girl)" Ta qarasa maganan tana jefawa akhnan harara. Idan tana gaban mammina din komawa take tamkar wata jaririya,wani irin gata da kuma kulawa mamminan take bata,zaka dauka yau aka haifeta tsabar kulawa da riritawa.

"Daina fadin haka aisa........shi maraya a kullum abun nuna kulawa ne......abun ayi masa abinda ranshi keso ne,ba'a bari hawayen maraya ya zuba ko a sakashi a damuwa" Ta fada tana dafa kan akhnan. Ire iren maganganun mammina kenan da kullum suke qarawa akhnan qaunarta,duk da tana jin cewa ita bata rasa mahaifiya ba sam sam,tunda gata ga mammina din.......bata taba sanin radadi ko ciwon rashin uwa ba tsahon rayuwarta.......tana jin mammina ta maye mata gurbi,gurbin sama da uwa ma. Sosai ta qanqame mamminan tana sakin qaramin murmushi,tana kuma iya hangen yadda aisa ke jifanta da harara.

"Tashi muyi magana akhanan" Mammina ta fada tana gyara muryarta. Sosai ta miqe ta zauna tana zubewa mammina blue eyes dinta da suka rusuna suka rage girma.

Itama idanun akhanan din take kalla wani abu yana huda zuciyarta. Idanu ne da kullum ta kallesu saisun taso da wani tsohon birnannen abu daga zuciyarta.......idanu ne da idan ta kallesu kullum sai sun tuna mata da wani abu......wata rana.......wani lokaci dukka da suka shude shekara ashirin da uku a baya.

"Altaab nu'uman" Mammina ta fadi sunan daya sanya girar akhnan tsukewa kadan.

"Yana da dukkan ingancin da nake zaton ya isa a soshi akhnan,wannan dalilin ya sanya na bashi qofar zuwa gurinki da amincewar me martaba.........ki nutsu akansa da kyau,idan yayi miki shikenan,idan baiyi miki ba babu me tilastaki......wannan din alqawari ne muka yiwa kanmu ni dame martaba".

Sai data zare jikinta daga na mammina sannan ta gyada kai. Qasan ranta kawai takeji wannan din bata lokaci ne da kuma bata bakinta kawai da mammina keyi din,gaba daya tsakanin jiya da yau tana jin kamar an bata mata awanninta ne kawai,tasota da sultane yasa akayi tun daga niamy......ya banbareta daga kan aikinta,ya barota daga ayyukan kamfaninta da take tsaye a kai,wani abu guda da bata taba gajiya dashi.......wata hidima qwaya daya da bata taba jin ta qosa da ita ba.......hidimar kamfaninta........kasuwancinta........kuma babbar kadarar da kaf cikin kadarorin sultane Muhammad hammud babu me kima da darajarta........wadda soyayyar da yake mata ya sanyata sallamar da ita ga AKHNAN din. Wannan din wani abu ne da yayi matuqar girgiza zukatan mutane da dama.........abune da ya bada mamaki ainun cikin masarautar gaba daya. Wani abune da ba'a taba hasashen faruwarsa ba tsahon zamanin,domin kamfanin ZUCIYA ce ta dukiyar sultane dama abinda ya mallaka.

Faruwar abin ya bude wasu qofofi da dama da a baya suke a rufe.....ya bude wasu qofofin da ba'a taba tsammanin budewarsu ba.......ya kuma qarasa bude wasu da motsi kadan suke jira su bude din. Yabar wasu irin tabbai.....da muhimman al'amura cikin zukatan mutane da yawa.......hakanan ya gadar da wani gagarumin shirin QUDURI da baisan zai zamewa rayuwar AKHNAN din BARAZANA BA......barazanar da take ci gaba da bibiyarta ba tare da idanun masu kallo nazari ko hasashe sunkai kai ba.

Da kanta mammina din ke biye da ita a baya tana kuma jeranta mata addu'o'in samun daidaito tsakaninta da altaab nu'uman,addu'ar da akhnan ke ji tana mata yawo akai da zuciya......tanason cewa mammina tabar addu'ar nan haka don bata tunanin zatayi amfani a wannan muhallin da gurbin,saidai miskilancinta dake a kusa ya hanata buda baki tace da mammina komai.

"Allah shi ja kwananki.........Allah shi karya maqiyanki". Kakkaurar muryar ta karade parlorn farko da mammina......wanda daga shi sai 'yar farfajiyar da zata fiddaka da sashen.

A nutse akhnan ta daga kanta tana ajiye dubanta daga sashen da take jiyo sautin. Tamim ne,mutumin da har yanzu ba zata iya tuna ko tantance lokacin daya samu kansa wanze cikin masarautar ba. Bama ita kadai ba,kusan duk wanda ke cikin masarautar bazaice ga sanda tamim ya zama halalin masarautar ba......ba wani wanda zai iya dorar da komai a kansa........an wayi gari yana rayuwa a masarautar kamar sauran al'ummar masarautar........kamar kuma yadda sauran hadiman cikinta ke rayuwarsu.

Yana da wani irin ladabi da ya siya masa kusanci da qauna me tarin yawa daga wajen mammina..........yana da wani irin biyayya da d'a sama da biyayyar bawan da ubangidansa ya zuba kudade masu kauri ya siyeshi........tamim din ya samu wani kusanci da sultane muhammad hammud ta hannun mammina din,wanda ha jima da zama dan gidanta.......kuma amintaccenta da ya kasance lamba na daya a bangaren maza hadimai na gidan. Yadda yake nuna qauna da kulawa ga akhnan........yadda yake nuna sadaukarwarsa akan duk wani sha'ani nata.......yadda yake nuna fansar ransa game da masarautar agadez dama duk wani lamari daya shafeta ya sanya ya sake samun shiga sosai wajen sultane muhammad,ya bashi yabo ya kuma bude masa wata qofa ta aminci yarda da kuma kusanci.

Tun kafin ta gama zama KHADEEJA take ganin irin wannan tsananin girmamawa daga tamim. Girmamawar da har qasan ranta duk da tarin izzarta da sarautar dake yawo a jininta takejin tafi qarfin nata girman. Ba zata taba iya tuna wata raba qwaya daya ba tun bayan data mallaki hankalin kanta da tamim ya taba tsaiwa a gabanta alhalin tana tsaye ba bare kuma a zaune,ba zata taba tuna wata rana guda daya da tamim ya hada idanu da ita ba ko ya gaidata yana sanya idanunshi cikin nata ba. Ire iren wadannan abubuwan suka sayawa tamim din wata 'yar daraja kadan daga gareta,duk kuwa da cewa ba zaka taba fahimtarta akan hakan ba koda da motsin yatsan hannunta ba.

Abu guda daya ne da har yanzun takeji game dashi,bai kuma taba gusawa ko motsawa daga ranta. Yanayin zubin halittarsa da qirarsa da idan ka kalla zakaga tasha banbam data sauran mazajen qasar agadez......hakanan kuma tayi banbanci da dukka qabilun dake qasar niger gaba daya. Idan kayi masa kallon farko aka ce maka

"Wannan din mutumin kirki ne" A karon farko zaka qaryata hakan,don babu wata siffa tashi guda daya dake nuna haka,saidai kuma mu'amalarsa sauqin kansa da kuma irin girman daya runguma yake basu gaba daya zai gaya maka gaskiyar abinda aka gaya maka da farko.

Ta gota tamim da taku kusan uku,amma haka kawai taji kamar an fusgi hankalinta. Ta waiwaya kadan ta saci kallon inda yake duqe har a sannan kanshi a qasa,mammina kuma na tsaye a gabansa ta dakata daga tattakin da take musu.

"Wanne irin yarda da aminci ya samu daga wajen mammina ne?,har yake iya ruskar inda take kai tsaye?,baya ga tarin dogarawan dake gadin sassan?" Ta yiwa kanta da kanta tambayar dake yawo qasan ranta.

"Yana da kirki da sauqin kai,amma har yanzu na kasa sabawa da ganinsa,sai na dinga jin shi dabanne a cikinmu" Akhnan ta furta a hankali da yanayin daya sanya aisa waiwayowa ta kalleta. Maida dubanta gabanta aisa tayi sannan a hankali tace.

"Komai naki ya bambanta dana mutane akhnan.....ki yawaita addu'ar daidaituwar dabi'unki dana kowa......kirkinsa shine abun dubawa ba wani abu na daban ba" .

Shuru tayi maganganun aisa suna dawo mata. Ita ta sani a karan kanta ba kowa bane yake iya fahimtarta ba,ba kowa bane yake iya karanta badinin halayenta ba,shi yasanya sau tari takan zabi yin shuru akan yin wasu bayanan........takan zabi yin shuru akan yin wasu maganganun.


*MOMMA*


Kamala gami da haiba ne suke magana da kansu a dukkan wani taku qwaya daya da zatayi zuwa kebantaccen parlor dinta da takan gana da baqin da suka kasance na musamman a wajen ta.

Doguwace irin tsahon da zaa kirashi da tsaka tsaki,irin tsahon da yake qarawa mace kyau kawai bawai don ya sanyata cikin jerin sahun kyawawan mata ba.

Sanye take cikin tufafin al'ada na cikakkun buzaye,tufafin da aka zamanantar dashi da wani irin sakakken dinki daya suturce jikinta gaba daya ya kuma qara mata kwarjini da cika idanu.

Ko ba'a gaya maka ba kana kallonta kaga buzuwa..........irin buzuwar da ko a cikin qabilarsu da yaren nasu ma ta musamman ce ita. Farace qal kamar zaka ita hangen jijiyoyin dake kai saqon jini a jikinta.........hannuwanta da qafafunta sunsha qunshin jan lallen da ba'a masa kowanne irin ado ba,an qunsa ne bisa siga da yanayin gargajiyar da aka saba. Koda kanta yake a lullube amma hakan bazai hanaka ganin tudun sumarta dake daure cikin lallausan farin mayafin data yane kanta dashi ba. Lokacin da qafarta kuma ta taka matakale qarshe mata biyun dake tsaye a gurin kamar masu jiran isowarta suka fara gaidata.

"Barka da saukowa......barka da fitowa".

"Barka kade.......sannunku da hidima mamo sannunku samia" Ta amsa musu cikin kulawa da yanayin nan nata na girmama dan adam koda wayeshi.

"Armelle ta iso?" Ta sake tambayarsu tana takawa a tsanake ga hanyar da zata kaita parlor din.

"Ta qaraso......tadan jima tana tsimayinki ma". Wadda aka kira da mamo ta fada tana kama stairs din saman nata,don ita da samia suke kula da tsaftar makwancinta.

"Yayi kyau" Ta amsa tana dokin isa ga armelle din.

"A fito lafiya" Samia ta fada tana bin bayan mamo zuwa saman.

"Allah yasa" Ta amsa su tana buda qofar da zata kaita ga parlor din.

Babbar macace zaune cikin parlor din saman tattausan kilishin dake mamaye a parlor din. Wani irin ni'imtaccen muhalli ne maras hayaniya wanda ke dauke da kalolin peach da coffe light,tare da wani lallausan qamshin apple freshner daya wadatu dashi.

Baqa ce kakkaura,wadda kana kallonta kasan ta fito ne daga qabilar Agadasawa. Sanye take da wasu irin tufafi tamkar na saqi ruwan bula me turuwa sosai da har ya sanya suka kasance masu duhu kadan. Akwai wani haske na nutsuwa saman fuskarta,tare da wata kamala da bata rasa nasaba da riqon ibada.

"Barka da fitowa" Ta furta tana miqewa da ganin fitowar momma.

"Barka kade armelle........zauna" Ta fadi kafin ita din takai ga zama tana mata nuni da kusa da ita.

Zamewa tayi ta zauna satin qafafunta sosai tana tattara nutsuwarta.

"Allah shi taya miki......"

"Ya ake ciki armelle?" Ta tambayeta qagauta da jin bayanan daga bakin armelle din yana sake fitowa sosai saman fuskarta.

"Altaab nu'uman ya iso masarutar nan" Armelle din ta fada a taqaice.

"Alhamdulillah" Momma ta samu kanta da furtawa,kalmar data fito hade da wani nannauyan numfashi,saita maida bayanta ta jinginar ga jikin kujerar da take kai alamun samun rangwame daga duk abinda takeson ji din yana zagwanye daga fuskarta.

"Armelle" Ta kirata a nutse.

"Ranki shi dade".

"Ina buqatar cikakken rohoto game da yadda komai zai wakana,ina kumce sauraron jin daddadan labari".




*Zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*MYNITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*

FREE PAGE O4
______________________________
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mutanen Zuzeam ventures
Ga wani sabon promo na bullo muku dashi don farin cikinku dajin dadinku
Kunsan promo na na dabanne namu ba irin nasu bane hajiya ta mai kike jira da 7500 dinki ki kwashi kayan 19k
1. Rabin kazar mallaka 4500
2. ⁠married femfresh wash 2k
3. ⁠garuka 7in1 masu wata 7 ajiki 2k
4. ⁠Gumbarmadaradanonon rakumi 1500
5. ⁠Tsimin mallaka 2500
6. ⁠maganin infection 1500
7. ⁠matsin mallaka ba aba mai kishiya 5k
Duka kayan 19k za a baki akan 7500
Kuma mutun 20 na farko sunada kyautar kayan 4k
Matsin maida tsohuwa yarinya 1k
Gumbar emergency 1k
Turaren mallaka 2k
Allah yaba mai rabo sa a Zuzeam ventures takuce 🥰👍🏼
Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi https://wa.link/l1gcz8 gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye ta WhatsApp 08144015291 muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
😁😁😁 https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
________________________________



"In sha Allah,na miki alqawarin komai zaizo kamar a gabanki suka gana" Ta fada kanta a qasa. Kai momma ta jinjina tana jin yarda da armelle,ta tabbatar ba za'a samu akasi ba......tayi imanin komai zai tafi daidai indai armelle ce har fiye da yadda takeso. Tsam armelle ta miqe sannan ta rusunar da kanta.

"Na barki lafiya" Ta juya a nutse tana takawa ta fita a parlor din.

3 / 21