Author : Safiyya Abdullahi Huguma Category : New Hausa Novels 2026
daga wajen kowa.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" Ta furta tana kuma sake zama sosai ta zauna cikin Kujerar,sannna ta ajiye carbin hannunta a glass table din dake kusa da ita.
"Armelle"
"Ranki shi dade" Ta amsa mata tana gaza dubanta.
"Ki gayamin komai kada kice zaki boyemin". Kai sosai Armelle ta jinjina,sannan ta daga kanta a hankali ba tare data iya duban momma ba.
"Shima taqi amsarsa.......taqi karbar tayinsa na aurenta".
"Allahumma la sahla illa maja'altahu sahla.......la haula wala quwwata illa billahil aliyyul azeem" Ta fada tana qoqarin danne fushin dake taso mata.
Maida kanta qasa Armelle kawai tayi ba tare data sake cewa komai da ita ba. Kowanne motsi na uwar dakinta sananne ne a wajenta da abinda yake nufi,koda bata fada ba tasan cewa fushi ne sosai yake taso mata shi yasa take maimaita addu'ar. Da alama tana qoqarin danne fushinne da nauyin addu'ar don gudun aikata abinda zai jawo musu dana sani.
"Armelle.......idan na lissafa daidai wannan shine karo na goma sha daya da biftu ke aikata haka?". Kai armelle ta jinjina,tana jin tausayin momma din yana ratsata da yadda take sake dulmiya cikin damuwa cikin kowanne wucewar rana kwanaki da kuma watanni dukka akan AKHNAN din ita kadai.
"Haka ne ranki shi dade.......amma dole abi abun a sannu....don......" Hannu momma ta daga mata tana dakatar da ita.
"Jeki abinki armelle......kiyi haquri......nan gaba kadan zan nemeki". Tsam armelle ta miqe,tasan halin dattakonta,tasan kuma halin karamcinta,da gaske tana buqatar space dinne kamar yadda ta buqata.
"Allah shi huci zuciyarki" Bata iya amsawa armelle ba,don tana jin kamar zuciyarta zata balle daga qirjinta ne ta fito.
"Ki saka buhaina ta dubamin yiwuwar gabawa da sultane". Maganar tadan bawa armelle mamaki sosai. Baqon abune a wajenta ganin sultane ko kebanta dashi,musamman a irin wannan lokacin na yammaci......a kuma ranakun da yake samun yawaitar baqi qwarai fiye da kullum,amma sanin yanayin da ake ciki ya sanya bata tunasar da ita akan komai ba ta saka kai tana ficewa zuciyarta ita kanta cike da alhini da kuma dogon nazarin da taso ace momma ta tambayeta wani HASKE Ko ta shigo da ita ciki,to amma ita dimma tana tsaiwa ne kawai inda aka buqata,duk da dadewa da kuma tarin amincin dake tsakaninta da MORSA SAFIYYA(momma).
Cikin kowanne bugawa da jini da kuma zuciyarta sukeyi ba abinda takeji a cikin ruhinta sai wani irin tashin hankali. Khadeeja ce?,khadeejan juhaifanta......jinin JUHAIFA ne.....jinin juhaifa ne ake waannan wasan kuran dashi?......idan ta zuba idanu gudan jinin juhaifa qwaya data tallin tal data bari a duniya ya wulaqanta haka shin TAYI ADALCI?.......anya bata zama BUTULU ba?,anya batayi cin amana ba?. Jinin juhaifa ya zarcewa duk wata kima da martaba a gurinta da idanunta......zatayi dukkan wani yaqi......zatayi kuma duk me yuwuwa na ganin bai wofanta ba.
Ko sau daya ko kuma daidai da qiftawar idanu..........bata taba daukan iqirarin MAMMINA da wasa ba. Wani irin kalamai ne da suka yiwa zuciyarta kyakkyawan dashe,irin dashen da girgizarsa ko tabuwarsa ba abu bane mai sauqi. Ta aminta da dukkan zuciyarta wani babban yaqi ne ya shigo rayuwarta,tun a wancan lokacin ta sani.......jikinta kuma yake bata cewa akwai wani shiryayyen abu da zai iya faruwa,ko a kusa ko a nesa........sai gashi a nesan da bata taba kawo irin wannan nesan ba.
Duk yadda zuciyarta ke bata shawarar ta zauna ko zata hutar da qafafunta ko hakan zai kawo sassauci ciki rai da gangar jikinta amma ta kasa. Tana jin mintunan da aka diba kafin ta samu amsar yiwuwar ganin me martaba din kamar sunyi wani mugun tsahon da suka kusa daidaita da tarin watanni.
Kasa juriyar ci gaba da tsaiwa cikin falon tayi,don haka saita matsa da dan zafi zafin nama ta sanya lausasan takalmanta ta gyara lullubin dake saman kanta sannan ta soma fita a parlor din.
Barka da fitowa hadimanta suke mata cikin sadda kansu qasa,ta daure zuciyarta qwarai wajen ganin ta amsa musu yadda ta saba,duk da cewa ruhinta da gangar jikinta ba yana a tare dasu bane sam sam.
"A dubomin buhaina a duk inda take.........a gaya mata ta shaidawa sultane ina nan ina sauraron ganawarmu" Morsa safiyya ta fada tana hade tafukan hannayenta guri daya,cikin qoqarin controlling abinda takeji yana mata kaikawo a zuciya.
"An gama" Nanay ta fada,Daya daga cikin hadimanta dake da wani irin zafin isar da saqon morsa safiyya din.
Wata nannauyar ajiyar zuciyar ta sauke tana janye jikinta da idanunta daga jikin window din,wanda yake tuna mata da abubuwa masu tarin yawa da suka shude. Daidai lokacin da hadiman guda biyu ke shigowa buhaina da nanay.
Daga bayanta suka zube cikin girmamawa kamar yadda suka saba,sannan buhaina ta fara magana.
"Allah shi riqa miki.......me martaba sultane yana cikin baqi masu yawa.........duk da kusan da yawa ya sallamesu........amma gajiya bana tunanin zata barshi ya ganki a dai.........". Wani irin suka maganarta ta yiwa zuciyar morsa safiyya,zafin daya ratsa zuciyarta ainun. Ba al'adarta bace ganin sultane barkatai irin haka ba........hasalima ita da sultane din akan dauki kwanaki uku ba tare data sanyashi a idanunta ba,duk kuwa da cewa miji yake a gareta kamar yadda mammina take mata a wajensa. Lokuta da dama a duk sanda zata buqaci ganinsa a irin wannan yanayin,tana yin hakanne bawai don buqatar kanta ko wani kebantaccen abu da ya shafeta ba,kusan dukka buqatar ta mutum daya ce wato akhnan,duk da cewa a idanu da zuciyoyinsu basa kallon hakan akan buqatar kansu face buqatar qashin kai.
"Daga wanne lokaci zai iya shiga lokacin taqaitaccen hutu?". Saida buhaina tayi qasa da kanta sannan ta amsa mata.
"Nan da mintina biyar zuwa goma ranki ya dade".
"A daukomin rigar waje" Tayi umarnin tana soma takawa a hankali tana nufar qofa,abinda ya gaya musu cewa tana da buqatar fita kenan.
Ba jimawa mariya ta dawo da rigar da sassarfa,ta rusuna tana yafa mata,yayin da morsa safiyya ta qarasa sakawa sannan ta qarasa lullube jikinta da wani irin yanayi dake nuna zafin da takeji a zuciyarta dama jikinta gaba daya,suka fara takawa suna ficewa ita da mutum uku cikin hadimanta.
Duk taku daya da takeyi tana fuskantar sassan sultane zuciyarta qara zafi take mata. Kusan bayyanarta a wajen a irin wannan lokacin wani irin baqon abune da ba'a saba da ganinsa ba. Mutum ce ita da zaka dauki dogon zama cikin masarautar baka sanyata cikin idanunka ba......mutum ce da zaka jima a cikin masarautar bakaji tace komai dangane da komai ba.......idan nace komai ina nufin umarni hani ko kuma zartaswa. Kaf ta tattara hankalinta da rayuwarta ne dama duk wani ikonta a kan gidanta KADAI. takan fadi lokuta da dama idan ta zauna hira da hadimanta.
"Ba kowanne abu bane yake da buqatar kayi magana sharhi ko tsokaci akai ba. Wasu abubuwan zaifi kyau kayi shuru a kansu,domin shurun yafi zame maka ado kima da Kuma kwarjini hadi da cikar kamalarka a rayuwa". A tare da ita sun koyi abubuwa masu yawan gaske,a tare da ita sun dauki wani irin darasi da babu shi a kowanne sashe na duniyarsu.
Kanta tsaye ba kuma tare da jiran umarni daga dogarawan dake da wani irin shiga tsari da horo na musamman ba,wadanda ke tsaron qofar da zata sadaka da kebantacciyan parlor da yafi kama da wata fada me zaman kanta ta doshi qofar kai tsaye,abinda ya tilastawa duk wani wanda yake gurin janye ganinsa kame kansa da killace ganinsa daga kanta.
Koda ita din ba daya daga cikin matan dake da daraja ta farko cikin qasar agadez ce ba.......ita din ta musamman ce,da wata irin kamala da kwarjini da sassanyar nutsuwa suka yiwa tufafi. Tana da wani irin girma a zukata da kuma idanunsu.......tana da wani irin matsayi da KAME KAI da tsame baki daga dukkan al'amuran da basu shafe ka ba dama wadanda suka shafekan suke siyawa dan adam.
Ba su kadai ba.......su buhaina dukka da ta taho dasu suma nan din shine qarshen inda aka lamuncewa takawarsu,don haka ita kadai ta tsoma qafa a palace din da ta kebanta ga sultane muhammad hammud da kuma iyalinshi a halinsa.
Hankali kwance,cike kuma da wani irin nutsuwa ta fidda kayan jikinta ta musanyasu da wasu kaya da birra ta ajiye mata. Dogon wando ne leggings me bin jiki sosai,sai gown dinsa me dogon hannu data zauna das a jikinta ta kuma bude sosai daga qasa. Birra tasan zabinta,kusan tana cikin mutum na uku data gama sanin komai da take so,duk da har yanzun ita kanta tasan tabar birra dinne kawai ta san abinda taso ta sani din.
Sassan nata babu motsin kowa,domin kuwa sanannen abu ne.......mutum ce ita ba koda yaushe take da buqatar mutane a kusa da ita ba,wannan ya sanya dukka hadimanta suke tsananin kiyayewa da dukkan abinda suka san bata so,domin ita din zuciyar SULTANE ce,HASKEN AGADEZ kuma.
Hankali kwance ta zaba ta kuma nutse cikin jerin sofas din dake parlor din,sai a lokacin hankalinta ya koma kan wayarta,don tayi imanin wannan matsalar ta gama da ita kuma. Ta sani......bawai abun ya qare bane......bawai za'a tsaya iya haka bane.......amma har cikin zuciyarta take gayawa kanta da kanta zata yiwa tufkar hanci.....zata kuma daqile afkuwar hakan a nan gaba.
Ta gaji da ganin fuskokin mazan da suke nuna kansu a gabanta. Mazan da zuwa yanzu ba zata iya riqe lissafin adadinsu ba,har yanzu tana ji a ranta BASU KAI BA,wannan alfarmar tata har yanzu ba wani DA NAMIJI da ya samu nasarar taka koda matakin farko na samunta.
Sashen adana lambobi ta nufa(contact),taci gaba da dubawa a nutse da wani irin aji daya zame mata dabi'a koda ita daya ce a waje.
Haleesha shine sunan data tsaya akai,ta kuma danna kira sannan ta sanya wayar a handsfree tana ajiyeta a hannun kujerar kamar yadda kusan dabi'arta ce hakan. Ba kasafai take sanya waya a kunne ba......muddin hakan ta faru lallai duk wanda take magana dashi din wani mutum ne muhimmanci qwarai da gaske a wajenta,kamar sultane mammina aisa shehinaz da ire irensu.
Bugu biyu rak aka daga wayar daga daya sashen,saboda sanin illa barin kiran ya zama miscall da zai iya jawowa mamallakiyar number.
"Barka da yammaci Madame......" Aka fadi da sautin dake nuna tsananin girmamawa. Sai da taja fasali tana duba dogayen yatsunta,ta lumshe idanunta sannan ta budesu kafin tace
"Ya kike haleesha?"
"Ina lafiya Madame" Ta amsa cikin jin dadin nuna qanqanuwar kulawarta a kanta.
"Yayi........an kammala karbar designs din?"
"Eh Madame......ke kadai ke jira". Kai ta jinjina,tana jin zuciyarta da hankalinta gaba daya ya koma niamy
"Wannan tafiyar ce ta kawomin tsaiko......amma ina hanya gobe in sha Allah". Kai haleesha ta jinjina tana mamakin dawowarta da wuri.
"Allah ya kaimu Madame.....don sosai kasuwa take buqatar kayanmu".
"Tout se passeda bien in sha Allah(komai zai daidaita in sha Allah,zan kum duba demande(request) da kika turawa enterprisé".
"Je vouse remercie Madame(na gode madam)" Haleesha ta fada cike da farinciki.
Bata sake cewa komai ba ta gintse wayar,ta maido hankalinta cikin falon tana furzar da siririyar iska daga bakinta.
Ita kanta tana mamakin yadda take jin qirjinta wasai,duk da lokaci lokaci tana dan jin tunanin yadda sultane zai tunkareta da batun hambarar da lamarin altaab da tayi,duk cewa tasan bata da wata matsala ko damuwa game da sultane....don duk abinda takeso shine cikar muradinsa......amma ita din bataso ta sanyashi ko yaya yaji ba dadi akan wani mutum da bata jin darajarsa da d'ara ko ina ballantana ya zama silar sosuwar ran sultane.
Irin so takewa sultane da mammina.......wani irin tattalin muradi da kuma farincikinsu takeyi. Murdinta na cika burinsu akan duk abinda suka sanya interest akai daban yake a zuciyarta......sai kuma akayi katari su din suka kasance mutane ne masu fifita maslaharta da muradinta akan nasu.
Waya ta jawo,ta saka wasu taqaitattun lambobi don yin kira bangaren hadimai da bayi,wanda cikin qasa da mintina biyar birra ta bayyana.
"Ki duba dressing room.......a canza min luggage sababbi na gaji da yawo da wadannan.........karki sakamin komai a ciki sai inner wears din da mammina ta aikomin dasu da sleepwears......suna cikin wani LV Luggage........gobe inaso muyi fitar sassafe.......ki shaidawa manu.......banaso nayi sallan azahar sai a niamy".
"Angama ranki shi dade" Ta fada tana yin qasa da kanta sannan ta yunqura ta miqe. Har birra din tayi gaba akhnan ta sake kiranta.
"Je voudrais un verre de lait,s'il vouse plaît(ina buqatar cup daya na madara)" Kai birra ta jinjina a hankali sannan ta juya zuwa can wani sashe na daban da freezers din ke jere kamar an haliccesu ne don kawai su bautawa buqataun akhnan. Tana ciro madarar data kasance zallar madarar shanu ce lafiyayya me kyau,duk da wasu lokutan tafi amfani da nonon raqumi da akan tatsoshi musamman saboda ita daga lafiyayyun raquman dake masarautar. Wasu irin raquma ne masu daraja da tsada,saboda irinsu na musamman ne da zai wahala ka samesu ayankin nijer idan ba gidan iko irin masarutar agadez din.
Tana mamakin yadda fiye da rabin rayuwarta ta dogara ne da shan madara nono da 'ya'yan itatuwa. Qwarararrun Cuisiniére(cook) ne da ita da suke qarqashin jagorancin mutum guda da akullum sukan bata awanni kawai don shirya mata abincin da zata ci wanda zai burgeta,saidai kusan dukkan a wannin nan sukan tashi a banza,don abinda zata tsakura taci din zakayi tsammanin yau ne ta fara koyon cin abinci.
Sunyi hannun riga da qiba ballantana kuma tumbi,saidai kuma madarar da ta abota ta taimaka mata qwarai wajen samun wata irin lafiyayyar fata tsadadda da skin care product din take amfani dashi suka taimaka wajen bata wani nau'in kala na musamman koda cikin fararen matan ma,gefe guda kuma da murjajjen jikin dake da wani irin shape da ake kira da qirar cocacola ko kuma qirar kalangu a hausance.
Sai data ajiye mata komai da take buqata sannan tace.
"Kina da buqatar wani abune ranki ya dade?,ko kina buqatar su bushira su zama kusa dake?" Kai ta girgizawa birra,don a yanzun kadaicewa kawai take da buqatar yi ta shaqi iskar data cakuda da iya numfashinta ita kadai. Kada kan ya bawa birra amsa,saita juya a girmame tana fita don cika umarnin data bata dazun.
Sallamar mammina ta sanyata ajiye kyakkyawan glass cup din glass din dake hannunta da aka yiwa wani irin ado da launin gold dake sake tabbatar da sarauta zallarta.
Miqewa tayi tsaye tana jiran qarasowar mammina din tare da qoqarin karantar yanayinta don sanin dame mammina tazo din. Kadan kadan fargaba nason rabarta......tana da tabbacin mammina ta samu labarin tayi rejecting altaab........batasani ba ko altaab din yaso ya zama zabin mammina amma tayi rejecting nasa?,tana tsoron hakan ta kasance kuma ya zama silar bacin ran mammina din.
Sai data sake matsowa kusa da ita sannan ta fahimci kadaran kadaham fuskar mammina take,wannan yadan bata sukuni kadan,sukunin daya sanyata fara takawa ta ruski mammina din ta kuma aza kanta saman kafadarta tana sauke ajiyar zuciya.
"Don Allah mammina......don Allah kada kice altaab kinso ya zama zabina". Sakanni uku mammina ta dauka,sannan ta dora tafin hannunta saman kan akhnan tana shafawa a hankali.
" Har abada zabinki shine nawa.......har abada ba zamu tilastaki ko mu tursasaki zuwa ga auren wani ba.......namu shine mu nusasheki,idan kin aminta muma yayi mana......idan baki aminta ba muma baiyi mana ba.......amma saidai......" Mammina ta qarashe fada da wani irin sanyi a muryarta,sanyin daya Sanya akhnan daga kanta daga kafadar mammina din tana kallon cikin qwayar idanunta.
Girgiza kai akhnan ta fara yi a hankali.
"Morsa safiyya?" Akhnan ta fada tana son gasgata hasashenta. Kai mammina ta daga a hankali cikin alamun nuna d'ari d'ari,sai kuma ta kama hannun akhnan din ta jata zuwa saman daya daga cikin kujerun ta zaunar da ita ita kuma ta zauna a qasa a kuma gabanta hannunta cikin na akhnan har yanzu. Da wani irin sanyi taci gaba da magana murya qasa qasa.
"Banaso morsa safiyya taci gaba da zargina.......banaso taci gaba da yimin wani kallo na daban.......banason wannan alaqar.......wannan dangantakar da naketa qoqarin gyarata tsahon shekaru taci gaba da wargajewa......"
"To idan ya wargaje sai me mammina?.......me yasa kike abu kamar kina tsoronta ne?" Akhnan ta fadi tana ware manyan blue eyes dinta akan mammina,alamu na soma tasirantuwar bacin rai suna bayyana qarara saman fuskarta.
Da sauri tahau girgiza kai
"Kul akhnan,kada na qara