Author : Safiyya Abdullahi Huguma Category : New Hausa Novels 2026
sultane da nannie ba.......ga morsa a gefe data tabbatar azabarta zata iya shafe ta kowa.
"Akhnan" Shehinaz ta kirata da nufin gwada kwatanta mata bayanin tabar wannan race din.
"Kada kice komai.......na gama cike komai na tura musu......damuwata daya shine......bansan abokin kara wasan ba......bansan wanne me gangancin bane yakeson sai munyi wannan wasan ba......na tabbatar nayi kuma imanin yayi hakanne don ya zubar dani,ya kuma ramawa wadanda na zubar haushinsu a kaina" Akhnan ta fada a nutse tana sake duba bayanai a kansa,saidai kuma blank take gani,don babu koda cikakken sunansa ma bare wani abu daya shafu tarihin wasannin daya taba yi,wanda wannan shine ita kuma zai bata nata hasken..
Abinda ya dauki hankalin shehinaz kenan itama,ta manta ma da batun bawa akhnan shawarar ta haqura din,suka shiga bincike akan komai daya shafi abokin wasan,saidai har suka gaji da ita da itan ba wanda ya samu komai a kansa.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 32
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
_____________________________
"Na tabbatar akwai manufarsa........bawai hakanan komai ya tsara kanshi ba.......amma na yiwa kaina alqawarin saina bashi kunya kamar yadda sauran na bayanshi suka kunyata" Ta fadi tana rufe system din cikin cin matsanancin alwashi. Alwashin da ko a wancan wasan bataji tana da sha'awar ta cishi ba,tunda wancan wasan wasane kawai da ita a karan kanta ta yishi ne kawai saboda nishadi,sabanin wannan da taji yana neman canza salo.
★Cikin kwanakin ta rufe duk wani hanya ko dalili da zai sanya a nemeta a agadez........ta kuma maida hankalinta wajen gwaji da qara qwarara kanta a babban filin dake cikin gidanta. Sam bata kawo aisa a matsalarta ba,bata ma sake bi ta kanta ba. Ba wannan ne karon farko da suke samun sabani irin haka ba,kuma suzo su shirya kansu kaman bai taba faruwa ba.
Duk yadda aisa takai ga cika baki tasan ba zata iya komai ba,ba zata iya tona mata asiri ba. Ba kuma aisa kadai ba,a tsakaninsu su ukunñ babu wani wanda yake iya tonawa asirin dan uwansa,kowanne irin laifi daya kuwa yayi,wannan ya sanya nannie ke kiransu da MUNAFUKAN 'YAN UWA.
Sunan yana bawa sultane dariya,ya sani gaskiya anne ta fada,kuma sunan ya dace dasu,amma yakance
"Ayi musu haquri,a canza musu suna".
★★★ *HIPPODROME NIAMEY*★★★
Duk girma fadi da tsahon gurin amma hakan bai hana mutane cike gurin cif cif ba. Wani irin cika gurin yayi,irin cikar da bai taba yin irinta ba a tarihin gurin.
Gurin kuwa baiyi cikar banza ba,don kuwa wasan ya zama wani na musamman,fiye da ma da wasan da akayi wancan satin. Ninkin mutanen da sukazo wancan wasanne suka halasci wannan wasan,don da yawa gulma ta fita game da wacece 'yar wasan......sunanta da sunan mahaifinta,harda tambarinta a matsayinta na mamallakiyar katafaren kamfanin suturun mata masu aji.....mata masu abun hannu wato SAHEL COUTURE.
Mintina talatin din farko kawai akayi aka tafi hutun farko,amma sai mintunan suka zama wasu na musamman a zukata da idanun 'yan kallo. Kamar yadda suka zama na musamman a wajen akhnan da wani madaukakin farinciki ganin score din data samu tun a zagayen farko.
Wani irin wasa daya zama baqo a idanun masu kallo......su biyu ne rak mahayan......wadanda gaba dayansu ba wanda kake iya ganin fuskarsa saboda helmet din dake kawunansu. Mahayin doki na farko kana dubansa zaka fahimci namiji ne,saboda qira da zubin jikinsa daya bayyana a kayan hawan dokin dake jikinsa.....yayin da ta biyu ta fita a suffar mace sak......tun daga yanayin qirarta da kuma launin suturar jikinta.
Yana sane yake bada dukkan wata dama ga abokin karawarsa.......ba tare daya tantance macace ko namiji ba......yana sane yake dage qafa saboda ba nasarar tseran dawakai bace ta shigo dashi niger........nasarar aikin hukumar binciken sirri ne ya kawoshi.
Cikin muhallin da aka basu saboda hutun mintunan,hakeem ne ya miqa masa bottle na ruwa,cikin murya qasa qasa yace.
"Sun saka hope da yawa akan dan wasansu......ban tantance sunan na mace bane ko na namiji.......amma da alama yana da cika baki da yawa......kayi wani abu mana akai" Hakeem ya qarasa fada qasa qasa yana ranqwafa kanshi saitin haisam.
Haisam din baice komai ba illa karbar ruwan da yayi. Sam wasan ba shine a gabansa ba,ba wanda kuma zai fahimci hakan a cikin su,bayaso kuma su fahimta din,faduwa ko nasarar bashi yake hange ba,yadda a yau zasu fice daga Niamey,subi jirgin da zai sauka a agadez kai tsaye ne damuwarsa.
"Hakeem" Ya kira sunansa a nutse.
"I beg you" Hakeem ya fada da yaren turanci yana hadewa haisam hannuwansa guri guda.
Cikin wani irin nishadi ta sauke helmet din nata tana ajiyeta a gefe. Gashinta ta kama ta tattarashi da kyau tana daureshi,fuskarta washe da wata irin fara'a da take jinta har tsokar zuciyarta.
Dukka kunnenta suna sauraren bayanan Shehinaz dake kwatanta mata yadda take sarrafa thunder da wani irin qwarewa gami da miqa mata ruwa.
Sai data saki miskilin murmurshin da iya sakin da fuskarta kadai tayi shine kawai zai alamta maka murmurshi tayi.
Ita kanta basai an gaya mata ba.......wasan yayi mata ba zata,saboda yazo mata da wani irin sauqi da bata taba zata ba. Ta zaci abun zai zame mata me tsananin wahala walagigi dashi,sai gashi cikin sauqi tanata samun damarmakin wuceshi. Da farko sanda yake fitowa don hawa nashi dokin sanye da helmet data hana mata ganin fuskarsa ta tsorata,sosai gabanta ya fadi,wata irin baquwar faduwar gaba da bata san da ita ba.
Ba yau ta saba ganin maza giant ba,Giant ne kuma ingarman da tsaiwarsa kawai zata baka labarin jarumtar dake gangar jikinsa da zuciyarsa,batasan me yasa take jin wani irin kwarjini yana hudata ba,wani irin yanayi da ya sanya tun a farko ta dinga jin faduw warwas a gasar.
Faduwarta kuma daidai yake da kafawa kanta da kanta tarihin abun kunya......kamar ita zai zamana wani babban abun Allah wadai ace wani da batasan ko wayeshi ya cinyeta a wasan da wancan satin ta zamana cikin tafin hannunta.
Izzarta da qasaitarta tana tare da ita,tana kuma zagayawa a jininta,wannan ya sanya taqi maida hankalinta ko idanunta ta sake kallonsa koda sau daya ne kuwa. Sai a yanzun cikin maganganun Shehinaz ta samu amsar
"Ko sau daya bai kalleki ba bare har ya damu da yadda kike tsere masa.......wallahi wannan ko waye shu'umi ne......kuma bansan me yasa bai dauki hankalinsa ya dora akan race din ba" Kai ta jinjina,ranta kuma ya fara mata saqe saqe.
Ko yaya ne bata son taci nasara cikin sauqi......ko yaya ne tana son su gwabza......tana sha'awar su fafata ta finciki nasararta koda tsiya ne a hannunsa. Abu na biyu ta sanya masa qatotuwar ayar tambaya......anya ba wani shiri a qasa?. Bata da wani zabi illa ta san yadda zata tona koma meye a zuciyarsa a wannan zagayen qarshen.
Saidai kuma akwai wani abu daya da tayi noticing.......ta fahimci kamar akwai wani sirrintaccen sirri tattare dashi......sirrin da ya zuba masa wani irin kwarjini na musamman. Bata iya ganin komai nashi,koda kuwa hannuwansa ne dake lullube da safar hannu irin ta masu hawan dawakai......hakanan qafafunsa ballantana fuskarshi,amma tana jin wani abu me nauyi game dashi
"Matso kiji Shehinaz" Akhnan ta fada tana murmushi gami da yafito Shehinaz din.
★Cikin sarewa gami da son wasan yazo qarshe hakanan ya sake hawa dokin. Saidai tun wasan baiyi nisa ba waqen da kambamar qasar da al'ummar gurin suka fara yi ya soma ruda kwanyarsa.
Yana da wani irin kishin qasa da ya sanya sake zama na musamman a NISS......yana da kishin qasar da baya yarda ko ya aminta ka zagi ko kaci mutuncin qasarsa.......qasarsa nada muhimmanci a wajensa.
A hankali tutocin qasar niger suka fara dagawa a gurin,suka soma yiwa gurin rumfa saboda dukka wanda yake kallon wasan ya gama yiwa wasan alqalanci. Bata yadda za'ayi abokin buga wasan ya farke wannan wasan,sun gama miqa wuyan bai iya komai a wasan ba.......akhnan din ita ke da nasara......da gaske ita din kallabi ce tsakanin rawuna.
Wuceshi da tayi da waiwayowa da tayi ta masa wani sign da hannuwanta ya fusgi hankalinsa. Abubuwa guda biyu ne suka tabashi. Na farko sign din data masa alamun raini ne ga duk wanda ke buga wasan horse race........abu na biyu kuma har cikin jikinsa yaji hasashen da yakeyi tun dazun......yanayin da jikinsa yake bashi yaji yana sake tabbata. Tun dazu jikinsa yake bashi wannan din da suke wasan macace,ba namiji bace,yanayin sarrafa dokinta da yanayin sarrafawar mace yayi masa kama.
"Me yasa omari?" Yaji ranshi yana baci da abinda omari yayi masa. A hankali idanunsa suka sauka akan team dinsa.....maleek,mutallab,omari,amjad,khaleed,khadeem. Tutar Ethiopia suka ware me fadi sosai.....kowannensu kuma yana riqe da wani bangare nata,sun kuma dan bada tazara a tsakanin su,abinda ya bawa tutar damar bayyana sosai.
Idanunsa ya zare a hankali,qasaitaccen murmushin nan nasa yana kubce masa,take yadda ya dauki wasan a ransa ya canza cikin qasa da second biyar. Ko basu ce komai ba yasan me suke nufi.....yasan saqon da sukeson aika masa.
A wajensa ba wani wasa bane me muhimmanci ba,wasa ne na samun damar shiga agadez da niger gaba daya ba tare da kowa ya gane ba.......amma a yanzun a ranshi shima yana jin koda hakanne,bai kamata ya bari qasarsa tasha kayi ba,bai kamata qasarsa taji kunya ba. A yanzun su suke wakiltar Ethiopia gaba daya,duk da duka dukansu a filin irgen yatsun hannu ne......amma ya kamata su barwa al'ummar niger suna da tambarin ETHIOPIA.
Ta saki jiki sosai,ta kuma bada amanna tana sarrafa dokinta hankali kwance......saijin iskar wucewarsa tayi,kafin tayi kowanne yunquri kuma ya soma mata nisan daya sanya hankalinta tashi,ta kuma qarawa thunder qaimi.
Murmushi ya sake ajewa ta cikin helmet dinsa,yana iya jiyo sautin takun dokinta,koda bai waiwaya ba kuma yana iya qididdige adadin tazarar data rage da zata iya bata damar taddoshi,don haka sai yayi mata qofar rago kawai.
Tana daf da iskoshi ya sake bata badda mata tunani,ya cilla da wani irin salo daya dauki hankalin kowa,ya sanya filin yin shuru ba tare da kowa ya shirya ba,ya kuma sauya akalar magana da tunanin me sharhin dake can sama yana ganin yadda abubuwa suke so su canza a mintunan qarshe na wasan.
Wani irin wasa da hankali ya soma yi da ita,wani walagigi ya fara yi da nutsuwarta da dukkan qwarewarta. Cikin mintuna qalilan gaba days ya ruda tunanin ya kuma rudata. Tsalle kawai zuciyarta keyi cikin qirjinta,wani irin tsoro taji yana saukar mata. Tunda take bata taba ganin salo irin wannan ba,ya toshe duk wani tunanin ta inda zata cimmashi ma bare ta gotashi......ya toshe duk wata kafa da zata tsammaci nasararta a kusa.
Fargabarta ta sake qaruwa da ganin adadin qananun mintunan da suka rage wasan ya tashi gaba daya..... Tashin hankali ne taji yana lullubeta a hankali,RASHIN NASARA yana daya daga cikin tarin abubuwan data tsana.......ta tsani FADUWA ta kuma tsani A FITA. Ta rayu ne a saman nasara......ta rayu a tudun fifiko,ta bude idanunta ne ta tsinci rayuwarta saman ta wasu......ta tsinci rayuwarta a qulle data wasu.....ba zata taba lamunta ba ace wani can yazo ya kunyatata a tsakiyar 'yan qasarta ba......a gaban talakawansu ba........wannan ya bata qaimin data miqe saman dokin ta kuma bashi wani irin qaimi da ya gigita hankalin dokin ya fita daga tsari da kuma horon da aka bashi.
Yadda dokin yake misbehaving ya mugun tsoratata ya kuma daga mata hankali,ta sake riqeshi da dukka hannuwanta tana jin wani gumi yana tsarto mata,domin ta tabbatar a irin wannan yanayin ta sake ta fadi ba shakka sunanta gawa.
Wani irin abu me nauyi ne taji ya saunar mata sanda dokinsa ya tsallakar iyakar dake tabbatar da kasantuwar nasara a hannunsa. Sautinsu amjad a amsa kuwwar da baisan inda aka samota ba da taken qasarsu ya sake ruda tunaninta da wani irin kalar zallar tashin hankali.
Tayi zaton dokin zai dakata daga inda ya cimma wannan layin shima......amma aah sai ya zarce yaci gaba da shillawa da ita da wani irin gudun walqiya.....daidai da sunan data bashi.
Wannan karon zuciyarta tsinkewa tayi gaba daya da wani irin tsoro,take ta fara gwada dukkan wasu dabaru ja tsaida doki a irin wannan yanayin.
Dabararta ko daya batayi ba,firgici ya sake shigarta,tasan irin wannan yanayin idan doki ya shiga iya controlling dinsa sai Allah. Zuwa sannan hankulan mutane sun fara yowa kanta,musamman hadimanta da masu tsaronta wadanda suke da alhakin kula da lafiyarta.
Sosai hankula sukayo kanta,al'ummarmu da son daukan abubuwa idan suka faru,da son ace sune suka fara dauka ko suka fara haskawa tuni suka fara nadar yadda abun yake kasancewa.
Da wasu dawakan aka soma bin nata dokin da zummar shan gabansa,saidai hakan ya sake zama kamar wani qaimi suka bashi,don tunaninsa yana sake bashi anci gaba da wasanne......ana kuma son cimmasu,yanason cika umarnin uwar dakinsa ne kawai na tserewa duk wata halitta da zata wucesu,bama halittar doki dan uwansa kawai ba.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽