Author : Safiyya Abdullahi Huguma Category : New Hausa Novels 2026
nanay.......ashe kuma taji,kafin yakai ga zabar malamar da zata kasance malamarsu sai zuwa yayi wani hutun qarshen mako ya samu samee din ta fara gabatar da karatun.
Idan yace baiji dadi ba yayi qarya......idan yace girmanta da kimarta basu dadu a idanunsa ba yayi qarya,don haka sai ya bada kwangilar dukka hijaban da zasu sanya harda malamar tasu. Yaransu yasa an tashi makarantar islamiyya gagaruma cikin gidan,wadda ta zama kyauta kuma sadaqatul jariya ga kowa,har yaran dake wajen masarautar. Mazajen gidan kuma ya kawo malami namiji da zasu dinga nasu karatun juma'a da asabar........yawanci asabar din shi yake zama yake musu litattafai guda biyu na fiqhu da hadith saboda inganta ibadarsu bayan qur'anin,wannan ya sanya itama samee ta saka ma matan littafin qwaya daya na fiqhu.....bayan sun saukeshi kuma take sanya ran saka musu hadith koda me hadisai darinnan ne.
A cikin jikinta taji akwai wai baqon abu me kaifi a wajen........a cikin jikinta taji wata baquwar halitta ta wanzu a wajen,don haka tana kaiwa qarshen ayar suka kama suna maimaitawa,saita daga idonta a hankali take suka fada cikin nasa.
Wannan qaqqarfan maganadisun ne taji ya fusgeta da wani irin qarfi,wannan kwarjinin nasa daya sanya gumi tsatsatsafo mata ta cikin hijabinta......wannan kyan nasa daya zame mata tamkar wata jarrabawa ya ratsa idanunta,duk sai taji wani abu yana tsumata,musamman a yau data samu damar ganin Fuakarsa gaba dayanta ba tare da suturtaccen mayanin nan nasa ba.......a kuma safiyar da dakusashen hasken rana ya bayyana fuskarsa tarwai.
"Subhanallah" Ta furta qasan ranta sanda ya sake mata dan siririn murmushin da iya labbansa ne kawai suka motsa,yana alamta mata jinjinawarsa,sannan ya juya a nutse yana bin qofar da zata sadashi da nanay din.
Sai data rasa numfashinta na wasu daqiqu kafin ta samu kamoshi,inda ta godewa Allah ta gaya biya musu suna maimaitawa ne tana musu gyaran inda suke da kuskure. Can qasan ranta tana tuhumar kanta da kalar tuhumar da har yau bata daina yiwa kanta ita ba. Me yasa ta jarabtu da kyansa?,me yasa ta jarabtu dashi?,daidai ne ta sakarwa zuciyarta linzamin kyau ado da qawa kuwa?.
Ta sani yana da wasu qualities da ba ita kadai ba.......mata da yawa dake kewaye dashi sunsan yana dasu.......ya mallakesu ya kuma samu baiwa dasu......to amma a karan kanta me yasa kyansa yake zama barazana a gareta?.
Akwai wani ra'ayinta guda daya da take dashi,bataso ta cusawa haisam kanta.......bataso a mishi tayinta......bataso kuma ya sota saboda wani abu na daban,tanaso ya sota da kansa......tanaso ya sota don ta cancanci ya sota din.
Tana karantarsa sosai,duk da cewa yawa yawan zamansa ba a jimma bane.....a addis ababa ne,zuwansa sai weekend,amma duk da haka ta karanci abubuwa da yawa a kansa.
Har yanzu bataga alamun da takeso take kuma sanya ran ganinsu a tare dashi a kanta ba,saidai ta sanya a ranta zataci gaba ta dukka hanyar data dace.
A nutse ya sake jaddada sallamarsa a parlor din kaman yadda ya saba a duk wani guri da zai shiga.
"Wa'alaikumussalam" Matashiyar budurwar dake zaune saman doguwar sofa ta amsa tana daga kanta. Qaramin murmushi ya subuce mata,ta miqe daga zaunen da take tana duban haisam da yake shigowa da kyawawan idanuwanta da suke kama dana haisam din. Wanda banda su ba abinda ta dauko na kammaninsa,saidai ko tsaho da nata yafi bayyana saboda jikinta baikai nashi murjewa ba.
"Akkam bulte(barka da safiya)" Ta fada murmushin nan yaqi barin fuskarta
"Akkam jirta rumaisa(kina lafiya rumaisa?"
"Alhamdulillah captain sheik" Rumaisa ta fadi tana murmushin daya sanya haisam yasan lallai akwai wani abu a qasa,musamman data kirashi da wadannan sunayen a jere haka guda biyu.
"Ehheeenn" Ya fada yana dage dukka girarsa biyun sama,abinda ya qara masa kwarjini kenan har a idanun rumaisa. Kai ta girgiza tana rage kaifin murmushin ta. Ganin data sama a ya zun da yadda Moroccan abayar jikinsa ta dace da zubi da tsarinsa,sai maganar daya daga cikin qawayenta me suna anniisa ya fado mata. Kusan sallar isha'i ta daren ranar da akayi irreecha festival yabar baya da qura......don qira'arsa ta tayar da sirrin boyayyun zukatan dake cike da boyayyar soyayyarsa cikin qawayenta. Ganin kamar bata shirya gaya masa ba sai ya kauda zancen yana tambayarta
"Nanay eessa jira?(ina nanay?)" Da hannu ta nuna masa bangaren dakunanta na musamman da banda iyalinta ba wanda yake da hurumin tsallakewa har nan.
"Tana ciki bata jima da shiga ba" Baice komai ba ya fara takawa,sai muryar rumaisa ta dakatar dashi.
"Obbo captain(sir captain)". Sunan da sukafi kiransa dashi. Dakatawa yayi daga tafiyar da yakeyi wadda rumaisa ka qarewa kallo tana kuma sake gasgata zancan anniisa
"Yana da wani irin taku na daban.......qasaitarsa tafi taku.....kuda kuke mata amma shine yake da jan ajin da izzar". Hararta kawai tayi a sannan,don itakam obbo haisam ba zata iya cewa ga wani sanda ta tsaya qarewa takunsa kallo ba.
Eh har gwara maganansa,ita kanta wasu lokutan idan yana magana burgeta yanayin tsarin maganarsa takeyi cike da ginshira......amma tafiya kam a yau itama ta shaida hakan.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 23
____________________________
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mutanen Zuzeam ventures
Ga wani sabon promo na bullo muku dashi don farin cikinku dajin dadinku
Kunsan promo na na dabanne namu ba irin nasu bane hajiya ta mai kike jira da 7500 dinki ki kwashi kayan 19k
1. Rabin kazar mallaka 4500
2. married femfresh wash 2k
3. garuka 7in1 masu wata 7 ajiki 2k
4. Gumbarmadaradanonon rakumi 1500
5. Tsimin mallaka 2500
6. maganin infection 1500
7. matsin mallaka ba aba mai kishiya 5k
Duka kayan 19k za a baki akan 7500
Kuma mutun 20 na farko sunada kyautar kayan 4k
Matsin maida tsohuwa yarinya 1k
Gumbar emergency 1k
Turaren mallaka 2k
Allah yaba mai rabo sa a Zuzeam ventures takuce 🥰👍🏼
Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi https://wa.link/l1gcz8 gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye ta WhatsApp 08144015291 muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
😁😁😁 https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
_____________________________
*_Addis ababa bole international airport(ADD)_*
Tafiyar awa daya da mintina biyar ta kaisu babban birnin na Ethiopia wato addis ababa,wanda cikin qasa da minti talatin ya kammala komai suka baro airport din qarqashin kulawar security din dake bashi tsaro cikin addis ababa din.
Kazanchis layout suka nufa......unguwar da ya mallakin gidan zama na kasan kenan bayan gidan da hukumar binciken sirri suka bashi. Unguwa ce data hada manyan mutane da qusoshin gwamnati. Baqi 'yan qasashen waje da kuma manyan ma'aikatu na alaqa tsakanin qasashe da kuma hukomomi manya na tsaro.
Gida ne dake da wani irin tsari da zai baka sha'awa qwarai,qaramar villa ce da batayi wani girma na azo a gani ba......amma tana da girman da za'a iya sanya matan aure hudu a ciki suyi rayuwa cikin walwala da sakewa.
Ganawa da ma'aikatan gidan shine abu na farko da yakanyi a duk sanda ya dawo.......yau dinma hakan yayi,saidai batayi tsaho ba,kasancewar yana sanya ran daga yanzu zuwa kowanne lokaci zai iya fita zuwa headquarter dinsu dake cikin kazanchis din.
*_AGADEZ_*
*NIAMY*
Tsaf ta kammala shirinta cikin wani kebantaccen guri na nusamman da aka bawa 'yan wasan dake filin gudanar da wasan don shiryawa gabanin fitowarsu. Wata irin shiga data sake fidda ainihin kyanta,wanda hatta da aisa da Shehnaz zama sukayi suna kallonta.
Farin skinny trouser daya fidda shape na qugunta da sosai......wata irin jacket data dora samansa me dogon hannu bayan riga 'yar ciki data saka. Ta daure wannan dogon gashin nata cif a tsakiyar kanta,saita sake jelar tana lilo. Takalmin qafarta wani tsadadden boot ne da tayi cinikinsa da Europe ba dolla ba takanas ta saka aka kawo mata shi. Komai na jikinta fari ne qal,kamar yadda kalar thunder (dokinta) ya kasance fari tas.......me wani irin cikar zati da ban sha'awa ga duk mutumin daya kalleshi. Koda bakasan doki ba.......bakasan kuma darajarsa ba idan ka kalli thunder sai ya baka sha'awa qwarai. Qosashe kuma ingarman dokin data sayeshi daga United arab Emirates wato dubai da kudade masu nauyin gaske. Kulawa ta musamman take bawa dukkan dawakanta da kuma me duba lafiyarsu na daban data ajiye a Niamey da agadez. Akwai me musu regular check up da vaccination don tabbatar da lafiyarsu,hakanan abinsu na dabanne bayan abincin ana ciyar dasu fresh fruits da vegetables irinsu apple da carrots da sauran kayan marmari. Hatta da SULTANE yana sha'awar dokunanta......wani irin qauna ce tsakaninta dasu. A shekarun baya kafin ta zama busy akan kamfaninta har haka akwai ranaku na musamman da take warewa kawai don hawa ko zaman kallonsu ko lura da lafiyarsu.
"Amma dai.......ki rufa mana asiri kada kallon tseren doki ya koma kallon biftu....." Wani murmushi ta saki sanda take dauko wasu safar hannu guda biyu. Sai data fara zurawa sannan fa daga kyawawan idanunta da kwallin data zizara musu a yay ya qara musu kyau.
"Jikar muhammad agg nake......diyar muhammad hammud......akhnan.....biftu......don kawai na na shiga gasar tseren doki sai kuma jikina ya zama me abun banza ga kowanne kare da doki?......arahata batakai har haka ba" Ta qarasa fada tana zama saman wata ottoman sofa tana daidaita riding globes dinta cikin hannunta.
Murmushi aisa ta saki,akwai abu guda dake burgeta game da akhnan din......tana martaba jikinta.......tana tsananin kula da qaunar jikinta,tana bashi kima da daraja,amma kuma wani abun na daban.....wannan izzar ta akhnan tana burgeta......wannan izzar ta akhnan tana saka mata shakku.......anya kuwa ba da gaske bane kuwa?,anya a yadda izzarta da alfaharin kanta yake zata iya auren wani d'a namiji bare wataran ya ganta gayarta?,bare wataran su hada gado kamar yadda tasha fada?......anya kuwa akwai wanda zai samu nasarar sauke wannan izzar?,anya kuwa akwai wani qarfi na wata aba soyayya da zai sauke wannan ALFAHARIN?.....ya cillata duniyar matsananciyar soyayya da shauqi?. Da wanann tunanin da yabar murmushi saman fuskarta ya kaita nisan da har akhnan din ta gama qarasawa shiryawa hankalinta bai kai ba.
"Ma sha Allah" Aisa ta furta can qasan ranta tana duban akhnan din. Wannan skinny trouser din daya bayyana shape dinta......ta batar da wannan surar tata ta hanyar dora wata irin riga me kama da alkyabba maras nauyi sam sam,sosai ta baje daga bayanta ta kuma rage fitar da shape dinta yayi kwata kwata,rigar tana hade da hula ne wadda zata aza saman Egyptian turban cap din kanta me azabar kyau da aka qawata da adon gold stones. Daga gaban rigar me kaman alkyabba akwai wata 'yar lanqwasa da aka yiwa ado da wani tattausan gashi tun daga fuskar hular dake saman kanta,ya sauko saman qirjinta ya rufe tudunsu daga sama,duk da hakan bai boye shape dinta ba....sannan ta dauki helmet dinta ta riqe a hannunta.
(08187255862 lu'u lu'u paying)
Fadin irin kyan da tayi bata baki ne.......abu daya aisa ta sake tabbatarwa shine,da gaske akhnan din ta dabance......da gaske kuma tasha banbam da mata masu yawan gaske.
Wani irin cika gurin yayi wanda bai taba yin irinsa ba,su kansu masu saida ticket na shiga gurin.....jami'an tsaro da kuma masu kula da kai kawon jama'a a gurin yawan ya rikitasu. Mafi yawan mutanen da sukazo kallon wasan sunzo ne don PRINCESSES AKHNAN MUHAMMAD HAMMUD.......don fiye da rabinsu basu santa ba sani na ido da ido. Sunanta ba boyayye bane cikin nijer dama agazed gaba daya......amma sanin anihin fuskarta abune da ba kowa ne zaice maka ga kamanninta ba.
Kusan ita daya ta rage bata iso gurin ba cikin jerin 'yan wasan dake wajen......farin dokin qwaya daya dake tsaye ba maishi a kansa shima ya zama abu na daban daya tsonewa 'yan kallo ido. Ko cikin abokan wasan nata babu wanda dokin bai burgeba,duk da gabadayansu suna saman wasu irin qosassun dawakai da suka sha bamban da wadanda aka saba gani.
*ADDIS ABABA*
_national intelligence and security service(NISS)_
*_Washegari_*
Wani irin sabo da horo ya yiwa ruhinsa,tun daga sanda ilimi da hankali ya gama wadatarsa kawo yanzu. Duk daren duniya......duk inda qarfe uku na dare yayi muddin akwai cikakkiyar lafiya a tare dashi to yabar makwancinsa izuwa saman abun sallarsa.......a kowanne dare a kowanne guri,hakanan a kowanne yanayi. Daga sanda ya karanta ya kuma fahimci ma'anar ayar nan ta cikin suratus sajdah aya ta sha bakwai da Allah madaukakin sarki yake cewa
(Jukkunansu na nisanta da makwancinsu suna kiran ubangijinsu suna masu tsoron azabarsa.....suna kuma masu kwadayin rahamarsa......sannan suna ciyarwa daga abinda muka azurtasu). Tun daga wancan ranar zai wahala wani dare ya kubce masa ba tare da ya rayashi ba. Abinda yayi masa tasiri sosai cikin rayuwarsa......ba wata buqata da zai dorata saman abun sallar cikin irin wadannan dararen ba tare da yaga cikarta ba. Wani irin haske ne ke mamaye ruhi dama rayuwarsa gaba daya. Da gaske sallar dare na daga darajar bawa,ta sanya wani haske na musamman a ruhi zuciya dama fuskar me yinta,ga kuma tarin nishadi da walwala da zaka wayi gari cikinsa.
Kiran sallar farko da wasu mintuna yabar saman abun sallar,ya koma bandaki ya sake sabunta alwalarsa don samun qarin haske akan haske(alwala haske ce......kuma itace ranar qiyama zata dinga zame mana tamkar fitila,itace kuma zata rarrabe tsakaninmu da kafirai,so yana da kyau ki zama me yawaita yin alwala ko zama da ita.....tana bada kariya daga dukkan sharrin me sharri).
A nutse yasa dan qaramin lallausan towel dinsa dake fidda wani sirrintaccen qamshi daya samo asali daga turarukansa da yake amfani dasu ya goge lemar jikinsa,sannan yabi jikin nasa da wani sassanyan turarensa da mafi akasari shi yaf amfani dashi idan zai fita sallar asuba.
(Turare kansa sunnah ce....sunnah me qarfi,cikin abinda aka sanyawa manzon Allah S A W sonsu akwai turare).
Qarshen layinsu masallacin yake,kuma kusan shike jagorantar sallar asuba din a yawancin lokuta,duk da wasu lokutan yanayin aiki ma baya barinsa kwana a gidan bare ga samu yayi musu limanci.
Cikin mintuna qalilan daddadar muryar nan tasa dake dauke da amon sautin karatu mafi daraja ya karade area din tasu,ya sake sanya nutsuwa sosai cikin zukatan duk wata halitta daka iya jiyo sautin nasa.
Sanda ya kammala jagorantar sallar yaso ya zauna a gurin kaman yadda yakeyi wasu lokutan ya jira fitowar hantsi sannan yayi salatudduha(wata garabasa ce me girma ayin haka,gwaggwaban lada ne ga bawa me yawan gaske,ladan hajji da umra cikakkiyar lada cikakkiyar lada cikakkiyar lada haka annabi S A W ya maimaita har sau uku,idan bakije hajji ko umra ba.....ga dama ta samu a sauqaqe na samun ladaddakinsu daga gida)".
Dole ya koma gida,don yana buqatar fita da wuri.....akwai abubuwan da yakeson dubawa kuma kafin ya isa headquarter dinsu.
A nutse yake takawa zuwa gidan.......qasa qasa yana motsa harshensa cikin tasbihi ga ubangijin halitta. Sassanyar iskar asubar dake busawa tana sake dauke duk wani nauyi dake qirjinsa,tana saukar da wani nutsuwa da nishadi sosai a ransa.
"Tsarki ya tabbata ga ubangiji" Ya fada qasan ransa,yana tuna yadda a alqur'ani ubangiji ke cewa a aya ta sha takwas cikin suratut takwiir
"Da asuba idan tayi numfashi(ma'anar wannan sassanyar iskar me dadi dake kadawa tsakanin sallar asuba,ki gwada shaqarta,tana saukarwa da zuciya nishadi sosai)".
"Ya akayi masu tsaronmu sukayi ganganci bar mana zakin qasarmu haka sasakai yana takawa zuwa gida haka gayansa?" Ya tsinci dattijuwar muryar daga bayansa.
Tun bai juya ba qaramin murmushin nan nasa dake alamta nutsuwar dake jikinsa ya subuce masa. Koda bai juya ba yasan ba kowa bane sai alhaji muntassir amari.
Dattijon da gidansa ke maqotaka da nasa ko nace yake kallon nasa. Dan