L U'U L U'U BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY HUGUMA.txt

Author :  Safiyya Abdullahi Huguma Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   16 / 21

45K to 48K   out of 62.7K words

zatayi yarinyar......har yanzu taqi fitowa sai dokinta data gabatar,duk ya kashe idon kowa a wajen" Ya sake ji barrak ya fadi.

"Yadda dokinnan yayi kyau na tabbatar kyakkyawa ce itama.......na qagu na ganta wallahi" Semere ya fadi. Samere din irin mazannan ne mash idanun kalle kalle da shegen son mata,wannan dabi'ar nashi ya sanya sam kanwarsa da suhaim basa jiquwa guri daya.

Mugun shakkar suhaim din yake saboda kwarjinin da yake masa,yayin da suhaim din ba kasafai ya fiya shiga shirginsa ba.

"Kamar gata nan.......gata can daga right side tana fitowa". Muryar data bashi mamaki,muryar omari ce......ko mene ya kawo omari cikinsu?. Yasan halinsa sarai ba irin shirginnan shima yake shiga ba.......amma tunda yaji anyi batun doki akwai alaqa me qarfi tsakaninsa da wasan dukka daya shafi doki,ba kuma omari din kawai ba......dukkan 'yan team dinsu ma. Wani abune da suka wareshi ya zame musu abu na nishadi a rayuwarsu cikin wasannin nishadi na halal. Wasan tseren doki,don kuwa halastaccen wasa ne tun zamanin ma'aki,don haka suka maidashi shima wasansu da sukanyi duk qarshen wata ko sati.

Kowannensu gwani ne kuma qwararre,saidai a tarihin tafitar kaf haisam ne kawai ba'a taba cinyeshi ko fiddashi ba.

Sau tari sukan zolayeshi da cewa.

"Masu abu da abinsu ne.......kukam tun kuna jarirai aka tabbatar ana koyawa yaro komai daya shafi sarauta a masarautar jimma" Murmushin nan nasa dake cakude da wata charisma yake saki kawai. Duk wani abu da zai nuna martaba da girmansa ko ya tuna masa shi din wai wani ne daban da yasha banbam da sauran mutane bai fiya so ba,yafiso kullum su barshi ya dinga jin kansa kamar kowanne mutum......su daina tuna masa shi din dan sarauta ne.

"Itace......wallahi itace" Daidai sanda semere yake fadin haka yana kasa daidaita zamansa saman kujerar da yake kai suhaim ya murza handle ya bude qofar yana shiga da sallama a bakinsa cikin husky voice dinnan nasa daya qara wani zurfi da fidda nutsuwarsa. Idanunsa na akan inda zai lalubo Omari,ya tuhumeshi da idanunsa akan dalilinsa na zuwa ya zauna a shirmen gurinnan bayan aikin dake gabansu?,cikin sa'a sai ya samu Omari din yana can gefe yana hada wata folder,abinda ya alamta masa akwai aikin daya shigo dashi office din kenan kamar yadda shima dalili ne ya shigo dashi.

Hadiye maganarsa yayi,cikin ransa yana furta.

"Subhanallah" Tare da sake imani da yaqini ga Allah. Tabbas shi yasa ubangiji ya jaddada muhimmancin yin bincike akan komai.

Shigowar tasa ya sanya kowa a cikinsu miqewa cikin girmamawa suna kai masa gaisuwa tare da shan jinin jikinsu. Somawa motsawa kowa yayi don barin office din,don doka ne hakan a garesu,sai idan shi ya basu izinin ci gaba da zama.

Ya fahimci wannan sak din da sukayi a yanayinsu,sai kawai ya basar yana amsa gaisuwar tasu,ya kuma doshi fannin da printers dinsu ke ajiye zai soma operating,salana ya dan matso.

"Sir.......me kake buqata?"

"Kebantaccen aiki ne" Ya fada a nutse yana daga masa hannu. Ya Fahimci yaren don haka ya koma mazauninsa,ya kuma dauki remote cikin dabara ya rage sautin tv din.

Ba kasafai a guri irin wannan kowa ke nuna zurfin alaqa tsakaninsa da wani ba saboda dalilai na tsaro,kamar hakan ce tsakaninsa da omari. Girma yake bashi kaman kowa,duk da ana ganinsu sau tari da omari din fiye da kowa a cikin ma'aikatar,don haka bayan gaisuwa basuce da juna komai ba.

A tsaye yake kyam yana aikinsa,dukka hankalinsa yana kan aikin ganin kowanne page ya fita daidai. A sannan dukka hankalinsu yana kan zazzafan wasan da ake kaftawa cikin birnin Niamey dake qasar agadez,wanda gidan TV na wasanni ta qasar yake daukoshi live tana watsashi a sassan duniya gaba daya.

"Ya salam" Semere ya fadi yana rasa inda zai saka kanshi.

"Kai subhanallahi"

"An tashi kaina!"

"Da gaske sarauniyar ce......ko a gudunta ma akwai izza da mulki a ciki" Wadannan dama ire iren maganganun nan su suke tashi cikin dakin cikin sauti na can qasa saboda wanzuwar haisam din a ciki. Suna zaton baya jinsu ko bazai jisu ba,saidai wani mugun kaifin ji Allah yayi masa tamkar dan maciji. Yana ji amma yayi kamar baiji ba.......yana gani sau tari amma yayi kamar bai gani ba......saboda qoqarin koyi da fadin ma'aiki YANA DAGA CIKIN KYAWUN MUSULUNCIN MUTUM.........YABAR ABUNDA BABU RUWANSA. Musamman idan abunnan bai shafi hani ko umarni ba akan wani abu daya zaman sabawa mahalicci ne.

Ya soma gajiya da jin soki burutsunsu da maganganunsu,don haka yaja kujera ya zauna yana sauke boyayyen numfashi. Zuciyarsa yaketa kaiwa nesa,baya so yace musu komai,don ba a kowanne muhalli da kowanne guri yake magana ba,kowacce magana tana da tata gurbin da muhallin a wajensa.

"Na jima banga wasan dokin da ya burgeni irin wannan ba" Omari daya bar abinda yake ya dawo cikinsu yaja kujera ya zauna ya fadi. Duk yadda yaso wasan kada yaja hankalinsa ya gagara yin hakan,wani irin wasa ne daya dauki hankula da idanun duniya. Zazzafan wasan da aka dauki dogon lokaci ba'a ga irinsa ba,saboda wanzuwar kallabi tsakanin rawunan dake cikin wasan wato AKHANAN MUHAMMAD HAMMUD sarauniyar yankin agadez.


Futar "innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Da kuma

"Subhanallah" Daga bakin omari kusan lokaci daya shine abinda ya fusgi hankalin haisam da hannuwansa ke saman shafukan takardar daya fitar ba tare da ya shirya ba. Kalmomi ne masu girma da nauyi a zuciyar kowanne musulmi,ya juya a hankali yana aza idanunsa kan allon television din,karon farko kenan da yayi hakan tun shigowarsa office din.

Faffada kuma yalwataccen filin wasan dokunan ya fara yi masa maraba. Tarin ingarman dawakan da suka dauki idanunsa daketa qoqarin tserewa junansu suda mahayansu......suke kuma yunqurin kamo wani qosashen farin doki qal daya kusa isa iyakar da zata tabbatar da nasararsa.

Ba'a zaune take saman dokin ba,ta miqe ne gami da duqawa kaman me shirin ruku'un riqe da linzamin dokin da wani irin zafi da yanayin dake nuna a yunwace take da isa ga nasararta don tserewa mafarautan mazan dake bayanta. Qarfin iskar dake ketasu ce ke dage alkyabbar dake jikinta,wannan ya bawa shape dinta dama skinny jeans din jikinta daya lafe a jikinta damar bayyana ta gefe da gefe.

Da sauri ya dauke idanunsa yayi qasa dasu yana furta

"Astagfirullah......astagfirullah" Wani bacin rai ya sauko masa,sai ya miqa hannu a zafafe ya kashe printer din ya kuma kwashe takardunsa yaja wani qaqqarfan tsakin da yaja hankalinsu. Dukkaninsu suka bishi da kallo yadda yake fita a office din a zafafe,kafin ihun da semere ya saki duka ta maida hankalinsu ga tv din.

Baiyi nisa da wajen ba sautin muryoyinsu ya biyoshi har inda yake takawa don ficewa daga block din. Ihun daya tabbatar masa suna taya gwanar tasu murnar samun nasara daga dukkan alamu.

Shi kadai yasake sauke ajiyar zuciya. Sam baiga alfanu ko dalilin da zai sanya mace irin wannan wasan ba. Idan har ta fito ne daga gidan sarautar da suke girmama addini da al'ada.......hawa dokin mace me haramun bane,ba kuma abu bane me muni,saidai yana da qa'idojin daya kamata a kula dasu. Qaramin tsaki yaja a ransa yana kuma ture maganar daga ransa. A yanzun akwai abubuwa masu yawa da suka fi wannan shirmen muhimmanci da suke a gabansa,sai ya miqa hannu ya dauki wayarsa wadda ya samu miscal din nanay har guda hudu.

"Subhanallah" Ya fada yana komawa a hankali saman kujerar ya zauna yana qoqarin maida kiran. Tun safe yaso ya kirata kamar yadda ya saba......amma tashi da yayi da ayyukan yau a ransa yasa bai samu chance ba.

*DAIDAI WANNAN LOKACIN*


*_AGADEZ SULTANE MUHAMMAD HAMMUD PALACE_*


"Lokaci tamkar takobi yake,idan kai baka yankeshi ba shi zai yankeka......kamar yadda lokaci baya jira........bai kamata muma mu jirashi ba........dogon jira wani lokacin kuskure ne......ganganci ne.......kuma wasa da dama ne........a wannan zamanin......a wannan qarnin TAMIM inajin cewa nakai iyaka......haquri na kuma yazo gaba.......kwadayina da buqatata akan taskokinnan sunzo iyakar da bazan iya juresu ba" Ta fada tana sake sarqe hannayensh da goyesu guri daya a bayanta,tana kuma takawa d'ai d'ai gami da zurfafa idanunta cikin na tamim dake zube qasa a gabanta.

Murmushin dake can binne cikin qasan zuciyarsa ya saki,saidai ko fuskarsa bata bayyana hakan ba.

"Akwai sauran lokaci.......gaggauta gabatar da komai zai iya tarwatsa komai din......"

"Tamim!" Mammina ta kirashi a tsawace tana sauke hannayenta daga goyasun da tayi.

"Kalleni da kyau!" Ta sake fada a kausashe tana fidda dukka idanunta waje kamar wadda ke buqatar ganin wani abu tarwai wanda bata samun damar ganinsa da kyau.

Jajayen idanunsa dake da girman gaske ya daga yana zubesu a kanta kamar yadda ta buqata.

"Kasan shekaruna nawa a duniya?" Ta sake fada nata idanun cikin nasa itama. Shuru na sakanni yayi,sannan ya girgiza kansa.

"Shekara uku kacal na bawa sultane a duniya......shekara uku kacal......shin kwana nawa suka ragemin ne a duniyar........idan wadannan taskokin.......wannan mafarkan........wannan rayuwar idan basu iso hannuna ba sai yaushe?......zasuci gaba da zama a can?......zasuci gaba da zama a hannunsu suci gaba da narkewa?......wannan tabbaci kake dashi akan MOOTI?" Ta fada da zafinta sosai tana nuna hanya kamar a nan din komai zai bayyana a gareta yadda takeso.

Wani gardin numfashi tamim ya fitar,sannan ya koma ya zauna sasai saman kilishin yana kuma sakewa.......tamkar ba shine wannan tamim din dake d'ari d'ari ba da iyakance muhallan da zai zauna ba. Yatsunsa biyu ya daga yana kallonsu kafin ya maida dubansa gareta.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*

PAGE 26
____________________________
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mutanen Zuzeam ventures
Ga wani sabon promo na bullo muku dashi don farin cikinku dajin dadinku
Kunsan promo na na dabanne namu ba irin nasu bane hajiya ta mai kike jira da 7500 dinki ki kwashi kayan 19k
1. Rabin kazar mallaka 4500
2. ⁠married femfresh wash 2k
3. ⁠garuka 7in1 masu wata 7 ajiki 2k
4. ⁠Gumbarmadaradanonon rakumi 1500
5. ⁠Tsimin mallaka 2500
6. ⁠maganin infection 1500
7. ⁠matsin mallaka ba aba mai kishiya 5k
Duka kayan 19k za a baki akan 7500
Kuma mutun 20 na farko sunada kyautar kayan 4k
Matsin maida tsohuwa yarinya 1k
Gumbar emergency 1k
Turaren mallaka 2k
Allah yaba mai rabo sa a Zuzeam ventures takuce 🥰👍🏼
Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi https://wa.link/l1gcz8 gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye ta WhatsApp 08144015291 muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
😁😁😁 https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
____________________________



"Iya wannan tazarar dake tsakanin yatsuna guda biyu......iya wannan tazarar ce kadai ta rage mana da shigarmu qasar......cikin wannan yankin kowanne dare mafarkina yake tuqewa......cikin wannan burin kullum tunanina yake saraya......tunanina yake narkewa......idan nace......"

"Allah ya taimakeki!" Sautin muryar tafisu daga bayan hijabi ta ratsa zaren kowanne magana dake tsakaninta da tamim.

A fusace ta waiwaya,saidai hankalinta a kwance yake. Hijabin data sanya daga kowanne idanu da zai iya ganin wanzuwarta a wajen ita da tamim......kamar yadda tafisun bata isa ta qara koda taku guda daga inda take tsayen ba. Uwa uba tafisun amintacciyarta ce.....kalar amintacciyar da ba irinta kaf cikin hadimanta,saidai kuma kowanne mutum tana tsaidashi a matsayinsa......a gurbinsa......a kuma matakinsa.

Sai data numfasa na tsahon wasu mintuna sannan ta daidaita muryarta da kanta.

"Ya akayi?".

" Maude ne yazo da wani saqo,yakeso ya gabatar miki dashi" Yalwa ta fada girmame.

Maude din yana daga cikin mutanenta na amana......kamar yadda ta tabbatar tunda tafisu ta tsallako har nan nemanta ba shakka abune me muhimmanci ya taso. Bata amsawa tafisu ba,tadai juya ta yiwa tamim kallon da yake gaya masa ta jirata,ta juya da takun mulkinta tana nufar qofar fita.

Idanu ta zubewa maude bayan ta zauna,baice komai ba ya matso yana miqa mata wayarsa. Tafisu ce ta matso tana karbar wayar daga hannunsa sannan ta qarasa da ita fuskar mammina.

Kallon mintina goma ta yiwa wayar......tana dab da cewa tafisu ta janye wayar sunan akhnan ya bayyana a jikin dokinta sanda take zabga gudu kamar bata tsoro ko hasashen abinda zai iya faruwa da ita idan ta fadi

"Me nake gani wannan?" Mammina din ta furta tana janye dubanta daga fuskar wayar,tana kuma hade girarta sosai tana son dora yanayin saman fuskarta yadda zai dace da fuskartata. Can qasan ranta kuma wani abu yana motsawa,wasu tarin abubuwa suka fara motsawa sannu a hankali.

Qasa maude yayi da kansa cikin tsananin ladabi.

"Ki gafarceni.....kiyimin afuwa........gimbiya akhnan ce,cikin gasar tseren dokuna ta yankin Niamey"

"Gasar tseren dokuna?" Ta fada cikin mamaki tana duban maude. Sake qasa yayi da kansa.

"Tabbas.....kiymin afuwa Allah ya baki yawan rai........na durfafeki da maganar ne saboda na tabbatar abune dake ba zakiso ba.......banason kuma ace me martaba yaji wannan maganar......na tabbatar zaki tsawatar zaki kuma yiwa tufkar hanci don lamari ne da bai dace da al'adunmu ba" Shuru kawai tayi tana juya maganar cikin ranta. Ma'aunai guda biyu ta aza maganar maude......ma'aunai masu nauyi da kuma zurfi tanason gane a wanne ma'auni ya kamata ta dora maganar.

Shuru ne yaci gaba da wanzuwa cikin parlor din. Tsahon wasu daqiqu,a hankali ta sauke wani boyayyen numfashi daya fito da wani sirrintaccen murmushi daga fuskarta. Duk da ba'a yanyin murmushin take ba......hasalima ba lokaci bane daya dace da fitar hakan saman fuskarta ba.....amma gilmawa da haskawar wani tunani cikin kanta ya sanya dole murmushin ya qwace mata. Yatsunta ta murza guda biyu wanda suka bawa maude hasken abinda take nufi,don haka ya sake rusunaw yana fadin.

"Na barki lafiya". Har yakai bakin qofa ta kira sunansa cikin izza.

"Maude"

"Allah shi baki yawan rai".

"Bana buqatar komai.....bana buqatar kowanne motsi......idan da wani buqata zan magantu".

"Yadda kikeso haka za'aci gaba dayi.......ba'a gidan bama.....a qasar agadez gaba daya" Ya furta da wani salo daya sake sanyata jin qarfin nata girman yana sake ninkuwa.

"Kiramin biftu ki bani ita" Ta sake cewa da yalwa ba tare data kalli yalwar ba. A ladabce ta miqe ta taka da hanzari ta fita. Ba jimawa ta dawo da wayar ta budeta ta kuma kira layin akhnan din kai tsaye.

Su uku ne kacal cikin motar banda motoci biyu a gaba da bayanta suke musu rakiya daga filin wasan zuwa gida. Wani irin nishadi takeji a zuciyarta,kalar nishadin data jima bata samu irinsa ba. Sosai takejin walwala,tana jin wani alfahari da kanta yana saukar mata.

Babban abinda yake qara ninka farincikinta........maza guda goma sha daya data yiwa zarra ta kuma zubdasu a filin........ta zame musu kallabi tsakanin rawuna. A cikin qwayar idanunsu taga zafin hakan,a cikin motsinsu ta hangi daci da bacin ran da sukaji game da hakan......hakan takeso........shine buri da muradinta.

Ta bata ran kowanne namiji da yakejin yakai.......tabar masa tabo da ciwo me taba zuciya a matsayinta na diya mace.

Dukkansu qwararrun 'yan wasa ne da akeji dasu cikin Niamey,tasha kallon wasansu,kusan kowanne a cikinsu tana da record dinsa....mayun wasa ne da ake matuqar ji dasua Niamey din da kewayenta.......sai gashi a yau bugun farko dukka ta zubdasu.

Daga nan inda take tana iya jiyo yadda ake kiran sunanta ta amsa kuwa. Lambobin yabo da na girmamawa......shaidar lashe gasar dukkaninsu ta watsar bata tsaya saurara ba bare ta karba ta taho abinta.

(08187255862 for lu'u lu'u payment)

Tasan akwai tarin daruruwan mutanen da suke son daukar hoto tare da ita. A wajenta wannan din duka shirmene,bata shirya bawa kowa dama yazo kusa da ita ba,uwa uba ita ba wani lambar yabo

16 / 21