Author : Safiyya Abdullahi Huguma Category : New Hausa Novels 2026
Kaman yadda musulunci ya tanada haka ya miqa musu hannu sukayi musabaha cikin nutsuwa,wanda mahaifinsa sarki abba jifar ya zamana na qarshe da suka gaisa din. Murmushi ke sauka a fuskar moorti abba jifar.....murmushin farinciki,murmushin nasarar da Allah ya bashi na mallakar haisam a mazaunin d'iyan cikinshi,d'iyan nasa da baisan adadin mutanen dake buri da fatan inama ace su suka samu d'a irin nashi.
Kyawawan kewayayyun idanunsa dake da wasu irin zara zaran eye lashes da kuma kwantacciyar girarsa data kusa hadewa da juna da tudun karan hancinsa da shatinsa ya bayyana kawai kake iya gani saboda wani salon nadin rawani da ya yiwa kansa ya lullube har hancinsa,amma hakan bazai hanaka fahimtar martanin murmushin daya maidawa mahaifinsa ba.
Gaisuwar tasu tazo qarshe saboda motsawar dogarawansa,abinda ya sanyashi miqewa don shima ya shiga tawagar ayarin rakiyar mahaifinsa ba tare da damuwa da tashi tawagar dake jiransa ba.
Yana daga gefan mahaifinnasa sanda suke takawa tare cikin zagayewar hadimansa. Cikin nutsuwarsa da dattijankarsa da ilimin addini ya yiwa ado yake takawa yana riqe da kaykkyawar baqar sandarsa me sulbi.
Bai dakata ba har sai da suka qarasa bakin qaramar motar da yakan koma gida a cikinta a duk qarshen biki irin wannan. Motace qarama me wani irin launi da sarakunan qasar England sukafi amfani da irinta tun tale tale.
Sai daya tabbatar da zamansa a motar,ya matsa da kansa ya gyara masa alkyabbar data kasance wani tambari na musamman na sarautarsu ya maida qaramar murfin ya rufe sannan ya rusuna cikin girmama da muryar da shi kadai zai iya ji yace
"Keessummaa sana nan tuffadha(zan sallami baqi)" Kai mooti abba ya gyada cikin salo na sarauta,ya daga hannunsa ga haisam sannan motocin suka fara motsawa suna ficewa daga fargajiyar masallacin,wanda tazara kadance tsakaninsa da ainihin fadar mooti abba jifar din.
Idanunshi akan motocin kamar meson tabbatar da lafiyar mahaifinnasa,sannan a nutse ya sanya yatsarsa yana jan rawanin dake fuskarsa daidai karan hancinsa yana sake rufeshi.
"Fuula kee dhoksuu filatta(me yasa kafi zabar rufe fuskarka?)" Yaji an fadi daga bayansa,abinda ya sanyashi waiwayawa a nutse duk da ya fahimci muryar waye.
Boyayyen murmushin nan nasa yayi cikin mayanin fuskarsa yana duban omari. Yasan ya sake maimaita maganar kawai don yayi tsokana.......ya kuma samu nasarar tuna masa da abinda shaf ya mance dashi.
"Omari.......ba zaka daina ba ko?"
"Ka gayamin ta yaya zan daina?,bayan nima naga abinda ta gani din?". Wani miskilin murmushin ya kuma saki wanda ba zaka samu nasarar ganinsa ba saboda rufaffiyar fuskarsa,ya kada kansa a hankali.
"Kana yi kaman bakasan komai akan muhammad haisam ba....."
"Idan nace nasan komai din kamar zai zamana na yiwa kaina qarya ne" Ya amsa masa yana bin bayansa sanda yake komawa zuwa babbar qofar masallacin don kaucewa idanu da kallon jama'ar dake wucewa nesa kadan dasu,don tunda har baibar masallacin ba masu tsaronsa yasan ba lallai subar kowa ya sake shiga ba banda na ciki da suka samu yin sallah a cikin wasunsu suma suke haramar fita.
Yana tube rufaffun takalmansa da bayansu ya zamana budadde muryar tayi sallama daga gefansa. A nutse ya daga kai yana amsa masa. Salawi ne......wanda ya kasance me hidimta masa ta fannin kula da abubuwan hawansa......dokunansa da motocinsa.
"Obbo(yallabai),a matso maka da farda(doki) ne?" Kai ya girgiza a nutse,so samu ma ya zauna cikin masallacin kafin ya wuce cikin gidan,to amma hakan yasan bazai samu ba.....don tabbas yasan anna tana can tana dakon shigowarsa......kome dare kuma bazata je ta kwanta ba sai ya shigo din.
"A wuce dashi gida......zan shigo cikin gidan yanzunnan.......zamu tako da qafa". Ya qarashe maganar yana sauke idanunsa akan taarik dake shigowa,da alama shima akwai baqin daya sallama.
Jijina kai salawi yayi yana juyawa yana barin gurin,tare da jinjina irin jarumtar uban gidan nasa,da cikakkiyar lafiyar da Allah ya hore masa. Wuni guda yau a tsaye suka yita,saboda tarbar baqin da bai zauna ba.....dashi aka dinga karbar baqin me martaba da sukazo taron har sai daya tabbatar anyi komai yadda zai dace da muradin mooti din......amma duk da haka yakejin zai qarasa gida a qafa ta hanyar kebantacciyar hanyar da zata sadaka da cikin gidan tun daga masallacin,wadda keda tsahon kilometers da kuma jami'an tsaron dake aiki a cikinta duk da ba kasafai ahalin gidan ke amfani da hanyar ba.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer π³πͺ*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITAπ*
*HUGUMANKU CE*βπ½
*H U G U M A*
PAGE 16
Cike da mutuntawa ya qarasa cikin baqin da yawansu suka kasance abokansa ne.... Abokai kuma irin wanda suka hadu da juna ta hanyar Neman ilimi. Kallo daya zaka yiwa kowa a cikinsu ka karanci yadda ilimi yayi musu ado da wata irin nutsuwa ta musamman. Duk da kowa a cikinsu matashine da jini ke guda na a jikinsa yadda ya kamata......da yawansu matasa ne da suka fito daga gidajen sarauta da gidajen mulki......irin mulki da sarautar da suka mallakawa kowa jin dadi dukiya me yawa da wani irin kwarjini na musamman.......saidai wannan nutsuwar......wannan kamalar da wannan haibar da ilimin addini da qur'ani ke saukarwa kowanne ruhi dake da abota dashi ta mamaye kowannensu. Hatta da yadda lafuzansu na magana da yadda suke tsokana da raha a junansu ta tsaftatacciyar hanya kadai abun burgewa na. Kusan matasa irinsu da suka hada baiwa irin tasu,kyau.....mulki......sarauta,ilimin addini dana zamani......mafi yawa daga cikinsu lokacine nacin duniyarsu da tsinke ta hanyoyi daban daban,sharholiya da sauran abubuwan da suka saba da addini da al'adunsu.
Kusan hirar tasu ta tuna baya ce.......don a cikinsu akwai wadanda aka jima ba'a hadu da juna ba,yau irreechaa day ta hadasu. Zolayar juna,tuna wasu abubuwa masu muhimmanci,abubuwa masu dadi da rashin dadin suketa yi wanda ya faru cikin makarantun da sukayi tare. Wahala da irin qalubalen da suka fata wajen haddar qur'anin da sukayi a shekarun qananun shekarunsu.
"Har yanzu ina mamakin yadda muke kwamciya da dare baka kammala haddarka.......amma da safen saika tashi ka haddace karatun gaba daya harda qari akan qa'idar daya kamata a tsaya?". Siririn murmushi ya saki yana lumshe kyawawan idanunsa dake da wani irin shape da yafi almond shafe tsaho kadan.
"Wannan baya baccin dare me yawa tun asalinsa.......amma nima ina da ayar tambaya a kansa wallahi.......inajin anya mooti bai bashi wasu sirrika ba irin na masarauta?". Dariyar dake cike da hankali suka saki,ya bisu da murmushi yana aza hannunsa gadon bayan wanda yayi maganar. Cikin sautin nan nasa da yasha banbam dana maza da yawa yace
"Indai ina da sirrika na sarauta.......lallai ba shakka kai din bappi ya baka sirrikan mulki.......shi yasa kujerar ka da gadonka har muka kammala ba wanda ke kwanciya akai" Dariyar suka sakeyi,yana tuna musu da rigima irin ta mutallab. Yafi kowa rigima a cikinsu,sannan yafi kowa bata musu daki a wancan lokacin,to amma duk randa ya taqarqare yayi gyaran dakin tofa kowa ma ya shiga uku a wajensa,basu da sukuni basu da sakat.
Wani irin team garesu a sannan me abun mamaki,ba wani a cikinsu da ubansa ba wani bane cikin qasar ta Ethiopia da maqwabtanta.......'ya'yan gata ne iya gata.......saidai gatan da yasha banbam da sauran gara gata,saboda wata irin tarbiyya da ilimin addini daya ratsa ruhin kowannensu,ya maidashi mutum me wata irin nagarta ta daban.
"Banda dare yayi lokaci ya soma ja.......da mun taba musaffa koda ta izu daya ce......don bana tunanin nan kusa akwai wani lokaci da zai sake hadamu kamar haka......duk kowa a cikinku yaqi fidda mata yayi aure bare mu saka ran haduwa a kusa kaman haka" Daya daga cikinsu da suke kira da naseeb wanda dan asalin Egypt ne ya fada yana duba agogon hannunsa sannan ya sauke dubansa akan haisam.
Shi din mutum ne me asalin fahimta da daukan haske akan magana ko motsin mutum.........hakan yake tun asalin halittarsa.......wannan ya bada gudunmawa sosai kan aikinsa na yanzu da yakeyi personally ba tare da kowa yasan wayeshi din ba. Yanayin yadda naseeb yayi maganar yasan me yake nufi,ina ya dosa. A cikinsu shidan naseeb yayi aure bada jimawa ba.......mutallab......khadeem.....maleek......amjaad......dukka suna da tsayayya.......shine har yanzu da babu koda wannan tsarin a gabansa,sau tari koda conference call sukeyi a tsakaninsu mutallab din kan tsokaneshi da cewa.
"Don Allah ku nema masa tsayayya wannan.......wannan an rasa me tsaya masa". Omari ne kanyu murmushi......saboda shi daya ne yafi kowa a cikinsu sanin wayeshi.......yafisu saninsu rufaffen sirri me girma dake cikin rayuwarsa.
Cikin qasa da mintuna talatin tawagarsu ta soma fita daga masallacin zuwa inda kowannensu abun hawansa da guards dinsa ke jiransa. Cikin wannan hirar da barkwancin gami da qaunar junansu,kamar ba zasu rabu ba haisam din daya kasance me masaukin baqi ya takawa kowa zuwa bakin motarsa cikin musabahar bankwana suka rabu.
Ya rage dagashi sai omari da suke takawa a nutse zuwa sirrantacciyar hanyar da yakejin kamar nan ne kawai yafi dacewa suyi magana da omari,bayan masu tsaron qofar sun bude masa cikin rusunawa bayan ya wuce suka maidata suka rufe.
"Omari......" Ya kira sunansa da tsinkakkiyar muryar nan tasa dake da wani irin amo......amon da hatta maza 'yan uwansa tana musu dadi ballantana diya mace.
"Wani lokacin sai na dinga jin kamar wannan matsayin......wannan girman da ake bamu kaman yana neman wuce gona da iri.......kamar akwai sabawa mahalicci a cikinsa" Ya fada calmly kyawawan idanunsan nan dake da wani irin haske suna motsawa wajen rufe kansu da budesu a lokaci guda yana duban tsahon hanyar da suke takawa cikin nutsuwa.
Murmushi omari ya saki......shi dinma daga gidan sarauta ya fito,da akwai banbancin yare tsakaninsa da haisam.....shi din yaren amheric ne......amma yanayin aikinsu ya sanya shida haisam din sukejin yaruka masu tarin yawa,harda yaren da ba na qasarsu bama,ciki kuwa harda yaren turanci bayan na larabci daya zame musu kamar yarensu na haihuwa. Sun iya hausa kasancewarta cikin yare mafiya girma da fadada cikin yarukan yankin africa,hakanan sun iya French......yarukan da suke cikin qasarsu kuwa kusan kowannensu saida suka iya shi,a qalla idan aka lissafa yare kusan goma suke ji,saidai ba kowa ne yasan da wannan ba.
A yadda omari yake kallon komai,duk wani motsi na gidan sarautar abba jifar yana cike ne da zallar ilimin addini dake magana. Hatta da shigar bayi hadimai da dogaran gidan yasha banbam dana masarautu da dama. Tsarin aurar da hadimai da bayi......gidajensu prison dinsu da makarantunsu.......komai nasu yasha banbam dana sarakunan qasar da dama. Omari bai samu damar cewa dashi komai ba.......babban saqon da yake qunshewa a cikinsa tun dazun ya fado masa
"Shugaba yayi kira.........yace kuma lallai gobe mu sauka addis ababa". A nutse haisam ya waiwaya yana duban omari,saidai mamaki ya bayyana sosai saman fuskarsa.
"Da gaggawa haka?". Kai omari ya gyada yana dubansa shima.
" Yace bai sameka ta kowanne platform ba.....shi yasa ya ajemin saqon......ajemin saqon da ganin da nayi kuma dole ya sakani cikin operation din.......dama wannan shine burina,addu'ata ce ta karbu" Omari ya qarasa maganar murmushi yana subuce masa. Dauke dubansa haisam yayi daga kan omari fuskarsa na nuna alamun qaramin murmushi ta yankin rawanin da har yanzu bai saukeshi qasan fuskarsa ba.
"Inaji a jikina kamar lokaci yayi......kamar wani abu ya bayyana game da abba *AJANI AHMED*" Yayi maganar da dukka yaqininsa.
"Ka duba mana tickets da suke available daga jimma zuwa addis ababa......idan baka samu available ba ka sanarmin mu tafi a mota....."
"Dama kafison hakan ai" Omari ya fada yana dan tsuke girarsa. Haisam bai waiwayo ya kalleshi ba......saboda yasan hade rai omari din yayi,sai wani lafiyayyan murmushi abinsa daya sake cikin rawaninsa.
"Kuyi duba izuwa tasirin rahamar Allah yadda yake rayar da qasa bayan mutuwarta............haqiqa cikin halittar sama da qasa da sassabawar dare da rana akwai ayoyi ga ma'abota hankali......omari ka manta da wadannan ayoyin?". Kai ya jinjina omari din yana sakin murmushi alamun aah.
"Akwai abubuwan lura da tunani da yawa akai kan ayoyin ubangiji......baka taba sanin hakan sai kayi yawo a duniya......ka keta dazuzzuga da tsaunuka......ka hadu da hadura masu yawa......abubuwan firgitarwa masu tsananin girma......ka tuna cewa duka mallakar madaukakin sarki ne......iya wannan kadai ya isheka ka qara imani da yarda da ubangiji" Kai sosai omari ya jinjina......shi kansa akwai surori cikin qur'ani da idan yana karantasu yakan tafi ne zuwa wata duniya ta daban ta zurafafa cikin lamarin ubangiji.
08187255862
A cikin jini da dabi'ar haisam suke........yana da bala'in son binciken boyayyun abubuwa irin wannan da suka shafi hikima da qudira ta ubangiji.......yana son nature sosai.......yana da son zuwa baqin gurabe muhalli da qasashen da baisan komai a kansu......qasashen da zai zama baqo da gasken gaske akan komai nasu.......baya da tsoro ko digo dis a ransa........baya tsoron shiga risk da hatsari kowanne iri ne......wannan shine ya zame masa sanadin shiga aikin masu bincike na farin kaya cikin sauqi wato Dss. Cikin qanqanin lokaci da fara aikinsa sai ya zamana kamar da experience dinsa ya shigo aikin gaba daya......wanda halitta ce a jininsa data zame masa dalilin samun qarin matsayi nan da nan......cikin shekaru kadan ya zama babba cikin NATIONAL INTELLIGENCE AND SECURITY SERVICE(NISS). Yakai matakin da zai zama shine na daya a wajen.......amma zuzzurfan tunani da kaifin hankali irin nasa ya sanya hangensa yakai kan abubuwa guda biyu.
Na farko shi wanda yake akai a sannan ya fishi shekaru nasa ba kusa ba......sannan babban aboki ne ga mahaifinsa me martaba abba jifar.......ya riga ya sani,komai iliminka......komai wayewarka da saninka......akwai wasu dabaru da wasu hange hange da sai wanda ya baka shekaru zai iya hangensu........yana kunyar abba muhammad dawuud ya sauka a matsayi shi yahau kai.....duk da lokacin retired dinsa yayi.....amma ya nema alfarmar a barshi cikin office din yaci gaba da zama......shi zai zama a madadin mabiyinsa.
Dalili na biyu......yakan ware wasu watanni a shekarar da qasar Ethiopia ke dashi da suka saba da namu watannin goma sha biyu......su din suna da watanni sha uku ne.....a ciki yana daukan wata daya yayi hutu,hutun da ba inda yake qarar dashi sai yin visa ya sayi ticket na wata qasar dake nesa da yankinsu da al'ummarsu.....masu babancin halaye dabi'u al'adu dama halitta irin tasu...... Wani lokacine da yake na musamman a rayuwarsa.......wani lokaci da yake jinsa na musamman shi kansa.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer π³πͺ*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITAπ*
*HUGUMANKU CE*βπ½
π *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*π
*H U G U M A*
PAGE 17
Yana samun wani 'yanci......yana jinsa cikin tarin sukuni da sakewa.......babu wadannan hadiman a tare dashi........ba wadannan masu kula dashi din,hadiman da mooti ko sau daya baya yarda haisam ya motsa ba tare da ko mutum daya ba......illa idan zai shiga NISS,kasancewar wani sirrintaccen abune da ba kowa yasa ma'aikacin hukumar bane......daga shi sai karan kansa a irin wannan yanayin da yakeyin nesa da qasarsa da mutanensa. Yakan yi tilawar qur'ani sosai fiye da yadda ya saba saboda samun sakewa da sukunin zuciya. To muddin ya karbi wannan matsayin zai rasa wannan damar,dole ya zauna ya dinga bada umarni.......shi kuwa yana ganin kamar hakan koma bayansa ne kuma koma baya ga baiwar fikira da basirar da Allah ya bashi ce.
Kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai idanunsu sun hange musu ita. Cikin hanyar data kadaita ga kowa. Sanye cikin wani wadataccen hijabi daya sauka ya lullube har saman qafafunta. Matashiya ce da shekarunta gaba daya ba zasu haura sha tara ba........lullube da wannan kebantacce kuma sirrintaccen kyan na 'yan asalin Ethiopia kuma 'yan qabilar Oromo.......wannan kyan da aka bar musu kayansu,hannunta dauke da wani madaidaicin kwali,idanunta kuma manne akan fuskar haisam din.
"Saami" Omari ya fada qasa qasa,abinda ya sanya idanun haisam qiftawa yana saukesu daga kansa. Daga randa suka zauna sukayi sharhi da fashin baqi akan ayar da Allah yake magana akan LOWERING GAZE cikin qur'ani da suka yiwa take da yaren oromo da *Ilaalcha gadi buusuun* cikin qur'ani Allah yana cewa
"Ka gayawa muminai su kame ganinsu kuma su kula da farjinansu......wannan shine yafi tsarkaka a garesu" Sai ya sake zama me tsantseni da kulawa sosai akan wannan din. Komai Allah yayi jan kunne gargadi umarni ko hani akai ba shakka akwai babban lamari da kuna batu akai......daga ranar da bincikensa yakai kai kuwa baya sake kusantar wannan abun.
Ko kafin sannan mutum ne shi me tsantseni ta wannan bangaren......tun daha sanda ya