Chapter 10 Reading Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc Arewa Novels

Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc

Author :  Binta Musa Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   10 / 25

27K to 30K   out of 73.5K words

gwara dai shidin yakaimu" shiru Na'ima tayi tanajin wani iri, tarasa ma ita fushi zuciyanta keyi dashi ko kuma son ganinsa takeyi oho..... dan har yanzu bata manta da maganganun data kyaba masa ba ranan, ta kuma quduri niyyan zata bashi hakuri akan hakan.

Ranan ma sake kwana Na'ima tayi a dakin nafisan washegari bayan sunyi sallah da sassafen ta fara tattare gidan, kayan abincin da suka siyo jiyan ta ware wanda tasan zasu baci ta maidasu leda zasu tafi dasu can gidan anty Amnahn, bayan ta gama tayi wanka ta gyara gashinta into dough ta shirya cikin wani sky blue din abaya tayi rolling gyalen, lip balm ta shafa dasu mascara sai kuma ta tsaya kallon kanta a madubin, aranta tana dariyan meyasa take saka effort gurin kwalliya kuma, tananan tsaye tajiyo door bell dinsu yayi qara...

Bintu Musa ce
'?=???
ArewaPen @Bintu Musa

('KUNCIN ZUCI('
Na Bintu Musa

ArewaPen https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c

Chapter 18

Goge lip balm din Na'ima tayi tana kallon kanta a madubin, ta koma gurin wardrobe dinta ta cire kayan jikintan sannan ta nemo dogon jalbab maroon tasaka, dan zama tayi bakin gado bata fita daga dakin ba tajiyo fitan Nafisa zata bude kofan
Saida taji shigowan Ahmad sun gaisa da nafisan ya tambayeta ya jikin sannan ta bude kofan ta fito a nutse, bata kallesa ba tace "Ina kwana" taji ya amsa ya kuma cewa "hope kun shirya" Nafisa tace "Eh yaya bari mu dauko kayan", bin bayan Nafisan itama Na'ima tayi suka fara dauko na Nafisan tace "ki bari sis in fitar, jikin ki babu karfi" ta qarasa ta dauko akwatin suka fice, ahaka suka fitar da kayan Ahmad na tayasu, sai kallon Na'ima yake zuciyarsa na muradin su hada ido ganin taqi kallonsa kwata kwata..
Fitansu waje Nafisa ta ware ido ta tana kallon motan dayazo da ita wata sport wrangler jeep baqa, wuce su Ahmad din tayi ta qarasa gaban motan tace "yaya this car is fire" dan murmushi Ahmad din yayi suka qarasa gurin motan shida Na'ima da itama sai kallon motan take, yace? da Nafisa "bakida lafiya da kinyi driving dinmu ai" juyowa Nafisa tayi ta kalli Na'ima da suka hada ido tace "hakane yaya, amma naji sauqi sosai ai yau din" ta qarasa maganan ta yin mita aranta tayi qarya kuma abun ya dameta yanzu ga ci ga rashi, zagayawa bayan motan Ahmad yayi ya fara saka musu kayan nasu yana cewa "sai kinji sauqi sosai tukunna"? nafisa ta dan turo baki ta bude back seat zata shiga Na'ima tayi saurin riqe hannunta tayi qan qan da murya tace "nafee ki shiga gaban mana" Nafisa tana danne dariyanta tace "zan kwanta ne ai, jikina yana ciwo" da haka ta bude ta shiga ta bar Na'ima nan tsaye bata shiga motan ba, Ahmad ya qaraso wajenta bayan ya gama saka kayan, a hankali yace mata "ko zakiyi driving din?" Na'ima ta kauda kai cikin sanyin murya tace "ban iya ba" shidai kawai kallonta yake ganin kamar kyau ma ta qara yi cikin kwanaki dayawan da bai ganta ba, ganin bazata juyo da kanta ba yasa ya bude mata front seat din ya tsaya yana jiran ta shiga, Nafisa na kallonsu ta cikin motan sai murmushi take lamarin nasu na sata nishadi, aranta tana ayyanawa wato "mutune biyu ne marasa yawan magana suka hadu guri daya sai ake gudanar da alaqan a aikace bada baki ba", hannu nafisa takai ta dan kwankwasa glass din Na'ima ta farga da ashe tana kallonsu, ta danyi saurin shiga gaban motan Ahmad ya rufe ya zagaya ya shiga suka wuce..

Shiru motan yayi Nafisa dake baya taqi cewa komai dan dama itace mai fara hira a motan to yau itama tayi shiru tana kallonsu, driving dinsa kawai Ahmad jefi jefi yana kallon Na'ima datayi shiru itama tana facing window, can yadan juya kansa back seat yace "bude muku abincin nan Nafisa", dauko ledan nafisa tayi ta dauki nata burger da ruwa sannan ta miqawa Na'iman tace "mungode yaya" baice komai ba, Na'ima ta ciro sai kuma ta miqo masa tace "zakaci?" juyowa yayi ya kalleta da dan murmushi a fuskansa yace "rowa zakimin" Na'ima tayi murmushi sannan ta girgiza kai tana qara miqo masa, kallon ta ya danyi sai kuma ya maida hankalinsa kan tuqinsa yace "naqoshi", bata ci sosai ba ta maida sauran burgern cikin box dinsa tafara karkade hannunta, zaro tissue Ahmad yayi daga ma'ajiyinsa ya miqa mata ta amsa tareda muttering "thanks", Nafisa dake baya tana kallonsu ta jijjaga kai tana murmushi ta miqo hannunta ta zari tissue din itama....
Saida suka ci rabin tafiyan sannan suka tsaya a wani gas station dake cikin wani town nan kan hanyan tafiyar tasu, fita Ahmad yayi zai qara mai a motan, Nafisa ta dan matso gurin Na'ima tace "sis bari naje restroom" Na'ima tacire seatbelt dinta ta juyo tace "bari na rakaki" girgiza kai Nafisan tayi tace "kijiki sai kace wata yarinya, yi zamanki yanzu zan dawo, mezan siyo miki cikin restaurant din" Na'ima ta jijjaga kai tace "naqoshi, Dan Allah karki dade" dan murmushi kawai Nafisa tayi ta fita daga motan, fadawa Ahmad dake tsaye yana filling motan inda zataje tayi, ya gyada kai yana cigaba da abunda yakeyi.
Bayan yagama ya shigo motan ya zauna batareda ya rufe kofan ba, rasa abun fada Na'ima tayi saitaga ya juyo gurinta a nutse yace "how have you been?" dago kai tayi ta kallesa tace "I'm fine" yasake cewa "ya karatun ku" tace "Alhamdulillah" sukayi shiru , ahankali tace "I'm sorry " yana kallonta yace "what for?" tadan sunkuyar da kanta tace "for what i said the other day" tajira jin amsansa sai kuma taji baice komai ba, dago kanta ta sakeyi suka hada ido tace "I didn't mean what i said" shima ahankali yace "I'm sorry too" bata kai ga tambayansa meyasa ba taji Nafisa ta bude kofan ta shigo, gyara zama Ahmad yayi ya rufo qofan shima ya tada motan suka tafi...
Isarsu gidan anty Amnah suka samu batanan taje asibiti, dayake sunsan pin din kofan yasa basu damu ba, Ahmad bai shiga gidan ba yace "ku gaisheta inta dawo" Nafisa tace bazaka shigo ka sha ruwa ba" ya girgiza kai yace "No" yana kallon cikin idon Na'ima yace musu "take care" Nafisa ta gyada tayi godiya, Na'ima tace "Mungode" itama, gyada kai yayi yakoma gun motarsa ya tayar yabarsu nan tsaye, Nafisa tabi baya motan da kallo tace "sai na karbo motan nan munje school da ita" Na'ima ta kalleta tace "kije dai bandani, daga ganin mota kin gigice nafisa" Nafisa na dariya tace "yarinya bakisan motan bane" jijjaga kai kawa??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????i Na'ima tayi suka wuce cikin gidan.

Sai yamma anty Amnah tadawo tareda twins data biya school dinsu ta daukosu, zuwa lokacin su Na'ima sunyi sallah sun huta har sun dafa musu abinci..
Suna zaune a falon ta shigo alamun gajiya bayyane jikinta tace "yan makaranta kun iso?" basu kai ga amsawa ba twins suka buga tsalle sukayi kansu, dariya Na'ima ta fara bayan sun danneta tace "oyoyo darlings" nan gurinsu Anty Amnah ta zauna tana kallon Na'ima tace "sai sun ballaki ai, Kai ku sauqa daga kanta" Na'ima tayi dariya batace komai ba
Gaisheta sukayi ya amsa tace da nafisa "How far..ya jikin naki?" Nafisa ta gyara zama tace "naji sauqi anty, gidannan kamar da magic cikinsa, sai naji na warware" dariya anty Amnah tayi sanin da hadin bakinta Nafisa tayi qaryan rashin lafiyan, tace "toh Allah ya qara sauqi"? Na'ima tace "Anty akawo muku abinci ko sai kun huta" Anty Amnah ta dan girgiza kai tana murmushi tace "a'a daughter ki barshi zamuje muci, thank you"
Itadai tun ranan farkon ganinta da Na'ima take sonta, zamansu da ita kuma ta sake fahimtan dayawa daga cikin halayen yarinyar wanda a lokaci da dama takanyi ta tunanin ta Ina yarinyar ta gaza da har abubuwa suka faru da ita haka?, kallon Na'iman tarinqa yi wadda ke biyewa hiran twins batasan ma san tanayi ba, ganin zata dago kanta yasa anty Amnah tashi ta wuce dakinta zuciyanta cike da tunani...
Da daddare suna having dinner tareda uncle yasir shima, yace "kuyi zamanku anan ku qarasa karatun naku kunji" Anty Amnah tace "nima haka nace fa" Na'ima tayi shiru tana jiran Nafisa ta basu hakuri akan zasu koma sai taji akasin haka dan Nafisa cewa tayi "toh uncle in Sha Allah" dan dago kai tayi tana kallon Nafisan datake cin abincin ta hankali kwance, Uncle yace "yauwa ko ku fa, trains din yanzu suna gudu sosai dan within awa daya da rabi ma zakuga kun isa, ko ya kika ce Na'ima?" ya qarasa maganan yana kallon Na'ima, gyada kai tayi ahankali tace "toh uncle" yace "ma Sha Allah, ai kun fara dissertation dinku ba?" Nafisa tace "A'a uncle muna kan yin research akai ne" yace "Allah ya taimaka, hope kunada group mates" Nafisa tace "Eh uncle" anty Amnah ta sake tambayan Na'ima da "kema kin samu group mate dinne daughter?" sai sannan Na'ima ta dago kanta tace "Eh anty akwai kawata da zamuyi research din tare" Anty Amnah tace"ma Sha Allah, Allah ya baku sa'a" suka amsa da Amin...
Bayan sun koma dakinsu basu yi magana ba, Na'ima ta shige toilet ta bar nafisa na rage kayan jikinta, bayan ta fito tasamu har nafisan ta kwanta, changing tayi itama cikin kayan bacci ta zo ta zauna bakin gado tace "Nafee we need to talk" Nafisa tadan yaye blanket din daga kanta ta dago tana gyara zama tace "inajinki meya faru?" Na'ima na kallonta tace "are you hiding something from me nafisa?"? ? Nafisa ta girgiza kai tace "haba dai..A'a kam, me kika gani" Na'ima tace "komai ma doesn't sit right with me nafisa, all of a sudden kince kin samu sauqi ko magani baki sha ba sannan uncle sunce muzauna bikiyi protesting ba kai tsaye kika yarda, kamar ba ke bace nafisan da nasani batason zirga zirgan tsakanin Oxford da London, what happened to you ?" Nafisa tadanyi murmushi tace "Kiji ki da wasu zance, dan na yarda mu zauna shine akwai abunda ke damuwa?" Na'ima bata komai ba ta qura mata Ido, dan matsowa Nafisan tayi kusa da ita ta riqo hannunta tace "habaa mana sis, kinsan ban taba boye miki abu ba fah" dan jijjaga kai Na'ima tayi tace "ai komai yanada mafari nafisa, nasani ko kin fara boyemin abubuwan da suka shafeki" Nafisa ta sake damqe hannun Na'iman tace "babu abunda nake boye miki, for better for worse kinsani you're my best person in this world" Na'ima ta gyada kai tace "nima haka, kawai banason changes din nan danake gani gurinki ne kwana biyun nan, you look strange" Nafisa tayi dariya tace "bawani changes Bobo" itama Na'iman dan dariya tayi tace "yanzu zamu zauna anan din kenan?" Nafisa tace "Eh..Amma in bakyaso sai mu koma" Na'ima tadan ware ido tace "A'a ni bance banaso ba, ai nan yafi ma" da haka suka fara hiransu da suka saba Nafisa ta ware suna surutu, dan dama shiru shirun nata bana Allah da Annabi bane...
Kiran Mami neh yashigo wayar Nafisan, tadan dakata da magana suna kallon fuskan wayan itada Na'ima, bayan ta daga sun gaisa daga dayan bangaren Mami tace "Baby nayi waya da maman twins tace min kunzo saboda baki da lafiya" Nafisa tace "Eh Mami banajin dadi ne" Mami tace "to kuma shine waninku bazai kira a fada mana ba, tun yaushe ne bakida lafiyan kuma me yake damunki?" ta amsa da "kwana biyu dasuka wuce ne fa Mami kuma na dan ji sauqi ma yanzu, dama ciwon kai ne sai kuma dan fever haka" Mami tace "toh Allah ya qara sauqi, tace min zaku dan zauna anan gidanta tunda ba wani lectures kukeyi a school din ba" Nafisa ta gyada kai tace "Eh..yasu Abba fa?" Tace "yananan lafiya bana kusa dashi, Ina Habibti fa bata muyi magana" miqawa Na'iman wayan tayi, bayan sun gaisa Mami tace "Habibti shine kuka qi kira ku fada mana babu lafiya" Na'ima tace "kiyi hakuri Mami wallahi na zata ta fada muku ne shiyasa ban kira ba" Mami tace "Antyn kuce ta kira ta fadamin, ya kuke toh, ba matsala ko" Na'ima tace "In Sha Allah Mami yasu Abba?" ta amsa da "lafiyansu kalau, kuyi zamanku nan gidan maman twins din tunda bakwa yawan shiga makarantan" tace "toh Mami in Sha Allah" da haka sukayi sallama tace su kirata fa in wani abun ya sake tasowa...
Basu je school ba washegari daya kasance Friday sai suka hutawan su suna taba karatun, dan anty Amnah ma ta fice gurin aiki ita da mijinta haka zalika twins Suma suna school....bacci Na'ima tayi mai dadi sannan ta tashi tayi brush da wanka ta shirya cikin qaramin riga da dogon straight skirt ta fice falon, Nafisa ta samu tana cin abinci taja kujera ta zauna tace "shine baki tadani ba, inata bacci har yamin yawa" nafisa ta zuba mata madara a cup ta miqa mata sannan tace "nima fa yanzu na tashi, masu gidan duk sun fice" gyada kai na'ima tayi takai cup din baki ta kurba tace "nafisa kaina yayi datti ki wankemin ko muje salon" Nafisa tace "wallahi kanki akwai wahalan wankewa, danayi miki last time fa kince salon zamuje next" Na'ima tace "toh ai yanzun ma cewa nayi ko kimin ko muje salon" Nafisa ta dan harareta sanin Na'iman tafison wankewan kawai fadan salon din take, dariya Na'ima ta farayi ta ajiye cup din tana kallon Nafisan tace "Dan Allah ki wankemin kinji sisi na" saikuma itama Nafisan tafara murmushi tace "toh zaki yarda ki rakani gidan yaya Ahmad ranan Sunday" tsaf Na'ima ta dinke fuska tace "ni narasa dalilinki na sai munje gidansa, kin fara maita ne bansani ba nafisa?"
Nafisa ta kwashe da dariya tace "bawani maita, ni nazata ma straight zaki amince ganin irin kallon da kukewa juna jiya" Na'ima ta harareta tace "banaso nafisa, ni yaushe na kalleshi?" Nafisa tadan ware Ido tace "lallai ma yarinyar nan kin rainawa kanki hankali ba ni ba, iyeee..sannu Na'ima" ta sake wani dariyan ta cigaba "ku gama kallon juna cikin soyayyar a gabana shine yanzu zaki wani kawo min wata maganan yanzu" Na'ima ta ajiye bread din hannunta ta miqe tace "barmin gashin nawa ya rube toh, soyayya kuma halan kin fara ganin komai a baibai ne cikin lamuranki yanzu" ta qarasa maganan tana wucewa daki fuskanta dauke da alamun murmushin da nafisan bata gani ba, Nafisa tayi wata dariyan tace "Muna tafe dai Na'ima"....

Bintu Musa ce
'?=???


('KUNCIN ZUCI('
Na Bintu Musa

ArewaPen https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c

WhatsApp group
https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z

Chapter 19

Ranan Sunday babu yanda Nafisa batayi da Na'ima akan ta rakata suje gurin Lauren data shigo garin ba taqi, Na'ima tace "Nafisa da ban sanki bane sai in yarda dake" Nafisa tana murmushi tace "kinji narantse ba gidan yaya Ahmad zamuje ba, ai tunda bakya son zuwa kuma na hakura" Na'ima ta jijjaga kai tana qara jawo laptop din gabanta batace komai ba, Nafisa ta zauna kusa da ita tasake cewa "haba mana Na'ima" still bata kulata ba tasake cewa "NA'IMAA" still dai ko a jikinta, nafisa bata hakura ba ta sake cewa "Na'ima Yusuf Dabo" sai sannan ta dago kanta ta kalli Nafisan tace "ita Lauren din kullum ne take zuwa London wai" Nafisa tace "shikenan kartayi yawo tana matsayin influencer" Na'ima tace "toh ai yau batanan gobe bata can ne gashi tanason ku rinqa yawon tare" Nafisa tace "wallahi kam, tace wai muje Licester jibi ma, amma bazan samu zuwa ba munada group research ranan nida teammates dina" Na'ima ta girgiza kai tace "toh meyasa kike binta ne ma wani lokacin" tace "Ha'a shikenan bazanyi yawon ganin duniya ba Na'ima, bature fa yace all work without play make jack a dull boy, hausawa ma sunce taba kidi taba karatu" Na'ima ta cigaba da duba abunda take typing tace "toh nidai bandani, inkinga nafita to sai gobe Monday zuwa school" Nafisa tace "toh kizo muje daganan sai mu biya salon a wanke kai din" Na'ima najin haka ta amince dan dama ta gaji da kan tana babu wanki...bayan sun shirya suka ari motan anty Amnah dan tasu sun barota can oxford daman, dagasken kuma gurin Lauren din sukaje , sun sameta a wani restaurant babba, Lauren tayi musu ordern abinci already, itada nafisa suka hau baza magana, itadai Na'ima sai bin abincin take da kallo taqi ci dan har wannan lokacin bata saba da ire iren abincin qasar ba, tanadai cin wasu amma batacin nama a kowanne restaurant gudun abata haramtaccen nama...Lauren? ce ta juyo ganin batacin abincin tace "what happen ne'ima" Na'ima tadanyi murmushi tace "I can't eat this" ta qarasa maganan tana daga hannu a waiter, sake order tayi na simple dish "fish and chips" ...
Salon din sukaje aka wanke musu kai harda Lauren din, tun kafin a fara wankewa Lauren din kai tafara video har qarshe, Rashin sabon ganin hakan a gurin Na'ima yasa ta dan kalli Lauren ta jijjaga kai tana dan murmushi da mamaki ganin komai nata yana media,Nafisa tunda ta samu wayanta bata kula da batun surutun Lauren ba ma....gashin Na'ima ba qaramin kyau yayi ba daya sha gyara aka daure mata shi in a dough, ita aka fara gama wa gyaran dan nafisa har da kitso za'a mata ita kuma Lauren za'a mata qari sosai..
Sai yamma suka koma gida bayan sun yi sallama da Lauren tace zata kawo musu ziyara nan gidan anty Amnahn
Isarsu gidan suka samu motan Ahmad fake a kofar gidan, Nafisa ta kalli Na'ima tace "iyee sai ga yaya Ahmad yadawo, shida yake wuyar ganuwa" Na'ima tace "ba kince dan'uwanku bane, ko dai banji da kyau bane lokacin da kikace cousin din ku ne" Nafisa ta fara dariya tace "wallahi in zan kwana Ina fadawa mutane iya yanko baqar maganar ki baza'a yarda ba" Na'ima ta danyi murmushi tace "ni me nace kuma" Nafisa ta nufi? gidan tana dan dariya tace "babu..Amma kinsan dai inason alaqan ku ko sis, like seriously kuna burgeni, the match was perfect, ke fara shi fari ke dogon hanci shima haka, ga kyau Allah ya baki shima haka....soyayyarku me shirun nan tana burgeni Na'ima" itadai Na'ima tarasa me zatace a farko sai kuma a hankali tace "Nafisa bazan iya soyayya ba, besides

10 / 25