Chapter 23 Reading Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc Arewa Novels

Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc

Author :  Binta Musa Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   23 / 25

66K to 69K   out of 73.5K words

kwanto jikinsa tareda kashe murya tace "something light" Na'ima ce ta fito daga kitchen din hannunta riqe da bottle water da drinks dan dama Sufi ke siyo mata duk wani kayan buqatu na gidan tareda umarnin Alhaji, qarasowa tayi ta ajiye musu nan kan glass table din idonta a qasa bata kallesu ba, cikin isa Bilal yace "Cook something light now" ta amsa da "toh" still idonta na qasa, Stella na kwance jikin Bilal din sai kallonta take tana qarajin wani abu ya tsaya mata a zuciya ganin irin kyan Na'ima'n me fusgan hankali, saida Na'ima ta zuba musu juice din a kofi sannan ta juya ta koma kitchen din tana dan gyara wuyan riganta saboda taquran datayi under their Eyes, bayan ta gama kwashe abincin qasan tana aiki a kitchen din tana jiyo dariyan su, da ta gama ma nan dining area ta ajiye bata kallesu ba tazo ta wucesu zata tafi dakinta, Stella har da janyo fuskan Bilal zuwa gareta tana kissing, itadai Na'ima kanta na qasa ta wucesu..Fitowan da bata sakeyi downstairs ba kenan, bayan tayi sallahn ta ko wanka ma bata samu yi ba ta hau gado ta zauna, Jiyo muryansu tayi sun hawo saman sai taji an bude dakin da ke facing din nata, dan bariki sai Stella taqi rufe qofan, haka Na'ima ta fara jiyo badalarsu Stella har da ihun ta, cikin sauri ta nufi drawer na mirro'nta ta dauko auduga tasaka a kunne sannan ta qudun dune da bargo nan kan gado tana addu'an Allah yasa kar suyi dogon zama a garin su koma inda suka fito....
Dakyar Na'ima tayi bacci saboda yanda takejin zuciyarta a wannan daren, wayewar washegari shima kasa fita tayi, tana nan zaune aka fara buga mata qofa da karfi tayi sauran tashi ta bude, Ido hudu tayi da Bilal yana kallonta yace "do i have to say it before you make breakfast?" Tayi saurin girgiza kai tace "yanzu zanyi yaya, Ina kwana" bai amsata ba yajuya tareda banko kofar a fuskanta tana nan tsaye, sake budewa tayi ta fito tareda wuce kofar dakin nasu dake kulle ta sauqa qasa zuwa kitchen din, cikin sauri ta kammala musu breakfast din tana cikin jerawa a dining Stella ta sauqo sanye cikin t-shirt din Bilal din da bum short, fara bude flask din tayi ta bi chips da fried egg din da wani kallo sai ta yamutse fuska tace "where is the tea?" Na'ima tace "yana kitchen tukunna" sai ta juya zuciyarta na quna ta shige kitchen, saida ta zubawa Stella tea tananan zaune hakimce a dining chair, takai baki ta kurba sai tayi saurin burtsoshi daga bakinta wanda hakan yayi daidai da sauqowan Bilal, yayi saurin qarasowa yace "what happened Baby" Stella na kyabe fuska tace "Baby what kind of tea is this, jiya ma haka naji gishiri cikin abincin nan" karban shayin yayi ya kurba sai ya jefawa Na'ima cup din tayi baya duk da haka saida shayin ya zuba jikinta tajiyo zafinsa har cikin jikinta, bata farfado daga wannan ba taji Bilal ya sauqe mata wani mari mai dauke ji a kunne, dafe fuskanta Na'ima tayi ta sake yin baya idonta na kawo ruwa, jikinsa har wani tsuma yake tsabar masifa yace "Don ub*nki kashemu zakiyi, bakiji yayi daci bane" batayi magana ba kanta a qasa sai ya kai mata wani dukan a fuskan yana cewa "sai na rinqa repeating magana sannan zaki amsamin kenan" kuka me sauti Na'ima tafara yi tana bashi hakuri, Stella ta dauko chip daya takai baki tana kallonsu with amusement batayi magana ba, Na'ima na kuka ta koma kitchen ta dora musu wani shayin, da ta gama nan ta sake kawo musu suna zaune a dining din ta zuba musu sannan ta koma sama cikin sauri, kuka ta fashe dashi bayan ta shiga dakin tana tsaye, juyawa tayi ta kalli mirror sai taga gefen fuskanta yayi ja ga lebenta na dan fitar da jini, tana hawaye ta dauko tissue tafara gogewa bata daina kallon kanta a madubin ba,
Gashi tanada lecture zuwa 11 batasan ta yanda zata fara fita daga gidan ba, dan tsoron tambayansa take kuma...

Allah ne ya taimaki Na'ima ta Jiyo muryansu a parking space can taji tashin motan nasu megadi ya bude musu gate suka fice, da saurinta ta shiga wanka bayan ta fito ta shirya sai ta hau neman face mask cikin kayanta tayi sa'a kuwa tasamu..
Bayan ta rufe gidan sai ta rasa yanda zatayi da key din kawai ta baiwa megadi tayi saurin tafiya bakin hanya dan neman abun hawa, isarta makarantar ta samu class mates din nasu suna fitowa daga hall din da za'ayi combined lecture din da nufin an samu change of venue, hango Nafisa tayi sai taga tayi saurin qarasowa wajenta tace "Na'ima lafiya kikayi latti, it's unlike you" ta amsa cikin sanyin murya da "Ban lura da lokacin bane" Nafisa ta gyada kai still tana kallonta ganinta yau kuma sanye da face mask, fara tafiya sukayi sai da sukayi nisa duk anyi gaba an barsu sai Na'ima ta kalli Nafisan cikin kwantar da murya tace "Nafisa Dan Allah kiyi hakuri da abunda ya faru jiya" da farko Nafisa batace komai ba sai kuma ta jefa mata tambaya tace "wacece wadda yazo tare da ita jiyan" juya kai Na'ima tayi idonta na kawo hawaye tace "bansan ta ba nima" cikin dan mamaki Nafisa ta kamo hannunta, qarqashin wata bishiya ta jasu suka tsaya sannan tace "Na'ima you can tell me everything, inaji ajikina akwai abunda yake damunki bazaki fada ba" kuka Na'ima tafara mara sauti sai kawai Nafisan ta dan rungumota tafara buga bayanta itama idonta taji yafara kawo hawayen, sai da Na'ima tayi kukan sosai sannan suka zauna kan wani rest bench a gurin Nafisa tace "Na'ima me yake faruwa dake Dan Allah" tana kallon gefe tace "He's assaulting me nafisa" tsabar mamaki har bude baki nafisan tayi sai Na'ima takai hannu tacire face mask dinta, cikin tashin hankali naifia ta kai hannu tana taba fuskan tace "he did this to you?" Na'ima ta gyada kai batace komai ba still idonta na hawaye, Nafisa tace "wane irin dabba ne wannan da zai kai hannu jikin mace, kuma kin fada a gidanku?" Na'ima ta girgiza kai, Nafisa ta sake cewa "baki fadawa maman ki ko babanki ba? Na'ima what is wrong with you, ace mijinki ya duke ki kuma sai kiyi shiru" tsayawa kallon Nafisan tayi cikin sanyin murya tace "iyayena sun dade da mutuwa Nafisa, a gidansu mijin nawa na tashi" zuwa lokacin kan nafisa ya kulle kuma sai ta damqo hannun Na'iman tana squeezing tace "tell me everything please" nan Na'ima ta sauqe idonta qasa tiryan tiryan tafara bawa nafisa labarin ta tun tana qauye har kawo yanzu da take zama gidan Bilal, hawaye Nafisa ta rinqa yi tana sharewa bata daina kallon Na'iman cike da tausayi ba, tace "you have to tell his father, this can't continue Na'ima, Kuma kinayin addu'a sosai?" sai Na'ima tayi shiru batace komai ba, Nafisa ta sake cewa "kina tashi cikin dare ki kai kukanki gurin Allah Na'ima?" Tunani Na'ima tafara dan gaskiya dan gaskiya ta fannin addini tanada rauni kasancewar both gidajen da ta taso duk ciki babu wanda aka bada himma ta fannin karatun addininta, sai ta girgiza kai Nafisa na kallonta tace "kina sake sosai Na'ima, Bilal yana alaqa da irin wadda nagani jiya kuma ace bakya yawan addua?" cikin sanyi Na'ima tace "ai bansan addu'o'in da ya kamata inyi ba" nan Nafisa ta fara karanto mata ganin bata ganewa sai ta dauko takarda daga jaka tafara rubuta mata su, shawarwari Nafisa ta hau bata suna nan zaune, lecture dinda basuyi ba ranan kenan, da nafisa ta tashi maidata gida nan ma tayi ta encouraging dinta akan ta samu Alhaji da maganan, itadai Na'ima sai gyada kai babu magana a haka har suka isa, tayi sa'a basu dawo ba kuwa nan ta hau dafa musu abinci cikin sauri, basu dawo gidan ba sai tsakar dare, Na'ima na kishingide kan sallaya tajiyo buruntun su, washegari ma sai da ta jira fitan su sannan ta fice school din, a bakin class ta hango nafisa na tsaye tana jiranta bata shiga ba, Na'ima na murmushi ta iddata sai nafisan tace "thank God, nazata wani abun ne ya faru" murmushi me fadi Na'ima tayi sai tace "shine kikaqi shiga class kuma" bata amsa ba mata ba sai tace "bazai barmu mu shiga ba yanzu, ya kusa gamawa", jansu tayi gurin cin abinci tayi musu order sunanan zaune, bayan sunci Na'ima tayi insisting biya Nafisa ta hanata tareda saurin miqa card nata, sai da suka tashi komawa gida na'ima tasan nafisan bata zo da motanta ba, tace su jira yayan ta da zai zo daukanta, basu wani dade ba wata wagon jeep ce ta faka a gabansu nan inda suke tsaye akayi rolling glass din gefen me zaman banza wani kyakkyawan yaron da bazai wuce shekara 13 years ba ya leqo kansa yana dariya, Nafisa ta hararesa tace "wallahi fitowa zakayi ma, dan ajiyata ce a gaban motan nan" wanda ke driving din yayi dariya yace "hala kwai kikayi a wajen" ta bata fuska tace "Yah faruk meyasa zakazo dashi Fisabilillah" bude motan yayi sannan ya fito be zagayo ba ya tsaya yana kallon Na'ima dake dan kauda kai dan ta cire face mask din a sannan, Nafisa tace "Yaya meet my friend Na'ima" da sauri Abu ya fito daga gaban motan yana murmushi yace "itace Anty Na'iman dama, ina wuni" murmushi Na'ima tayi ta amsa sannan ta kalli faruk tareda gaishesa, ya amsa bai bar kallonta ba, Abu na murmushi ya danyi qasa da murya yace da Nafisa "she's beautiful" a bayyane Nafisa tace "kai dalla tanada Aure" sai sannan faruk yayi saurin kauda idonsa yace dasu "ku shiga muje mana"... Har gida suka kai Na'ima dazata fita tayi musu godiya Abu yace "yaushe zakizo gidanmu anty?" tana murmushi tace "zanzo wani sati in sha Allah" da haka sukayi sallama nafisa tace "I'll call you" shidai faruk bai sake cewa komai ba idonsa na kan wayarsa yana pressing...

Karfe dayan dare na ranan tana zaune kan sallaya bayan ta idar da sallah taji shiru har Lokacin Bilal basu dawo ba gashi ta bar qofan falon nasu a bude, tsoro ne taji ya dan fara shiganta sai ta miqe ta fice daga dakin taje ta kulle kofan sannan ta koma daki, bata fi 30 minutes da fara bacci ba taji an fara buga kofan falon da qarfin bala'i, ta miqe da sauri har jikinta na rawa ta isa falon ta tsaya, kasa budewa tayi dan bugun ya mata karfi sosai, Jin muryan Bilal tayi da qarfi yace "Open this damn door Na'ima" sai tayi saurin qarasawa jikin kofan, bata qarasa bude kofan ba ya banko ta tareda hankata tayi baya ta fadi da karfi, fuskan nan tasa tayi jajir sai warin taba da alcohol yake, miqewa Na'ima ta farayi ganin yanayinsa aikuwa beyi wata wata ba ya qaraso ya kwasheta da kafa, tiim ta fadi qasa tareda yin qara, yana huci yace "ko a gidan ubana da kika zauna kin taba ganin sun kullemin kofa?" Ta girgiza kai tana kuka dakyar kafin ta sake wani magana ya sake kai mata wani harin da qafa, dukanta ya hau yi iya kafinsa yana cewa "who are you, da zaki kullemin kofa" tana kuka ta cigaba da jijjaga kanta, sai da ya gaji dan kansa sannan ya sake mata wani tsawan "answer me" tana daga kwancen kan tiles tana kuka tace "kayi hakuri" ya buga tsuka me karfi ya tsallaketa ya wuce sama, kifa fuskanta tayi kan tiles din tana kuka mara sauti tareda dafa cikinta, saida takai almost 1 hour a wajen sannan ta miqe dakyar ta gyara gashinta daya sauko fuskanta, dafe da cikinta ta nufi saman zuwa dakin ta tana hawaye, baccin da batayi ba kenan har asuba idonta biyu, data hada breakfast ma shi kadai ta samu zaune kan dining chair din, tayi serving dinsa hannunta nadan rawa shikuwa gogan idonsa na kan wayarsa, tsuka ya buga me karfi tareda Kai hannu ya tunkude plates din suka kife nan qasa, da sauri Na'ima ta masa gefe tana damqe idanunta dan ta dauka duka ze kai mata ma sai taga ya nufi sama da sauri ransa a bace, tsugunnawa tayi ta fara kwashe kayan idonta na cikowa da hawaye, saida ta gyara gurin sannan tafi dakinta, tana tsaye gaban mirror tana shafa rob a ciwon dake gefen idonta tajiyo fitar motansa, da sauri da shirya itama amma madadin ta tafi makaranta sai ta wuce gidansu aranta tana addu'an samun Alhaji....

Dont forget, your reaction gives me courage to do mored'?

Bintu Musa ce
'?=???

https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c

('KUNCIN ZUCI('
Na Bintu Musa

Chapter 31


Isarta gidan nasu bayan ta sallami mai mashin suka gaisa da megadi sannan ta shiga cikin gidan tana gyara face mask din fuskanta, shiganta falon yayi daidai da fitowan Hajiya daga corridor'n kitchen hannunta riqe da tray alamun zata kai breakfast din Alhaji, tsugunnawa Na'ima tayi har qasa ta gaishe da hajiyan ta amsa tana mata wani kallo sai tace "zauna anan bari inzo" gyada kai Na'ima tayi tareda amsawa da toh sannan ta zauna anan main falon Hajiya ta wuce sama, bata wani dade ba ta dawo, nan falon ta zauna tana kallon Na'iman tace "ya da sassafe haka?" Na'ima ta danyi jim batace komai ba kanta a qasa sai Hajiyan tace "zama zamuyi tayi cikin shiru kenan" ta girgiza kai idonta na kawowan hawaye ta sauqe face mask din, kallonta Hajiya ta tsaya fuskan ta babu alamun wani emotion guda daya, cikin rawan murya Na'ima tace "dukana yayi jiya Hajiya" kadan ya rage Hajiya batayi tsaki ba ta danne zuciyarta tace "shine dan Miji ya dake ki sai ki taho gida da sassafen Allah ke mai iyaye kenan, kin fa san waye Bilal kuma kinsan muma a sannu muke bi dashi a gidan nan, in kikace bazaki saka hakuri cikin lamuranki ba to bazaki taba ganin daidai ba Na'ima, kowa da kika gani hakuri yake a gidan mijin nan, asannu ake bin miji sai kiga komai yawuce kamar ba ayi ba" Hawaye Na'ima ta rinqa yi tanajin zuciyarta na mata zafi, a hankali ta amsa da "toh Hajiya" miqewa Hajiyan tayi tace "Alhajin na bacci yanzu kije tukunna, dududu ma auren naku wata nawa ne ma har kin fara kawo qara Na'ima, hakane hakurin naki da muka sanki dashi kenan?" Na'ima ta girgiza kai bata daina hawaye ba, sai Hajiyan ta sake cewa "ki koma gida yanzu, in ya tashi zan san yanda zan masa maganan, kuma shima Bilal din zan ja kunnenshi" Na'ima ta gyada kai tareda miqewa itama tace "zanje daukan kayana a daki" sai Hajiyan ta gyada kai tareda cewa "toh, ki gaida gida, arinqa hakuri shine ribar zaman duniyan gaba daya" nan kuma Na'ima batace komai ba ta nufi dakinta da take zama a gidan a da hajiyan na bin bayanta da wani kallo har sannan bata dai yi tsukan ba amma ita kwata kwata ma ji take ta tsani Na'iman, saboda ada tayi zaton auren zai zaunar da dan nata a garin sai kuma taga ba haka ba shikenan ta fara shiga dana sanin auren wanda har hakan kusan saka sabani yayi tsakaninta da Larai, ga abunda ta gano kwanaki a dakin Alhaji cikin takardun dukiyarsa...

Na'ima na shiga dakin ta fara kuka mara sauti ta zauna kan gado, tasani Alhajin na nan bai fita ba kuma taci alwashin sai ta hadu dashi yau dan babu wani abu da zata dauka a dakin kawai zaman jiran fitowan Alhajin zatayi, aikuwa bata wani dade ba taji alamun sauqowarsa yana waya ya fita daga falon, cikin sauri ta fito daga dakin ta bishi, iddashi tayi a parking space yana waya har sannan bai gama ba sai ta tsaya tana jiran ya gama, bai dauki mintuna ba ya gama ya juyo yace "Ahh Na'ima yanzu kikazo ne, ya gidan naki" gaishesa tayi ya amsa sannan ta ja face mask din fuskanta ciwukan fuskanta duk suka bayyana, kafin yayi magana sai ga Hajiya ta fito, juyawa Na'ima tayi ta kalleta sai da zuciyarta ya tsaya na wasu daqiqu ganin Bilal abayanta shima yana tahowa, hankali adan tashe Alhaji yace "meya samu fuskarki haka Na'ima?" kasa magana tayi sai Hajiya tayi saurin cewa "wai faduwa fa tayi a bandaki jiya shine tazo ta nuna mana" Alhaji ya sake kallon Na'ima yace "subahanallah garin yaya haka ta faru" sai Na'ima tayi qasa da kanta wasu hawayen na cikowa a idanunta, Alhaji ya juya ya kalli Bilal yace "kana kula sosai Dan Allah son" sai ya sake kallon Na'iman yace "sannu Na'ima Allah ya kare na gaba" Hajiya tace "ita ce ai yakamata tana kulan, banda rashin nutsuwa kawai sai ki fadi a bandaki da girmanki" shidai Bilal sai kallon Na'ima yake yanajin ranshi na qunaa, Alhaji yace "duk ba wannan ba yanzu dai son ka wuce da ita asibiti a wanke ciwon nan babu dadin gani" ciki ciki Bilal ya amsa da "toh" sai ya kalli Na'ima yace "ki samoni a mota" ya qarasa magana tareda sallama a iyayen nasa, cikin tararradin Na'ima ta musu sallama Alhaji na sake mata sannu har da Hajiyan ma dan ganin idon Alhajin, sannan ta bi bayan Bilal din zuciyarta na bugawa, saida ta shiga motan ya tada suka fice daga gidan Alhaji ya kalli Hajiya yace "sai naga kamar batada lafiya ma, ko an samu qaruwa ne?" da sauri Hajiya ta kallesa sai tayi masking fuskan nata da murmushi tace "ze yiwu, ai kasan yanzu wata kunya ta qaro, nikuma na fada mata ba sirikarta bace ni" Alhaji na murmushi yace "Allah yasa muji alheri" azuciyarta tace "ba Amin ba" a bayyane tace "Amin" tana murmushi.....
A hanyarsu ta komawa Bilal baice da Na'iman qala ba Kuma har sannan ji yake kamar ya shaqeta ko zai huta ma shikam, kiran wayansa akayi ya dauka tareda sakawa a handsfree, Stella dake dayan bangaren tace "Baby har zanyi fushi bazaka kulani ba" yace "in kina biye Nasir zamu samu matsala sosai kinsani" cikin shagwaba tace "dagaske ne ya ganka

23 / 25