Chapter 18 Reading Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc Arewa Novels

Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc

Author :  Binta Musa Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   18 / 25

51K to 54K   out of 73.5K words

ga yunwa sai cinta yake a sannu, bayan ta gama hajiya tace ta dauko tsintsiya da mopper ta karkade nan falon saman, nan ma ta hau shara tana kade ko Ina hajiyan na zaune tana danna wayarta jefi jefi take nuna mata yanda zatayi mopping din, bayan ta gama ta sauqa qasa hannunta da bokatin shafa ta fito daga kitchen tace "inata jiran sauqowarki 'yar nan, zo kici abinci" da sauri Na'ima ta gyada kai tabi bayanta hannunta riqe da bokatin, anan kitchen din shafa ta bata shayi da biredi ta zauna tafara sha, ko kurba uku batayi ba taji hajiya ta yanko mata kira da qarfi, jikinta na rawa ta ajiye kofin shayin ta fice zuwa falon, a matakalan stairs ta ganta tsaye fuskar nan babu annuri tace "canjo ruwan da nasaki kenan" Na'ima tace "gashican Ina canjawa ne umma" hajiya tace "ba sunana umma ba" Na'ima tayi saurin gyada kai tace "toh" sai kuma ta sake cewa "inje in dauko bokitin?" Hajiya tace "tambayata kikeyi ma" nan ma Na'ima tayi saurin jijjaga kai tace "A'a kiyi hakuri" ta juya cikin sauri zata je dauko ruwan mopping din da ta baro a kitchen, shafa na bin ta da kallo har ta dauka ta fita batace komai ba....
Ranan Hajiya bata dubi qananun shekarun Na'ima ba haka ta rinqa yanko mata aiki kamar wata babba, haka ta rinqa aiki daga wannan sai wannan bata zauna ba, da rana suna aikin abinci itada shafan hajiya ta shigo kitchen din, ganin Na'ima na faman gyara hijab tana aikin wanke kayan miya yasa hajiya cewa "ki cire hijab dinnan karki saka mana datti a abinci" itadai Na'ima komai akace sai cewa "toh" takai hannu ta cire hijab din, Hajiya da shafan sukabi gashinta da kallo wanda ke dunkule an daureshi da igiyan zani da aka yaga, tun parking dinda anty Amarya tayi mata da zata zo ne akanta jikinta kuma sanye da wata kodaddiyar atamfa, ganin hajiya na kallonta yasata kai hijabin kanta da nufin? daurashi sai hajiyan tace taje ta dauro dankwali ta dawo,
Haka suka rinqa aiki itada shafa kuma dayake ta dan saba da wahalan sai bai wani dameta ba, komai akasata yi take cikin azama?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? gashi tayi hakuri da yunwan cikin nata bata tambayi shafan ta bata guntun biredin nata na dazu ba, bayan sun gama shafa ta fita kai abincin dining tadawo ta cigaba da hada juice din kankana, Na'ima na nan zaune an saka mata abincin a plate tanaci a hankali, data gama sai ta miqawa Na'iman tray me dauke da jug tareda kofuna tace ta kaiwa su hajiya suna can dining area, wanke hannunta tayi ta karba ta nufi fita daga kitchen din, da hajiya ta fara tozali sannan wani farin saurayi da bazai wuce shekaru 24-25 ba yana nan zaune gefenta yanacin abincin shima, sai Na'ima taji shakkar qarasawa gurin nasu gudun hajiya tayi mata fadan batayi daidai ba, dago kai saurayin yayi yadan tsaya kallonta hannunta riqe da tray, juyawa yayi ya kalli uwar tashi yace "who is she?" Hajiya bata dago kanta ba tanacin abincin tace "mahaifinka ne ya debo ta daga qauye jiya" yasake juyowa ya kalli Na'ima sai kuma ya daga wani cup nan gefensa ya miqo mata alamun ta zuba masa abun hannun nata, da saurinta ta qarasa ta zuba masa yana bin zara zaran yatsunta da kallo, bayan ta zuba masa yana kallonta yace "shekarar ki nawa" Hajiya ta dago kai ta kallesa tace "Bilal....." ya juyo yana kallonta ta jijjaga masa kai alamun bataso, ta kalli Na'ima tace "je ki gama aikin dana saki" Na'ima ta juyi ta koma kitchen din Bilal na bin bayanta da kallo...

Alhajin da Na'iman bata sake ganinsa ba kenan a gidan sai da tayi kwana biyar dan da sassafe yake fita sai kuma dare can yake dawowa kasancewar dan kasuwa ne babba sai ya zamto har tafiye tafiye yana yawan yi akai akai, a 'yan kwanakin nan Na'ima ta gane shayi ruwa ne a fagen aiiki gurin hajiya, zuwa sannan ma bata ganin Bilal a gidan dan inta San ya fito cin abinci ma zamanta takeyi? a kitchen ko dakinta har sai taji ya tafi, abincin dare daman can falon saman yawanci shafa take kai masa shida hajiyan..
A rana ta biyar din ne tayi sa'ar samun Alhaji a falon lokacin da taje gaishesu, Bilal na kishingide kan kujera yana danna waya ya dago ya kalleta, ganin Na'ima yasa alhajin cewa "Ayya daughter kinyi ta cigiyata ko" Na'ima tayi murmushi ta zauna nan qasa kan carpet ta gaishesu Bilal na kallonta, amsawa sukayi har da hajiyan, Alhaji yace "yau dai zanyi waya inji batun makarantar nan, nadan shafa'a wallahi" ya kalli hajiya yace "kuma baki tunamin ba" Hajiya ta dan juya kai tace "nazata kana sane toh" yace "wallahi na manta, I'll talk with sufi anjima se yazo ya kaita su mata interview" Hajiya ta gyada kai, ya sake cewa "ba'a siyo mata kaya bane, what is she wearing haka" ko ci kanka hajiya batace ba ta juya kai tana kallon tv, ganin bazata kulasa ba yasa shi dauko waya yayi transfer din kudi nan zuwa account din hajiyan yace "ki aika ko shafa ta siyo mata kayan anjima" sai sannan ta gyada kai ta juya gurin Bilal tace "Babana akawo maka shayin nan?" ya jijjaga kai tareda cewa "bazan sha ba dai hajiya" cikin lallashi tace "ayya bakaci komai ba dai har yanzu, ko ayi maka kunun madaran?" sai sannan ya gyada kansa ya maida hankalinsa kan wayarsa, kallon Na'ima hajiya tayi tace "je ki kiramin shafa" Na'ima ta amsa da "toh" sannan ta tashi ta fice tabarsu nan zaune falon.....

Daren ranan Na'ima ta fito daga kitchen zata je dakinta Bilal ya shigo falon ta kallesa, sai lokacin ta qara lura ma harda qaramar chain ashe a wuyansa, kansa cike gashi me uban yawa ya tara da wani farin dan kunne qarami maqale a kunnensa guda daya, sauqe idonta qasa tayi ganin yana kallonta, cikin sanyin murya tace "Ina wuni" bai amsa ba yace "what's your name?" tace "Na'ima" yace "shekarunki nawa?" nan ma a hankali tace "Sha hudu" kallonta ya rinqa yi tun daga sama har qasa kafin ya wuce zuwa stairs, sai sannan ta sake numfashin da take ta riqewa tun dazu tayi saurin shigewa dakinta, cikin dare tana cikin bacci taji qarar mota alamun an shigo gidan, farkawa tayi adan firgice ta miqe Jin qarar motan da dan qarfi ta nufi window tana leqawa, Bilal ne ya fito daga cikin wata sport car anan parking space, hannunsa riqe da karar taba yana zuqa, saurin sauqe labulen Na'ima tayi gudun kar ya kamata tana leqensa, jefar da taban yayi sannan ya shiga gidan Bilal, samun hajiya yayi saye nan gurin stairs cikin kayan bacci tana jiran shigowarsa, marairaice murya tayi tace"Babana bazaka dinga haquri da fitan daren nan ba Fisabilillah, hankalina baya nutsuwa kasani har se ka dawo, haba Dan Allah" be kulata ba yazo ze wuce ta kusa da ita ta dan riqo hannunsa ganin alamun yau ma ya shawo abar, tace "muje ka cire kayan nan duk wari suke" ya gyada kai idonsa yayi jaaa baice komai ba suka wuce dakinsa dake nan falon saman shima, jibgewa nan kan gadon yayi bai cire kayan jikin nasa ba sai hajiya ce ta miqa hannu ta cire masa takalman kafan sa tana kallonsa, Alhaji ne ya shigo dakin ransa a dan bace yace "Bilal sit up and take off those cloth" Hajiya ta dan riqo Alhajin tace "easy mana, kansa ke masa ciwo dai" yace "bakiji kayan na wari bane" ta dan marairaice tace "yanzu ze cire ai" Bilal ya mirgina dayan side din gadon cikin magagi yace "Oh God" Hajiya ta riqo Alhajin tace "mutafi, da asuba ze cire kayan" Bilal ya sake riqo kansa bai ce komai ba, atare Hajiyan da alhajin suka duqa cikin damuwa suka fara tambayansa meya faru, ya bude idonsa da yayi jaa a hankai yace "ku barni nayi baccin" Hajiya ta gyada kai tareda lulluba masa blanket tace "toh shikenan sai da safe mayi magana" ta riqo hannun Alhaji suka fice, nan bakin qofar dakin suka tsaya bayan ta rufo kofan a hankali, Alhaji na kallonta yace "it's getting worse, we have to do something" Hajiya ta kwantar da murya tace "mubari zuwa safiya tukunna, sai mu sake masa fadan cikin lallami, har yanzu dai bai cika ashirin da biyar ba, da sauran sa a fagen hankali Alhaji" Alhaji ya gyada kai tareda cewa "banason yabi jikinsa muzo muna danasani ne" ta gyada kai itama tace "mubi komai a sannu tukunna, yaron nan kasani shi kadai ne farin cikinmu, tun yanzu in mukace zamu taqurasa sai ya shiga wata hanya daban kuma" a haka hajiya ta lallaba mijin nata suka koma makwancinsu zuciyarsu cike da tararradin hanyar da dan gudaliyan nasu dauko....

Washegari Na'ima taje falo gaishe da hajiya ta sameta zaune ita da shafa dake tsaye, gaishe da hajiyan tayi bata amsa ba ta cigaba da maganan da takeyi da shafa, bayan shafa ta gama sauraron saqon da hajiyan ke bata ta juya ta fice, jawo ledan gefenta hajiyan tayi ta wullo wa Na'ima a jiki tace "ga kayan nan, sai ki dena saka tsummokar nan kuma, ya isa haka" Na'ima ta riqo ledan tace "nagode hajiya Allah ya saka da alkhairy" gyada kai kawai tayi bata ce komai ba, ganin shirun yayi yawa yasa Na'ima miqewa ta fice daga falon riqe da ledarta, duk da kayan ba wasu na azo a gani bane hakan bai hana Na'ima yin murna sosai ba, ta fito da kayan da daddaya tana kallo, dinkin kaya kala shida,hijabai guda uku da takalma guda uku, murmushi ta rinqa yi tana gwadawa a jikin ta? nan gaban mirror, sai data gama gwadawa? sannan ta maidasu cikin wardrobe nacikin jakanta kuma ta adanasu suma bata zubar ba, da rana saiga sufi yazo kaita makaranta, sai lokacin ta gane ashe shine driver'n daya kawosu daga Adamawa lokacin da zasu zo garin kano, Sufi PA din Alhaji ne dan yawanci ba aikin waje ba har na cikin gida yana sashi yayi masa su, dazasu tafi hajiya na dakinta tana bacci bata fito bama...
Wata makarantar kudi Alhajin yasa aka kai Na'ima, sai baza Ido take tana kallon yaran manyan mutane a nan cikin compound din makarantan, basu wani bata lokaci ba bayan interview din a inda sukaga kan Na'iman na ja sosai, daukanta Jss 1 sukayi akan zuwa gaba dole a mata jumping dan tayi girma a jss 1 a wannan lokacin..murna gurin na'ima ba'a cewa komai, ranar uniform dinda suka bata ma kasa sakawa tayi a wardrobe, nan ta ajiye su kan gado bini bini tana kallo...
Haka rayuwan Na'ima ta kasance gidan kawunta, da shafa kadai take samun yin dogon magana dan hajiya dai qarara ta fito fili ta nuna mata bata yinta kuma, Alhaji kuma yau yana gida gobe baya qasar haka dai rayuwan take tafiya, ta fannin Bilal kuma sai tayi sati basu hadu ba dan in akace yau yashawu ma sai ya wuni a gidan yana bacci hajiya na leqashi, bayan yawan zaman falon qasa sosai saidai na sama gurin hajiya wanda nan din daman ba gurin zuwan Na'iman bane, duk dare kuma yanacan club sai daren ya tsala zai dawo yayi ta buga horn yana tada duk masu bacci a gidan, ana cikin haka Alhaji ya sake nema masa wata makarantar a qasar Europe, wata university dake nan cikin Luxembourg, dakyar suka lallabashi ya tafi hoping that a wannan karon Bilal zai maida hankalinsa yayi abunda ya kaisa batareda ya sake katse karatun nasa ba...

Watarana Na'ima ta dawo daga makaranta ta samu Kawu Ayuba nan tsaye a compound din yana jiran Hajiya tayi masa iso, yakai minti talatin a wajen tsaye bata aiko ya shiga falon ba, Na'ima na ganin kawun nata tayi saurin qarasa gurinsa tana murmushi ta gaishe sa, yana kallon ta cikin fara'a yace "Na'ima haka kika koma?" tayi dariya tace "kawu yasu umma da anty Amarya?" Yace "duk sunanan lafiya sunce a gaisheki suma suna nan tafe, zasuzo ku gaisa" Na'ima ta gyada kai still tana murmushi, duk da ba wani dadin kawun nata tajiba a rayuwa ba at least taji sanyi da ta gansa, saboda har yau zuciyarta ta kasa amincewa nan din da take zaune shima kamar gidan babanta ne..
Suna nan tsaye kawu Ayuba yace ta shiga ciki, wucewa tayi ta shiga falon, hakimce ta samu hajiya tana zaune anan falon gabanta kuma wasu laces ne nan kan table tana waresu da daddaya, ganin Na'ima yasa ta cewa "je kice baban naki ya shigo" Na'ima ta juya ta samu kawu Ayuba nan tsaye ta isar masa saqon, cikin azama ya amsa da "toh" ya biyo bayan Na'ima suka shiga falon tare, bayan sun gaisa da hajiyan inda dakyar take amsawan , kawu Ayuba yace "dama inata kiran layin yaya ne baya tafiya shiyasa na zo da kafata in sanar masa Allah ya yiwa goggo rasuwa satikai biyu da suka wuce" Hajiya tace "baya qasar yanzu tukunna" Kawu Ayuba yace "Allahu Akhbar, ashe shiyasa layin baya tafiya" Hajiya tace "Allah yaji qanta, in ya dawo za'a fada masa" kawu Ayuba ya amsa da godiya, nan hajiya tayi shiru bata sake cewa komai ba, ganin yanayin atmosphere din yasa shi cewa "toh Hajiya ni zan wuce, Allah ya qara girma" ita ta fara miqewa tace "a gaida gida" sannan ta wuce stairs Ayuba ya dan bita da kallo sai shima ya miqe, fita yayi daga falon Na'ima dake jiran taji fitarsa ta fito daga dakinta cikin sauri ta bi bayansa, anan compound din tace "baba" da dan qarfi, juyowa yayi ya tsaya har ta qaraso ta miqa masa ledan? hannunta me dauke da sabbin kayanta kala biyu da kuma tsofin datazo dasu gidan? harda takalmi kala daya da hijabi guda biyu tace "Baba gashi a kaiwa salame"? karba yayi yana murmushi yace "Allah ya miki albarka Na'ima" ta gyada kai yasake cewa "ki bi mutanen nan sau da qafa kinji" ta amsa da "toh" hawaye na kawowa idonta tace "baba yaushe zanje in ga goggo" shiru yayi be ce komai ba da farko sai kuma yace "kibari sai iyayen naki sun baki iznin zuwa tukunna kinji" ta gyada kai tareda cewa "toh" da haka sukayi sallama kawu Ayuba yabar gidan ko ruwa hajiya bata bashi yasha ba balle azo batun kudin mota kuma....

Bintu Musa ce
'?=???

ArewaPen
https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c


(' KUNCIN ZUCI ('
Na Bintu Musa


Chapter 26

A haka har Na'ima ta cika seven months a gidan kawun nata, rayuwa take cikin shiru da kunci a gidan with no one to talk to except shafa, the only place da takejin sauqi a zuciyarta daman shine in taje makaranta dan har qawa tayi a school din, watarana sun wayi gari ranar asabar bataje makaranta ba tana moping din main falon gidan, bayan ta yi Rabin aiki ta dauki bokitin zata je canjo ruwan, tanason bi ta kitchen zuwa backyard din amma tana gudun haduwa da hajiya da ke kitchen din gudun ta kyare ta akan wani laifin da batasan sa ba, a tarun lokuta Na'ima ta kanji a ranta ko Hajiyar batason ganinta ne saboda indai tana waje sai Hajiyan ta tsiro da wani abun da zata kyareta ko cikin magana ne, daukan ruwan tayi ta fita ta main entrance din falon, batakai da zagayawa baya ba maigadi ya bude kofa wata mota ta shigo gidan, tsayawa Na'ima tayi tana kallon motan, cikin sauri driver ya fito ya bude bayan motan wata babbar mace in her 70s ce ta fito riqe da sandarta na qarfe tana dan duqawa, Na'ima na nan tsaye Matar ta fara takowa gurin entrance na gidan idonta be bar kan Na'iman ba, Dan tsugunnawa tayi ta gaishe ta, ta amsa da "lafiya 'yan mata" sannan ta shige cikin gidan, sai da Na'ima ta zagaya ta debo sabon ruwa sannan ta koma falon, Nan ta samu Hajiya babba hamkince kan kujera ga Hajiya nan zaune kan carpet suna gaisawa, cikin ladabi hajiya ke gaisheta wanda Na'ima bata taba gani ba ko sanin akwai wanda Hajiya zata gani ta rusuna kamar haka ba, zata cigaba da goge gogen kenan Hajiya tayi mata tsawa "Bakiga munyi baquwa bane, fita da mopper'n nan" Hajiya babba tace "A'a barta mana tayi aikinta, ba mai aiki bace" Hajiya tace "A'a, baban Bilal ne ya dauko ta daga Adamawa wai 'yar qaninsa ce" Hajiya babba ta juya tana bin Na'ima da tayi tsuru tsuru da kallo, sai tace "toh sannu yarinya, jeki abunki" Alhaji ne ya sauqo shima ya qaraso falon cikin ladabi yafara gaishe da uwar goyon tasa, sum sum Na'ima ta bar falon bata sake komawa ba sai zuwa hantsi taji Hajiya ta kwalo mata kira daga can compound din gidan, da saurinta ta fita ta samu ashe Hajiya babban ce zata tafi su Alhajin sun rako ta, bayan Hajiya babba tayi sallama da hajiyan wadda ke ta murmushi kamar bakinta ze yanke sai Abdullahi ya bude mata backseat ta shiga shima ya shiga gaban motan da nufin ze rakata, Na'ima na nan tsaye gefen hajiya tana jiran sanin dalilin kiranta da hajiyan tayi sai kuma ta ji shiru, dagowa tayi da nufin ta sake cewa "gani Hajiya" sai taga Hajiyan tabi bayan motarsu hajiya babba dake fita daga gidan da wani irin mugun kallo, bayan motar ta gama fita daga gidan Hajiya ta buga wani uban tsuka me karfi sannan ta juyo ta kalli Na'ima, shan jinin jikinta tayi da kallon da Hajiyan ta bita dashi, sai kuma Hajiyan ta wulla mata ledan hannunta zuwa jikinta cikin bacin rai tace "ki kai dustbin" sannan ta juya fuu ta koma cikin gidan tabar Na'ima nan tsaye riqe da ledan a jikinta, data je zubar da kayan ledan ne taga ashe fruits ne dasu daddawa? hajiyan ta kawo gidan, tana ta mamakin zubarwan da hajiyan tace tayi, haka dai tayi abunda aka satan sannan ta koma falon saman dan gama aikinta, bata kai ga qarasawa cikin falon ba taji hajiya na waya cikin daga murya tana

18 / 25