Chapter 4 Reading Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc Arewa Novels

Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc

Author :  Binta Musa Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   4 / 25

9K to 12K   out of 73.5K words

kwanciyanta, da haka suka koma wani baccin
Sai wajen qarfe takwas Na'ima ta tashi ta fita daga dakin tabar nafisa dake bacci, sanin Mami na bangaren Abba yasa ta wuce nata dakin ta shiga wanka, bayan ta shirya ta sauqa babban falon dake downstairs,
hango faruk tayi zaune dining yana breakfast shikadai hannunsa riqe da waya yana dannawa, ta qarasa wajensa da murmushinta, ya dago kansa daga abunda yakeyi yace "habibtin Mami harkin tashi" taja kujera daya tazauna tace "Eh yah faruk badai har fita zakayi ba" yace "yeah, I'm swamp up with work at office these days wlh" tace "Ayya, Allah ya bada sa'a" ya amsa da Amin sannan yace "kun sake zuwa kallon wani match din keda nafisan kuwa?" Kafin ta amsa taji nafisan dake bayansu tana tahowa tace "me nafisan tayi da sassafen nan yah faruk" ta qaraso taja kujera itama faruk yace "laifi kikayi babba" na'ima na murmushi tace "he was asking ko mun sake zuwa football match" nafisa ta kalli ya faruk tace "can you believe the tickets were sold out within 24 hours" faruk yace "may be baki siya da wuri bane, first hours akafi samun tickets daman"? Zatayi magana aka kirashi video call a WhatsApp dinsa, yadan dagawa nafisan hannu yace let me take this, ya dauka yana kallon fuskan wanda ke cikin wayan yace "Good morning yaya" ta daya bangaren Ahmad ya amsa cikin deep voice dinsa yace "morning faruk, ya mutan gidan?" Faruk yace "Alhamdulillah" Ahmad yace "Good...I've send you some papers via email, I need your review on them" faruk yace "sure, ba matsala yaya" nafisa tazo bayan faruk tasako kanta tace "Good morning yaya" Ahamd ya amsa "lafiya nafisa, yaushe kika dawo?" ta amsa da "jiya,yasu mamma?" Na'ima dai na sauraronsu tana binsu da kallo, saita samu kanta da sauraron na cikin wayan jin yanayin accent dinsa that was so thick and it sounds British but not that deep British.
Bayan sun gama gaisawa Ahmad ya maida hankalinsa kan faruk yace "please do take a good look on them I need answers, karka dau lokaci" faruk yayi murmushi yace "in Sha Allah yaya, I'll drop by tomorrow to give you the feedback" Ahmad yace "see you then,thanks Man" sukayi sallama nafisa na kallon faruk tace "wai yadawo gari daman" faruk yace "ya rigaku dawowa ma" tace "ya Adam fa?" ya amsa "wannan yana gari da dadewa ma ai, what's with the questions?" Tadan daga kafada tace "I just want to know ne" . Na'ima ta miqe ta wuce kitchen tabarsu nan suna magana.
Shiganta kitchen tasamu lantana tana aikin hada breakfast dinsu ta gaishe da Matar da kana ganinta kasan she's in her late 30's fuskanta cike da bille. Na'ima tace "mama sannu da aiki,Ina kwana" lantana ta amsa "lafiya habibitin Mami, jiya kun dawo bananan ko" Na'ima tace "Eh mama, ya hakuri Kuma Mami tace an muku rashi" lantana tace "wlh dai,can suleja naje, yar wata qanwata ce ta rasu,yarinya qarama da ita, jiya kwanana hudu acan" na'ima tace "Allah sarki, Allah yasa mai ceto ce" lantana tace "Amin habibitin mami, bakiga yarinyar ba kuwa fara sol kamar ke dinnan, abundai abun tausayi" na'ima tayi murmushi ta fara tayata aikin, suna aikin lantana na bata labarai gameda rasuwan wanda itadai na'ima ba fahimtan wasu take ba, nafisa ta shigo itama suka gaisa lantana na fada mata uzurin rasuwan, bayan nafisa ta gama nuna nata alhinin? tace "mama kince zaki soya mana gyada mai gishirin nan idan zamu dawo" ta qarasa maganan tana taya lantana bare maggin da zata saka a pepper soup dinda ke dahuwa nan gabansu, lantana tace "aikuwa yau zan soya muku"
Nan suka kammala sauran aikin tareda lantana, Mami ta shigo kitchen din bayan sun gama tace "sannu lantana,sannunku kuma" suka amsa.
Ta dauki breakfast dinsu ita da Abban ta tafi kaiwa can falonsa while su nafisa suka kai nasu dinning lantana na tayasu, basu jima da fara ci ba su Al'ameen da Abubakar sukayi joining.

Bayan sun gama suka kai kayayyakin kitchen suka dauraye, don ladabtarwan mami ne akan bakomai mai aiki zatayi musu ba,abubuwa da dama dakansu sukeyi a gidan. bayan sun gama nafisa ta fice, na'ima ta dauko plate ta debi sauran cupcakes dinda mami tayi musu jiyan ta wuce upstairs, shiga dakin nafisa tayi ta sameta gaban madubi zaune, na'ima ta tafi ta zauna kan gadon nafisan dake gyare neatly ta ajiye snacks din hannun nata tace "oya..spill the beans, meya hadaki da umar din jiya?" Nafisa ta baro gaban madubin tadawo bakin gadon itama ta zauna tace "sis I don't know what is wrong with Umar, bansani ba ko jealousy ne ko kuma insecurity ne yake damunsa, kai duka ma" na'ima tace "Amma ai so ne yasa hakan sis" nafisa tace "Ina sonsa ai nima but this is too much and i hate it with all my heart, sometimes I wonder why i stayed with him for this long and why i can't let go" na'ima tace "I know that loop, kinsani...I know what it means to be trapped In a loop going around without escape" nafisa tace "But...." Sai kuma tayi shiru tana kallon Na'ima tarasa abunda zatace
Na'ima tayi dan murmushi me ciwo tace "shiyasa bazan taba judging dinki ba akan wannan conflict relationship din da kuke having, the guy loves you and you do too, try and resolve things tunda kowa yasani ba iya rabuwa zakuyi ba" ta qarasa tana murmushi. Nafisa ta dau cake daya takai baki tace "tabdi, rabuwa kai, jiya ma nace masa I'm done yayi fushi kuma nakashe wayana" Na'ima ta jijjaga kai tana dan cin cake din itama tace "nidai banason ku rabu, Ina laifin mai kishinka nafisa?" Nafisa ta miqe ta koma bakin madubi tafara cleansing fuskan ta tace " I'm serious this time" Na'ima ta jijjaga kai tana dan dariya kawai, ta janyo laptop din nafisa dake kan bedside drawer ta kunna zata fara kallo.

Wattpad: Bintu Musa @bintuuu02

('KUNCIN ZUCI('
Na Bintu Musa

Read my book "KUNCIN ZUCI" on ArewaPen, Platform available: "all" :: https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c

WhatsApp group =?G?
https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z

Chapter 09

A Week Later...
Na'ima ce zaune cikin dakinta akan gado, hankalinta yana kan abunda take typing cikin laptop dinta, yau satinsu daya da dawowa gida and a lot has happened, sunje shopping, nafisa ta jasu outing cikin gari and all other fun things, jiya ma part dinsu ya farukn dake gefen main building din gidan suka wuni suna game din ps wanda har da Al'ameen da Abubakar din sukayi.
Nafisa ce ta shigo dakin hannun ta riqe da leda ta miqa mata, karba na'ima tayi tana duban cikin ledan taga sweets da chocolates masu yawa, nafisa tace "karki fado sunana idan mami ta kamaki kinasha wlh" na'ima tayi dariya sanin Mami ta hanasu yawan shan kayan zaqin, farkon dawowansu ta barsu sunasha amma ganin suna iya shanye chocolate kusan ashirin a zama daya tace bataso, karsu sake siyo kayan zaqi masu yawa a gidan.
Nafisa tace "ki shirya muje gurin fitting dinnan meerah nata kirana a waya" na'ima tayi mata questioning look tace "fitting kuma?" Nafisa ta amsa "na gown din da zamu saka wajen event din bikin salma mana" Na'ima tace "nifa bazanje event ba nafee" zama nafisan tayi kusada ita tace "meyasa? Mami ta hanaki ne" ta jijjaga kai tace "a'a kawai bazanje bane" shiru nafisa tayi batace komai ba har na'ima ta maida hankalin ta kan laptop din dake kan cinyanta ta cigaba da typing, can nafisan ta miqe ta fita na'ima ta bita da kallo jikinta na sanyi.
Fitan nafisa ta shiga falon mami ta sameta nan zaune da faruk suna magana, turaren wutane gaban mamin tana mixing dinsu cikin kwalba, nafisa taqarasa kan kujeran gefen faruk ta zauna
Mami tace "baby baku fara shirin fitan bane rana tanayi fa, kincemin zaku fita dazu" faruk yace "Ina zasuje?" Nafisa tace "dama fitting zamuje gurin meerah na gown din event din bikin, Mami kinji Na'ima nacewan bazataje gurin dinnern ba" Mami ta dago kanta daga abunda takeyi tace "ai daman ban aika kayan events da ita ba" kafin nafisa tayi magana faruk ya katse ta da "Ai tafiki hankali datace bazataje ba" nafisa tace "haba yah faruk it's just event fa" yace "yes but nafee kinsan kalan mijin da salma zata aura ai, you know who he is, yawanci guys masu ji da tashe acikin Abuja da wajenta zasu halarci event din, you can't be exposing na'ima to that sort of places" Mami dai na sauraron fadan da faruk yakewa nafisan batace komai ba, nafisa tace "but yah faruk i thought it's high time she starts living her life, doing the things she likes the way she wants to" Mami tace "Many things but not this nafisa, and you know things are not over yet" Nafisa na kallon Mami tayi shiru batace komai ba, Mami ta cigaba "quite sure zataje gidan bikin ta gaisa da wasu 'yan'uwan because it'll be rude of her not to,tunda komai dadewa zasu iya haduwa da ita a cikin gidan nan, but not going to parties...and that's final" nafisa tace "Yes Mami" ta miqe ta fice daga dakin suka bita da kallo.

Haka suka shirya Na'ima zata raka nafisan gurin dinkin, cikin abaya na Na'ima black while na nafisan maroon color, bayan sunyi sallama da Mami ta basu saqon toiletries da zasu biya super market su siya mata, suka fice a motan nafisan.

Bayan sun isa babban fashion store din wanda yakasance gurin dinki, designing da kuma saida dinkakkun kaya suka tadda meerahn tsaye a reception tana magana da receptionist din nata, ganinsu na'iman yasa ta tako garesu tana murmushi tace "look who we have in town" ta qaraso tayi hugging din nafisa suna fara'a sannan ta juya tayi hugging din Na'ima tasake cewa "I've been waiting for you guys like for'everr" na'ima na murmushi dan tasan meerah, ita tayi mata duk dinkunanta farkon zuwanta gidansu nafisa, Nafisa tace "sorry sis" meerah na fara'a ta amsa da "now you have to pay me double" sukayi dariya gaba daya ta jasu suka tafi fitting room din,bayan tayi serving dinsu ruwa na'ima na zaune kan resting sofa wasu staff mata guda biyu suka shigo tare da meerah suka hau gwada nafisa dake tsaye kan gajeran stool, nafisa tace "husna tazo kuwa?" Meerah tace "tazo almost a week now"

Bayan angama sukayi salla a shagon dinki sannan suka wuce gurin aiken da mami ta musu, basu suka dawo ba sai yamma.

Shigowarsu gidan bayan sunyi parking Na'ima ta lura da wata baquwar mota, wata sleek ride dake fake nan parking space din, suka fito Nafisa ma data lura da motan tace "Su yaya Ahamd sunzo kenan" suka wuce cikin gidan hannun nafisa riqe da ledan kayan da suka siyo.
Shigarsu falon Na'ima ta hango Mami zaune da wasu maza biyu zaune kan kujera sunyi backing dinsu, dayan yana having conversation da Mami while dayan yana riqe da waya a hannunsa yana kallonsu mamin, qarasawa sukayi cikin falon nafisa na gaba, Mai maganan yadan dago ya kallesu yace "Nafisa" ta amsa da "Yah Adam sannunku da zuwa" yace "yauwa" Mami tace "baby kundawo" nafisa tace "eh Mami" Suka qarasa nafisa ta ajiye kayan gaban Mami sannan suka zauna kan kujera kan Na'ima na qasa, Nafisa ta sake cewa "Yaya sannunku da zuwa, Ina wuninku" Ahmad ya dago cikin husky voice dinsa yace "lafiya nafisa" shima Adam ya amsa, Cikin sanyin murya Na'ima tace "Ina wuni" tadaiji Adam ya amsa amma mai deep voice din da ake kira da Ahmad dinne bataji ya amsa ba, tadan dago kanta ta kalleshi, Caraf idonta cikin nasa yana nazarinta.
Kauda idonta tayi da sauri ta maida kallonta kan tv dake falon tanajin bugun zuciyarta acikin kunnenta, Tunda take bata taba ganin idanun da suka mata kaifi takasa jure kallonsu kaman na bawan Allahn nan ba. Shima Ahmad dauke idonsa yayi yana cigaba da danna wayarsa, Mami tace "kadai ce bazaka dawo gida ba Ahmad, ka riqe Lagos ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?dinnan har dawowa yana maka wahala" Ahmad ya juya ya kalli Mami a nutse yace "akwai wasu abubuwan danakeson nayi settling ne acan mami" Mami tace "ai zamanka dai anan din yafi,tunda can din bawai iyali ka ajiye ba" ta cigaba tareda juya wa tana kallon Adam "kaima Adam baka fada masa gaskiya ko" Adam yayi dariya yace "nima gajiya nayi da fada masa gaskiya, may be yanzu zeji taku Mami" Mami ta maida hankalinta kan Ahmad tace "Ai mamma tacemin kunyi maganan kuma har yanzu baka dawo ba" Ahmad yadan shafa kanshi yace "in Sha Allah za'ayi yanda kuka ce din Mami"
Itadai na'ima duk ta taqure acikin falon kaman ace cass ta arce, Adam ya juyo yana kallonsu yace "nafeen Mami yaushe kika dawo?" Nafisa da tunda ta gaishesu ta maida hankalinta kan waya ta dago kanta tana murmushi tace "for a week now yaya" yace "Ma Sha Allah, kin kusa gamawa amma" ta gyada kai tace "Eh saura 4 to 5 months haka" yace "Allah ya bada sa'a" yana kallon Na'ima da tun dazu idonta ke kan Tv bata juyo ba yace "Mami baquwa kukayi ne" Mami ta amsa da "Eh 'yar dan'uwana ce dake can Nijar,tare suke karatun da nafisan ma" Adam yace "Allah sarki" Mami tace "zo ku miqamin kayan sama in na shigo zan waresu" na'ima ceh farkon miqewa kamar wanda falon ke mintsini, Ahmad yadan dago ya sake kallonta ta qarasa ta karbi kayan, nafisa tace "to yaya sai anjimanku" suka amsa da toh, tabi bayan na'ima da har ta isa stairs, suna shiga falon mamin nafisa tace "ke yanzu naga texts din mutumin bari kiga" Na'ima dataji duk kafafunta a sanyaye ta nemi kujera ta zauna anan falon tana tuna idanun wannan bawan Allah data baro a falo, nafisa ta qaraso kusa da ita tana nuna mata wayan tace "Kiji wai yanzu ma yana hanya zaizo" cikin sanyi na'ima tace "kibarshi yazo sis, you have to settle fadan nan naku once and for all" nafisa tace "Allah ko?" Na'ima ta gyada kai, shiru nafisan tayi kamar me nazarin wani abu sannan ta miqe ta tafi dakinta,diban kayan na'ima tayi ta dorasu kan table din dake nan falon sannan ta fice tana ture duk wani tunani daga ranta.

Bintu Musa ce
'
('KUNCIN ZUCI('
Na Bintu Musa

Read My Book "KUNCIN ZUCI" on ArewaPen::https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c

WhatsApp group =?G?
https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z

Chapter 10

Daren ranan after maghrib suna zaune falon Mami itada nafisa, ipad ne a hannun Na'ima tana game don tunda suka dawo gidan bata bude wayanta dake ajiye cikin box dinta ba
Hira sukeyi jefi jefi da Mami dake zaune itama tana kallon hiran da akeyi cikin tv a tashar BBC, Mami tace da nafisa "baby kina jira sai nace kije ku gaisa da iyalan uncles dinki ko?" Nafisa ta dago daga danna wayan datakeyi kwance a kujera tace "Mami I thought tunda za'ayi bikin nan basai naje bafa" Mami na kallonta tace "ke tunaninki bazai baki kije ku gaisa kafin ku hadu a gurin bikin ba ko, for a week now na zuba miki Ido ai" nafisa tayi shiru batace komai ba Mami ta cigaba "gobe ki shirya kuje tareda Na'ima ku gaishe su and that's final" Nafisa ta amsa da "Yes Mami"
Mami ta maida hankalinta kan Na'ima data ajiye ipad din nata jin mamin na magana tace "Habibti, gobe kuje gidansu baba ku gaishesu" cikin sanyi na'ima ta amsa da "toh Mami in Sha Allah" bayan sunyi sallahn ishansu nan falon tareda mami,sauqa sukayi downstairs suka bar Mamin
Zama sukayi anan falon nafisa na turo baki ita a dole abunda Mami ta sa suyi bai mata dadi ba, Na'ima ta kasa shiru tana murmushi dan yanayin nafisan dariya ma yabata tace "Nafee it's just ziyara fa, what's the harm in that? Beside, ba kince yayun Abba bane sudin" Nafisa ta bata rai tace "Eh..amma Mami ce take taqurawa sai munje alhalin su ba wani zuwa gidan nan suke ba,
tunda muka dawo kinga yaran gidan sunzo gaisheta ne?.." Na'ima batace komai, Nafisa ta cigaba " har gwara ma su yaya Adam da anty Fatima sai dan dama dama husna, Amma 'ya'yan anty da mummy fa bawanda yake zuwa gaishe da Mami" Na'ima da bawai saninsu tayi ba, tanadai jin labarin su wani lokaci a bakin nafisan, tace "yaran anty sune twins da Salman da za'ayi bikin nata ko?"
Ganin na'ima ba wani saninsu tayi ba yasa nafisan cewa "Kinga yaya Ahmad,wanda sukazo rannan to shine babba a gidan baba, forget it bari na miki dalla dalla, su Abba su hudu iyayensu suka haifa that is Babba sai Abba sannan Daddy and last dinsu Anty Amnah, to gidan baba yanada mata biyu da mamma sannan anty, yaran mamma sune yaya Ahmad,Anty Fatima,Husna sannan hafsa saikuma yaran anty wanda Salma itace fari sannan twins safiyya da sumayya" Na'ima ta gyada kai alamun fahimta at the same time idanun Ahmad neh suka fado mata arai tayi stiff tana tuna yanda yake kallonta dazu.
Nafisa ta cigaba "sai gidan Daddy kuma, kinga yaya Adam shine babba wanda shi mahaifiyarsa ta rasu so practically he was raised by mamma tareda yaya Ahmad, Mummy ce Matar Daddyn ita kadai, ita kuma yaranta akwai anty murja,anty ummi sannan Laila ce autarsu, to anty Amnah kam kinsanta ai" Na'ima ta gyada kai tace "Nagane" nafisa tace "Mami itadai kayi ta zuwa gaishesu kamar wa'enda akayiwa mutuwa" Na'ima tayi murmushi tace "to ai 'yan'uwankune nafisa, yazama dole" Nafisa tace "ni ba gidan Baba bane banason zuwa, gidan Daddy ne, mummyn ce ba sauqi a lamarinta" yar dariya Na'ima tayi tace "kijiki sai kace wata sa'arki" Dariya itama nafisan tayi tace "bazaki gane bane"
Abba ne ya shigo tareda samarin gidan dawowansu daga masallaci kenan su na'ima suka gaishesu, nan kowa ya nufi dinning don yin dinner Mami ta sauqo itama, Na'ima ce tayi serving dinsu, don tun farkon zuwanta gidan Mami kan sata itama tayi serving a table din so that she could feel at home, hakan yazame musu al'ada ko ita ko nafisa sune servers in an zauna cin abinci, Abubakar ne ya? bubbude flask din ganin babu tuwo yace "anty yau ba'ayi mutuminki tuwo ba" Na'ima data koma ta zauna tayi

4 / 25