Chapter 20 Reading Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc Arewa Novels

Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc

Author :  Binta Musa Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   20 / 25

57K to 60K   out of 73.5K words

ya waiwayi gida kuma bai tashi dawowa ba saida tsara ba babba..Hajiya daman ta shiryawa zuwansa dan an tabbatar mata yananan kan hanya kwana kusa...
Ranar da ya dawo, kwatsam su Na'ima suka ji shigorwa motarsa gidan a lokacin tana kitchen tana dafa abinci, bayan wasu lokuta shafa ta shigo cikin kitchen cikin sanyin jiki tace "Na'ima je ki kai wa Bilal ruwa yana falo, bari mu dora masa wani abu cikin sauri"
Gyada kai Na'ima tayi ta debi drinks daga fridge ta fice zuwa kai masa, zaune ta samesa Hajiya na tsaye kansa bata zauna ba, duk wani annurin fuskanta ya dauke ganin irin rakiyar da Bilal din ya samu, wata mace ce gefensa nan kan kujera, bleaching duk ya cinyeta da kitson attachment wanda yakai har mazaunanta tareda dogin nails da eye lashes, irin mata masu kama da ashawon Lagos dinnan dai masu BBL wanda in sun zauna mazaunansu sai yaci rabin kujera...toh ita Bilal ya kawo gida kuma kyam take kallon Hajiya dan Hausa ma ba isarta yayi ba,? qarasowan Na'ima wajen itama saida ta tsaya kallon wannan mace dake manne gefen Bilal kamar ta shige jikinsa, ajiye ruwan tayi cikin sanyin jiki ta dago sukayi Ido hudu da STELLA,? cikin sauri Na'ima ta sauqe idonta tanajin idon stellan ya mata kaifi dayawa......



https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c

WhatsApp group
https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z


('KUNCIN ZUCI('
Na Bintu Musa

Chapter 27


Cikin sanyin jiki Na'ima ta nufi hanyan kitchen bayan ta ajiye ruwan, aranta tana ayyana yau kuma wace irin drama za'ayi a gidan dan itama kanta Na'iman a dan zaman da tayi a gidan na 'yan shekaru tasan Hajiya ba mace bace me son a rabi danta ko da wasa, shiganta kitch???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?en din shafa ta juyo tace "kin kai musu ruwan" Na'ima ta gyada kai, shafan ta sauqe numfashi cikin jimami ta sake cewa "Allah ya kyauta dai" Na'ima batace komai ba suka hau aikin abincin tare babu wanda ya sake cewa komai cikinsu dan kowannensu da abunda yake saqawa arai..
Hajiya na tsaye nan kansu Bilal sai kallonsu take with confusion, dakyar ta zauna cikin sanyin jiki nan kan kujerar dake facing dinsu ganin Bilal yaqi kallon idonta, daukan juice daya yayi ya tsiyaya a cup ya miqawa Stella dake dan murmushi a Hajiyan, yace "Ina wuni Hajiya" fuska a dinke Hajiyan ta amsa da "wannan fa? wacece Bilal?" sai Stella ta duqar da kanta kadan alamun ladabi tace "inah woni ma.." ko kallon inda take Hajiyan batayi ta sake tambayan Bilal da "Babana a ina kasamo wannan?" Bilal yace "Hajiya tana gaishe ki fa" tace "ba matsalata bane wannan, a ina kuka hadu har ta rakoka gida" Bilal yace "Girlfriend dina ce, mun kwana biyu tare da ita and mun fara maganar aure ne shiyasa muka yanke shawaran ta fara zuwa ku ganta tukunna" Hajiya ji tayi a lokacin kamar ta kai mangari a dan nata tukunna, tace "toh ita mahaukaciyar ina ce dan kun fara maganan aure sai ta biyo ka gida" Bilal yayi saurin cewa "tana dan Jin Hausa da hajiya, mamarta 'yar nasarawa ce" Hajiya ta juya ta kalli Stella dake kallonta kyam cikin Ido,? ta bude baki zatayi magana sai ga megadi ya shigo kinkime da akwatuna, sanin kayan bana Bilal ne kadai ba yasa Hajiyan miqewa tace "muje sama muyi magana, da kai kadai kuma" ya juya yace da stella "Baby im coming" stella ta gyada kai tareda cewa "ina jiranka fa" gyada kai shima yayi duk Hajiya na kallonsu cikin mamaki, danne zuciyarta tayi ta nufi stairs Bilal din yabi bayanta suka bar Stella nan zaune tana bin bayan hajiyan da wani mugun kallo, dauko juice din tayi ta sake tsiyayawa a cup ta cigaba da kurba tana bin falon da kallo....

Isarsu Saman ko zama basuyi ba Hajiyan ta juyo tace "sakayyar da zaka mana kenan Bilal, wai me yasa bakason kaga hankalina ya kwanta ne a koda yaushe" Bilal ya matso yace "wallahi inasonta Hajiya, Stella tanada kirki sosai sai kin zauna da ita zaki gani" Hajiya ta ware ido tace "au har zama zamuyi da ita kenan, tukunna ma da ka kawo kayanta cikin gidan kana nufin anan zata zaune kenan, a wane gidan bahaushe ka taba ganin anyi haka, Bilal meyasa kullum burinka kasamun ciwon kai ne" ya kwantar da murya tareda cewa "na fada mata hakan tun acan, toh batada kowa a Kano ne shiyasa nakawota nan din ai hajiya" jijjaga kai Hajiya ta fara sai ga stellan ta shigo falon cikin kashe murya tace "Baby i need to pee" cikin masifa Hajiya tace "yau naga jaraba, duk? dakunan qasan bazakiyi fitsarin acan ba sai nan, ki fitaaa nace" Stella ta kalli Bilal tace "Bilal what is this? You promise me they are going to like me" Bilal ya nufeta hankali tashe zeyi magana Hajiya ta mulmulo zagi ta hada da "dan uwarki ki bar gidan nan, dan iskanci har gida zaki biyomin da saboda gidan ku babu tarbiya" Bilal yace "Haba Hajiya, meya hakan kikeyi kuma" kawai Stella ta juya ta nufi fita daga falon Bilal yabi bayanta da sauri, daskarewa Hajiyan tayi nan tsaye sai can ta nemi guri ta zauna batasan me ma zata fara tunani ba..
Na'ima ta fito daga kitchen zataje dakinta taga stellan ta fito cikin sauri zata nufi kofa tana cewa "I can't stay here" Bilal dake biye da ita a baya be ma kula da Na'iman ba yace "Baby wait..." Tsayawa kallonsu Na'ima tayi har suka fice daga falon Bilal be daina cewa wait din ba, sauqe numfashi tayi sum sum ta wuce dakinta cikin sanyin jiki, saida ta koma daki ta danyi uzurirrikan ta sannan ta fita backyard din gidan debo kayanta da ta wanke dake nan kan igiya, muryoyunsu ta rinqa jiyowa a nan parking space na gidan, Bilal ya kwala kira a megadi yace masa yaje ya debo kayan da yakai cikin gidan, shima cikin sauri ya wuce ciki yin abunda aka saka sa, bayan Na'ima ta koma daki tana zaune kan gadonta tana linke kayan nata tajiyo tashin motarsu Bilal din sun fice daga gidan...
Da suka gama yin abincin sai shafa ta miqa mata na hajiyan tace ki kai mata sama ba lallai yau ta sauqo ba, Na'ima ta gyada ta nufi can din riqe da tray din, shiganta falon ta samu Hajiya na waya hankali tashe, muryarta har rawa yake? tana cewa "wallahi banga ta zama ba larai, anyi ba ai ba ne wannan, na kirenye'n yaci sa amma kuma na menene harda dawowa gida da kilaki, nashiga uku ni ladi" sai tayi shiru tana sauraron larai daga daya bangaren, kasa qarasawa Na'ima tayi tana sauraron wannan abun al'ajabin, Hajiya da idonta ya fara kawo ruwa ta cigaba da magana cikin tashin hankali? tace "komawa gurin dan hauren zamuyi Larai, dan wallahi a yanayin yanda naga ya bita ba qalau yake ba, ni dama bahaushiya ce shine zan samu sauqin bullowa al'amarin, amma irin arnan nan tsorona kada ta kaimun da gurin 'yan shan jini" ta sake cewa "toh shikenan sai kin fito goben, ki fito da wuri Dan Allah nima Alhajin bayanan" da haka ta ajiye wayan tana dafa goshi, dan gyaran murya Na'ima tayi tareda sallama Hajiyan ta juyo cikin sauri tana kallonta, Na'ima tace "ga abincin Hajiya" tace "ajiyeshi nan ni tsk" haka Na'ima ta ajiye abincin tanajin wani irin ta juya ta fice, zama tayi akan gadonta tana tariyo maganganun hajiyan cikin mamaki...
Washegari ko breakfast Hajiya batayi ta sauqo nan falon cikin shirinta harda face mask, Na'ima dake sharan falon ta dago kai tana kallonta, fadawa Na'iman tayi "in shafa ta fito kice mata akwai kayan wanki na dana hada ta wanke" Na'ima ta amsa da "toh" tabi bayan hajiyan da kallo ganin ta fice da sassafen kuwa...
Bayan Na'ima ta gama aikace aikacenta taci abinci sai takoma dakinta ta kwanta dan ta dan ta huta, madadin tayi bacci sai ta hau tunani kuma, rayuwarta tafara tariyowa tiryan tiryan daga sanda akace yau mahaifiyarta ta mutu zuwa lokacin da mahaifinta ya bita shima, hawaye taji yana kawowa idonta takai hannu ta share still bata daina tunanin ba, tananan kwance tajiyo qarar bude gate aka shigo falon, muryan Sufi taji yana gaisawa da shafa sai ta miqe tasaka hijaba tafita, bayan sun gaisa ne sufi yace mata ta shirya sannan ta debo takardunta ze kaita makaranta suyi screening....

Stella ce kwance akan gadon cikin dakin hotel da suka kama nan cikin garin kano, saida ta tabbatar Bilal ya shige wanka sannan ya kuma rufo qofan sannan ta dauko wayanta ta fice balcony na dakin nasu tayi kira, daga daya bangaren qanwarta me suna chiamaka ta dauka suka gaisa cikin yaren pidgin sannan stellan ta fara bata labarin zuwanta gidansu Bilal din, duk ta cikin yare suke maganan dayake hausan bawani kwarewa sukayi acikinta ba se ya zamto sunfi yin yaren Igbo da pidgin in suna tare, chiamaka'n ce tace "toh datace ki fitan ke kuma se kika fitan kenan?" Stella tace "ai gashinan muna tare dashi anan hotel tunda na baro gidan, kuma na rantse sai naga dama zata sake ganinsa ma" chiamaka tace "ai daga hotel din ku taho Lagos abunku, ita tasan wahalan da kikasha akan dan nata ne gurin rabashi da mata da har zata miki rashin mutunci, har yau fa bamu gama biyan cikon kudin me maganin ba Stella" gyada kai stella'n tayi tace "zata san ni ta zaga, itada Bilal se gani a nesa yanzu kuma, dama ta barni a gidan at least zata rinqa kallonsa ma akai akai" chaimaka tace "yanzu kin shafa masa wancan din?" Ta amsa da "Eh" sai chiamaka ta sake cewa "toh yaya zakiyi da wanda akace kisa cikin katifarsa"? Stella tace "tunda ba zama zamuyi ba zan bar wannan din kawai" , da haka sukayi sallama ta dawo dakin daidai Bilal din ya fito daga bandaki daure da towel, ta qarasa ta rungumesa tayi masa kiss a kumatu tace "Baby im so tired of this place, we have to go back to Lagos" Bilal ya gyada kai tareda cewa "it's okay, but you have to meet my parents again when we come back next time" ta gyada kai tana qara riqesa aranta tana cewa "there won't be a next time"........

Weeks Later.....
Zuwa wannan lokacin Na'ima ta samu admission dinta na makaranta har sun fara cuku cukun fara registration wanda duk Sufi ne ya shige kan komai yanda Alhaji ya umarcesa, dan zuwa sannan Alhaji ya dawo gari, duk wanda ya kalli Hajiya a wannan lokacin yasan tana cikin damuwa saboda yanda duk tabi tasawa kanta damuwan rashin dawowan Bilal har sannan tun wannan fitan da yayi daga gidan tareda Stella, har wata yar rama Hajiyan tayi sai tunani kuma, dayawan lokuta in Na'ima taje gurinta zata sameta tayi nisa cikin tunani kuma, gashi har lokacin malamin nasu yayi buge bugensa ya bata assurance na cewan Bilal din zai dawo gidan da qafarsa ta kwantar da hankalinta saboda akwai abunda yake cin danta kuma za'a karya sa da sannu... Ranan suna zaune da Alhaji suna magana tace "yanzu Fisabilillah rashin dawowan yaron nan gida baya damunka?" Alhajin yace "ladi kinason dagawa kanki hankali, yaron nan fa aikinsa ya koma ya cigaba da yi, mun samu ya nutsu yana aikin yanzu sai kice ba haka ba" idon Hajiya ya kawo hawaye tace "Amma aiki ne shine baze waiwayi gida ba, kana gani wayata ma be cika dauka ba, sannan Alhaji da mace fa yadawomin gidan nan, Mace faaa, kuma arniya" Alhaji ya kwantar da murya yace "daya kawo macen sai ki tsaya ki sauraresa ai, ke fa kikace mubisa ta lallami, ai bawai an haramta aurensa da yarinyar bane, sai ki tsaya ki fahimci yaya alaqan yake, sannan wace irin yarinya ce" masifa tafara tana cewa "A'a wallahi, banda kirista Alhaji, zai dawo gidan nan ya sameni ya gama zaman Lagos din kenan, kuma gaskiya ka dawomin da dana cikin garin kano da aiki hakanan, aure kuma 'yar uwarsa bahaushiya zamu aura masa bawani zance wannan fitinanniyar yarinyar, wallahi baze yiwu ba" Alhaji ya tsaya kallonta na wani lokaci sannan ya sauqe numfashi yace "I'll talk to him then" tace "Ahtoh, ba ita tayimin naqudar dana ba wallahi bata isa baa" Alhaji yace "duk me ya kawo wannan maganar Kuma?" Tace "nidai fada nake, baze yiwu ba wallahi, yarinya me tarbiya zan aura masa in Sha Allah" Alhaji ya gyada kai sannan ya miqe sai kuma tace "kunyi finalizing takardun can dinne " ya gyada kai batareda yace komai ba, ganin alamun ransa ya baci ne yasa bata tambayesa abunda ke cin ranta ba, dan satikan da suka wuce Alhajin ya fara kammala duk wasu dukiyansa zeyi finalizing Will din sa a ajiye (yawancin masu tarin dukiya sukan rubuta will dinsu tareda shaidun lauya ko lauyoyi sannan a ajiye koda me dukiyan zai riga iyalinsa mutuwa, a lokacin ne za'a ciro takardun a kuma karanto kason kowa da me dukiyan yayi niyyan badawa) toh hakan ce ta faru ta fannin Alhaji, kuma duk yanda hajiya tabi na sanin ko kadan daga cikin mind dinsa yaqi bata daman haka...

Lamuran makarantar Na'ima ya kankamaa sosai tasamu admission nan Bayero University har sun fara registration, wanda duk Sufi dinne ya shige mata gaba takeyin komai, a lokacin da time table dinsu ya fito ta sanar da Alhaji yayi mata addua sosai yace duk wani abun kudi da ya kama na school din ta rinqa magana da Sufi ze bata, godiya ta masa sosai tanajin dadi hakan har ranta, Hajiya ko bi takanta ma batayi ba da taje mata da batun makarantan, itama tana ta kanta, sai yawon bala'i da suka sako kai itada kawarta larai, yau sune nan gobe sune can, sunyi chanjin malamai sunkai uku adan tsakanin nan abu yaci tura har lokacin Bilal muqut kakeji ba labarinsa Stella ta kammale abunta..
Ranan Na'ima ta je falon Hajiya kai wa larai ruwan sha, tasamu suna zancen nan dai da suka saba Hajiya na cewa "kinji nayi rantsuwa larai, wallahi ko zanyi yawo babu kaya sai na raba Bilal da yarinyar nan, kuma indai Ina numfashi bazai aureta ba, ke indai ina numfashi Bilal baze auri wadda yake so har ransa ba, bazan raini dana na tsawon lokaci dayawa a rayuwa wata banza can ta rabani dashi sama ta ka ba, inaaaaa" Larai tace "Gaskiyarki kawataaa Kuma kedai muzuba Ido akan wannan din, aikinsa sosai yake ci kinsani tunda Bilal yana daukan wayanki akai akai yanzu, da sannu komai ze zo qarshe" Na'ima ta kawo ruwan ta kafin ta ajiye Hajiya ta harareta tace "ke fita muna magana" tace "toh" sai kuma ta gaishe da larai dake bin ta da kallo ta juya ta fice, Larai tace "kefa kawataa ga maganin matsalarki a gida kina gani amma idanunki sun rufe" Hajiya ta kyabe fuska tace "mene?" Larai tace "yarinyar nan mana da kike riqo, kiwon ki ce sai abunda kika ce tayi zatayi, kuma kince Bilal din ba wani kulata yake ba ai ke hakan yazo miki a daidai" Hajiya ta sake cewa "bangane ba kawata, fitomin a mutum" dan matsowa Larai tayi tace "kinsan fa malamin nan yace yaron nan yana dawowa gida ayi gaggawan yi masa aure sai mu bar masa sauran aikin ze ji da komai, da kike ikirarin zakiyiwa Bilal din aure toh wa kike nufin aura masa da toh?" Hajiya tayi shiru tana tunani, ganin haka yasa larai cigaba da magana tace "na daya ba son yarinyar yake ba, na biyu kince daga kauye kawunan ta suka baku ita a gantale, na uku ke kika riqe yarinyar sai yanda kikaso zata tafiyar da Bilal, na hudu batada rawan kai da magana..toh me kikeso bayan nan" Hajiya tace "Allah ko..yanzu tayaya zan bullowa lamarin toh?" Larai tace "matso in miki dalla dalla"......

Ranar da Na'ima zata fara zuwa lecture tun asuba ta fara aikace aikacen gidan tana dokin zuwa school din, ita kadai tana aikin tana murmushi, bayan tayi wanka ta dauko gogaggun kayanta da hijabi dogo data ajiye wanda zata fara zuwa aji dasu, data shirya din ma a gaggauce taci abincin anan kitchen sannan ta nufi falon su Alhajin dan tayi musu sallama, bata samu Alhajin ba sai hajiya dake zaune tana kallo, tsugunnawa tayi nan qasan carpet ta gaishe da hajiyan, amsawa tayi tana bin ta da kallo wanda yasa Na'iman duk ta taqura, sai tace "makarantar zakije ne?" Na'ima tace "Eh" tace "Toh Allah ya bada sa'a Na'ima, Allah yasa kufara a sa'a" dan daskarewa Na'ima tayi Jin yau Hajiyan nayi mata addua akan abunda ya shafi rayuwanta sai kuma ta amsa tareda miqewa ta nufi fita daga falon Hajiya na bin bayanta da kallo...
Rataye da class bag dinta taje hall din da zasuyi morning lecture din, bayan ta samu guri dan baya haka malamin ya shigo, nan ya fara bada darasin Na'ima ta maida dukkan hankalinta tana sauraro kuma tana joting key words a qaramin takardanta, sai sa suka kwashe 2 hours kafin malamin ya fita, Na'ima ta dan yi miqa tana hamma na gajiya, yan class dinne suka fara fita da daddaya Na'ima ta dan kwantar da kanta akan desk ta rufe idanunta kamar me bacci, ji tayi a jikinta kamar ana kallonta sai ta bude idanun nata, Ido hudu tayi da wata budurwa yar baqa haka dake opposite dinta tana kallonta at the same time chocolate ne a hannunta takai baki tana gutsura bata daina kallon Na'iman ba, dan gyara zama tayi ta miqe zauna tana kallonta, ganin Na'iman na kallonta kyam yasa ta dan daburce tafara murmushi sai kuma ta miqowa Na'ima chocolate din hannun nata alamun ta karba, murmushi ne yazowa Na'iman bata shirya ba ganin wai miqo mata chocolate take kamar wata yarinya qarama....

Bintu Musa ce
'? =???

https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c

WhatsApp group
https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z


(' KUNCIN ZUCI ('
Na Bintu Musa


Chapter 28

Sake miqo mata chocolate din budurwar tayi sai Na'ima ta jijjiga kai har lokacin murmushin be bar fuskanta ba tana mamakin wannan baiwar Allah, kawai daga ganinta sai miqo mata chocolate, sai tace "A'a nagode" budurwar ta sake cewa "Allah kisha, yanada dadi sosai" daga hannu kadan Na'ima tayi alamun "A'a" , kafin yarinyar ta amsa mata

20 / 25