Chapter 2 Reading Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc Arewa Novels

Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc

Author :  Binta Musa Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   2 / 25

3K to 6K   out of 73.5K words

Na'ima ipad din, karba tayi taga fuskan mama akan wayan tana mata murmushi tace "Habibti ina kika baro wayanki inata kira"
Na'ima ta amsa "yana daki ne, ina kwana Mami" tace "lafiya lau na'ima,kun tashi lafiya" kafin ta amsa Abubakar dan autan Mamin ya sako kanshi ta bayanta yana gaisheta, Na'ima ta amsa tana murmushi tace "Abu yau bakaje school bane" yace "jiya muka gama Waec anty" Nafisa ta matso tace "Kai dalla ka bawa Mami wayan su gaisa" Gwalo Abubakar ya mata , Na'ima tayi dariya sanin draman da suke kwasa a tsakaninsu tace "rabu da ita,saura Neco yanzu ko" yace "Eh" tace? "Allah ya baku sa'a"? ya amsa da Amin yana matsawa fuskan Mami ya shigo tace "daughter ba wani matsala ko?" Na'ima tace " A'a babu komai"
"Ma Sha Allah,ku rinqa karatu fa kunji" ta amsa da "toh Mami in Sha Allah" Mami tace "Allah ya taimaka yayi albarka" bayan ta amsa sukayi sallama ta miqawa nafisa itama sukayi sallaman.

Na'ima ta gama hada musu breakfast sunaci anan kitchen din dayake akwai kujerun zama jikin kitchen island din nafisa tace "yau zamuje wajen taron movie premiere a London" Na'ima tace "Really?..wane movie ne" nafisa tace "British movie ne,Lauren ta siya mana tickets ashe tun last week" hankalin na'ima na kan plate din abincinta tace "then me zakujeyi awajen toh" nafisa tace "ita zataje for her content nima dai sort of that,kizo muje it'll be fun"
Na'ima ta juya ta kalleta tana ware ido tace "waaa?..school zan tafi yanzu ma ina gama cin abincin nan" Nafisa tace "muma fa sai mun gama morning lecture tukunna, it'll be fun I'm telling you" Na'ima ta girgiza kanta tace "Bazan je ba"

Tuesday..
Tsaye take a balcony na apartment din nasu dake 4th floor cikin 10-story building. Bayan tadawo daga school kadaici ya dameta a gidan ta fito nan don tasha iska, tana tsaye daga inda take tana hango wucewan mutane da dama a street din nasu, Most at times batason zaman shiru sosai in Nafisa batanan, takan nemi wani abu da zeyi keeping dinta busy to abstain herself from thinking.
Wasu couple ta hango suna tafiya suna dariya, Na'ima ta bisu da kallo har suka wuce, ta dago hannunta tana kallon wani tabo dake tafin hannunta
qurawa tabon ido tayi tanajin zuciyarta na karyewa abubuwa da dama suna dawo mata cikin kanta , digar hawayenta akan tafin hannunta ne yasa tayi saurin goge idonta tabar balconyn takoma cikin falo , dauko mopper tayi ta fara tattare gidan tana gogewa.
Ranar har bandakin nafisa saida ta wanke , ta sake rearranging din wardrobe dinta dana nafisan ta dafa musu rice and stew, kuma duka ayyukan nan din tayi ne don kawai tasamu something to keep her mind off, something that will abstain her from thinking too much.

Ranar juma'a suna zaune a falo da safe suna hira jefi jefi sun saka skin face mask, na'ima tana karatu a ipad dinta aka kira nafisa, tashi zaune nafisan tayi daga kwanciyar datayi kan kujeran a fili tace "yah faruk" Na'ima tabar abunda take ta juyo, amsa kiran nafisa tayi suka gaisa sai kuma ta miqe da sauri ta leqa balcony, ihun da tayi ne yasa Na'ima ajiye ipad din da sauri ta bita balconyn itama tana duban street din
Yah faruk ta hango jikin mota a gefen street din maqale da waya a kunne yana dago musu hannu, ware idanu tayi ta rufe bakinta da hannu saboda mamaki, buga kafa nafisa tafara yi tana ihun murna batareda damuwan mutane na dago kai suna kallonsu ba, Yana dariya ya matsar da wayan daga kunnenshi Jin tana ihu, da gudu nafisan ta koma falo tayi hanyan fita kayan bacci neh jikinta me dogon hannu da dogon wando ta fice da sauri.
Na'ima ta dawo falon ta tsaya tana murmushi don har ga Allah itama tayi murnan zuwansa don yah faruk mutuminsu ne kuma yayansu....An investment banker sannan first born a gidansu nafisa,shine wanda nafisa take bi, daga ita sai Al'ameen da yake makaranta a Toronto Canada sannan last born dinsu Abubakar. 'ya'ya hudu yan gata wajen Mami da Abba sai Na'ima da suka hada ta zama cikon ta biyar acikinsu.
Tananan tsaye a falon taji beep din password suna kokarin shigowa, da sauri ta juya ta koma daki don dauko hijab itama kayan baccin ne jikinta dan tunda sukayi sallah asuba suka koma bacci nan falon, tashinsu ne bayan sunyi brush sunyi breakfast nafisa ta tsiro musu da saka face mask kafin suyi wanka
Bayan ta sako hijab din tacire face mask din ta dawo falon, suna zaune nafisa sai zuba take kamar gyada, na'ima ta qaraso ta zauna kanta a qasa ta fara gaisheshi tana murmushi
Amsawa yayi shima yana murmushin sai kallonta yake ganin duk ta chanja from the broken girl he once knew, cikin tsokana yace "Habibtin Mami" miqewa tayi tana sunne kai cikin kunya ta wuce kitchen don kawo masa abun sha
Nafisa tace "ya faruk I thought direct flight to Abuja ko Lagos zaka bi daga can Paris din fah" ya juyo yana kallonta yace "what's that on your face?" Sai lokacin nafisa ta tuna da abunda ke fuskanta ta fara dariya tana cirewa.
Na'ima tadawo falon riqe da plate with snacks,drinks and bottle water ta jawo tabe zuwa gabansa ta dora akai ta koma ta zauna suka qara gaisawa yana tambayansu karatunsu

Hira sukasha sosai nan falon cikin raha, a dan zaman da tayi can gidansu nafisan ta fahimci yah faruk mutum ne mai kirki da son 'yanuwan sa, ga kyauta da fara'a, shekara shida ya basu itada nafisan ayanzu da suke cikin shekarunsu na ashirin da hudu
Ganin hiran taqi qarewa especially yanda nafisa take ta zuba yace "toh yanzu dai ku shirya zan koma London tare daku, anty Amnah tace intaho mata daku" nafisa tace "dama fa gobe muke shirin zuwa" yace "Nah..ku shirya mutafi yanzu dan nima goben nakeson wucewa gida" nafisa ta turo baki "haba yaya, kabari sai Sunday mana" yace "a'a ai nazo naga lafiyarku" ya juya yana kallon Na'ima yace "ko habibtin Mami" tayi yar dariya tana kauda idonta tace "kayi kokari yaya mungode sosai" yace "yauwa...ku tashi ku shirya karku dau lokaci please" suka miqe kowacce tayi nata dakin suka barshi nan falon ya miqe yafara kashe kayan wuta na gidan.

Wattpad: Bintu Musa @bintuuu02

('KUNCIN ZUCI('
Na Bintu Musa

Read my book "KUNCIN ZUCI" on ArewaPen, Platform available: "all" :: https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c

WhatsApp group =?G?
https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z


Chapter 04

Basu wani dau lokaci ba suka Isa London,suka dau hanyar gidan anty Amnah dake arean Kensington.
Anty Amnah likitace kuma tana auren babban likita mazaunin London da yaransu twins maza kimanin shekaru bakwai. Sunyi murnan ganinsu sosai, twins sai tsallen murna suke.
Bayan sun huta anty Amnah tayi serving dinsu abinci sunaci ana hira

Daren ranan suna bisa gado cikin dakinsu wanda suke sauka idan sunzo gidan, Na'ima na zaune ta miqe kafanta hannunta riqe da ipad dinta twins suna kwance jikinta suna game tare, Kiran Abba ne yashigo wayan ta dauka da sallama tana gaisheshi, amsawa Abba yayi ta dayan bangaren tareda tambayanta ya karatu,tace? "Alhamdulillah Abba" yace "hope babu wani matsala" tace "Eh" yace "Ma Sha Allah, ku dage da karatu Na'ima,banason wasa" tace "in Sha Allah,nagode Abba" yace "Ina nafisan" ta amsa da "gatanan" tana miqawa nafisa wayan, bayan sun gama gaisawa da Abban taji nafisan na tambayan ina Mami,?
Suna cikin maganan dinki da Mamin ta miqo mata wayan bayan ta saka a handsfree, bayan sun gaisa Mami tace "Na'ima ga kayanku nan ansiyo wanda zaku saka a bikin, inason aika muku wajen me dinkin nafisan bansan wani kalan dinki kike so ba kuma" cikin sanyin murya Na'ima tace "kowanne kalla yayi" Mami tace "A'a badai kowanne kowanne kala ba,saka wayan a handsfree" Nafisa dake gefe tace "a handsfree yake fa Mami"
Mami tace "yauwa kinaji nafisa, ta fada miki kalan wanda takeso din sai ki turawa meerahn, nidai zan aika kayan gobe sai ku gama tsakaninku" Nafisa tace "toh Mami zanyi magana da ita a WhatsApp" da haka sukayi sallama nafisa tace "Meerah never disappoint, zansa ta turomin latest one's sai mu zaba"
Na'ima bata amsa mata ba? ta karbi wayan nata ta miqawa jabeer dake kusa da ita ya cigaba da game dinda sukeyi.
Suna nan zaune anty Amnah ta shigo dakin tace "sun hanaku bacci ko" na'ima tace "a'a game ai mukeyi" nafisa tace "anty ya faruk bai dawo ba?" tace "A'a" don tunda yakawo su nafisa aka taba hira dashi ya sake ficewa akan akwai gurin da zaije.
Anty Amnah tace "Boys, it's time for bed" jabeer yafara kukan shagwaba akan shifa a wajensu na'ima sai kwana tace "my friend get down from that bed" Na'ima tace "anty kibarsu mu kwana anan din" anty Amnah tace "a'a zasu takuraku, oya muje" Haka ta tusa kansu suka bar dakin tana musu saida safe.

Washegari suna breakfast gaba dayansu, nafisa ta saka faruk a gaba da roqon sai yayi rescheduling flight dinsa anty Amnah ma na tayata , mijinta da yake gurin yace "what if he has something to do back home" Anty Amnah tace " babu ma...beside, it's weekend. work can wait till Monday, right son?" faruk ya danyi dariya yace "zan duba available flight for Monday then" nafisa tace "zaka samu in Sha Allah" mijin anty dasuke kira uncle yasir yace yayi murmushi yace "su nafisa qorafi ya fara karbuwa" dariya tace tace "zai samu uncle"
Itadai na'ima tayi shiru tanacin abincin dake gabanta sannan tana sauraronsu, faruk ya amsawa nafisa da "I'm not sure yet" ya dauki wayanshi dake kan table din zai duba
Nafisa ta juya ta kalli Na'ima tareda kai mata qaramin bugu a kafada tace "kinaji inata faman roqo ko ki tayani" Na'ima tayi murmurshi batace komai ba tacigaba da shafawa jafar nutella a jikin bread, faruk ya dago kansa yace "habibtin Mami ko in tafi" dariya tayi kadan tace "a'a yah faruk" Anty Amnah tace "itama batason ka tafin ai, kawai nafisa tafita baki ne"
Faruk ya gama rescheduling flight din ya ajiye wayan yace "there... it's done, saiku shirya anjima mu tafi park" nafisa ta ajiye tea din hannunta tayi masa thumb up tace "you're the best" twins ma sai sannan suka fara ihun murna jin ance park

Haka suka tattara aka tafi park anty Amnah ta hada musu lunches dinsu suka saka a booth dan ita da Abban twins sunce baza suje ba zasu huta a gida.
Wunin ranan a park sukayi, acan sukayi sallolinsu suka ci abinci, faruk yasasu sun hau different wheels yana musu video sannan sunyi games kala kala shima har nafisa taci kyautan teddies ma twins, sunci banza sunci wofi dai sannan suka koma gida da yamma duk a gajiye.

Washegari wayewar sunday yakamata su na'ima su koma oxford don school, amma tunda suka tashi nafisa take mitan itafa ta gaji, bayan sun idar da sallah ta cigaba da mitan, na'ima najinta batace komai ba ta miqe tana linke sallaya.
Ganin na'ima bata kulata ba tace "sis ko mubari sai gobe?" Na'ima tana murmushi tace "Allah ya kaimu toh" dan tasan qarshenta hakan ce zata faru daman, nafisa tace "Kinga dama bawani lectures muke ba dama, it's not a big deal"? na'ima ta koma kan gadon ta kwanta tace "hakane anty Nafisa"
A gurin breakfast nafisa ta fadawa su anty Amnah bazasu koma school ba acewarta basuda wani active school activity ranan Monday din" faruk ya juya yana kallon Na'ima yace "dagasken take?" ta gyada kai tace "Eh" baice komai ba anty Amnah tasake tambayanta "na'ima are you sure" ta sake amsawa da "Eh dagaske ne anty"? nafisa tana murmushi tace "bafa karya mukeba" faruk yace "ai nasanki ne nafisa" anty Amnah tace "toh shikenan sai ku huta sosai, nima zanje hospital akwai patient dina dazan duba she's under my care" faruk yace "Ina uncle fa" tace "yana bacci tukunna, ya kwana a hospital jiya"

Yammacin ranan sai ga faruk da ticket na football match da za'ayi da dare cikin Chelsea stadium, one of the most known stadiums in London, tsalle nafisa ta rinqa yi kamar ba ita tayita mitan gajiya ba, itadai na'ima nata fara'a batasan komai gameda ball ba amma tanason zuwa taron itama don she's curious to see the match in person.

Dawuri faruk ya kaisu stadium din dan 8:00 pm za'a fara match din, bayan yayi parking a gurin da yayi booking suka fito zasu taka zuwa cikin stadium din babu anty amnah, tace batason shiga hayaniya kanta yana ciwo kuma ta gaji, shigansu cikin stadium din yayi gaba suna binsa a baya yana neman seat numbernsu. Nafisa ta juyo ta kalli Na'ima tace "Nice huh?"? Na'ima tana murmushi tace "it's beautiful..so beautiful" after sun samu gurin zamansu basu jima ba aka fara match din faruk ya miqe yace "I'm coming" yafara kutsawa cikin mutane zai fita daga stadium din, bai jimaba yadawo hannayensa riqe da popcorn da drinks ya rumgumosu a qirjinsa, zama yayi yana miqa musu yacewa nafisa "what did i missed?" ta amsa da "not much"
At first na'ima bata gane yanda wasan yake tafiya ba sai nafisa ke kwatanta mata kasancewar ita ta taso cikin maza a gidansu suna yawan kallon football match.
Cheering din mutane da ihun nafisa dake gefenta ne yafara sa mata interest sosai akan wasan, aqarshe dai da ita aka miqe ana ihu a stadium din. Ba qaramin nishadi match dinnan ya sanya na'ima ba, bakinta har kunne dan fara'a, faruk ya sunkuyo kusa da ita yana daga murya yace "do you like it?" Tana jijjaga kai cikin yar dariya tace "sosai"
Ranan taga football celebrities dinda ko a mafarki bata taba tsammanin ganinsu face to face ba, it's one of the nights that na'ima bazata manta ba.
Bayan an tashi daga match din suna komawa gida ta tambayi faruk "Kuma yanzu shikenan an kori dayan team din" yana dariya ya amsa da "Eh" ganin she's new to it, nafisa ta juyo daga front seat tace "BoBo zan siya mana tickets muje next match tunda kinaso" Na'ima tace "ai da dadi ne,bansan haka ball din yake da dadi ba"? nafisa ta juya tana kallon faruk sukayi dariya sannan ta juyo tace "welcome to the team girl"

Wattpad: Bintu Musa @bintuuu02

('KUNCIN ZUCI('
Na Bintu Musa

Read my book "KUNCIN ZUCI" on ArewaPen, Platform available: "all" :: https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c

WhatsApp group =?G?
https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

Chapter 05

Washegari da safe suka kai yayan nasu airport da motan anty amnah, hatta na'ima saida taji kaman tayi kuka balle nafisa datara fara hawaye
Faruk yace "come on girls, nan da 3 weeks or so zaku dawo fa kuma"
Nafisa ta qarasa kusadashi tariqo hannunsa tana hawaye, yana murmushi ya zare hannunsa,ya dagawa na'ima hannu alamun Bye itama ta daga nata hannun cikin sanyin jiki, ya juya na nufi cikin waiting lounge.
Na'ima tadan daga murya tace "Allah ya kaiku lafiya yaya"
haka suka koma gurin motan su cikin sanyin jiki suka bar airport din. Bayan sun koma gidan anty Amnah suka shirya kayansu tareda mata sallama suka tafi train station dan komawa oxford saboda motan da faruk din yaje daukansu na anty Amnah ne.

After that memorable weekend in London, rayuwa ta cigaba yayinda suka maida hankali kan karatunsu wanda saura few months su gama.
The weeks that follows sunyi
qoqari wajen hada wasu daga cikin thesis dinsu before the spring break, don dama auren Salman yazo within their break, hakan yasa lokacinsu yazamo swamp with schoolwork, dukda basa zuwa school din akai akai don sun shigo phase na research a fagen karatun nasu, wani lokacin raba dare suke zaune nan falo kowacce tana nata aikin bisa laptop

Duk da ayyukansu na makarantan da suka sako gabansu hakan bai hanasu zaman hira da cinye cinyen banza da hofi ba, Dan nafisa ta koyawa na'ima cinye cinyen itama basa zama shiru haka nan, aikace aikacen gidan nasu kuwa daman tun farko basu raba a junansu ba, duk wacce ta samu time yi take wanda dama na'ima ce rinjayen aikin da dafa musu abinci most at times, Kuma hakan bai taba damunta ba infact she love doing all the work tabar nafisan ta huta because she'll ba glad to do more than that to nafisa.
Ance kaso mai sonka, to hakan take wajen Na'ima, tanason kyautatawa nafisan
most at times takan shiga dakin nafisan ta gyara ko Ina ta wanke toilet sannan ta debo kayanta na wardrobe ta goge mata su tas ta jera. Wani irin bond ne mai tsafta a tsakaninsu wanda in ba wai sani kayi ba bazaka taba cewa qawance ne mafarin haduwarsu ba. Gashi dai ko daga yanayinsu mutum zaiga banbancin dabi'a sosai yayinda na'ima ta zamo mara hayaniya,don in kaga tana dogon surutu to da nafisa ne, ga hakuri da shanye komai a ciki while nafisa mutum ce mai surutu da rashin hakuri a wasu lokutan,
But friendship blend them together and became sisters from different mothers.

As lokacin tafiyansu gida yana kusantowa sai Na'ima ta zamo so uneasy ta zamo wata sanyi sanyi har nafisan tafara ganewa amma batayi mata magana ba saboda wasu dalilai
Ana gobe zasu tafi, na'ima na dakinta tayi wanka tana zaune gaban mirror tana shafe shafen ta na al'ada, bayan ta gama tacire hulan wankanta tana kallon kitson da sukaje saloon aka mata ta dauko wani hair oil tafara shafawa acikin lines na kitson tana tunani, bayan ta gama ta maida hulanta tasaka kayan baccinta ta hau gadon,ji tayi ta kasa baccin, ta jawo laptop dinta dake bedside drawer shima zata dan duba ko zai dauke mata hankali, shima tana dannawa ne absent minded, daga karshe kawai ta miqe ta tafi kitchen
bude cupboard tayi ta debo chocolates da cheese balls ta fito ta nufi dakin nafisa
Samunta tayi ta dora box dinta akan gado tana gaban wardrobe tana zaben kayanda zata koma gida dasu, Na'ima ta shigo ta zauna kan gado tana cewa "wai dama baki gama hada kayan naki ba?" Nafisa na tsaye ta kama qugu tana nazarin kayan wardrobe din tace "sai na hada sai kuma inji badasu nakeson tafiya ba" na'ima tace "Allah ya shiryeki nafee, hada kayan ma saikinyi ruwan ido bayan tulin kayanki da kika baro can gida" Nafisa ta juyo tace "Hey...it's not my fault, I want nice and big collections" Na'ima tayi murmushi tace "ruwan ido dai,bawani nice

2 / 25