Chapter 11 Reading Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc Arewa Novels

Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc

Author :  Binta Musa Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   11 / 25

30K to 33K   out of 73.5K words

Ahmad can't handle a messed up person like me" Nafisa ta dan dafa kafadanta tace "Haba Na'ima...kiyi living rayuwanki, ki ajiye duk wani batun abun da ya faru a baya ko wani auren da kika tabayi, idan anzo wannan ramin Ina tabbatar miki zaku tsallaka tare indai yana sonki, yaya Ahmad mutumin kirki ne kuma kinsan shine the right person da zai iya standing up to mahaukaci irin Bilal dasu Hajiya" Na'ima ta jijjaga kai hawaye na kawowa idonta tace "kinsan nakasa yarda har yanzu baisan inda nake ba nafisa, bansan me yake shiryamin ba kuma tunda yace duk inda naje sai yadawo dani gidansa" Nafisa tace "wannan ne kuma bai isa ba, shidin banza, Allah ya fisa wallahi, ki kwantar da hankalinki babu abunda zai faru" Na'ima tayi shiru tana kallon kofar gidan anty Amnah, Nafisa ta riqo hannunta tace "mu shiga sis, babu komai, shi bai isa ya hanaki son wanda kikeso ba wallahi" Na'ima ba biye da ita batace komai ba suka shiga gidan...
Zaune suka samu Ahmad shida anty Amnah a falon ga twins a kusadashi, suna hada Ido da Na'ima taga murmushi yayi mata sai ta samu kanta da maida masa murmushin itama, zama sukayi nan falon suma suka gaishe sa ya amsa idonsa akan Na'ima da itama kallonsa take jefi jefi, twins ne suka bar jikin Ahmad suka dawo jikinta, Jafar ya miqa mata popcorn din hannunsa akan taci, diban biyu tayi takai baki, anty Amnah tace "anyi wankin kan?" suka amsa da Eh, hawa jikin Na'ima jabeer yayi ya ja gyalen abayan nata atake gashinta ya bayyana yace "anty muga naki" ta dan ware Ido zata karbi gyalen Jafar dake jikinta ya ja ribbon din shima yace "anty naki yayi kyau", Anty Amnah tadan musu tsawa tana cewa "wallahi zan saba muku in baku daina wannan haukan ba, my friend maida mata gyalenta" saurin karban gyalen Na'ima tayi ta maida kanta, ribbon din kuma ta riqe a hannunta kunya duk ta rufeta ta juya ta kalli Ahmad da tunda abun ya faru yake kallonta, dauke ido tayi ta miqe zata tafi daki, yabi bayanta da kallo, nafisa ma miqewa tayi? ta dunguri twins din daya bayan daya tace "marasa ji kawai" Anty Amnah tace "sai na mammakesu tukunna, wato kun rainata ko" hakuri suka bawa maman tasu suka koma jikin Ahmad da baice komai ba yananan zaune yana danna wayarsa....

Ranan Monday sun tashi zasuje school suna breakfast anty Amnah tace "jiya yayanku yace zai turo akaiku school din aiki sun dan riqesa bazai samu kaiku ba" Nafisa tace "Anty a yanayin aikinsa in mukace yakaimu makaranta ai mun taqurasa daman" Anty Amnah tace "nima hakan na fada masa" Na'ima batace komai ba tana sauraransu while tanacin abinci gabanta..
Drivern da Ahmad din ya aiko ne ya kaisu har cikin makarantan yace musu zai shiga cikin town din akwai uzurin da zeyi sannan yadawo daukansu, suka amsa da "babu damuwa" ...
Bayan Na'ima ta hadu da zara sukaje library duban wasu takardu ne take fada mata yanzu tana London da zama ba oxford ba saidai zata rinqa qoqarin zuwa suna research din nasu tare in Sha Allah, dayake itama zarahn tana yawan zama a London din tace mata karta damu zasu rinqa haduwa acan ma bawani abu..

Bayan sun koma ne ranar Thursday da safe sai ga kiran zarahn a wayan Na'ima akan tana cikin London din su hadun.
Na'ima ta shirya cikin black abayanta dayake sanyi yadan fara sauqa sai ta saka jacket din da laptop dinta cikin jakanta na goyon kafada, Nafisa na kwance a gadon tana duba wani littafi hannunta riqe da chocolate tace "Dan Allah na'ima karki manta da dunuts dinnan, zan kiraki ma" Na'ima ta gyada kai tana zuge jakan tace "zan siyo miki dai bazan manta ba" Nafisa ta sake cewa "Dan Allah ki siyo na gurin da mukaje ranannan yafi dadi wallahi" gyada kai Na'ima tayi ta miqa hannu ta wafce chocolate din hannun Nafisa tasaka a jaka tana murmushi tace "I'll take this" Nafisa tace "naji..nidai karki manta" sallama sukayi Na'ima ta fice, study room din Abban twins ta shiga tasamu anty Amnah zaune nan gabanta akan desk din kuma laptop ne da wasu manyan takardu tana dubawa , qarasawa ciki tayi a nutse tace "Anty zanje study group meeting" Anty Amnah ta dago tana cire glass din idonta tace "Okay,? zarahn tana garin nan din ne" Na'ima tace "Eh itama tana zama gidan yayanta" gyada kai anty Amnah tayi tace "Toh..hope dai zaki fita da wayanki" Na'ima ta amsa da "Eh" taciro wayan daga jaka ta nuna wa antyn, Anty Amnah tace "yauwa daughter, ki kiramu fa if something came up, London is a big city, be careful, Allah ya bada sa'a" Na'ima ta gyada kai ta amsa da "Amin" sannan ta fice..
Uber dinda tayi booking ne yazo ya dauke ta har nan qofar gida inda take tsaye, A wani babban shahararren Cafe ta hadu da zarahn, hugging dinta zarahn tayi tana fara'a dan tanason Na'iman tun farkon haduwansu a school din, kawai Na'iman ce bata yawan kulata, a wani seat dake lungu suka zauna suna facing din juna, saida suka gama gaisawa zarah tamusu order na mocktail, da waitern ya kawo musu Na'ima ta tambayesa wifi password din su ya fada mata dan sunsan cafe din yana offering free wifi ne ma shiyasa sukayi deciding su hadu anan din, nan take suka bude laptops dinsu suka fara abunda yakawosu, suna discussion din sannan suna rubutu..
Hankalin Na'ima yayi nisa cikin abunda take typing zarahn ma haka, saida takai qarshen abunda take rubutawa din ta dago hannunta tana matse yatsunta da suka danyi tsami, bin Cafe din tafarayi da dan kallon ganin mutane sun dan cika wanda bata ma lura da hakan ba.

Idonta ne yafada cikin na Ahmad yana kallonta while yana sipping coffee, zaune yake da wasu maza su uku shi cikon na hudu yana facing din table dinsu Na'ima, tun shigowansu ya ganta amma hankalinta na kan laptop din gabanta bata lura ba, jefi jefi yake kallonsu while suna dan magana da abokan nasa, sai yanzu idon Na'ima yakai garesa...jitayi komai nata ya tsaya da irin kallon da yake mata, itama sai ta tsaya kallonshi, coffee din hannunsa ya ajiye still yana kallonta, zarah ta dan tabo ta sannan ta dauke idonta tace "Uhm" zarah tace "what happen?, you seem lost" Na'ima ta girgiza kai tace "No.. it's nothing" zarah tace "take a look at this, I don't understand this line" ta qarasa maganan tana juyo fuskan laptop din nata ma Na'ima, bayan Na'ima ta karanta suka fara magana akai, bata sake yarda ta kalli inda Ahmad yake ba,

Miqewa su Ahmad din sukayi bayan sun biya tab dinsu suka nufi hanyan fita Na'ima ta dan kallesa taga magana yake hade da murmushi shida daya daga cikin abokan nasa, fita sukayi tana kallonsu sannan ta maida hankalinta kan abunda takeyi
Saida suka sake spending wani 40 minutes din cikin Cafe din sannan suka fara tattara kayansu zasu tafi, sunje biyan kudin abunda sukaci ne akace musu ai an biya musu, zarah ta tambayeta waye ya biya, Na'ima tace mata yayanta ne..

Fitansu daga cikin Cafe din ta hangoshi tsaye jikin motansa hannunsa daya cikin jacket din jikinsa while dayan yana duba wayansa, dago kai yayi ya kalleta sai ya gyara tsayuwansa itadai duk ta tsaya tana kallonsa, zarah ta tambayeta ko shine yayan nata, ta gyada mata kai sannan suka qarasa gurinsa zarah nata fara'a ta gaishesa ya amsa shima babu yabo babu fallasa, sallama tayi da Na'iman ta tafi, Na'iman na daga mata hannu sannan ta juyo ta kallesa, murmushi kawai tayi a nutse tace "for how long kake tsaye?" Shima yana kallonta? yace "ban dade ba" tace "kun kusa kai hour da fita fa" ya dago hannunsa ya duba wristwatch dinsa sannan yace "bansan lokacin ya tafi haka ba" dan girgiza kai kawai tayi batace komai ba tana murmushi, shima murmushin yayi bai ce komai ba, can kuma a hankali yace "I'm still making you uncomfortable ko" Na'ima tadan turo baki tace "nafa baka hakuri ranannan" yadanyi dariya yace "I like that you feel this way around me" juya kanta tayi tana murmushi, ya miqo mata safunan hannu daya ciro cikin aljhun jacket dinsa yace "here, put this akwai dan sanyi yau din" karba tayi tafara sakawa ta kalleshi tace "kaifa?" ya girgiza kai kawai baice komai ba, bayan tagama sakawa ne ya dan matso yana kallonta a hankali yace "you're beautiful Na'eemah", maganan nashi yayi taking nata by suprise ta kallesa tana murmushi, ya rinqa kallon idanunta shima yana murmushi yace "you have beautiful Eyes" ta kai tafin hannunta ta rufe fuskanta tana dan dariya, ji yake kamar ya kamo hannun nata amma sanin bazata so hakan ba yasa beyi ba, sai yace"Ina wayanki fa" ta bude fuskan nata takai hannu jakanta ta ciro wayan ta miqa masa ya karba, dama babu password akai daya bude, yayi danne dannensa saiga kira yashigo wayarsa sannan ya miqa mata wayan ta karba, a hankali yace "that is my number, kiyi saving kinji" Na'ima ta gyada kai tana kallon numbern,yana kallonta ya sake cewa "kin gama karatun yau din?" ta amsa da "Eh" sai yace "Okay let me take you home" sannan ya bude mata front seat din ya karbi jakan kafadan nata, saida ta shiga sannan ya miqa mata jakan ya rufe motan shima ya zagaya ya shiga, zai kunna motan aka kirasa a waya yace da Na'ima "sorry, I have to take this" ta gyada kai, daukan kiran yayi yafara amsawa a nutse, sai bayan ya gama wayan ya juyo yace mata "akwai inda zakije ne kafin gidan" ta girgiza kanta tace "A'a" sai kuma a hankali yace "zaki rakani office inyi wani qaramin uzuri kafin in kaiki gidan" Na'ima ta kalleshi tace "akwai Uber ai" yace girgiza kai yace "No" ta sake cewa "it's okay, i understand aikine yataso maka ai" sai yayi qasa da murya yace "ban gaji da kallonki ba" sai suka tsaya kallon kallo, ta dauke idonta tace "ba gashi ka kallenin ba" ya sake cewa "bangaji ba" , tada motan yayi suka dauki hanyar office branch dinsu dake nan London, babu wanda yasake cewa komai a cikinsu, bayan sun isane Na'ima ta fito tana dan bin tall building din dake gabanta da kallo, Ahmad yafara tafiya tabi bayansa sai kuma taga ya tsaya ta qaraso suka jera atare suna tafiya suka shige cikin building din, office dinsa na 10th floor saida suka shiga elevator ya kamo jakan kafadanta yace "me kika saka a jakan, babu nauyi ne" ta gyara zaman jakan tace "babu nauyi" riqo jakan yayi ta sake masa ya sakala a kafadansa, sunzo wuce secretary dinsa daya kasance namiji ya miqe yana gaishesa, Ahmad ya amsa suka qarasa bakin office din nasa, da yatsansa ya bude door din suka shiga Na'ima nabin office din da kallon ganin komai na cikinsa black and white ne, ta tsaya bata qarasa ciki ba yatafi ya ja labulayen dake jikin glass wall din haske ya bayyana ko ina wanda kana tsaye daga inda kake kana kallon komai na city din, juyowa yayi ganinta tsaye yace "Babe kizauna mana" nan ma sunan yayi taking nata by suprise ta dago ta kallesa taga shi gurin fridge ya nufa ko a jikinsa, qarasawa tayi ta zauna a dogon kujeran dake lounge din office din, ruwa ya dauko da Apple juice me sanyi ya kawo mata, saida ya tsiyaya mata a cup ya miqa mata ta karba tareda cewa "thank you" takai bakinta, zubawa kanshi yayi shima a cup tareda zama? a kujeran da take yabar gap a tsakaninsu, bayan ta ajiye cup din tana kallonsa tace "the interior looks unique and beautiful" ya dan bi office din shima da kallo yace "you like it?" Ta gyada kai tana dan murmushi, sai yace "zanje meeting room yanzu bazan dade ba zan dawo" batace komai ba kanta a qasa, yayi qasa da murya yace "Babe" ta dago kanta? ta kallesa ya sake cewa "bazan dade ba, i promise" sai ta gyada kanta kawai, ya miqe ya wuce gurin executive table dinsa ya dauki wani takardu ya nufi kofan fita tana kallonsa, shima saida ya juyo ya kalleta sannan ya bude kofan ya fice..Sauqe numfashi Na'ima tayi aranta tana ayyana meyasa to bata tafi gidan bama ta biyosa, a fili tace "get a grip Na'ima" sai kuma tayi murmushi ita kadai, tajawo qaramin pillow dake kan sofan ta kwanta taciro wayanta tana kallon numbern sa, rasa da wane suna zatayi saving tayi amma tsaf ta haddace nombobin a kwakwalwarta, tananan kwance shiru bai dawo ba tafara gyangyadi a sannu kuma bacci ya kwasheta...
Meeting ne na gaggawa ya riqe Ahmad gashi shine head, anayin meeting din hankalinsa na gurin Na'ima, duk ya rasa nutsuwarsa ma a dole yake zaune yana sauraron turawan dake dakin suna magana, saida sukayi spending 1 hour kafin atashi, yayi sallah ya aika personal assistant dinsa ya siyo masa lunch sannan ya koma office din, ganinta nan kan sofa tana bacci yasa shi qarasawa a hankali yana kallon fuskanta tana baccinta cikin kwanciyan hankali, komai nata burgeshi yake tun daga kan idonta har yatsun kafanta, miqewa yayi Jin zuciyarsa na rinjayarsa dayawa ya cire jacket din jikinsa ya lulluba mata , ajiye ledan takeout din yayi kan qaramin glass table din dake nan gaban sofan sannan ya wuce work station dinsa ya zauna...bude desktop din sa yayi yafara typing, jefi jefi yake kallonta da har lokacin bata tashi ba yayi murmushi yana ayyana irin baccinta a ransa..

Kwankwasa kofan akayi sau biyu sai kuma aka bude, wani baqin guy ya shigo hannunsa riqe da pappers yana cewa "Man you have to go through these papers, jason didn't...." bai qarasa maganan ba ya tsaya kallon Ahmad da yakai yatsansa baki alamun yayi shiru, dan bin office din da kallo guy din yayi idanunsa suka sauqa kan Na'ima dake kwance tana bacci, kamar hadin baki itama ta bude ido ta kallesa sai kuma ta fara miqewa zaune,? guy din yana kallonta da murmushi fuskansa yace "ma Sha Allah, who is this sleeping beauty?" Ahmad ya hararesa yace "fita min daga office lamin" juyowa lamin din yayi ya taho gurinsa yana dariya ya ajiye papers din kan table yace "you have to go through these again" Ahmad ya dauki takardun yana kallo sannan lamin juya zai fita yana kallon Na'ima, tace "Ina wuni" yace "Lafiya, our beautiful princess" daga inda yake zaune Ahmad ya sake cewa "Out Lamin", yana dan dariya ya fice...
Miqewa Ahmad yayi ta qaraso gurinta yace "kin tashi" Na'ima ta gyada kai , miqa mata table water dake kan table din yayi sai ya fara bude takeouts din, ganin yana bude abinci yasa a hankali tace "zanyi sallah tukunna" yace "Okay, ga toilet nan" ta miqe ta nufi toilet din zatayi alwala, fita yayi daga office din shima, bayan tayi alwala tafito taji wayansa daya bari nan kan sofa na ringing, bata kula ba saida aka sake wani kiran ta qarasa tana kallon fuskan wayan, Sunan Laila tagani baro baro akan fuskan wayan......


Bintu Musa ce
'?=???

https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c

WhatsApp group
https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z

('KUNCIN ZUCI('
Na Bintu Musa


Chapter 20


Tsayawa kallon wayan Na'ima tayi tanajin yanayin zuciyarta na chanjawa, kuma batayi gigin daukan wayan ba, tananan tsaye Ahmad ya sake shigowa office din, ganinta tsaye yasa a nutse yace "sorry ban baki darduma ba ko" Na'ima ta dan gyada kai batace komai ba kuma taqi kallonsa, wucewa yayi gurin da yake ajiye spare kayansa a office din, mutum bazeyi tsammanin akwai kofa a gurin ba saida Ahmad ya saka yatsansa sai ga kofa ta bayyana ya bude ya shiga, bai dade ba ya fito hanunsa riqe da linkakkiyar darduma ya warware, nufansa Na'ima tayi ta karba kafin yace zai shimfida mata dan taga alama zai iya yin haka...daukan wayan nasa Ahmad yayi yana dubawa, Na'ima na tsaye tana kallonsa sai taga yayi saurin dagowa ya kalleta bayan yadanyi dube dubensa a wayan, kallon kallo suka tsaya yi, ita tafara juya kanta ta gyara gyalen abayan jikinta dayake babba ne tafara sallah, Ahmad da yasan taga miscalls din Laila yasa shi rasa me ma zaice sai ya saka wayan a aljihu ya zauna nan kan sofan yana dan juyawa ya kalleta, bayan ta idar da sallan ta linke darduman ta ajiye nan kan sofan sai ta dauki jakarta zata maqala a kafada, ganin abunda take Shirin yi yasa Ahmad kallonta a hankali kuma yace "ga abinci nakawo miki" ya qarasa magana yana bude ledan, jijjaga kai Na'ima tayi ta wani sha kunu tace "Naqoshi, gida zan tafi" ai Ahmad baisan lokacin da ya miqe ba sanin meya bata mata rai kuma, ya tsaya nan gabanta ahankali yace "Babe..." Na'ima ta juya kanta gefe bata kulasa ba sai ya miqa kansa side din take kallo, idonsa ne yafada cikin nata tayi saurin kulle idanun nata, Ahmad ya fara yar dariya still yana kallonta, ta wani turo baki cikin shagwaba tace "banaso, ni na qoshi" yana dan dariyan kuma yana kallonta, ji yake kamar ya hadiyeta ma ko zai huta da abunda yake ji akanta, ya sakeyin qasa da murya yace "Okay naji, me kikeso sai akawo miki" sai sannan ta bude idonta ta dan juyo tana kallonsa tace "gida nakeson tafiya" jitake ranta duk babu dadi a wannan moment din, gashi bata da hurumin tuhumarsa akan kiran Lailan data gani saboda itama har yanzu bata gama tantance matsayinta a gurinsa ba... Sai kuma unexpected taji yayi qasa da murya yace "zanyi blocking dinta Babe" dagowa tayi ta kalli cikin idanunsa itama a hankali tace "wa zakayi blocking, wani abu ya faru ne?" Ahmad yayi murmushi ya kai yatsa ya dunguri hancinta yace "Na'eemah", samun kanta tayi da yin murmushin itama ta miqa hannu ta dauko jacket dinda ya lullaba mata ta miqa masa, tace "thank you" karba yayi ya saka ajikinsa, ta sake cewa "I want to go home, na dade fa" Ahmad yace "Okay muje to" ..
Tare suka fita daga company din babu mai magana acikinsu suka shiga mota, ita Na'ima ba abunda ke bata mamaki irin

11 / 25