Chapter 22 Reading Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc Arewa Novels

Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc

Author :  Binta Musa Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   22 / 25

63K to 66K   out of 73.5K words

qarasawa tayi gurin anty Amarya tanajin kuka na zuwa mata, rungumeta Anty Amaryan tayi tana murmushi, Umma dake gefe baki washe tace "Oh ni jummai, wai Na'ima ce ta koma haka" salame dake gyara goyon danta a baya tace "toh umma ke bakiga gidan bane, ai Na'ima ta huta itadai" sake anty amaryan Na'ima tayi ta koma gurin umma Amma bata rungumota ba amma ta riqo hannunta tana murmushi, Hajiya ce ta fito cikin isa Umma tayi sauri karbe hannun ta daga gurin Na'ima ta nufeta tana tace "Hajiya sannu da fitowa" Hajiya tace "yauwa sannunku da zuwa" sai ta kwala kira wa maigadi tace yazo su miqa kayan can BQ inda shafa take zama, sannu tayiwa su kawu Ayuban suka amsa cikin fara'a kamar ba ita tayiwa Ayuban rashin mutunci ba da dade??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????wa, Na'ima sai rarraba Ido take tana jiran ko zata ga goggo acikinsu amma dai shiru sai tace da Anty Amarya "Ina goggo fa, bakuzo da ita bane?" Tsit gurin ya dauka kowa ya fara rarraba idanu, ita Hajiya sai lokacin ma ta tuna ashe zuwan Ayuba ya fada mata goggon ta rasu da dadewa, ganin kowa yayi shiru yasa Na'iman kwantar da murya ta sake tambayan antyn, sai Umma tayi saurin cewa "tana gida ai bata Jin dadin jikinta ne shiyasa ba'a zo da itan ba" sanyi jikin Na'iman yayi sosai a haka ta tayasu suka kai kayan can masauqinsu, da dare bayan sun gama dafa abinci da shafa ta tafi kai musu, tasamu duk sun kwamutsu nan falon suna hira, mazan kuma Alhaji yasa ankaisu nan wani gidansa dake cikin gari, Umma ce tace "Na'ima yaushe zamu shiga cikin gidan ne, duk mun matse anan din, gashi Hajiyan tace zatazo kuma shiru" batace komai ba ta ajiye musu abincin nan tsakiyar falon, salame tace "ni sai na lura ma kamar ba mutane fa, sai kace ba biki za'ayi a gidan ba" Umma tace "ko sai gobe zasuzo inaga, angon ne ma mukeson gani dan bamu taba ganinsa ba" nan kuma jikin Na'ima yayi sanyi, Anty Amarya ta fito daga bandaki ta zauna gefen Na'ima tace "ya kamar ba'a miki gyara ba Na'ima, Hajiyan bata kaiki gurin gyaran jiki bane" nan ma batace komai ba dan tasan inta bude baki to kuka ne zezo shiyasa...
Zuwan da Hajiya batayi ba kenan gashi Na'ima nason Jan salame suje dakinta amma tana tsoron Hajiya tayi mata fadan haka, sai tayi deciding ta kwanta nan tare dasu amma umma tace gurin ya musu matsi ta tafi,.
Washegari ranar daurin Auren Hajiya ta kirata da safe ta miqa mata wani lace tace in tayi wanka ta saka, haka ta karba tayi godiya ta fice, Ranan ba qaramin dauriya Na'ima tayi ba gurin danne abun da takeji a zuciyarta, Lokacin da Anty Amarya ta fada mata an daura auren ji tayi iskan qirjinta ya mata kadan, kawai ta shige bandaki ta sulale jikin qofan tana kuka mara sauti, dasu kawu Ayuba da Alhajin suka kirata yi mata nasiha bata ma fahimtar su, dan abunda takeji ya wuce tunani, su Umma jummai dai anan Bq suka qare bikin dan Hajiya bata bar ko dayansu ya kwana cikin main building ba sai dai suje gaisheta sukoma, wannan abu ba qaramin daurewa daurewa Anty Amarya kai yayi ba amma sanin tanayin magana mijinta ze ce ba haka ba yasa taja bakinta tayi shiru..dan komai na bikin bata ganin yana tafiya akan seti..
Na'ima na kuka kamar zata shiqe su umma na bata hakuri aka sata a mota Sufi ya tuqasu aka kaita nan gidan da Alhajin ya siyawa Bilal din wanda babu wani nisan tashin hankali tsakaninsu....

Bintu Musa ce
'?=???

https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c

('KUNCIN ZUCI('
Na Bintu Musa

Chapter 29


Basu wani dade ba suka isa gidan Bilal din da ya kasance bawani babba can ba amma me kyau sannan stair building ne, har dakin Na'ima dake sama suka kaita, balaifi Alhaji yayi qoqari sosai gurin saka musu kaya masu tsadan gasken da ko 'yar cikinsa iyakaci, su umma jummai sai santin gidan suke bakin su yaqi rufuwa, itadai Na'ima na zaune kan gadon idonta yayi jaaa, sunanan zaune Larai ta shigo dakin fuskan a dinke tace "yauwa ga mota can za'a maida kowa gida" su salame suka bude baki cikin mamaki dan sun taho da niyyan kwana ne gidan, umma zatayi magana anty Amarya tayi saurin miqewa tace "ku taso mu tafi" fashewa da wani kukan Na'ima tayi sai anty amaryan ta riqota tana bata hakuri da kuma nasiha, itadai Na'ima duk nasihohin nan da ake mata bata gane komai dan har lokacin bata iya hasko wane irin zama zatayi a gidan bama balle taji aranta ga abunda ya dace tayi, Matar kawu Nasiru ma sai qananun magana take tana cewa "toh angon da baya nan ne za'a bar yarinya ita kadai a babban gida haka" Larai tace "ba matasalarku bace wannan, ango kam duk inda yake ai yau zezo tunda an kawo masa amaryarsa" umma jummai sai ido ba baki ganin Hajiya larai na magana jiki duk gwalagwalai, haka Larai ta tusa kowa na gidan a gaba suka fice Na'ima na kuka, bayan tafiyansu sai ta kalmashe kafafunta a qirjinta anan zaune kan gadon ta cigaba da kukan babu me lallashi...
Har dare yaja Na'ima nanan zaune sai da taga kukan bazai kaita ko'ina ba sannan ta tashi fara cire kayan jikinta, kayanta ta gani plus na akwatin acikin wardrobe ta nemi dogon riga mara nauyi aciki ta saka sannan ta shiga bandaki tayo alwala, anan dakin ta sake neman sallaya tayi sallahn, cikin sujud ta rinqa addu'an sauqi cikin lamuranta tana kuka, nan kan sallayan tayi bacci....Washegari tunda ta idar da sallah bata koma bacci sai ta sauqa falon qasa Jin kamar qarar gate, leqawa tayi taga ashe da megadi ma agidan, sai taji hankalinta ta dan qara kwanciya jin ba ita kadai bace a gidan..har zuwa rana tana ta zuba Ido ko 'yan'uwan nata zasu dawo amma shiru, sai la'asar mota ta shigo gidan Na'ima tayi saurin leqawa taga Sufi ne ya fito daga motan ya qaraso yayi knocking, sai da ta koma ta sako hijab sannan ta bude masa suka gaisawa, zama yayi ta kawo masa ruwa sai ya miqo mata kwalin waya tareda kudi masu yawa yace "gashi inji Alhaji, yace zai kiraki" godiya Na'ima tayi ta karbi wayan tanajin kamar ta tambayesa dalilin rashin zuwan su umma, miqewa yayi ya mata sallama sai ta jefo masa tambayan ya amsa da "ai sun koma Adamawa tun da safe" daskarewa tayi nan tsaye tanajin hawaye na zuwa mata, sallama sufin ya mata ya tafi, Na'ima na nan tsaye cikin sanyi ta koma daki...

Ashe komawan su umma washegari da safe Hajiya ta kira motan da zai maidasu gida, aika shafa tayi akan ta fada musu su shirya da wuri drivers din na jiransu, da aka fada musu duk sunyi mamaki barin ma Anty Amarya da ranta yafi na kowa baci, cikin haushi suka fara hada kayan nasu sai ga su kawu Ayuba ma sunzo, da aka zo shiga motan ne anty Amarya tace dashi "yanzu Fisabilillah yarinyar nan ko sallama bamu je munyi da ita ba zamu koma, hakan ya dace kenan?" Ayuba yace "toh daman sintiri zakuyi tayi ne gidan yarinya" Umma tace "toh wai ina angon ma ni jummai" yace "yana hanyarsa ta dawowa daga Lagos, ashe wani uzuri ne ya taso masa babba shiyasa be zo ba" itadai Anty Amarya kawai sauraronsa take amma komai na bikin nan ya sire mata arai kuma tausayin Na'ima take sosai ganin akwai abunda ke damun yarinyar amma ta danne, saida suka shiga motan Hajiya ta fito ta miqawa Ayuba bunch din dubu ya karba baki har kunne yana godiya anty Amarya na hararansa ganin shi ko ajikinsa wulaqancin da aka musu.....

Week Later...

Na'ima ita kadai take rayuwa cikin kadaicin a gidan kuma abu daya ne ke debe mata kewa shine Jin motsin megadin gidan, inta tashi da safe haka zatayi wanka ta shiga kitchen ta dafa abinci dayake akwai komai na amfani cikinsa, tayi sallah tayi bacci dan ko baqo batayi, dama tun ranar da Sufi ya kawo mata waya bayan tafiyansa tayi waya da Alhajin suka gaisa ya tambayeta ko akwai abunda take buqata tace babu, hakuri ya bata akan Bilal din yana kan hanyar dawowa wanda ita Na'ima hakan fargaba yasaka mata da tashin hankali be sani ba, tun daga wannan lokacin kuma bata sakeyin waya da Alhajin ba kasancewan ya fita qasar waje wani aikinsa shima, ranar da ta cika kwana goma sai ta shirya zata tafi makaranta abunta, bayan ta shirya cikin doguwar riganta da hijab tayi sallama da megadin gidan da ya kasance bafulatani..
Batayi lattin zuwa ba dan tsirarakun mutane ta samu a ajin dayawa basu qaraso ba tukun ta samu waje ta zauna, can sai ga Nafisa ta shigo wadda ganin Na'iman yasata ware idanu ta nufeta, zama tayi nan kusa da ita kafin ma su gaisa tace "Na'ima lafiyanki kuwa, meya faru bakya zuwa? gashi banida number'n ki balle in kiraki" sai Na'ima tayi murmushi tace "wani uzuri ne ya tasomin Nafisa" Nafisa bata ja tambayan ba ganin Na'ima bata sake da ita ba har sannan sai tayi shiru, ranan har yamma suka kai kafin su gama school activities din nasu, da Na'ima tayi wa nafisan sallama sai ta nemi ta rage mata hanya, farko qi tayi sai da Nafisan ta nuna ranta ya baci sannan ta hau motan nata, sunyi nisa cikin tafiya Na'ima ta budi baki a hankali tace "Aure akaimin Nafisa" dan burki Nafisan ta taka kafin tace "what?..Aure kuma" Na'ima na kallonta ta gyada kai batace komai ba, ta sake cewa "yaushe? within last week zuwa yanzu kenan?" Na'ima tace "Eh", da farko shiru nafisan tayi sai ta dan yi murmushi tace "Ayya Allah ya sanya alkhairy kice da amarya nake tare yau din" murmushin dole Na'ima tayi batace komai ba suka cigaba da tafiyan cikin shiru, sake kwantantawa nafisan sabuwar unguwar su Na'iman tayi, bayan sun isa sai nafisa tace "Na'ima, to tell you the truth gaskiya banji dadi ba, I understand that baki sanni sosai ba or you don't want to be friends with me, amma ace har kiyi aure bazaki fadamin ba in miki ko addua ma" sai jikin Na'ima yayi sanyi tace "Dan Allah kiyi hakuri auren ne yazo cikin gaggawa shiyasa, na dade da daukanki matsayin kawata wallahi nafisa, ga wayata ma ki sakamin number'n ki" karban wayan Nafisa tayi tace "kuma dama tun can da goron sa ne akanki shiyasa akayi auren da wuri haka?" Na'ima ta danyi shiru sai tace "Cousin dina ne" Nafisa ta gyada kai sai Na'ima ta sake cewa "ki shigo mana ko ruwa kisha" Nafisa ta dan girgiza tace "A'a Amarya Nagode sai wani lokaci, may be ma Ango yananan ciki yana ta jiran dawowarki" ta qarasa maganan tana dan dariya, da farko dan stiff Na'ima tayi sai tayi murmushi ta mata sallama ta fice daga motan cikin sanyin jiki...

Kwance Bilal yake akan gado tareda stella dake kwance jikinsa, tunda Bilal ya dawo gari Lagos yake tunanin ta inda zai fadawa Stella maganar auren da akayi masa, gashi Alhaji ya bashi adadin wasu lokuta akan ya koma, shafa attachment din stella'n yafara yi a hankali yace "Baby i want us to talk" dago kai Stella tayi tana murmushi tace "What is it Baby?" Yana kallon idonta ya sake kwantar da murya yace "you know i love you right?" Ta gyada kai tanajin wani dadi a zuciyarta, yace "no matter what.. you'll always be my woman, no one else " dan gyara kwanciya tayi takai hannu tana shafa fuskansa suna kallon kallo cikin ido, sai da ya sauqe numfashi yace "iyaye na sunmin Aure Baby" dan stiff tayi daga kwancen sai kuma ta fara kokarin miqewa daga jikinsa ya kamota ta yi saurin fincike hannun tace "don't you dare touch me" miqewa sukayi dukansu suka tsaya nan tsakiyan dakin tace "wallahi baka isa ba" ya girgiza kai kafin yayi magana ta kai hannu tafara dukan qirjinsa tace "you've betrayed me Bilal, bamuyi haka dakai ba" ya rugume ta tareda cewa "ke kadai nakeso baby and you know that" hankali tashe Stella tace "you're not going anywhere Bilal" ta dago kai ta kallesa ta fara hawaye tace "in ka taba wata mace zan iya mutuwa" yayi saurin girgiza kai yace "what are you saying Baby? Me zanyi da yarinyar can da banason ganinta ko na minti daya" rungume Stella yayi yacigaba da fadin kalmomin lallashin da duk sukazo bakinsa, a wannan lokacin ji take komai zata iya yi akan Bilal din kuma har iyayensa bazata bari ba....

A rikice Stella taje gidan qanwarta yammacin ranan bayan sun gaisa chiamaka ta fara tambayanta meya faru ganinta ba'a nutse ba, Stella tace "shikenan chi, they've won against me, aure iyayen Bilal suka masa" chiamaka ta ware Ido tace "ta nan suka bullo kuma, lallai da mu suke zancen" Stella tace "I can't let Bilal touch her, zan iya mutuwa Chi" tace "meyasa zaki tada hankalinki akan wannan, kema fa kinsan abunda baze yiwu bane" dan jijjaga kai Stella tayi tace "sai kin ga yarinyar zaki shaida hakan Chi, i can't compete with her, duk da inada tabbacin Bilal ba sonta yake ba impact nasani yama tsaneta sosai, amma kinsan in akwai abu daya da bariki ya koya mana shine rashin yadda fully da namiji, wallahi bai isa yazauna da wata mace ba, wahalar da nayi akansa bazata fadi a banza ba" ...Stella bata bar gidan qanwar ta taba sai da suka gama qulle qullen yanda zasu bullowa lamarin kuma duk ba ta hanya me kyau ba...

Two months Later..

Zuwa wannan lokacin Na'ima har ta saba da rayuwan kadaici cikin gidan aurenta, sabo ne sosai ya shiga tsakaninta da nafisa zuwa sannan, yawansu a makaranta tare, cin abincin su tare karatunsu tare, kuma har zuwa wannan lokacin Na'ima bata samu courage din bayyana damuwanta ga Nafisan ba, ranar da nafisa ta fara zuwa gidanta wuni sukayi suna hira, sukayi girki sukaci anan kitchen din ma suna raha kamar ba Na'iman da take fargaban zamanta gidan ba,tana iya qoqarinta na zuwa gaishe dasu Hajiya in anyi kwanaki amma har zuwa lokacin basa wani dogon magana ita da Hajiya, Alhaji ne dai gamuwanta dashi baifi sau biyu ba saboda baya zaman gida sosai gashi bayan auren nasu yayi wata doguwar tafiya zuwa china wanda har sai da Hajiya ma ta bisa, a wannan haduwar nata dashi ya bata hakurin rashin zuwan Bilal, har ya nemi tabbatar da karyar da Bilal din ya masa akan suna waya da Na'iman har ya so ta bishi can Lagos din to sai tace A'a, shi Alhaji Jin wai Na'ima tace A'a din se ya dauka akan makarantar ta ne tace haka din shiyasa bai ja magana ba, amma a zahirin gaskiya ma Bilal be san Na'ima na zuwa wata makaranta ba ma, Na'ima ta amsawa Alhajin da cewa "Eh hakane" saboda batasan me zatace ba toh, dan har ranta batason dawowan Bilal Kano saboda tasan ba alkhairy ne zai hadata dashi ba...
Ranar wata asabar Nafisa tayi alkwarin zuwa gidan Na'iman akan zasuyi karatun exams dinsu dake gabatowa, zuwa 11 na safe sai gatanan da motarta, Na'ima na bude mata qofa suka fara fara'a, Nafisa ta dago ledan hannunta dake dauke da snacks da sweets tace "da guzuri na nazo, Mami bata bari insha zaqi a gida" Na'ima tayi murmushi tace "tanada gaskiya ai, kuma bakya ciwon ciki?" Nafisa ta zuba? kayan nan kan kujeran falon ta zauna itama sannan tace "tab babu abunda yakemin, a boye nake sha in na seta lokacin da bata kusa ai" Na'ima ta danyi dariya tace "Laa to sai na fallasaki" Nafisa tace "aikuwa Mami na tambayanki sosai, yaushe zakije? kinsan na nuna mata hoton ki, da zan taho dinnan ma har Abu saida yace in gaishe da ke" Na'ima na fara'a tace "Ina amsawa, in Sha Allah zan je Nafisa" da haka suka hau hira a anan zaune falon basuyi karatun ba, sunayi sunashan chocolates din Nafisa na bata labarai suna dariya, sai da Na'ima taga lokaci na neman qurewa ta tafi kitchen dafa musu abinci, nan kitchen din nafisa ta biyota tafara tayata suna hira, bayan sun gama nafisa tajiyo wayanta na ringing acan falo ta fice daukowa, zuba abincin Na'ima tayi a plates guda biyu zata kai musu falon, shiganta Falon ta ganshi tsaye ga Nafisa nan zaune waya kare kunnenta binsa da kallo tareda wacce ke bayansa, wani irin bugawa zuciyan Na'ima yayi saida plates din suka fadi daga hannunta, da sauri Nafisa tayi gurinta ta tsugunna zata dauke plate din tace "lafiyanki Na'ima" idon Na'ima na kan Bilal dake kallon ta kamar yaga mutuwar sa, qarasawa kan kujera Stella tayi ta zube alamun ta gaji tana bin Na'iman da kallo, Bilal na kallon Na'iman ya nuna Nafisa yace "Who is this?" Kasa magana tayi jikinta na rawa Nafisan na kallonta, sai Bilal ya sake mata wani tsawan yace "I'm talking Na'ima" murya ta na rawa tayi saurin cewa "kawata ce yaya"? yace "me tazo yimin a gida?" Miqewa tsaye Nafisa tayi hannunta riqe da plates din ta dan ware ido cikin mamaki sai Na'ima ta girgiza kai tace "kayi hakuri" kallon Nafisa yayi yace "Get Out" sai ta tsaya kallonsa cikin ido amma data juya ta kalli Na'ima taga tayi tsuru tsuru da ita sai batace komai ba ta ajiye plates din nan qasa kusada inda abincin ya zube sannan ta nufi kujera ta dauki jakanta tana bin Stella da wani irin kallo, cikin sanyin jiki Nafisa ta fita daga falon Na'ima na nan tsaye ta kasa bin bayanta...

Bintu Musa ce
'?=???

https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c

('KUNCI ZUCI('
Na Bintu Musa


Chapter 30


Sai da Nafisa ta fita suka Jiyo tashin motanta sannan Stella ta kalli Bilal tace "Baby i need water" yace "Okay" ya sake kallon Na'ima yace "Get her water and clear this mess now, you stupid" ya qarasa maganan tareda nuna mata abincin dake zube nan qasan, gyada kai Na'ima tayi sannan juya ta koma kitchen din, sai sannan Bilal ya zauna nan kan kujeran kusada Stella yace "Sorry Baby, me kikeson ci?" tadan

22 / 25