Chapter 6 Reading Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc Arewa Novels

Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc

Author :  Binta Musa Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   6 / 25

15K to 18K   out of 73.5K words

juya kanta dariya na taho mata, nafisa ta fara dariya tace "wallahi mami tun safe bamu sha ba sai yanzu" Mami ta wuce gurin wardrobe zata dauki abu tace "yamuku kyau, ku cigaba" Atare suka bata hakuri bata kulasu ba ta fita daga dakin. Nafisa ta juya ta daka duka a na'ima, sosa gurin na'ima tayi tana dariya tace "Auchh..to ai zan miki magana naga ta fito daga toilet din"

Hiransu suka zauna nan dakin Mamin sunayi, nafisa na pressing wayanta, cannta yi wani tsuka mai karfi tana kallon wayanta tace "ni nataba kallon yarinya mara zuciya da aji irin yarinyar nan kuwa" na'ima na kallonta tace "me kuma ya faru?" Nafisa ta tashi zaune ta miqo mata wayan a fuska tace "Laila mana,kiga post dinda tayi a IG, ke yanzu wannan yamiki kama da hannun yaya Ahmad dan Allah" shiru na'ima tayi tana kallon wayan wanda hoton hannun mace da namiji ne sarqe cikin na juna dan ba sanin hannun Ahmad din tayi ba tace "nafisa nikuma Ina nasan yanda hannunsa yake?" Nafisa tace "nidai ko kaffara bazanyi ba wannan ba hannunsa bane,yaushe ma ya dauki kiranta balle har ya kai da riqe hannunta" na'ima tace "to ke me ruwanki in ma hanunsa ne,ba budurwarsa bace, meye na rantsuwan" nafisa ta dan harareta tace "waa? Yaya Ahmad din, lallai bakisan wannan ba, anfada miki yanada lokacinta ne...ke har matan ma in general, harkan kudade kawai yasani wannan kowama yasan haka" Na'ima tadan kyabe baki tanajin wani iri aranta batace komai ba nafisa tacigaba da maganan tace "har da wani love caption, Eh lallai Laila" ta qarasa tana dan dariya ta sake miqa wayan fuskan na'ima tace "kiga caption din har da hashtagging din sunan yayan fa" Na'ima ta kauda idonta daga kallon wayan jin ranta na dan baci babu dalili tace "amfanin me kallon zemun,kinada problem wallahi nafisa" Ta juya ta jawo blanket din kan gadon Mamin tayi kwanciyarta, ganin abunda tayin like she's not interested in the talk yasa nafisa daukan pillow ta kwada mata,fashewa da dariya na'ima tayi tace "Allah kedin ce ai nafee,hiran is not productive,I don't see why kike tada jijiyan wuya" nafisa ta sauqa daga gadon tace "bazaki gane bane" ta qarasa tana fita daga dakin Na'ima ta bita da kallo tana tunani aranta kan meyasa ma zataji wani abu a ranta game da hiran to, after all batada hadi da kowanne cikin biyun, bata dade da fara bacci ba nafisan ta dawo ta kwanta, nan dakin Mamin suka kwana ranan.

Lokacin bikin yanata matsowa and na'ima is not even interested in it, itadai ta dawo taga su Mami ne daman bawai bikin wata Salma can da bata santa ba.
Da bikin ya zama saura kwanaki kadan meerah ta aiko musu da kayan nasu, kaya sunyi kyau har Abba saida aka nunawa
nafisa ta kaisu salon akayi musu qunshi akayiwa nafisa kitso while na'ima tace bataso aka gyara mata gashin kawai.

Cikin week din bikin nafisa tace suje can gidan bikin Na'ima ta jijjaga kai tareda cewa "A'a bazanje ba nafee sai ranan auren" Kuma Mami ta yarda da hakan lokacin da nafisa ta kai qaran na'iman.
Haka na'ima na gani Mami suke zuwa gidan bikin tace ita sai ranar auren zata je..Ana gobe auren duk 'yan gidan sun tafi can gurin event aka bar Na'ima ita kadai da lantana, girki sukayi bayan sun gama na'ima ta wuce dakin Mami ta debo kayan ta na laundry sannan ta shiga dakin nafisa ta debo nata ta wanke su tas a washing machine
Har dakin Abubakar ta shiga dake nan falon downstairs ta gyara masa ko ina, she kept herself busy sunata hira da lantana.
Sai dare faruk yadawo dasu Mamin, sun shigo lokacin tana salla a dakinta bayan ta idar ne ta tafi wurinsu nan falon Mami, shiganta dakin Mami tace "habibti ya zaman shiru" ta shigo ta zauna gefen mamin tace "sannu da dawowa Mami"
Mami ta amsa da yauwa, nafisa dake gefe akan kujera itada faruk bayan ta chanja kaya, tace "Husna tace in bakije ba gobe dakanta zatazo daukanki" faruk yayi murmushi yace "meyayi zafi, kamar abun dole" ya kalli Na'ima yace "habibtin Mami kiyi zamanki ma in goben bakyason zuwan" na'ima tayi murmushi tace "toh yaya" ta qarasa maganan tana dan ware Ido ma nafisan alamun "to dai kinji" Nafisa tace "wallahi baki isa ba sai kinje, in ban ciccibeki nakaiki ba" Mami da faruk sukayi yar dariya Mami tace "to fah" ta juya tana kallon Na'ima tace "Habibti kinci abinci dai ko" na'ima na dariyan nafisan ta gyada kai tace "Eh Mami, akwai naku a dining ko a kawo muku nan" Mami tace "barshi mu huta tukunna"
Faruk sai kallon Na'ima yake ganin she was openly herself these days, harda tsokala wanda a farkon zuwanta gidan she can go days batayi murmushi ba.
Ranan ba'ayi hira falon Abba ba, kowa ya tafi makwancinsa da wuri a huta gajiya.

Washegari da sassafen Mami ta tafi gidan bikin ta barsu suna bacci, na'ima bata tashi ba sai almost nine shima yunwa ce ta tada ita ta sauqa yin breakfast cikin purple color din kayan bacci Mai laushi kamar cutton a jikinta, hulanta yayi baya kwantaccen gashin goshinta duk a waje, kitchen ta shiga, tana tsaye bakin fridge nafisa ta shigo itama da kayan baccin tana miqa? alamun tashinta kenan, zuba madara na'ima tayi a cup ta miqa mata, nafisa ta karba tana kaiwa baki tace "yaushe zamu shirya mutafi,husna called me" Na'ima tayi hanyar fita daga kichen din hannunta riqe da kofin madaran tana cewa "nafee mu dan bari anjima mana,it's so early" nafisa ta bita suka fita tace "kinsan fa zamuje wurin makeup dinnan" zama sukayi a nan dining zasuci abincin.

Basuyi nisa da fara cin abincin ba faruk yashigo, on a normal circumstances na'ima ba wani damuwa tayi ba dan babu hijab a jikinta sanin cewa tana zama da normal kaya ko a gabansa dan kamar yaya na jini ta dauki faruk kuma shima bai damu ba, Amma ganin wanda ke biye dashine yasa ta daskare a wurin takasa kai cokalin abincin bakin ta aranta tana cewa "yau kuma me wannan mutumin yazoyi da safe haka" because tunda ta fara rayuwa a gidan bata taba ganinsa ba sai kwanannan.

Qarasowa dining din Ahmad yayi yana dan kauda idonshi daga kallonta ganin yanayin kayan jikinta.
Sanye Ahmad yake cikin white polo shirt da blue jean shima in a casual way, ganinsu yasa nafisa cewa "Yaya,good morning" Ahmad ya zauna yace "nafisa,kin tashi lafiya" nafisa ta amsa tareda gaisheda faruk sannan ta miqe ta fara serving dinsu abincin, Na'ima ta ajiye cokalin tadan fara gyara hulanta da jelan? gashin yaqi komawa duka tace "Ina kwananku" faruk dake kallonta ganin how cute she looks, yace "lafiya na'ima,I thought kun tafi gidan bikin fa" na'ima tadan jijjaga kai tace "sai anjima" Ahmad ya kasa jurewa saida ya dago ya kalleta, na'ima taqi kallon gefensa,? murmushinsa na yau saida yadan bayyana ganin still dai she can't look at him kuma baisan meyasa ba yake bidan ta kalleshin .
Hira sukeyi sama sama suna cin abincin, nafisa tace "yaya anan ka kwana ne?" Ya dan jijjaga kai hankalinsa na kan abincin dayake ci kadan kadan,yace "A'a can gidana na kwana" faruk yace "gidan baba is crowded i don't know how yaya Adam is cooping" Ahmad ya dan gyada kafada yace "wannan jama'a basa damun baccinsa ai" nafisa da faruk suka danyi dariya
Na'ima dake jinta so uncomfortable under his Eyes yasa tun dazun idonta ke kan plate din gabanta bata dago ba aranta tana ayyana meyasa wannan bawan Allahn ke sa mata rashin nutsuwa ne, samun kanta tayi da dan dagowa tana kallon hannunsa hoton rannan da nafisa ta nuna mata yana fado mata arai.
Koda su na'iman suka gama bata tashi ba har seda Ahmad ya tashi suka nufi falon Abba sannan ta miqe tafara taya nafisa tattare wajen.

Bayan sunyi wanka suke shirya cikin simple attire, nafisa ta saka musu kayansu cikin bag suka wuce gurin makeup din.
Sunyi kyau sosai bayan angama make up din barinma na'ima kamar ka sace ta, ankon daya kasance na leshin ba qaramin haskata yayi ba.
Isarsu gidan bikin bayan sun gaisa da mutanen da suka idda a main falon gidan suka wuce part din mamma dan nafisa tasan acan zasu Sami Mami, aikuwa ta na zaune tareda wasu yan'uwansu manyan mata, bayan sun gaisa dasu, nafisa ta jasu dakin Salma
'yan mata suka samu a dakin kowacce na yauqin ta isa, husna da salma basa dakin,Laila da qawayenta sun hakimce kan gadon salman, nafisa tace "sannunku..Laila Ina husna?"? Laila ta amsa dakyar "bansani ba" Zama sukayin kan tsabtacaccen carpet din dake shimfide a dakin, na'ima daman bata kulasu ba tayi zamanta ko kallonsu batayi ba.
Laila ta kallate sannan tace da nafisa "yar zaman gidan naku bata tafi ba kenan" Nafisa ta juyo tana dan hararanta Lailan tace "bangane ba, what do you mean?" Laila ta kyabe baki tace "wannan ta kusa da ke din" Nafisa tace "first of all sunanta Na'ima and secondly, I'm in good spirits yau dinnan Laila karki batamin rai dan banida lokacinki" kafin Lailan ta amsa luba tace "Ha'a taga bare a cikinku ai dole tayi magana" Nafisa tace "sannu lubabatu, sannu 'yar'uwarmu ta jini, kinga idan ina magana ta hankali ki daina tsomamun baki, ke asuwa?" sanin masifan nafisa yasa luba juyawa tana tsuka me qarfi, cike da tsiwa Laila tace "An fada din bare, dan wannan farin nata ba ta inda kuka hada jini da ita" Nafisa ta miqe Na'ima tayi saurin riqo gyalenta, ranta ya sosu da wannan maganar da suka fada har hakan saida ya nuna akan fuskanta tace da nafisa "Mu fita nafee" ganin yanda bacin ranta ya fito fili yasa nafisa batayi musu ba ta jira miqewan na'ima sukayi hanyar fita daga dakin,'yan matan dakin da suka tsaya kallon drama suka bisu da kallo, Laila tayi tsuka tace "gwara ku fitan dan nima banida lokacinku" wata qawarsu tace "to ke Laila me farar yarinyar ta miki?" Laila ta kalleta a fusace tace "babu ruwanki"

Haka na'ima tayi wunin gidan bikin ranta duk babu dadi dan nafisa ta zage itada husna sai bidirinsu sukeyi, na'ima ta qi binsu haraban gidan?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? da ake taro ta na zaune a main falon gidan riqe da yarinyar anty Fatima immediate sistern Ahmad, sai wasa yarinyar take da dankunnen na'iman.

Bayan ankai amarya dasu gidanta dake cikin wata shahararriyar unguwa nan Abujan, suna zaune cikin Mini falon amaryan na'ima tace "nafisa ki tashi mu tafi" husna tace "A'a ku bari ango suzo mana" Na'ima tadan bata rai sai kuma a hankali tace "har sai mun jirasu?" kafin husna tayi magana Nafisa tace da husna "kinsan jaraban na'ima kuwa, muje naji anty Amnah tace zasu tafi yanzu dan har ta kira za'a zo? daukansu" Miqewa na'ima tayi Jin haka dan duk a taqure take a gidan gashi ta gaji, gurin su anty Amnah nafisa ta kaita, anty amnah tace "gaskiyarki na'ima bari mutafi tare, barsu su gama rawan kansu" nafisa tayi dariya tace da na'ima "to sai na dawo"
Sunanan zaune aka kira anty Amnah, bayan tagama magana dana dayan bangaren ta kashe tace "tashi muje na'ima mai daukanmu yazo" ta qarasa tana fadawa wata mace dake gefenta, miqewa sukayi anty Amnah ta sake cewa bari muyi sallama da amarya suka wuce upstairs, Hanyan waje na'ima tayi akan zata jirasu can gurin motan, fitanta ta hango wata black mota a haraban gidan ga light dinta a kunne, qarasawa tayi tadan tsaya ba daf da motan ba, nacikin motan ya bude ya fito yana kallonta, dan riqe numfashinta tayi kadan ganin Ahmad.

Bintu Musa ce
'?=???
ArewaPen @Bintu Musa

ArewaPen
https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c


('KUNCIN ZUCI('
Na Bintu Musa

WhatsApp group =?G?
https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z

Chapter 13

Rufe cab din motan Ahmad yayi bayan ya fito, ya jingina jikin motan hannuwansa cikin aljihun kayan jiikinsa yana kallonta, kauda kai na'ima tayi daga kallonsa Jin zuciyar ta tafara bugawa kamar yanda takeyi aduk lokacin da suka hadu, dan sunkuyar da kansa yayi yana dan murmushi sannan ya dago ya cigaba da kallonta baya ko kifta ido, sunanan tsaye babu me magana ya dan gyara tsayuwa zai fara takawa gurinta Laila ta fito daga gidan, Ahmad ya dauke kai daga kallon Na'ima ya kalli lailan, tuni ya dinke fuskanshi kamar bashi yake murmushi yanzu ba, tunkarosa Laila tayi, tadanyi wani irin kallo a na'ima sannan ta qarasa wajensa tana murmushi kamar bakin ta zai yanke tace "yaya..Ashe kazo, Ina wuni" babu yabo babu fallasa yace "Lafiya" Laila tace "ko inzo mu koma gidan tare" Ahmad yadan kalleta yace "tare mukazo ne?" Laila batasan lokacin da ta juya ta kalli Na'ima data juya kanta ba, ta sake juyawa tana kallon Ahmad tanajin kunyan tsinka ta dayayi a gaban na'iman, ta sake cewa "kaiii yaya" coldly Ahmad yace "su anty Amnah nazo dauka" kafin ta amsa sai ga anty Amnah ta fito daga gidan itada wasu wata guda biyu, qarasowa sukayi gurin motan daya daga cikin matan tace "Laila kema dake zamu koma kenan" Anty Amnah ta riga Laila amsawa da "a'a haba dai, ai salma bazata ji dadi ba, bayan ga 'yan uwanta can suma suna jiran ango da abokansa" matar tace "Gaskiya dai, ki jira abokan angon suzo su maidaku tukun" Shidai Ahmad tuni ya bude motan ya shiga, Laila ta matsa zasu bude kofan motan, anty Amnah ta juya ta kalli Na'ima dake Shirin shiga back seat tace "zo na'ima ki shiga gaba, mu saimu shiga bayan" Na'ima ba don ranta yaso ba ta bude gaban motan tashiga, Laila sai hararanta na'ima jin kamar ta maketa.
Shigan na'ima cikin motan qamshin turaren Ahmad mai sanyi wanda ya rikide dana motan ya bugeta, Jin proximity dinsu yayi kusa yasa ta Jin kamar ta fice daga motan amma haka ta dake idanunta na kallon gabanta, Ahmad yatada motan suka wuce aka bar Laila nan tsaye kaman ta fashe....
Na'ima tayi shiru kamar bata cikin motan, su anty Amnah sai hiransu suke, sunyi nisa anty Amnah tace "Habibtin mami yaushe hutun naku zai qare" cikin nutsuwa da sanyinta daya zame mata jiki na'ima ta amsa da "next week in Sha Allah anty" Anty Amnah tace "mu zuwa Monday zamu koma gaskiya" daya daga cikin matan tace "itama a England din take ne?"
Anty Amnah ta amsa da "Eh suna makaranta acan tareda nafisa, yarinyar Mami ce itama" matan suka amsa da "ma Sha Allah...Allah ya taimaka" ciki ciki na'ima ta amsa da Amin, Ahmad yadan juyo ya kalleta.

Isarsu gidan Mamin sun fito dukansu Anty Amnah ke tambayan na'ima "Anan zaki kwana ne kema" Na'ima ta dan jijjaga kai tace "yaya faruk zaizo mu wuce, zan dauki jakan mu a dakin husna ne" Anty tace "toh"
Wuce su tayi tabarsu nan suna magana da Ahmad din daya fito shima ya tsaya.
Shigarta falon ta tadda mamma ta fito daga kitchen din dake nan downstairs hannunta riqe da wasu ledoji, na'ima ta qarasa zata tayata riqe wasu, mamma tace "No, kibarshi daughter i can manage" duk da haka saida ta karba suka fara tafiya zasu wuce upstairs su anty Amnah suka shigo, mamma tace "kun dawo" a gajiye su anty Amnah suka zube akan kujera nan falon tace "mun dawo mamma, Ahmad ne yakawomu, kinganshi can waje wai bazai shigo ba da mutane gidan" murmushi mamma tayi tace "nima sai asuba yake shigomin tunda aka fara hidiman bikin nan" ta qarasa magana ta na maida hankali kan Na'ima dake tsaye tana jiran su gama magana tace "muje daughter", Sai da na'ima ta taya mamma ajiye ledojin inda yakamata sannan ta wuce dakin husna dauko jakarsu, wasu 'yammata tasamu a dakin kwance kan gadon kowacce na danna waya, dagowa sukayi suna kallonta
Na'ima ta wuce gurin wardrobe din husna ta dauko kayan nasu ko kallon gefen 'yammatan batayi ba, daya daga cikinsu tace "kema a garin nan kike ne?" Na'ima tace "Eh" suka sake tambayanta "ke yar'uwar su nafisa ce?" wannan karon gyada kai kawai na'ima tayi ta fice daga dakin aranta tana mitan "kamar ita kadai ce aka gani baquwar fuska a taron bikin, sai tambaya ake mata kaman wadda taje gidan jarida"
Tana sauqa stairs kiran faruk ya shigo wayanta ta dauka, daga dayan bangaren yace "Na'ima kinanan gidan Baban ne?" tace "Eh yaya" yace "to ki fito compound ki jirani ganinan na kusa qarasowa" ta amsa da "toh" sannan ta qarasa sauka tayi sallama da su anty Amnah dake nan falon basu tashi ba..
Fitanta wajen taganshi tsaye jikin motan hannunsa daya cikin aljihu dayan kuma yana danna wayanshi, Jin takun mutum yasashi dagowa ya kalleta
Na'ima tadanyi stiff a tsaye ganin Ahmad aranta tana tunanin "daman bai tafi ba"
Gyara tsayuwa yayi yana kallonta yace "Let me drop you" Na'ima bata bashi amsa ba ta tsaya kallonsa, sai da taga ya bude front seat sannan tace "daman yaya faruk yace...uh..uh..munyi waya.." Zuba mata idanu Ahmad yayi batasan lokacin da tafara tako wa gurinsa ba, miqa hannu yayi ya karbi jakan ta sake masa, ya zagaya ya saka a booth sannan ya dawo wajenta ya jira ta shiga motan ya rufe mata kofan sannan ya shiga driver seat.
Sun fito daga street din gidan Baban na'ima ta hango motan faruk zai shiga street din shikuma, juyawa tayi ta kalli Ahmad da hankalinsa na ga tuqinsa, dan juyowa yayi, tayi saurin kauda kanta..Saida sukayi nisa na'ima taji yace "Did i got something on my face?" Na'ima tadan juyo batareda ta kalli fuskansa tace "Na'am?" parking motan yayi a gefen street, na'ima batason lokacin da tadan ware idanu ta juya ta kalleshin ba, hada idanu sukayi yadan duqo kanshi kusada ita yana kallonta, na'ima jitayi isakan motan ya mata kadan kamar ta bude motan ta fice.. Ahmad yayi qasa da murya yace "meyasa bakyason kallona?" Na'ima ta kauda kanta tana kallon titi bata amsa ba, ji take muryanshi na karya duk wasu gabobi na jikinta, ya sake yin qasa da murya yace "Look at me Na'eemah" tadan juyo bata kalleshin ba cikin sanyin murya tace "meyasa zan kalleka" still yana kallonta shima cikin sanyin murya yace "because i want to see your eyes" batasan lokacin da ta juya kanta tana kallon window ba tana dan

6 / 25