Chapter 15 Reading Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc Arewa Novels

Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc

Author :  Binta Musa Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   15 / 25

42K to 45K   out of 73.5K words

na da rufin asiri sai Abdullahi yasamu kula da ilimi daidai gwargwado a gidan, ya taso cikin nema a fannin kasuwancin da mijin hajiya babba yakeyi, asannu asannu hajiya babba take sa Abdullahi bin mijinta kasuwa yana ayyuka har shima Allah ya hore masa yayi nasa shagon, a wannan lokacin ne kuma ya waiwayi gidan, babu yanda hajiya ta iya haka ya dan tattaro guntun chanjinsa yazo duba mahaifinsa, su Ayuba sai a sannan suka sanshi, Yusuf bai hadu dashi ba dan baya gari ma lokacin da Abdullahin yazo, ganin jikinsa da alamun maiqo ne yasa Ayuba da Nasiru suka rinqa yin nan nan dashi kamar su maidashi ciki, Abdullahi bai wani dade ba ya koma kano gurin aikinsa...
Bai sake waiwayansu ba saida Malam yayi kwana arba'in da mutuwa ya dira garin, rana tsaka ya zo musu da wata mota mai dumi ya faka ta nan qofar gidan Malam, lokacin duk su Ayuba suna gurin aiki, goggo Mahaifiyarsu Yusuf dince ta sauqe shi sannan ta tura ayi mata kiransu su Ayuba dake nan kasuwar da ba nisa tsakaninsu, Yusuf dai qin barin aikinsa yayi, dan duk wata martaba ta Abdullahi kuma ya daina gani tunda har mahaifinsu zai mutu ace har ayi taro a watse babu alamunsa, sudai Ayuba da Nasiru cikin mazari suka kada kafarsu suka tafi, hankalinsu bai sake tashi ba saida suka ga motan da Abdullahi yazo da ita nan kofar gidan, Yanda kasan fir'auna da bayinsa haka suka rinqa tsugunnawa yayan nasu kamar su goya shi, babu wani batun baizo mutuwar ubansu ba, wannan bayanin ya kau kuma tunda yazo musu da chanji..ganin irin yanayin 'yan'uwan nasa ne yasa Abdullahi yi musu rabon kudi suna godiya kamar bakinsu zai yage, sai yammaci Yusuf ya baro gurin aikinsa, gidan mahaifiyarsa ya nufa dan gaisheta kafin ya wuce gida gurin iyalinsa, yayi mamakin ganin motan Abdullahi har sannan bai tafi ba, shima Abdullahin ganin Yusuf din sai yaji ya kama kansa, gashi dai ko da wasa Yusuf bai kaishi a shekaru ba amma yaqi sake masa kamar yanda su Ayuba sukayi, kuma cikin wani ikon Allah sai nan da nan Abdullahi yaji yanason Yusuf din, babu yabo babu fallasa Yusuf ya gaisa da yayan nasa sannan yace zai shiga cikin gidan ya gaisheda goggo, gyada kai Abdullahi yayi ya bayansa da kallo, Ayuba dake nan tsaye kusada Abdullahin ne yace "kasan ai da'aka je kiran namun baya nan shiyasa baka ganmu tare ba" Abdullahi bai ce komai yana kallon bayan Yusuf din..Da yammacin ranann Abdullahi ya juya bai kwana garin ba...

Lokacin da Haihuwar Binta yazo sai abun yazo mata da matsala sosai, yau ciwo gobe lafiya, Hankalin Yusuf duk ya tashi sai mahaifiyarsa ce me dan saka hannu a lamuran nasa dan 'yan'uwansa dai kowa ta kansa yake, kar ma azo zancen Ayuba, dan shi idan bazaka qareshi da kudi ba to kai da banza ma duk daya, ta yanda hatta mutan gari sun san halinsa , kudinka mutuncinka a gurinsa dan kome kace yayi maka indai zaka bashi kudi to tsaf zeyi..

Ahaka dai binta tayi ta fama da jinya 'yan kudaden Yusuf duk suka tafi wajen neman magani, a satin da haihuwan ta fara tasowa gadan gadan wani irin sanyi Binta tayi har hakan yana baiwa Yusuf din tsoro, Na'ima dake Shirin shiga shekara na 9 a duniya ma saida ta fahimci wani abun na damun mahaifiyarta duk itama sai tazama shiru, makarantar ma bata son zuwa dan Yusuf daman tunda rashin lafiyan Binta ya tsananta ya maida zuwa aikin nasa sama sama..
Ranar da naquda ya tashi daman da asuba Yusuf ya nufi wajen mahaifiyarsa suka taho gidan nashi tare tashiga dakin wajen Binta daketa salati da juyi, Yusuf nanan tsaye bakin gadon mahaifiyarsa tace ya dauko kaya su kaita asibiti wanda shi sai a lokacin ma hakan yazo masa kai tsabar birkicewa, riqo hannunsa Binta tayi tace ya matso kusa tanason suyi magana, anan ne kuma tashin hankalinsu yafara linkuwa, dan Binta wasiya tafara bashi akan Na'ima, ta nemi ya kula da ita sannan ta fara neman yafiya, damqe hannunta Yusuf yayi ya fara kuka kamar qaramin yaro yana gyada kai tareda da tabbatar mata zata samu lafiya, Na'ima da tashinta kenan daga bacci, ta shigo dakin mahaifiyar tata itama, kuka ta farayi goggo ta dauketa suka fice, Kafin tadawo dakin Binta tace ga garinku nan, ta koma ga Allah da cikin da bata haifeshi ba kenan....
Hasbunallah...ranar Yusuf kowa ya shaida gigicewarsa, magana yake yana kauce layi, duk wanda yaga yanayinsa sai ya tausaya masa ainun, saboda wani irin tashin hankali ya shiga na rashin abokiyar rayuwan tashi da ba'a iya misaltawa, Na'ima babu baki sai kuka, in ta juya nan da can taga tarin mutane a gidan nasu kuma babu ummanta sai kuka, kuka kam sunyi shi ita mahaifinta har akayi sadakar bakwai basu dawo daidai ba, da qanwar maman Na'ima dake yola tace zata dauke ta Yusuf atake daman yace babu wannan zancen, zai riqe 'yarsa abar masa abunsa,ga kuma mahaifiyarsa tana raye zata tayasa kula da Na'iman, haka ta haqura bayan zaman makoki takoma gidan mijinta babu Na'ima..
Haka rayuwansu ta cigaba me cike da gibi babba, in sun tashi da safe daman tsaf ze wanke 'yarsa ya shiryata, tare zasuje siyo abun karyawan su dawo, sai ya tabbatar ta qoshi sannan ya zuba mata na tafiya wanda zataci a lokacin break, dorata yake bisa Keke su tafi makaranta, a lokacin break daman tun fil azal ma gurinshi take cin abinci, da zaran an tashi kuma ba gida yake maida ita ba, can gurin goggo yake kaita sannan ya wuce gurin sana'arsa a kasuwa,daga gurin goggon ne kuma zata sake shiryawa ta tafi islamiya, sai ya dawo kuma ya sake daukanta su wuce gida wanda babu yanda ita goggon batayi dashi akan ya bar mata Na'iman ba amma abun yaci tura, shidai be fito fili yace A'a ba, amma bini bini in 'yarsa na gidan to ko ya dawo anan zai kai har dare, har se goggon tace ya tafi, da fari yana tafiya gida ya kwana shi kadai amma daga baya sai yayi shinfidi nan bakin kofar goggon yace nan zai kwana, da ta tambayesa dalili yace "goggo gidan yana sakamin kunci arai kullum na shigesa" ganin haka yasa tafara barinsa ya tafi da Na'iman in yaso in sun taso daga makaranta sai ya kawota, dan lamarin Yusuf babu alamun qara aure nan kusa kuma....
Ina labarin Ayuba da dan'uwansa? Nasiru? dan lubabatu tayi nata auren da da dadewa daman har da yaranta manya anan qauyen dake kusa da garin, shi dama Ayuba mata biyu garesa ta farko Jummai sunanta yara na kiranta umma, sannan ta biyu mai suna Abida ana kiranta anty Amarya, shikuma nasira Matarsa Mai suna Laraba yara na kiranta da umma laraba har 'ya'yanta ma haka suke kiranta,
Ta fannin gidan Ayuba dai Allah ya hadasa da guda daya shima, dan jarabar Umma har shi Ayuban tsotsewa take balle anty Amarya, irin fitinannun matan nan ne wanda su a rayuwa kar a zauna lafiya ga son abun duniya, cikin 'ya'yanta mata babu wanda bata dorawa tallan abinci kuma ko nawa za'a kawo mata ko da akwai qari akan kudin baruwanta itadai lafiya lafiya, A lokacin da Binta ta rasu bayan an kwana biyu tisa Ayuba tayi a gaba sai ya dauko mata Na'ima, yarinya ga kyau ba qaramin kudi zata kawo mata ba, to sai aka samu akasin shi Yusuf ba irin mutanen nan bane masu saka saka da lamura, yayun nasa ma tun sa'in da ya fahimci irin rayuwar da suka daukowa kansu , ya rage shiga sabgoginsu, haka duk suka zubawa Yusuf idanu yana kula da 'yarsa tare da tallafin goggo....

Ranan Na'ima suna kan hanyarsu ta dawowa daga makaranta ita da mahaifinta, ya tsaya nan wani kanti ya siya mata biscuits da sweets tanata murna, saida ya bare mata ya bata tafara ci sannan ya hau keken suka qarasa gidan goggo, sun sameta zaune nan kan taburma a tsakar dakinta hannunta riqe da tasbaha tana zikr, bayan Yusuf ya gaishe ta, Na'ima ta miqo mata ledan biscuit din tana murmushi tace "goggo gashi kici kema" ta qarasa maganan cikin muryanta me sanyi hadeda yarinta, murmushi goggon tayi itama tace "kici abunki Na'ima, Allah yayi albarka" Na'ima ta gyada kai ta zauna nan kan taburman, miqa hannu goggo tayi qasan gadon karfenta ta ciro musu kwanon abincinsu da take ajiyewa kullum kafin su dawo, miqawa Yusuf tayi yananan zaune, Na'ima ta miqe ta debo musu ruwan wanke hannu, tare suka ci abincin anan dakin goggon suna hira jefi jefi har suka gama, sai da Yusuf ya miqe zai wuce kasuwa goggo tace "zan aika yarinyar nan taje gidan kawunanta su gaisa anjima tunda babu islamiya" Yusuf yace "toh goggo can din zanje daukanta kenan" goggo ta girgiza kai tace "ai ba wani dadewa zatayi ba" ya gyada kai sannan sukayi sallama ya shafa kan Na'ima dake yi masa murmushin sannan ya fice
Bayan fitarsa ne goggo tace da Na'iman "maza yi sallah sai kiyi wanka ga kayanki nan na fitar miki, kije gidan kawunki ki gaishesu" gyada kai Na'ima tayi tace "gurin anty Amarya?" Goggo tace "A'a har umma ma duk zaki gaisar in kinje" ta amsa da "toh" sannan tafara yin abunda aka sata..
Bayan Na'ima ta shirya goggo tace ta dauki biscuits din nata taje, dayake gidan kawu Ayuban anan unguwar yake kuma tasani sai nan da nan ta isa, shiganta gidan da sallama tasamesu nan tsakar gida, Umma ta girke nan kan kujera hannunta riqe da muciya tana juya marden alala dake cikin kafulas a gabanta, yarta me suna salame zaune gefenta tana murza manja a ledojin da zasu qulla, bin Na'ima sukayi da kallo dukansu har sauran yaran, Umma sai kallon kayan dake jikin Na'ima take ganin yarinyar fes da ita ga uban ya gyara mata gashinta gwanin sha'awa, gaishe da umma Na'ima tayi, Umma bata daina kallonta ba tace "lafiya autar babanta" sai Na'ima tarasa me zata sake cewa gashi duk suna kallonta, tananan tsaye yaron umman me suna Salim ya fizge biscuit din hannunta, ta daga kai tana kallonsa batace komai ba, Salame ce tace "toh da kika tsaya mana aka din bazaki zauna bane, zo ki bude mana leda" da sauri Na'ima ta gyada kai ta zauna nan aka fara aikin alalan da ita, sai da suka gama kulla alalen nan tas da ita sai gumi take na rashin sabo, bayan sun gama ta kalli umma a hankali tace "Umma zanje gurin Anty Amarya" Salame ta sake cewa "wani ya hanaki ne" miqewa tayi tafara karkade riganta ta nufi dakin anty Amarya da ke nan gefen na umma, a kwance ta sameta kasancewar tana fama da laulayin sabon ciki, Anty Amarya na ganinta tafara murmushi tace "wace wannan kaman Na'iman abbanta?" Na'ima ta fara dariya dan tanason anty Amarya kaf gidan ita kadai take mata fara'a har ta bata abu in tazo, Anty Amarya ta sauqo daga kan gadon nata dakyar ta kama hannun Na'ima tana tambayanta ya makaranta, sai lokacin Na'ima ta sake tafara magana, data fita debo ruwa ma Anty amaryan Umma tace tazo tazauna ayi gyaran shinkafah da ita, komawa gidan goggon da bata ba kenan sai nan gidan kawu Ayuban babanta yazo ya dauke ta a kekensa suka wuce gida, da daren ranan Na'ima na zaune da mahaifin nata anan veranda na qofar dakinsu tace "Abba" ya dago kai yace "Na'am 'yar Abba" tace "dazu Salim ya kwacemin biskit dina" yayi murmushi tareda kai? hannunsa ya shafa kanta yace "sharing is caring daughter, kinga kin 'yammasa kenan" Na'ima ta jijjiga kai tace "toh zaka siyamin wani?" Ya sake gyada kai tareda cewa "gobe ma" cikin son kawar da zancen yace ta fara fado masa karatun da sukeyi a islamiya, nan tafara yana kallonta fuskarsa cike da walwala, ganinta a ko yaushe na tuna masa da Binta sosai wanda tun hakan yana sosa zuciyarsa har ya saba, sai kallonta yake tana magana aransa yana roqon Allah...yabashi tsawon rai su rayu tare da 'yarsa har girmanta.

But, if wishes were horses......

Wayewar washegari Na'ima ta riga mahaifinta tashi, dama anan dakinsa take bacci shi a qasa ita akan gadon, sauqa tayi takai hannu tadan tabasa, jin kamar yana bacci yasa ta fita abunta dan dama a matse da uzurin fitsari ta tashi, har taje tayi ta dawo bai tashi ba, ta zauna tana jiran ya tashi suyi alwalan tare shiru bai tashi ba, sake taboshi tayi tace "Abba" shiru kamar me bacci gashinan idonsa a rufe, fita tayi tayo alwalan sannan tadawo tafara sallah, har gari ya waye bataga Abbanta ya tashi ba, daga qarshe ta miqe ta? fita daga gidan, gidan goggo ta nufa tana sauri, isarta gidan tasamu kawu Ayuban yazo gaishe da goggon sunanan zaune a daki, ganin Na'ima ita kadai da sassafe yasa goggo tadanji hankalinta ya tashi ta fara tambayanta meya faru, fada musu tayi Abban ta yana bacci tayi tayi ya tashi kuma shiru, Ai atare goggo da Ayuba suka miqe,fita sukayi a gigice basu tsaya ko Ina ba sai gidan Yusuf suka shiga har cikin dakinsa suka samesa nan kwance kamar yanda Na'iman ta barshi, Ayuba ya jijjaga shi goggo ma ta matso tana kallonsa hankali tashe, a sannan ne suka gane rai yayi halinsa..
Yusuf ya koma ga Allah acikin baccinsa......


Bintu Musa ce
'?=???

https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c

WhatsApp group
https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z


('KUNCIN ZUCI('
Na Bintu Musa


Chapter 23

Na'ima dake nan tsaye bakin kofan sai raba idanu take alamun tsoro duk ya bayyana a fuskanta bata qaraso cikin dakin ba, fara gyara masa kwanciya kawu Ayuba yayi kuma sai akayi sa'a jikinsa har lokacin da laushi, goggo sai hawaye take tana cewa "wayyo ke duniya, wayyo ke duniya, Yusuf na yafe maka, Allah na gani kai da ne me biyayya, Allah ya yafe maka Yusuf" kawu Ayuba ma da idonsa suka ciko da hawaye yafara amsawa da "Amin Amin Amin, Allah ya maka rahama dan'uwana" sai kuma ya fashe da kuka yakai yatsunsa yana danne idanunsa gwanin tausayi, sai sannan Na'ima ta fara takawa cikin dakin, goggo da ta manta tare suke da ita ne tayi sauri miqewa ta tarota kafin ta qaraso, kawai Na'ima tafara fisgewa zata kai ga gurin mahaifin nata dake kwance tafara cewa "Abba" "Abba" duk girman Na'ima haka goggo ta fara ciccibarta tayi waje da ita tana cewa "muje waje yana bacci tukunna Na'ima" bin bayansu kawu Ayuba yayi shima ya rufo dakin sannan ya fita daga gidan..kuka Na'ima tafarayi da goggon ta shiga da ita dayan dakin, itama kanta goggo zuciyarta a wannan lokacin cikin nauyi yake na rashin danta amma haka ta rugume Na'ima a jiki tafara lallashinta...
Su umma ne da anty Amarya suka fara zuwa gidan suma hankali a tashe sannan mutanen unguwa suka rinqa tittilo gidan, zuwa wannan lokacin su kawu Ayuba har sunyi duk wani abunda ya kamata, Na'ima sai ido, bin kowa take da kallo babu uhm babu A'a, ganin mutanen cike a gidansu yana qara tuna mata cewa hakan akayi fa lokacin na mahaifiyarta kuma har yau gashinan bata dawo ba, sai sannan tafara ayyanawa a ranta abbanta ma haka zai faru kenan?, ai batasan lokacin da ta miqe ba ta nufi fita daga dakin tana tsallake mutane, fitan ta tsakar gidan yayi daidai da fito da mahaifin nata cikin makara, Ihu tayi da qarfi ta nufesu anty Amarya na kamota tana fisgewa, tana kukan tana cewa "wayyo abbana, wayyo kubarmin Abbana" babu wanda bata sashi hawaye a wannan lokacin ba ganin yarinyar da bata rufa shekara goma ba maraici ya mata kamu dumu dumu babu wa ko qani a duniya, Haka Na'ima tanaji tana gani aka fice da mahaifinta tana kuka kamar zata suma ta kwanta ajikin anty Amarya, rayuwa kenan, Yusuf yazama tarihi sai a bisa da addua...
Da Ayuba ya kira Abdullahi ya shaida masa mutuwan dan'uwan nasu, shima yaji mutuwan sosai barin in ya tuna lokacin da yaga Yusuf din, hakuri ya bawa Ayuba ya bashi uzurin baya qasar a wannan lokacin amma da zarar yadawo zaizo nan gidan.

Zaman makokin ma maidashi gidan goggo akayi, ta shiryawa Na'ima dukan kayanta suka koma can gidanta aka kulle nan gidan Yusuf din, a wannan satin duk wanda yaga Na'ima sai ya zubda hawaye, magana daya biyu zatace Abbana, sai dai tayi ta bin mutane da kallo bata iya cin abinci har se anty Amarya ko goggo wani cikinsu ya tusata gaba sannan zataci kadan..
lokacin da qanwar maman Na'ima tazo, bawani saninta Na'iman tayi ba sai dai kallonta kawai data rinqa yi, ta rungumota ta fashe da kuka, tanajin har mutuwan Binta na dawo mata sabo..
Bayan anyi zaman makoki na tsawon kwana bakwai kuma ta nemi tafiya da Na'iman dukda itama bawani qarfi mijinta ke dashi ba, goggo ce ta hana, dan inta su Ayuba ne baifi ragin wani nauyin ba, goggo tace da halima yarinya ba rasa madafa tayi ba tunda ga iyayenta maza sunanan, dan haka ta barta nan cikin dangin mahaifinta za'a kula da ita.
A wannan lokacin ne Na'ima ta fara daukan dangana, sai shiru kuma daya sake shiganta har hakan yana baiwa goggo dan tsoro wani sa'in, a tarin lokuta zata farka cikin dare kawai tayi ta kuka nan kan gadon goggon, sai da goggon ta fara hadawa da addu'o'i sannan Na'ima ta fara samun nutsuwa....

Bayan 'yan satikai goggo ta fara sata zuwa makaranta, Na'ima bata taba sanin nisan makarantan haka yake ba sai ranar farko da ta fara zuwa a qafa, tana tafiya hawaye cike idonta tazo tawuce ta gurin da mahaifin nata ke siya musu abinci idan ze kaita makaranta, data je makarantan ma bata gane komai ba, kawai zama tayi shiru ta rinqa kallon window, da aka tashi break ma nan kan bench dinta ta kwanta bata fita ba, da aka tashi ma haka tafito ita kadai zata tafi, gashi bawani qawaye gareta ba, daman qawarta daya ce kuma a islamiya ne, haka ta sake takawa da kafa tana gumin cikin rana ta koma gida...

Ana wannan halin goggo tayi Kiran Ayuba da Nasiru wata rana da safe bayan Na'ima ta tafi makaranta, bayan sun dan taba hiransu da ya shafi rayuwa goggo ta

15 / 25