Chapter 16 Reading Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc Arewa Novels

Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc

Author :  Binta Musa Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   16 / 25

45K to 48K   out of 73.5K words

gyara zama tace "toh, kunga dai dan'uwanku Allah ya karbi abunsa saidai mu bisa da addua da kuma fatan in tamu tazo Allah yasa mu cika da imani" suka gyada kai cikin fahimta tareda amsawa da "Amin" , goggo ta cigaba "ga jininsa nan ya bari, kuma hakki ne da ya wajaba a kanku da ku kula masa dashi, wannan yarinya yanzu gatan ta shine Allah sannan ku da nidin gaba daya" Ayuba ya sake gyada kai yace "wannan haka ne goggo" goggo tace "yauwa, acikin ku biyun nan dole dayanku ya dauki ragamar kula da rayuwan yarinya da dawainiyarta" Nasiru ne yafara magana yace "Toh goggo da kika ce mu kula da rayuwan ta, kin fa sani, ni dinnan ba iya kulawa zanyi da karatun ta ba" Ayuba yace "atoh, kar nayi magana ne ace daman na fiye subul da baka, goggo kina gani dai muma 'ya'yanmu ba makarantar nan suke ba" goggo ta dan gyara zama ta kwantar da murya tace "haquri zakuyi ai, tunda Allah ya dora mana nauyin gaba daya" Ayuba ya jijjaga kai yace "A'a goggo, wanda Allah ya dorawa nauyin yau babushi, hakuri zatayi da bokon nan, ni dai in kulawa da ita ne naji na dauka a kaina, tunda yanzu tana zama gurinki sai ta cigaba da zaman har lokacin da Allah zai kawo mijin aure, in kuma 'yar sana'ar nan zaki fara qulla mata irin nasu salame ne to duk daya" goggo tayi shiru tana kallonsu duka batace komai ba, haka suka karkade rigansu suka mata sallama dukansu suka fice daga gidan, aka barta nan zaune jikin duk yayi sanyi ainun....

Isar Ayuba gidan yasamu umma da anty Amarya nan tsakar gida, umma na zaune bakin murhu tana iza icce na dafin awarar da su salame zasu fita siyarwa da rana, gidan babu yara wasu sun tafi yawo wasu kuma sun fice tallan kunu, su salame da dayar qanwarta sa'ar Na'ima daman sun tafi tuyan qosan safiya can bakin titi..
Tsayawa nan tsakar gidan Ayuba yayi matan nasa suka gaishesa ya amsa sannan ya fara musu bayanin abunda suka tattauna da goggo, umma na gyara daurin dankwali tayi masa wani irin kallo tace "toh yanzu da kulawan yarinya ya dawo hannunka din, can gidan zaka rinqa binta kana kulawan da ita kenan" Ayuba yace "bangane maganar ki ba jummai" umma ta sake cewa "toh ai naga indai aka bawa mutum ragamar kula da maraya daman dauka yake a gurinsa ya riqe, wane irin kula ne kuma an baka ita kuma an riqeta, haka ake bada yaron dama" Anty Amarya dake zaune bakin kofar dakinta tana kulla kayan miyanta a leda tace "toh yanzu ina aibu anan maman salame" Umma ta daga mata hannu tana hararta tace "Kinga ni ki daina???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? tsomamun baki in ina maganar arziqi, yarinya ba da gwal aka sassaqeta ba sai nan nan ake da ita kamar qwai" ta kalli Ayuba dake tsaye tace "akawota nan din a hadeta da sauran yaran, ai da bai fi da ba" Ayuba yace "yanzu dai duk wannan maganar bata taso ba, daman ai ni nace da goggon ta cigaba da riqeta a gurin ta ganin sun fara sabawa" a dan fusace umma tace "to wai har kun aminta da riqon kaka kenan, sai yarinya tazo ta tabarbare duniya ta rinqa zagin ku akan kun barta sakaka tun farko, to wallahi bazai sabu ba, nan za'a kawota duk ka hadeta da naka 'ya'yan ka kula dasu tare" Anty Amarya ta jijjaga kai bata ce komai, Ayuba yace "shikenan ai, dama bokon nata mun tsaidashi haka nan, zata dawo nan din da zama" Anty Amarya sai kallonsa take tanajin kamar ta makeshi, shi kenan kullum sai abunda umma tace a gidan yake amfani kamar wani qaramin yaro, Ayuba yafara murmushi sannan ya sake cewa "yanzu akwai sauran kunun da qosan ne jummai?" Umma ta juya kai tana magana dakyar? "gashi can daki ai na ajiye maka" cikin bacin rai Anty amarya ta dauki farantin kayan miyan nata ta shige daki umma na bin ta da wani kallo...
Washegarin ranan da Ayuba yaje gaishe da goggo ce mata yayi ze tafi da Na'ima, goggo ta dan tsaya kallonsa da farko sai kuma ta sauke numfashi tace "kafara canja magana kenan?" yace "abun da yakamata ne goggo, in Ina ganin ta a gabana zan fi sanin halin da take ciki ai, kuma zanfi kula da ita" goggo tace "nan da can din ma ai duk dayane nagani" Ayuba ya sake cewa "goggo yarinyar nan na amsheta akan ragamar komanta yadawo wuyana, kuma inason daukanta sai ace ba haka ba" goggo ta jijjaga kai tace "ya taka ce ai Ayuba gaka ga ita, sai ka tafi da itan" tsayawa kallon goggo yayi Jin yau ta kirasa da sunansa, Na'ima ta shigo dakin hannunta riqe da kayan makarantar ta data debo daga gurin shanya, Ayuba ya kalle ta yace "Na'ima ki shirya kayanki anjima da yamma ki koma can gidan" A sanyaye Na'ima tace "toh kawu" sannan ta ajiye kayan ta sake ficewa daga dakin tabarsu nan zaune suna bin bayan ta da kallo...
Da yammacin ranan goggo ta hadawa Na'ima kayanta acikin akwatinta, ta kalli Na'iman dake zaune bakin gadon karfen dakin tace "ki rinqa zuwa akai akai kinji Na'ima" dan har ga Allah kallon Na'iman na rage mata wani radadin na rashin Yusuf a tare da itan, gyada kai Na'ima tayi tana jin hawaye na zuwa mata, addua take Allah yasa ta zauna a gurin anty Amarya in taje can din, sunanan zaune Kamal yazo dan gidan umma wanda ya girmewa Salim, aikosa Ayuban yayi akan su taho da Na'iman tare, haka tayi sallama goggo na jaddada mata cewa "nan da can din duk dayane Na'ima, koyaushe kikeson zuwa kizo abinki" Na'ima na hawaye ta juya suka tafi tare da Kamal din ..
A qofar gidan suka samu kawu Ayuban kasancewar bai dade da dawowa daga gurin sana'arsa ba suka shiga gidan tare da Kamal Na'ima na biye dasu a baya, dakin anty Amarya shi kawun ya nufa yafara daga labule yana leqa ciki, umma ta fito tana gyara zaninta ta tsaya nan kusa dasu, Ayuba ya kalleta sannan ya tambayeta Ina Abida dan bai ganta cikin dakin nata ba, Umma tace "gurin abidan zaka bada itan kenan" Ayuba ya gyada kai tareda amsawa da "wai hakan naga kamar yafi" Umma ta tabe baki tace "toh da cikin nata zataji ko da riqon dan wani Malam, nidin kana ganin zan mata wani mugun abune da bazaka bani riqon nata ba ko me" Ayuba yace "bana son fitina jummai, dan zan bada yarinya gurin Abida ba yana nufin zaki mata wani mugun abu bane" A dan fusace umma ta sake cewa "Malam fifiko kawai kakeson kayi anan, ace Ina babba agidan nan zaka kawo yar riqo kabawa Abida, narantse bazata sabu ba ai ba ita kafara aurowa a gidannan ba" Ayuba ya karbi akwatin hannun Kamal ya jefashi nan gaban jummai din yace "ga ki ga ita" ya juya ya fice daga gidan sanin in suka fara irin haka da umma toh ba'a qarewa qalau, Umma ta kalli Na'ima dake nan tsaye kamar ruwa ya cinyeta tace "zo ki dauki jakarki ki ki dakin su salame, can? zaki zauna" Na'ima tayi saurin gyada kai ta dauki akwatin ta wuce dakin, ranar dakyar Na'ima tayi bacci nan kan wata yolokuwar katifa, su salame duk sun matseta..
Washegari da sassafe Na'ima ta tashi, bayan tayi sallah ta fito zata debi ruwan wanka taga randa wayam, umma dake hada wutan girkin safe tace "zo ki dauki bokati ki debo ruwan acan bakin bohole din dan'iya" Na'ima ta amsa da toh ta dauki bokatin ta nufi fita daga gidan, layi ta iddasar maqil a bakin famfon, haka ta ajiye bokatinta a layin ta bi sahun 'yan jira suna nan tsaye..
Ruwa ta rinqa judowa da safiyar Allah su salame na zaune bakin murhu tareda uwarsu suna aikin kunu da hada qullin qosai, bayan Na'ima ta debo ruwan sosai tazo gurin umma a hankali tace "umma zanje inyi Shirin makaranta" Umma tace "inace makarantar ance babu ita yanzu kuma, to ki jira baban naki yazo kiji ta bakinsa" Na'ima da duk jikinta yayi sanyi ta amsa da toh ta juya zata tafi salame ta kirata tasata daukan itacen da zasuyi tuya acan wajen, tare suka tafi hannun Na'ima riqe da itacen, ranan anan gefen salame tayi wunin safiyar, babu baki sai bin kowa da Ido, in anason chanji ita ke badawa, dan miqo takarda da leda, har iza icce duk ita keyi, tun idon ta na hawayen hayaqi har ya hakura, baiwar Allah data dawo ma ba'a barta taje islamiyan ba, sai da anty Amarya tayi magana, umma ta hau masifan cewa ai yarinya dai ance tagama karatu kuma, inba Sana'a ta kama ba to bacci zatayi agidan kenan..
Daga wannan lokacin kuma rayuwan Na'ima ya chanja salo kuma tun tana binsu salame tayasau ayyuka har aka fara dora mata nata tallan, kuma babu laifi tana ciniki saidai har yau kuma babu dogon magana a lamarinta, in kaji bakinta tana magana to lissafin kudi suke da umma, sauqinta daya da ta samu shine umman tafara son ta ganin irin kawo mata kudin da takeyi, dan Na'ima komai nacin mutum bata basa bashi, gashi gurin da take kai abincin ba dogon magana take ba, sai ba kowa ke shiga harkarta ba, ana cikin wannan halin ne watarana da safe kafin Malam Ayuba ya fice aiki wani yaro ya shigo akan yana sallama dashi, bayan Ayuba ya fitan ya samu wani mutumin tsaye yana jiransa, gaisawa sukayi sai a sannan Ayuban ya gane sa abokin Yusuf ne kuma wajen aikin koyarwarsu tare, Sambo yafadawa Ayuban akan yazo ne kan batun komawan Na'ima makaranta yaga shiru bata zuwa shine yazo yaji ko lafiya, Ayuba yace "batun makarantar yarinya mun dade da ajiyeshi a gefe Sambo, sanin kanka ne duk cikin yarana babu me zuwa makaranta balle ince zan ware Na'ima ita kadai takoma karatu, toh ma da wane kudin zan kaita makarantar?" Sambo yace "toh Malam yanzu duk wannan dai bazai zama matsala ba in Sha Allah, munyi zama na amana da Yusuf wanda baici ace bayan ransa munkasa saka masa da alheri ba, Na'ima 'ya ce a wajena nima kuma in zaka amince zanyi iya kokarina na ganin na biya kudin duk wani hidimomin makarantar ta" da farko qin amincewa Ayuba yayi da batun sai da Sambo yadan bashi wani abu shima yace gashinan babu yawa yayi hidiman gidansa sannan ya yarda,bayan tafiyan Sambo ya? qirge kudin ya sake su aljihu sannan ya juya ya shiga gida, tijara umma tafara yi akan hakan bazata sabu ba, Na'ima na zaune tana taya anty amarya kullin kayan miya, ta dago kanta tana kallonsu Jin abunda da kawu ya fada, zuciyarta taji yana sanyi saboda tanason makarantar kawai anfi karfinta akai ne, Ayuba dai ya tsaya tsayin daka ranan kan jummai, akan sai Na'ima ta cigaba da makarantar ta, miqewa Na'ima tayi ta shiga dakinsu ta fara duba akwatinta, ciro kayan makarantar tayi tana murmushi zuciyarta cike da farin cikin da bazai misaltu ba..
Daga wannan ranan ne kuma Na'ima ta fara samun sauqi a lamuranta, zataje makaranta daga nan ta biya gurin goggo su gaisa dan lokacin da aka sakota gaba da tallan bata samun zuwa gurin goggon ma, islamiyan ne dai yakoma asha ruwan tsuntsaye take masa, yau taje gobe umma ta dora mata talla, haka dai rayuwan ta cigaba..
A lokacin da Na'iman takai shekaru sha uku a duniya wani dan mai unguwa dake bibiyanta akai akai ya fito gadan gadan akan yana sonta, zuwa lokacin Na'ima ta gama primary, da Sambo ya nemi ta cigaba da makarantar gaba da primary daman Ayuba cewa yayi besan wannan zancen ba kuma, yanzu kuma umma har ragamar bata nata tuyan doyon takeyi, itace me tuyan da qannenta daya zuwa biyu masu zama kusa da ita suna taimaka mata gurin saidawa, sau tari in lawan yazo gurin ta har ya gama surutunsa bata dago kai ta kallesa ma, aikin gabanta takeyi haka zai qaraci surutu ya siyi doyan ya qara gaba, da lawan yaga ba samun kanta yake ba ne yasa ya biyo ta bayan fage direct ya samu kawu Ayuba da maganan, ranan farko da yazo gurin sa daman da babbar ledarsa kasancewan yanada kantin sa na saida kayan abinci kuma ba laifi yana samun rufin asiri da sana'ar, da lawan ya gama fadawa kawu Ayuba buqatarsa sai ya hada da miqo ledan hannun wadda ke cike da kayan abinci da kuma dan abubuwan amfani na yau da kullum, ba kunya Ayuba ya miqa hannu ya karba yana godiya yace masa zai turo masa Na'iman in ya shiga kuma ya kwantar da hankalin sa yarinya babu goron kowa akanta daman, murya gurin lawan ba'a cewa komai..

Da Ayuba ya shiga gidan umma ya fara fadawa wannan abun arziqi, zuwa wannan lokacin duk wani zafin umma akan Na'ima daman ta sauqe shi tunda yarinya na kawo mata riban Sana'a isasshe ga babu qiwiya a lamuranta, washe baki tayi tace "Na'ima dai yarinya da qashin arziqinta take yawo" Ayuba yace "yaro kam da arziqinsa, kantinsa na nan babba a bakin kasuwa" Umma tace "gashi ance har buhunhunan shinkafah yake sarowa daga legas" salame dake zaune bakin kofan umma tace "kuma wallahi umma duk Thailand, babu 'yar tsinta" itadai Na'ima na zaune kan kujera tana dinke hijabin ta da zare da allura batace komai ba, Amma zuciyarta se zafi take jin wai lawan dinda bataso suke qoqarin qaqaba mata, sauqar da kanta tayi gudun kar su ga hawayen da ya taru a idonta, Anty Amarya tace "Amma Malam baka nemi amincewar yarinya ba har da karban abun hannun yaron Fisabilillah" Umma na gyara daurin zaninta tafara nuna anty Amarya da yatsa tace "ke fa dadi na dake indai aka fara magana ta arziki sai kin san yanda kika yi kika lalata ta, abun naki zai fara komawa hassada kuma" Anty Amarya tace "meyasa zanyi hassada a Na'ima tana matsayin yar cikina, gaskiya ce dai bakwa so" Ayuba ya dubi Na'ima yace "ke, ajiye abunda da kikeyi kije yaron na waje yana jiranki" Na'ima ta zare alluran sannan ta miqe tazo ta wuce ta gaban su suna tsaye ta shiga dakinsu kanta a duqe, umma tace "ahtoh, yaro da rufin asirinsa kuma me za'a jira, ai duk gidan da akace akwai abinci, toh lafiya lafiya" Anty Amarya ta jijjaga kai tace "shine kawai damuwanki" umma tace "shine damuwar kowa ma, shi kawun nata kinga yana kawowa akai akai aci a qoshi ne, ba kowa tasa ce take fisshesa ba watarana a gidan nan" ganin abun ze dawo kansa ne yasa kawun cewa "ya isa hakan nan banason wata fitina kuma"...duk yanda lawan yaso shawo kan Na'ima ta masa magana taqi, wani daskarewa tayi nan tsaye idanunta na kallon gefe dan ko fuskarsa batason gani, yace "kiyi hakuri bansan ta yanda zan bullo ki aminta dani bane, wallahi Ina sonki Na'ima" duk qananan shekarun Na'ima a wannan lokacin ta san me kalman so din ke nufi, tace "ni banaso kasake zuwa gidanmu, makaranta nakeson inyi" lawan ya marairaice yace "indai makaranta ne zan barki kiyi har ta gaba da sakandiri Na'ima, nidai ki amince kawai muyi aure" bata amsa masa ba ranta a bace ta juya ta shige gidan ta barsa nan tsaye..hakaa lawan ya maida kofar gidan kawu Ayuba gurin zuwansa akai akai, gashi duk lokacin da zezo indai kawu Ayuba yananan toh sai ta fita ko bata so, dan baya zuwa babu leda, wanda hakan kesa Ayuba qara ganin arziqinsa..
Ahaka magana ta fara nisa tsakanin lawan da Na'ima, Ayuba ya fadawa goggo shidai ze aurar da Na'ima hakanan tunda a musulunce takai gejin aure, ganin irin rayuwan da Na'iman keyi a gidan Ayuban na sana'ar abinci yasa goggo amincewa, aranta tana fatan ko hakan zai zama rufin asirin Na'iman inta kama dakin mijinta itama...lawan?bai dau lokaci ba ya turo iyayen sa da goro aka bashi Na'ima wanda hakan ba qaramin farin ciki ya sashi ba ganin Na'ima ta kusa zama mallakinsa..
Babu yanda Na'iman ta iya haka ta fara kulasa ba'a son ranta ba, bin ta yake har gurin tuyan qosanta yana tsattsare maza masu kulata, har hakan yafara taba mata kasuwanta, umma ce tayi magana da Ayuba akan yaja masa kunne tun ba'aje ko Ina ba zai kashe musu kasuwa sannan yadaina zuwa, Amma kam duk dare lawan da guzurin ledarsa yake zuwa gurin Na'ima duk dan kawai yasamu kanta yanda yake so amma abu yaci tura, zaizo ya qaraci surutunsa amsarta sune "uhm" ko "A'a", ranar da yazo yace mata zeyi tafiya zuwa Lagos Na'ima ji tayi kamar an yaye mata damuwanta bila adadin, dan har ga Allah ta gaji da ganinsa bini bini koyaushe a qofar gidansu..
Watarana ta gamo sanarta da hantsi qannenta sun riqo mata murhu da robobinta suna tafiya, a hanya ta gamu da qawarta wanda sukayi islamiya tare, a bakin sa'ade taji wai ashe tafiyan da lawan yayi zuwa Lagos din, zuwa yayi siyo kayan aurensu, dan sa'ade'n 'yar uwarsa ce, tabe baki Na'ima tayi tace "Allah ya taimaka" tayata riqe wasu kayan sa'ade tayi suka tafi gidan tare suna hira jefi jefi, isarsu gidan suka samu wata mota dalleliya fake nan kofar gidan, tsayawa sukayi kallon motan dan ita dai Na'ima bata taba sanin kaf danginsu ma akwai me mota irin wannan ba.......

Bear with me please, munzo fagen dake buqatan hausan shiyasa zakuga kuskure cikin hausan nawa, dakyar nake kamallota

https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c

WhatsApp group
https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z


('KUNCIN ZUCI('
Na Bintu Musa

Chapter 24

Qarasawa qofar gidan su Na'ima sukayi idonsu na kan motan, sa'ade na ware Ido tace "wai, ke kinga wata mota, dama kunada 'yan'uwa masu kudi Na'ima?" shiru Na'ima tayi batace komai ba suna tafiyan, sai da suka zo daidai jikin motan sukaga wani dan dan babba mutum daga daya barin motan yana zaro bendir din taliya, dagowa yayi suka gaishesa gaba dayansu, itadai Na'ima har sannan bata gane sa, shigan su dan lungun dazai sada mutum da cikin gidan sukaga wani babban mutum cikin manyan fararen kaya hakimce nan kan babbar tabarma me dauke

16 / 25