Chapter 8 Reading Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc Arewa Novels

Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc

Author :  Binta Musa Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   8 / 25

21K to 24K   out of 73.5K words

gurin na'ima ba, atake abubuwa dayawa suka darsu mata acikin rai.....

Bintu Musa ce
'?=???

('KUNCIN ZUCI('
Na Bintu Musa

ArewaPen
https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c

Chapter 15


Tsaye suke a restroom din gaban sink me madubi, nafisa ta kunna famfo ta tara hanky din sannan ta cigaba da goge jikin rigan na'ima, itadai na'ima ta riqe rigan tana kallon yanda nafisan ke goge mata ranta in yayi dubu to ya baci a wannan lokacin, dan itadai tasan miqa hannun datayi beci ace hannunta ne beyi reaching to Laila ba har coffee din ya kware mata a jiki, tarasa me ta tsarewa yarinyar da ta fara sakota a gaba haka, tana cikin wannan tunanin taji nafisa tayi tsuka me karfi tace "narasa ta Ina Laila ke tunani, ita duk wani abu dazatayi cikin rashin da'a yinsa take kamar ba mace ba, dan ko kaffara bazanyi ba da gangan ta juye miki a jiki, kuma wallahi kinji nayi rantsuwa..bashi taci"
Na'ima tadanyi murmushi da iyakacin sa leban ta tace "ki barta nafisa, yaushe ma zata sake ganina?" Nafisa ta dago ta kalli Na'iman tace "Ai batada hankali ne shiyasa zan koya mata" na'ima jijjaga kai tace "a'a wallahi ki barta nafisa" Ahaka suka gama goge gurin da coffee din ya taba suka fito tare daga restroom din.
Komawansu gurin 'yan'uwan nasu basu samu Laila ba a wajen sai mazan dake tsaye still, dan barinsu na'ima wajen takaici ya ishi Laila anan tsaye tamusu sallama inda ba wanda yakulata cikin su sai Adam da Al'ameen, haka ta juya cikin qunan rai ta bar gurin ta koma gida..
Isowarsu na'ima gurin faruk yadan matso garesu yace da na'ima "Are you sure you're okay na'ima?" Na'ima tayi murmushi ta gyada kanta tace "ya gogu ai yaya" faruk yace "but you're drenched ai, ko zaki koma a chanja kayan" na'ima ta sake jijjaga kai tace "a'a babu komai zai bushe a hankali" Ahmad dai dan kallonsu yake baice komai ba, Adam yace "sorry na'ima" ta gyada kai tana murmushi tace "laa bakomai dai yaya"...ice coffee dinda kowa bai sha ba kenan aka barshi anan waiting area kan kujera.
Sunanan tsaye bada jimawa ba akayi calling jirginsu , sallama suka farayi da juna, Nafisa tayi hugging siblings din nata da daddaya, na'ima na tsaye tana kallonsu jikinta duk a sanyaye, kasa daurewa Abubakar yayi sai da ya matso gurinta yayi mata hug din, yace "anty na..we will miss you" tadan shafa bayansa tana dan dariyan qarfin hali.
Ahaka sukayi sallama Ahmad yayi gaba su na'ima suna biye dashi a baya janye da box dinsu, shigarsu cikin jirgi sukaga shi yayi hanyan kofan da zai sada mutum da first class, qarasawa seat dinsu sukayi dake business class..bayan sun ajiye kayan nasu a sama Na'ima ta zauna jikin bakin window tafara maqala seatbelt dinta..
Basuyi nisa da tashi ba wata waitress tazo seat dinsu ta tsaya ta kalli Na'ima tace "are you Na'ima?" dan gyada kai na'ima tayi tana yiwa waitress din kallon tambaya while nafisa ta amsa da "Yes..she is" miqo wa na'ima jacket din hannunta tayi wanda qamshinsa duk saida ya cika musu hanci tace "here...someome from other side of the plane send me to give you this" kallon waitress din na'ima ta tsaya yi bata karbi jacket din ba, sanin Ahmad ne ya aiko wa na'iman jacket din jikinsa ganin jikinta a dan jiqe earlier yasa nafisa karban jacket din daga hannun waitress din, tayi murmushi tace "thank you miss" murmushi waitress din tayi ta juya tabar gurin su, Na'ima ta juya kanta tana kallon window batace komai, kawai ji tayi nafisa na lulluba mata jacket din a jikinta tayi saurin juyawa tana kallon nafisa dake murmushi kamar bakin ta ze yanke, hannunta tasa tafara ture jacket din daga jikinta itama tace "ni nace miki inaso ne, ke ki lullaba ajikin naki mana" dan dariya nafisa tayi tace "to ai bani na jiqe ba baby na'ima" Na'ima ta harareta tace "wace babyn?" Nafisa ta dan daga gira tace "ke mana... gashinan saboda riganki ya jiqe ana lallabaki harda jacket" Na'ima ta tsaya kallonta kawai takasa magana ma, dariya nafisa tayi itama tana kallon nata tace "Kinga wani instinct dana gani gurin yaya Ahmad yau, girl you have alot to gist me and i mean everything" Na'ima ta sake juya kanta tace "kin shiga uku da wannan mind din naki nafisa, ni babu komai tsakaninmu" nafisa ta cigaba da lullaba mata jacket din tace "naji..yanzu dai let's get you warm baby" na'ima ta sake buge hannunta tana dan murmushi tace "zan miki ba dadi nafisa"
Nafisa tana dariya ta sake cewa "Baby"
Haka Na'ima ta hakura nafisa ta lulluba mata jacket din a jikinta qamshin rigan na cika mata hanci, ahaka bacci ya dauke ta zuciyarta na saqa abubuwa daban daban...

Sai shida saura jirginsu ya isa London, bayan anyi announcing fitan su, na'ima ta sauqe jacket din daga jikinta ta miqa kan cinyan nafisa tafara shirin miqewa, dan ware Ido nafisa tayi tafara dariya tace "lallai ma yarinyar nan, ni na lulluba dashi ne?" na'ima ta miqe tana gyara squeezing din riganta tace "ke kika karba daga hannun wadda ta kawo ai" kawai dariya nafisa tayi ta dan gyada kanta...fitarsu basu gamu da Ahmad ba suka fara tafiya Nafisa nata waige waigen inda zata hangoshi suka shiga cikin airport din, saida suka wuce arrivals nafisa ta ciro wayanta daga jaka ta fara kiransa, bayan ya dauka sun gama magana Nafisa tace da Na'ima "muje sis"
A wajen airport din suka samesa tsaye da jaka a rataye cikin white t-shirt mai dan kauri, jacket dinsa dake rataye hannun nafisa ta miqa masa tace "gashi yaya mungode" karba yayi ya kalli Na'ima dake tsaye, bude bakinta tayi a hankali tace "thank you" Ahmad ya gyada kansa yace musu "The driver is on his way"? sannan yafara saka jacket din a jikinsa, nafisa tace "toh yaya"
Dayake spring season yadanyi nisa sai ya zamto garin babu wani sanyi sosai....suna nan tsaye wata sleek ride tayi parking a gabansu wani bature yafito yana gaisheda da Ahmad, amsawa yayi, drivern ya gaisa dasu nafisa sannan yafara diban kayansu yana sakawa a booth Ahmad na tayashi..bayan sunyi settling acikin motan Ahmad na gaba ya fadawa drivern unguwar anty Amnah suka dauki hanya.

Isarsu gidan anty Amnah bayan driver ya sauqo musu da kayan nasu suka wuce bakin entrance din nafisa ta danna door bell din, basu jima anan tsaye ba Anty Amnah ta bude, cikin fara'a tayi hugging dinsu tace "oyoyo 'yan makaranta sun dawo" ta jasu suka shige cikin gidan nata mai kyau dake screaming luxury, twins basa nan suntafi makaranta shikuma abbansu yana asibiti, kafin su zauna nafisa ta wuce gurin dining area ta dauko musu bottle water data gani a gurin ta dawo falon tana miqawa na'iman daya tace "anty tare muke da yaya fa" Anty Amnah ta dan ware ido kafin tayi magana taji an danna door bell din again, miqewa tayi ta je ta bude Ahmad yace "Momma kin rufeni a waje" Anty Amnah tayi dariya ta riqo hannunsa suka shigo cikin gidan tana cewa "Na isa son, kaida ganinka yayi tsada a London ma" zama shima yayi nan falon Anty Amnah tasake cewa "Kasan ban kawo araina tare kuke bane wallahi" Ahmad yadanyi murmushi kawai..miqewa anty Amnah tayi ta debo musu drinks harda snacks, da kuma abinci tace "zakuci yanzu ko sai kun huta?" Na'ima batace komai ba sai nafisa ce tace "A'a anty zamu huta tukunna, sai munyi changing ma" Anty Amnah tace "toh" nafisa ta juya gurin na'ima tace "muje sis" suka miqe suka nufi dakinsu dasuke sauqa in sunzo gidan suka bar anty Amnah takawo refreshments din nan gurin Ahmad.

Bayan su na'ima sunyi wanka sun dan nutsu, komawa sukayi falon basu tadda Ahmad ba anty Amnah tace musu ya wuce, dining area suka nufa suka fara cin abinci, bayan sun gama ne suka dawo falon sannan suka fara hira da anty Amnah

Haka su Na'ima sukayi zamansu nan gidan anty Amnah suna hutawa akan sai Sunday zasu koma oxford, Kuma sun fadawa anty Amnah hakan

Ranan Saturday da safe nafisa tayi waya da kawarta Lauren akan tashigo london, haka nafisa ta shirya zasu hadu a wani Cafe tace da na'ima suje tace bazataje ba..
Wunin ranan na'ima da twins tayisa dan su anty Amnah da mijinta ma basanan sunje asibiti sunada shift, ta ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?tafi kitchen da twins ta hau yi musu cake, dan nafisa ce ta koya mata yanda akeyin cake din farkon zuwansu oxford harta koya, twins sai hira suke mata tana biye musu, sunyi having fun sosai dan twins suna sonta sosai indai tazo gidan kuma sunanan to bini bini duk inda na'ima tasa qafa suna biye da ita kaman dama tuncan sun santa tun tashinsu.

Daren ranan Na'ima na zaune dakinsu ta jingina bayanta da fuskan gadon tana kallo a laptop, gefenta plate ne dauke da sauran cake dinta tayi, kwance Jafar yake a dayan gefenta yayi bacci shima...Nafisa ce tashigo dakin na'ima ta dan dago ta kalleta, Nafisa tace "sannu uwar twins, sudai yafe mamansu sukeyi ma in kikazo" Na'ima tayi murmushi tace "kin dawo?" zama nafisa tayi a bakin gadon ta dauki cake daya dake plate nan kusa da Na'iman takai baki tace "Duk na gaji ma" Na'ima tace "Ina da Ina kukaje haka?" Nafisa ta amsa da "ashe housewarming party Lauren tazo attending garinnan da kuma yin content akan gurin partyn....sis akwai masu kudi a London, waiii.." Na'ima tayi murmushi tace "kijiki saikace bakisan kudi ba" Nafisa tadan ware Ido tace "banda irin wannan kudin Bobo" Na'ima ta dan jijjaga kai ta cigaba da kallonta, Nafisa ta cigaba"Guy dinda ya sayi mansion din ashe cousin din Lauren ne....kawai sai gani ga yaya Ahmad, na zagaya wajen pool din gidan naganshi zaune da wasu friend dinsa" Na'ima ta dan dago ta kalli nafisa tace "Allah sarki" Nafisa dake lura da expression din na'ima tace "kinsan ya tambayeni yakike" Maida idonta kan kallon Na'ima tayi cikin sanyin murya tace "Ayya, ya yake shima?" Nafisa tace "lafiyansa lau, narasa ina yake haduwa da friends irin wa'inda nagansu tare yau, they all scream money" Na'ima bata ce komai ba Nafisa tasake cewa "kinsan yaya Ahmad yasha creating apps da sukayi gaining global reach" sai sannan na'ima ta dago kanta tace "he's a programmer?" Nafisa tace "babba ma kuwa, bayan aikinsa na company da baba ya dora shi head ai yana programing manya manyan apps, zuwansa dayayi this time ma maqasudin zuwan ashe saida wata app din yazoyi gurin investors, ina tsaye kusadasu naji yana maganan da wani white friend dinsa" Na'ima ta gyada kai kawai batace komai ba, Nafisa dake son cusa mata maganan Ahmad din ta sake cewa "dan dai ba shaquwa nayi dashi bane, saboda sai nayi shekara abu bai hadoni dashi ba kuma shi bayason arinqa shige masa cikin al'amuransa kai tsaye, dana jaki watarana munje gidansa dake London dinnan" Na'ima tace "to ma tayaya zamu kwashi kafa muje gidansa nafisa..akan wane dalili?" miqewa nafisa tayi tafara rage kayan jikinta tace "Ha'a muda yayanmu..yanada kirki fa kawai ba komai zaki gansa yasa kansa aciki ba kamar yaya Adam" Na'ima jijjaga kai tace "ai bance baida kirki ba kawai bazan je bane" cikin son kawar da zancen yasa ta sake cewa "Bayan celebrities dinda Lauren din keyin content akansu, yanzu ta koma yi har a gurin housewarming party ne? Ko bada ita kukaje yin content gurin movie premiere ba kwanaki?" Nafisa tace "wannan babu inda bata tabawa indai akazo batun content, da celebrities din, Entrepreneurs, business tycoons duka ko ina ma" Na'ima ta gyada kai tacigaba da kallonta..

Washegari Sunday yakasance ranar komawarsu oxford, da wuri suka shirya komai nasu bayan sun idar da sallan safe, sannan suka tafi kitchen girka nasu breakfast din dan yau Sunday su anty Amnah yawanci suna yin dogon bacci na hutu,
Bayan sun gama hada komai nan dining sannan suka zauna suka fara ci, Anty Amnah ce tafito cikin long pajamas, gaisheta sukayi ta amsa sannan taja kujera ta zauna tace "sannunku...kun gama shirya kayan naku dai ko" nafisa tace "tun tashinmu" Na'ima tace "twins basu tashi bane anty?" madadin anty Amnah ta amsa sai tace "meya samu muryanki daughter? Mura ne?" Na'ima tayi gyaran murya tace "nadan tashi da tari ne anty" anty Amnah tace "sannu dear, akwai magani a cikin first aid box, zaki gani a study room din abbansu, ko bari idan natashi zan dauko miki" Na'ima ta gyada kai tace "toh anty nagode"
Nan sukayi breakfast din da anty Amnah suna hiransu, bayan sun gama suka koma daki sukayi wanka suna cikin Shirin anty Amnah tashigo dakin tace musu "ku fito yayanku yazo daukanku" sannan ta fita.
Na'ima ta juya ta kalli nafee tace "wani yayan" nafisa na zipping riganta tadanyi murmushi tace "yaya Ahmad mana, I told him yesterday akan yau zamu koma da safe" Na'ima ta dan tsaya kallonta sai kuma ta juya ta cigaba da saka kananun kayayyakinta a qaramin jakanta batace komai ba.
Fito da kayansu suka fara yi Abban twins yatayasu daukan wasu ya fita waje dasu, bin bayansa su na'ima sukayi dauke da wasu kayan anty Amnah ma haka.

Bintu Musa ce
'
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z


('KUNCIN ZUCI('
Na Bintu Musa

Read my book "KUNCIN ZUCI" on ArewaPen, Platform available: "all" :: https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c

Chapter 16

Tsaye na'ima taga Ahmad bayan motansa suna saka kayan nasu shida Abban twins at the same time suna magana, qarasawa sukayi gurinsu Anty Amnah tace "son mun tado ka da sassafe ko, ai da ka turo driver ya kaisu bakomai" rufe booth din Ahmad yayi yana murmushi ya matso ya karbi ledan hannunta yace "Bakomai Anty..ina kwana" ta amsa masa su na'ima suka miqa nasu kayan back seat suma Nafisa ce ta fara gaishesa ya amsa sannan ya kalli Na'ima, gaishe sa tayi cikin sanyin murya sai kuma tari yadan zo mata tafarayi kadan kadan, dan qura mata Ido Ahmad yayi sai kuma ya kauda kansa ya yayi sallama dasu anty tareda bude mota, sallama suma sukayi dasu anty Amnah, tayi hugging dinsu tace "sai na ganku on weekends kuma" Abban twins yana murmushi yace "bayan sun koyi qin zuwa akai akai yanzu" nafisa tayi dariya tace "uncle hanyan ne akwai gajiya wani lokaci, amma upper week zamuzo" ya gyada kai yana murmushi yace "Allah ya nuna mana" Na'ima tace "anty in twins suka tashi ki gaishesu" gyada kai anty Amnah tayi tana murmushi tace "toh daughter, safe journey"
Haka sukayi sallama, na'ima tayi saurin bude back seat ta shige, nafisa na dan dariya ta zagaya ta shiga front seat Ahmad ya tada motan suka wuce aka bar su anty Amnah tsaye suna daga musu hannu..
Shiru sukayi while Ahmad yana driving, Nafisa tayi breaking silence din tace "yaya baka taba zuwa gidan da muke zama a Oxford ba ko?" Ahmad ya gyada kai idonshi na kallon titi yace "nadade banshigo England ba nafisa.... bedsides, ai daga baya ma naji labarin tahowanki nan karatun" Nafisa ta gyada tace "hakane...kuma har yanzu kana living a gidanka dinnan dana sani?" Ya amsa da "Eh inanan nafisa, zakije ne?" Tana murmushi tace "Eh yaya zamu kai maka ziyara nida na'ima in Sha Allah..ai zaka dade kafin ka koma ba" yadan kai yatsa yana sosa girarsa kadan yace "I don't know, ina tunanin zuwa New York ne next week" Nafeesa na kallonsa ta gyada kai, ya cigaba "but ba damuwa, ku kirani time dinda kuka shirya zuwan i may be around" idon na'ima kaman ya zazzago dan hararan nafisa, ita ta rasa meyasa nafisan ke son suje gidan Ahmad din all of a sudden, hada Ido tayi dashi yana kallonta ta mirror din gaban motan, tayi saurin kauda kai ta koma daf da window tana kallon titi, tana jinsu suka cigaba da hira sama sama har bacci ya dauketa....
Shigarsu cikin town din Ahmad yayi parking gaban wani babban store yace "I'm coming" sannan ya fita ya shige ciki, bai wani dau lokaci ba ya fito da wata qaramar leda a hannu ya shiga motan suka tafi, basu kai ga isa arean su nafisan ba ya sake tsayawa a gaban wani restaurant nan ma yashiga bai dade ba yafito hannunsa riqe da takeouts, miqa package din yayi gurin nafisa ta karba ta ajiye kan cinyanta, ya zagaya ya shiga motan..

Bayan sun isa haka Ahmad ya tayasu diban kayansu suka shiga elevator dazai kaisu floor dinsu..
Shigansu apartment din Ahmad ya dan bi middle space din nasu da kallo sannan ya wuce gurin mini dining area din nasu ya ajiye su takeouts din da car key dinsa, Na'ima ta fara daukan kayan dake nan falon tana kaiwa dakinta batareda ta kalli inda yake ba, ruwa nafisa ta dauko daga kitchen takawo masa ya karba, yace "Ina duster?" Ta koma ta dauko saita fara goge masa kujeran dining din, bayan ta gama yace "thank you" sannan ya zauna ya ciro wayansa yafara dannawa, fara bude takeout din nafisa tayi yace mata "kunada kayan shayi nafisa" ta gyada kai tace "Eh akwai yaya, in hada maka ne" ya miqe yace "No, zo kibani" shigewa kitchen sukayi Ahmad zai dora shayin

Itadai Na'ima tunda tagama shigo da kayansu daki bata sake fita ba, ta cire dankwalinta da ribbon din da ta daure timilin gashinta sannan ta nemi waje nan bakin gado ta zauna tana jin wani iri sanin presence din wanda ke cikin apartment din nasu...
tananan zaune tana jiyo hiransa da nafisan jefi jefi can kuma saiga nafisa ta shigo ta juya ta rufe kofan sannan ta qaraso gurin na'ima cikin qasa da murya tace "meye hakan kuma na'ima mutum yakawo mu tun daga London amma kin wani shigo daki kin barsa a falo" Na'ima tana kallonta tace "ba gashi kuna hiran ba nafee, mezance masa in na fitan" Nafisa tace "A'a Na'ima, yayanmu ne fa, saikace wani baqo, at least show your care mana, shida ba wani dadewa zeyi ba yanzu zakiji yace zai tafi ma" Na'ima ta gyada kai tace "to ganinan fitowan" Nafisa ta miqe tace "yauwa ko kefa" ta fice..shiru Na'ima tayi sai can kuma ta dauki ribbon din nata tasake daure gashinta ta dau veil din tamayar jikinta kafin ta fice falon, zaune ta

8 / 25