Chapter 12 Reading Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc Arewa Novels

Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc

Author :  Binta Musa Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   12 / 25

33K to 36K   out of 73.5K words

bude mata cab din motan dayake yi aduk lokacin da zata shiga, batasan meyasa hakan yake narkar mata da zuciya ba, such a gentleman..
Saida Ahmad yayi parking gaban wani babban supermarket Na'ima ta tuna da dunut din Nafisa, ita kadai ta fara murmushi tuna irin jarabar da zata sha agurin nafisan inda ta manta, kallonta yayi yace "zaki rakani ciki babu damuwa?" Ta gyada kai tareda cewa "Toh" dan itama tanada mata uzurin.
Cart Ahmad ya turo Na'ima na gefensa, sanin bazata zabi abunda takeson ba yasashi loda duk wani junk foods da abubuwan kwadayi cikin cart din, dan ware ido tayi dan a tsammaninta nashi ne , haka ta rinqa bin bayansa yana loda kaya cikin cart sai da ya debi son ransa ya juyo ya kalleta a nutse yace "akwai wani abun da kikeso bayan wannan?" Na'ima ta ware idanu tace "all of this?" ya dan daga kafada yace "akwai su nafisa ai" tuna nafisan nason ire iren abubuwan nan din yasa Na'ima bata sake protesting ba tace "tace in siyo mata dunut" yace "Okay" gurin part na snacks suka je nan ma ya dibo masu yawa dayake acikin package suke, bayan yayi inserting card nashi anan counter aka cire kudin sai cashier'n ta hada kayan ya karba, miqa hannu Na'ima tayi zata tayasa riqewa ya kada kansa alamun ta bari but saida ta karbi wani ledan suka fice..
A komawa gidan ma shiru sukayi sai Ahmad dinne yace "kinayin WhatsApp?" Ta girgiza kai tace "A'a" kallonta yayi sai kuma ahankali yace "then how am i supposed to see your face anytime" ta juya kanta tace "nidai banayi" murmushi yayi bai sake cewa komai ba har suka isa, tana shirin bude kofan motan ya tsayar da ita ta dalilin dan riqe bakin gyalenta dayayi, ta juyo ta kallesa batace komai ba, sai kallonta yake wanda haka yasa ta sauqe idonta, yayi qasa da murya yace "I'd love to wake up everday seeing those Eyes Babe" rufe idonta tayi tafara murmushi muryansa na kashe mata duk wani kuzari na jikinta, iskan cikin motan ne taji yafara mata kadan ta sake juyawa zata bude kofan yace "yaushe zaku sake fita karatun" shiru tayi kamar baza ta amsa ba, ahankali kuma tace "sai jibi Saturday" ya gyada kansa yana sakin bakin gyalen nata suka fice daga motan tare, sai da tajira shi nan tsaye ya debo kayan daga booth sannan ta qaraso garesa zata karba yace "barshi, muje ciki" ta dan ware ido tace "shiga zakayi" yace "Eh, ko da wani abun" tadan turo baki tace "in suka ganmu tare fa" murmushi yayi yace "toh ki fara shiga sai anjima can in biyo bayanki" ta gyada kai sannan ta nufi gidan yana kallonta fuskansa dauke da murmushi ya dan jijjaga kai, tana bude kofan ta shiga kenan mutanen falon suka dago kai duka suna kallonta, anty Amnah, Abban twins, Nafisa da kuma twins din, tsayawa Na'ima tayi itama tana kallonsu ganin irin kallon da suke mata, lura tayi ba itan suke kallon ba bayanta suke kallon sai itama ta juya, ganin Ahmad tayi a bayan nata tadan ware ido, yana dan murmushi ya wuce ta ya shiga falon hannunsa riqe da kayan, miqewa Nafisa tayi ta karbi kayan tana masa sannu da zuwa, anty Amnah tace "Son sannu da zuwa" samun guri yayi gefen Abban twins ya zauna, sai a sannan Na'ima ta fara takawa a hankali cikin falon ta nemi waje ta zauna tana kallonsa yana gaisawa da uncle, Anty Amnah tace "Na'ima kin dawo" ta gyada kai tareda cewa "Eh Anty" ta sake tambayanta ya karatun ta amsa da Alhamdulillah, gaishe da Abban twins tayi ya amsa shima, tadan juya tana kallon Nafisa dake mata wani irin kallo tana qunshe baki kamar me tare dariya, dauke kanta Na'ima tayi tana shafa kan jafar daya zo kusada ita, Anty Amnah ta sake cewa "son kai ka kawota kenan" yace "Eh Anty" anty Amnah tace "Ma Sha Allah" Na'ima sai jira take taji yace haduwa yayi da ita sannan ya kawota gidan amma sai taga shi ko a jikinsa ma yana barewa jabeer ledan biscuit, miqewa tayi tace "anty zanje ciki" anty Amnah ta gyada kai tace "Okay, amma inkin gama ki fito kici abinci fa" ta amsa sannan ta wuce dakinsu tabar Ahmad nan yana hira da uncle yasir..

Sai da tayi wanka ta fito daure da towel ta zauna kan stool nan gaban mirror zata shafa mai Nafisa ta shigo dakin hannun riqe da dunut tanaci, Na'ima ta wani sha kunu ita a dole kar nafisan ta kawo mata wargi, dariya Nafisa ta fara ta qarasa wajenta tana cewa "inaaa..ai ko aman wuta idonki yakeyi Na'ima sai nayi magana" Na'ima batasan lokacin da tafara dan dariyan ba itama ta jawo cream dinta tafara shafawa, tsayawa nan gefenta nafisa tayi tadan jingina da mirro'n tace "iyee Na'ima, Au anty Na'ima zance dan na fara shinshinowa kinzama anty na ma" Na'ima ta dan jijjaga kai tace "kici kanki Nafisa" nafisa bata dena dariyan ba tace "naji..yanzu dai fadamin a Ina kuka hadu harda siyayyarsa haka, chaiii Na'ima" Na'ima tace "toh dena dariyan tukunna sai in fada miki", gyada kai Nafisa tayi takai dunut baki bata daina kallonta ba fuskanta da murmushi, Na???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?'ima tace "a Cafe dinda mukaje karatun na hadu dashi, shikenan?" Nafisa ta gyada kai tace "sai me kuma?" Na'ima tace "kamar me? ni babu komai kuma" Nafisa tace "a sannu zaki fadamin komai ma, sun tafi yin sallah shida uncle yanzu" itadai Na'ima bata sake cewa komai ba tacigaba da shafa manta, Nafisa tace "Oh yaya Ahmad, kuma nikam tayaya kuke maganganun soyayyan ne ma" Na'ima ta kalleta sannan tace "ce miki akayi maganganun soyayya yakeyi?" Nafisa ta dan daga hannu tace "A'a mu yayanmu ba daga nan ba wallahi, yanada himma a lamuransa" Na'ima tadan ware Ido tana dan dariya tace "tanan kika bullo kuma Nafisa" tace "A'a ai ni bani nan bani can ne, dangin miji ce nima kuma dangin mata" miqewa Na'ima tayi ta nufi wardrobe zata saka kaya tana dan kada kai tace "kin fi qarfina kuma" haka nafisa tayi ta janta da surutu tana amsawa har ta gama saka kayan suka fita cin abincin tare, basu samu Ahmad a falon ba ashe daga fitansu sallan bai dawo ba kuma ya wuce gidansa.....

Daren ranan Na'ima na zaune kan gado tayi shirin bacci hannunta riqe da wayanta ta maida hankali tana dannawa, Nafisa ce ta shigo dakin tace "bakiyi bacci ba" Na'ima ta gyada kai batace komai ba, nan kan gadon itama Nafisan ta zauna ta jawo laptop dinta zata bude, can dai Na'ima ta dan gyara zama tace "Nafisa kiga...uh..uh..idan na bude WhatsApp da number'n danake amfani anan qasar, in na koma gida sai nayi changing number ko?" Nafisa tace "bangane ba, WhatsApp zaki bude kaddai" Na'ima ta dan gyada kai tana kallonta, ai da sauri Nafisa ta ajiye laptop din tace "Na'ima yau din..Bobo kece kuwa?" Na'ima tayi murmushi tana dan basarwa alamun kunya, Nafisa ta sake cewa "kin gaji da Zoom app din ne" Na'ima tace "A'a, nidai ki bani amsa ta mana" karban wayan Nafisa tayi tace "Ai kawo ma in bude miki" tana danna wayan kuma tana dariya tace "Na'ima you're full of surprises these days" itadai batace komai ba tananan zaune sai murmushi takeyi...

Washegari Friday nafisa nada uzuri a school tun da sassafen ta tafi school din tabar Na'ima nan dakin tana baccin ta, jiyan saida tayi bacci Ahmad ya kirata ta dauka muryanta cike da bacci, shima jin hakan yasashi cewa tayi baccinta saida safe zai kirata
Bata tashi ba sai kusan goma na safe, sanin masu gidan sun fice yasa ta fito jikinta sanye da pyjamas ta nufi kitchen neman abunda zataci, tasamu anty Amnah ta ajiye mata nata breakfast din, zama tayi zata fara cin abincin sai kuma wayarta tafado mata a rai ta sake tashi ta koma dakin ta dauko, aikuwa miscalls dinsa tagani guda biyu duk a lokaci ma banbanta, saida ta zauna gaban abincin sannan tabi bayan kiran, Ahmad yana office a wannan lokacin kiran ya shigo wayansa ya juya yana kallon wayan, saida ya jira kiran ya katse sannan ya bi bayan atake, shiru sukayi a farko kowa da wayan a kunne sai Ahmad yace "Babe yanzu kika tashi ne?" Na'ima ta gyada kai tace "I'm sorry ka kira Ina bacci" yace "bakomai nayi tunanin hakan" gaishesa tayi ya amsa suka sakeyin shiru, can yace "do you have Zoom app?, I want to see you" shiru Na'ima tayi at first sai kuma a hankali tace "na bude wancan din" Ahmad yace "WhatsApp din?" Ta amsa da "Eh" yace "Okay let me call you" Na'ima tayi saurin kallon kayan jikinta tace "No,I'm in my..." Sai taji ta kasa fada masa kayan bacci ne a jikinta , ji tayi yace "irin wa'enda na ganki dasu a gidan Mami?" cikin jin kunya tayi shiru batace komai ba tana murmushi, ya sake cewa "Babe kinyi kyau ranan, dakyar na dauke idona" murmushi me sauti tayi shima daga can bangaren murmushin yake, sai ya kuma cewa "yanzu dai iya fuskanki kawai zan gani, I promise" tace "uhm uhm" yace "nayi alqawari fa" ta sake cewa "ni dai A'a" haka Ahmad yayita lallabinta akan fuskanta kawai yakeson gani Na'ima taqi, ganin bazata yarda ba yasa shi hakura ya sake tambayanta gobe Saturday din zata fitan tace "Eh" yace "ko nazo na kaiki" ai da sauri tace "nidai wallahi a'a, ai ban manta abunda kayimin jiya ba" yafara dariya, ta sake cewa "you broke our plan" yace "Babe I'm sorry, shikenan bazanzo ba toh"...haka suka dau lokaci suna hira wanda ta fannin Ahmad barin aikin nashi yayi duk ya lalace a jikin wayan, hira sukeyi jefi jefi cike da annushuwa wanda hakan ke sake sarqe zuciyoyinsu guri daya...sai Na'ima ce ta fara masa sallama tace zataci abinci sannan Ahmad ya kashe wayan ya koma kan aikinsa...
Da nafisa tadawo da yamma ne take fada wa Na'iman boat race din da za'ayi between Oxford university da Cambridge, Anty Amnah da fitowanta daga kitchen kenan tace "Au wai har gobe ne sport din" Nafisa tace "Eh anty, ban iya riding bane ai shiyasa babu ni, amma ni da Lauren muna cikin cheering squad" Na'ima tadan ware ido tana dariya tace "sannu nafisa" Nafisa tace "da ban karbo matching wears din dake bama ki gode Allah" Na'ima tace "bama zanje ba" Anty Amnah tace "gaskiyarki daughter yayi hayaniya gurin, akwai jama'a" Nafisa tayi dariya tace "it'll be so much fun kuwa,Allah kizo muje Na'ima" ta kalli anty tace "Anty ki fada mata ta shirya muje" ganin Anty Amnah ta Jan jijjaga kai alamun tabar maganan yasa Nafisa gane me take nufi sai tayi shiru kuma, ita harta dan manta dalilin zuwansu nan gidan anty Amnahn ma in the first place...

Ranan Saturday din da safe zarah ta kira Na'iman a waya akan su hadu at same Cafe din ranan can, bayan Na'ima ta gama shiryawa cikin farin blouse din riga mai dogon hannun wanda qarshen hannun da roba, tahada da brown jeans ba matsattse can ba, rigan a bude take sosai ta sauka har gwiwanta ta yafa brown veil, saida ta gama shirin tace da Nafisa dake nan kwance "sis ba yanzu bane game din naku" Nafisa ta qara Jan blanket tace "sai dan anjima tukunna" ta qarasa maganan tana sake lulluba blanket din har kanta..fita Na'ima tayi bataga su anty Amnah a falon gidan ba kasancewan Saturday sunacan ana bacci sai ta ciro wayanta tafara kiranta, tananan tsaye anty Amnahn ta fito daga side dinsu jikinta sanye da kayan bacci tace "harkin shirya daughter" Na'ima ta gyada kai anty Amnah ta sake cewa "bakiyi breakfast ba kuma ai" tace "zanyi acan Cafe din anty" Anty Amnah ta gyada kai tareda cewa "toh, ki kula sosai fa Na'ima" tace "toh" sai kuma ta tsaya bata tafin ba kanta adan duqe tarasa ta Ina zata fara maganan datake son yiwa anty'n, ganin hakan yasa Anty Amnah'n ta sauqar da murya tace "daughter menene? feel free with me kinji" Na'ima ta dago kanta ahankali tace "dama rancan da yaya yakawonin a Cafe din muka hadu Anty" murmushi anty Amnah tayi tace "ya fada mana bayan tashin ku daga gurin, kuma ma ai shi yayanku ne Na'ima, what's there dan ya kawoki gida?, I know who is Ahmad" Na'ima ta gyada kai sannan sukayi sallama ta fice Anty Amnah na bin bayanta da kallo still bata daina murmushin ba...

Nan Cafe din Na'ima tayi musu ordering sandwiches da tea itada zarahn, saida suka gama ci sannan suka fara research din nasu, yau ma dogon discussion sukayi sosai, sun dauki lokaci me tsaho suna abu daya sannan Kiran Ahmad ya shigo wayan Na'ima dake nan kan table, dauka tayi suka gaisa daga can bangaren a nutse yace "nazo at the wrong time ko?" sai Na'ima ta daga kanta tafara bin Cafe din da kallo tana nazarin mutanen cikinsa, kusada entrance ta ganshi tsaye waya kare a kunnensa yana kallonta, hannunsa daya cikin aljihu, murmushi ta masa wayan yana kare a kunnenta,cikin sanyin murya tace "sorry.. dan qaramin few minutes Dan Allah" ya dan yi murmushi tareda gyada kai sannan ya nemi table ya zauna yana kiran waiter..

Magana ta cigaba dayi ita da zarahn jefi jefi tana kai idonta gurin da yake zaune yana kallonta, aduk sanda suka hada ido zata dauke kai tacigaba da magananta da zarah, sai taji duk ta taqura kuma under his eyes, kawai tace da zarahn su bari sai wani lokaci yanzu yayanta yazo daukanta.

Zara tace "where is he?" Kallon gurinsa Na'ima ta sakeyi sai zarahn tabi gurin da kallo itama, ganin Ahmad yasa cikin fara'a ta daga hannunta alamun gaisuwa, sai ya taso ya qaraso gurin nasu ya zauna anan gefen Na'ima, qara gaisawa yayi da zarahn kafin tafara tattare kayanta zata miqe....
Bayan tafiyan zarahn ya juya yana kallon Na'ima yace "ya research din" tace "Alhamdulillah" ya sake yin qasa da murya yace "kinyi kyau Babe" ta dan yi murmushi sai kuma yau din ta amsa da "kai ma kayi kyau" dan bin jikinsa da kallo yayi yana dan murmushi yace "Really?" ta gyada kai tana kallonsa still da murmushi a fuskanta, yace "Thank you dear" sai ya sake cewa "akan me kukeyin research din, Na'ima ta juyo masa da fuskan laptop din tafara masa bayani a nutse tanayi tana dan nuna masa lines din da yatsanta, gyada kai yakeyi akai akai alamun fahimta yana dan mamakin iliminta, sai kuma idonsa yakai kan tabon hannunta ya rinqa kallon baya ko kifta ido, ganin kamar hankalinsa ya tafi wani gurin ne yasa Na'ima dan kallonsa sai taga hannunta yake kallo, saurin boye hannun tayi ajikin riganta, Ahmad yadan matso ahankali yace "Babe please ki fadamin tabon menene wannan a hannunki" ta sauqe idonta qasa tace "dagaske da wuqa naji ciwon" sai yace "a garin yaya kika yanke sosai hakan?" sai ta rasa me zatace, shidai sai kallonta yake yana jiran amsanta, tace "da ina yanka..uh..lokacin ina yankan dankali ne" sai taji shiru be ce komai ba tadan dago idonta taga kallonta yake alamun maganan bata shigeshi ba, sai kuma ya sauqe numfashi yace "Allah ya kare na gaba" tace "Amin"
Ce mata yayi ta tashi su tafi akwai gurinda zai kaita ta tambayesa ina ne, yace "it's a surprise" tace "nidai ka fadamin Dan Allah" yace "akwai boat race na 'yan school naku da za'a yi yau" Na'ima tace "nafisa tace zataje" yana kallonta yasake cewa "bakyason zuwa?" sai Na'ima taji tanason zuwan tare dashi, jijjaga kai tayi tace "A'a inaso" Ahmad ya fara tattare mata kayanta yana sawa a jaka suka miqe, sai da ya biya kudin abunda taci itada zarahn wanda Na'ima tana ta magiyan ya bari yace A'a, sannan suka fice daga Cafe din..
Isarsu London bridge din suka samu acike da mutane ta ko Ina, ahaka ya kamo hannunta suka kutsa cikin mutanen har suka kai gaba inda suke kallon komai a gabansu, Na'ima tsayawa tayi tana kallon racers din da duk suke cikin nasu boat din suna jiran abasu dama sufara, Ahmad ya sunkuyo yace mata "a bayan wane team kike?" Tadan kallesa tace "na makarantar mu mana, kaifa?" Ahmad yadan daga kafada yace "ya na iya, ina bayan na makarantar naku nima" ta danyi dariya tace "da Cambridge ka zaba?" yana murmushi yace "kedai ina bayan nakun kawai" ta cigaba da dariyan tadan jijjaga ta maida hankalinta gurin tseren..
Wasa yayi dadi saiga Na'ima har da ita acikin masu ihun son team dinsu suci, Ahmad sai kallonta yake yana dariya ganin ta dage itama tana daga hannu tareda cewa "go,go,go" wayarsa ya ciro yafara daukanta hoto batasani ba, ana cikin haka ta hango nafisa da team dinsu daga dayan bangaren bridge din sai yekuwa suke, dukansu sanye suke cikin blue din polo shirt da facing cap, turawan duk suna sake cikin gajerun wanduna baqaqe while nafisa ta saka dogo ita..Na'ima tadan tabo Ahmad tana dariya tace "yaya ga can nafisa" kallon gurin yayi yana dan girgiza kai ganin su nafisan sun dage da ihu harda waqa yace "Hajiya Nafisa"..

Makarantar su Na'ima ne suka lashe kofin wasan, dazasu bar gurin bakinta yaqi rufuwa dan murna sai hiran take wa Ahmad shidai yanata binta da kallo ganin fara'anta abun sha'awa, tana yi masa kyau in tana dariya...
Basu hadu da nafisa ba dan tabi 'yan qungiyarsu sun tafi, Ahmad dinne ya maida Na'ima gida ranan, rikice masa Na'ima tayi akan ala dole bazai shiga gidan ba, yana dan dariya kuma yana kallonta kamar yau ya fara ganinta, ta wani bata fuska bata sake cewa komai, ganin haka yasa Ahmad din yana murmushi yace "Okay,Okay, bazan shigan ba, are you happy?" ta gyada kai ta juya ta bude motannan sannan ta fita yana kallonta har sannan bai daina murmushi ba, hakanan ya hakura yaja motansa yatafi tananan tsaye, tabi bayan motan da kallo sannan ta juya ta shige gidan.....

Bintu Musa ce
'?=???

https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c

('KUNCIN ZUCI('
Na Bintu Musa

Chapter 21

Zaune suke a falon suna hira banda Laila da ta wani bata fuska tanajin ranta duk a dagule, wayanta ne riqe a hannunta

12 / 25