Chapter 3 Reading Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc Arewa Novels

Kuncin Zuci (Love & Heartbreaking story) by Bintu Musa.doc

Author :  Binta Musa Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   3 / 25

6K to 9K   out of 73.5K words

or big collections, kowanne so kike" Nafisa tace "wlh kuwa, duk wanda na dauko sai inga inason bari, kawai zan barsu Inaga" Na'ima tace "kinjiki, sai munje ki damemu da mita akan da kin dauki wasu,matsa in nema miki" ta amsa da toh tana dawowa wajen gadon ta dauki chocolate daya zata bare. Miqewa na'ima tayi ta tafi wajen kayan tana dubawa sukayi shiru na wasu mintuna sannan cikin kwantar da murya Nafisa tace "na'ima in bakyason komawa babu me saki dole..you know that" juyowa na'ima tayi tace "nafee we've talked about this over and over and i said yes, why don't you believe me?" Nafisa tace "the eyes don't lie na'ima I saw it in you, how you became silent these days, shin in tambayeki...why do you choose to deprive yourself happiness ne wai na'ima?" Ta miqe ta qaraso gaban na'iman tace "that pathetic,stupid person!! Should be the one hiding, not you" ta dafa kafadan na'ima tace "those vicious and wicked people should be the one's living unhappy now, not you Na'ima"
Fashewa da kuka Na'ima tayi nafisa na riqe da ita suka zauna nan gadon, nafisa na hawaye.
Tayi kukan tana goge idonta cikin sanyin murya tace "tsoro nake kada ayi forcing dina back to where i left, I don't don't know how to face what I've left nafisa" nafisa tace "Abba da mami bazasu taba barin hakan ya faru ba kinsani"
Na'ima tace "Amma dole watarana hakan ya faru" Nafisa tace " bance bazakije wajensu ba tunda bakida kamarsu, but forcing you back dinne ba wanda zai saki hakan, kuma kisani Allah yana tare dake a komai" Na'ima batace komai ba tana share hawayenta idonta na kallon kasan dakin.
Nafisa tacigaba "we will always be there, abubuwan da suka faru sun riga da sun faru,bance babu sauran gwagwarmaya agabanki ba amma what I want you to do is to Embrace life strongly as it comes,life is too short for you to be stuck up because of that stupid man, Embrace love when you find it,rayuwar nan bata jiran kowa? na'ima, it's high time you actually start living to the fullest" tana gama fadin haka ta miqe ta koma wajen kayanta tafara diban na tafiyan, Na'ima na nan zaune tayi shiru tana maimaita maganganun nafisa, encouraging words din suna shiga cikin kwakwalwanta.
May be it's high time she start seeing all of this in a different direction, duk abubuwan da suka faru a baya zata ajiyesu for now idan lokacin komawanta yazo Allah zai mata jagora.

Nan dakin nafisan ta kwana sukayi ta hiransu kafin suyi bacci
nafisa na bata labarin yanda umar ya dameta da kira wai zaizo daukan su in sun sauqa, na'ima tace "blocking dai ya fasu" nafisa ta ture ta da hannu tace "kin shiga uku da rashin mantuwa" na'ima ta kama dariya

Wayewar washegari suka tattare gidan sukayi storing abunda sukasan zai baci kafin su dawo sannan suka tafi airport dan jirgin safiya zasu bi
Jirginsu ya tashi zuwa Nigeria zuciyar na'ima cike da wani irin yanayin da bazata iya fassarashi ba.

Wattpad: Bintu Musa @bintuuu02

('KUNCIN ZUCI('
Na Bintu Musa

Read my book "KUNCIN ZUCI" on ArewaPen, Platform available: "all" :: https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c

WhatsApp group =?G?
https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z

Chapter 06

Tsaye yake a parking space dake compound din babban gidan.
gida ne babba wanda kana gani kasan naira ta zaunu gurin mazauna cikinsa,
Yananan tsaye jikin motansa da ya bude driver seat kuma bai shiga ba, wayarsa yake dannawa cikin nutsuwa yana nazarin saqon da aka turo masa.
Mai gadin gidan ya qaraso ganinshi tsaye nan bai shiga motan ba yace "yallabai ko da abunda za ai maka?"? ya dago yana kallon maigaidin yace "a'a yakasai jeka abunka" yakasai yace "toh yallabai afito lafiya" ya juya yana komawa bakin aikinsa.
Shiga driver's seat din yayi batareda ya kulle kofar motan ba ya miqo kafarsa daya waje yacigaba da abunda yakeyi.
Yananan zaune for almost twenty minutes wata mota ta shigo compound din, bai dago kansa ba saida ta qaraso tayi parking dan nesa dashi sannan ya daga Ido yana nazarin motan,
ganin wadda ta fito daga driver seat yasa nan take yayi danasanin tsayuwarsa a wajen bai fita ba, aranshi yana cewa me yasa tun dazun bai tafi ba inyaso sai yadawo inya nutsu ya duba saqon nashi.
Laila ta juyo ta kalleshi, take ta fara murmushi tana gyara gyalenta data saqala a kafada, a daya side din ma qawartace ta fito suka taho tare Laila na gaba tana qarasowa cikin zumudi
Duk wani mood din fitan yaji ya fita daga ranshi, ya fito daga motan ya rufeta yana maida wayansa aljihu.
qarasowan su wajen Laila tace "yaya ashe kadawo?..Ina wuni" gently Ahmad ya amsa da "lafiya" batareda ya amsa tambayanta na farko ba, qawarta mai suna luba ta gaisheshi ya amsa shortly, Laila tace "nakira ba adadi baka dauka ba, i just want to know how you are" ta qarasa tana murmushi bakinta kamar gonar auduga" Ahmad yace "oh really?, may be bana kusa"
Amasanshi ta qular da ita wanda har yanayin fuskanta yaso nunawa tayi saurin waskewa da wani murmushin tace "Kai yaya, I've been calling fa" bai bata amsa ba ya dago hannunsa yana duban wristwatch dinsa yace "I'm late Laila, and nayi mantuwa" ya juya tareda cewa "ki gaida su mommy" ya nufi babban part dinsa shida Adam wanda ke nan compound din gidan, yabarsu Laila nan tsaye a parking lot.
Laila ta cika kamar zata fashe, qawarta ta tabo kafadanta tace "kawata waye wannan din?, kinga yanda yake mana magana kuwa,ko shine Ahmad din naki?"? Laila bata juyo ba balle ta bata amsa ta qurawa side din su Ahmad ido ta jijjaga kai tana kwafa tace "daman naji labarin yadawo nazo na ganewa idona" luba tace "uhm, guy dinnan is full of himself" Laila tace "zanyi maganinshi ne, nikuma!!...yakusa zuwa hannu wlh" luba tace "a yanda kike rawan kafa a gabansa dinne zakiyi maganinsa, girl you must be fooling yourself" Laila ta juyo tana murmushi kadan tace "kedai ki zuba ido ki gani" ta nufi gurin motanta tace "mutafi" luba tace "ha'aa bazamu qarasa ciki mugaisa da mutanen gidan bane?" Laila tace "nagama abunda yakawoni nidai, in zaki zo mutafi to" luba ta kyabe baki ta taho suka shiga motan.
Haka Laila ta tada motanta ba kunya megadi yasake bude musu gate suka bar gidan batareda ta qarasa ta gaishe da iyayen Ahmad ba, wanda mahaifishi ya kasance yayan nata mahaifin

Bayan Ahmad ya shiga part din nasu yawuce Adam dake zaune nan falo yana kallo ya nufi stairs zaije dakinsa dake sama zai chanja kayan jiikinsa don dagaske kuma fitan ya fice masa arai, bayan yayi changing into qananan kaya ya dawo nan falon ya wuce qaramin dining area ya hado tea dinda Mamma, mahaifiyarsa ta aiko musu dazu.
Ya zauna a kujera Adam ya juyo ya kallesa yace "badai har kaje kadawo ba" Ahmad yace "nafasa fitan" Adam ya gyada kai yana maida hankali kan kallonsa, sukayi shiru while Ahmad ya ciro wayansa yana dannawa as yana sipping tea dinsa.
Bayan wasu mintuna Ahmad ya ajiye cup din shayin yana kallon Adam yace "the investors has reached out, they want a meeting" Adam ya juyo yace "wait....about the app?" Ahmad yace "yes" Adam yace " but for real though, you really want to sell it?" Ahmad ya gyada kansa, Adam ya cigaba "Dude, you have almost 6.5 million users, this is huge you know" Ahmad yace "I know, but they are offering big money on this. Beside, this year nakeson launching sabon ai" Adam yace "it's settled then, a Ina sukayi setting meeting din?" Ya amsa da "London but bamuyi arranging date ba tukun" Adam yace "Okay, dama ka dade baka leqa branch nacan ba, this is your chance" Ahmad yayi murmushin gefen baki yace "mundade dai" Adam yace "Dude I'm not the head,you are" ya daga kafada yace "it's part of your job too" murmushi kawai Adam yayi yace? "anyway, I'm happy for you...for real" Ahmad yace "thanks man" ya miqa hannu ya dauko ipad dinsa dake kan table yana qara duba email dinda investors din suka tura masa.

Wuraren qarfe sha biyun rana jirginsu Na'ima ya sauqa Abuja,suka fito duk a gajiye
Bayan sun gama duk wasu formalities suka wuce bangaren arrivals, nafisa sai juye juye take tana neman wanda yazo daukansu, tayi tsuka tace "yaron nan bai iso ba kenan" Na'ima tace "waye yaron, Umar?" Nafisa ta juyo tace "wani Umar kuma, haka kurum yaga kamar nima ina zumudin ganinsa ne" Na'ima batasan lokacin da dariya tazo mata ba tace "nafee babu mai iya miki sai Allah" nafee ta juya tana neman qaninta da Mami tace zaizo daukansu tace "sis mazan ne kamar zuma suke saida wuta" na'ima jijjaga kai kawai tayi batace komai ba.
Can gefe suka hango Al'ameen riqe da name sign da sunayensu rubuce ajiki, shima hangosun da yayi ya ajiye sign din ya nufosu yana fara'a su na'ima suka nufeshi suma, qarasowa yayi tareda yin side hug wa nafisa sannan ya juyo yana kallon Na'ima yace "anty na'ima ya zaman gajiya" tace "Alhamdulillah"
Ya riqe wasu daga akwatin nasu suka qarasa wajen motansa nafisa tace "shine ko ka fada mana ka dawo sai gurin Mami mukejin labari" yana murmushi yace "surprise naso muku fa Mami ta batamin shiri" Suma murmushin sukayi suka shiga motan,bayan ya gama sa kayansu a booth din? ya shiga motan yaja suka bar airport din suka dau hanyan gida.

Shigan motan nasu cikin gidan daya kasance babba wanda kana gani kasan masushi dasu ake murza nera a qasar
suka hango Mami tsaye a entrance din building din ta fito Jin qaran mota, dasauri nafisa ta fice bayan sunyi parking tayi wajenta da gudu gudunta, Mami ta ware hannu tana dariya tace "oyoyo yarana" nafisa ta rungumeta tana murna
cikin nutsuwa na'ima ta qaraso tana murmushi itama, Mami ta sake nafisa ta rungumota tana cewa "welcome habibti" kaso tamanin cikin damuwan da na'ima ta taho dashi taji ya washe jin embrace din Mami,cikin raha suka qarasa cikin main falon gidan suka bar Al'ameen yana debo musu kayan nasu megadi yana tayasa.

Wattpad: Bintu Musa @bintuuu02

('KUNCIN ZUCI('
Na Bintu Musa

Read my book "KUNCIN ZUCI" on ArewaPen, Platform available: "all" :: https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c

WhatsApp group =?G?
https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z


Chapter 07

Sunga gata gurin Mami don tun kafin suyi wanka su huta ta fara sallamansu da home made juices datayi musu na musamman. Al'ameen ya shigo musu da kayan mami tasashi yakaimu dakunansu,
Bayan sun huta kadan anan falon suka nufi stairs gurin dakunansu dake jere gefen na Mamin, na'ima ce dakinta daf da falon mami
Tasamu dakin sai tashin qamshin turare yake, ko ina neat ta miqa hannu kan gadon ta dauko teddy bear dinda Abubakar ya taba kawo mata farkon zamanta gidan, ta rugume teddyn tana bin dakin da kallo kamar yau ta barshi,qarasawa tayi ta bude babban wardrobe dinta, nan ta ga kayanta jera cikin tsanaki sai qamshi suke ga sabbin kaya a gefe masu yawa an jera matasu wasu a hanger,
tana nan tsaye gaban wardrobe din a sannu farin ciki yake samun waje cikin zuciyarta aranta tace "I missed this" lallai tayi missing pampering dinda mami take mata, and she made the right choice coming back
Mami ce ta shigo hannunta riqe da sabbin towels wankakku tana cewa "Kinga dazu fa nace lantana ta jera muku su a bandakunan ku, ashe ta manta" na'ima ta qarasa da fara'a zata karbesu daga hannun Mamin, bata miqa mata duka ba ta dauki uku ta bata tace "sauran na nafisa ne" na'ima tace "bari nakai mata mami" tace "a'a kiyi wankan tukunna sai ku sauqa qasa ga abinci can, Na'ima ta amsa da "toh" Mami tayi murmushi tace "welcome home daughter" itama murmushin tayi kawai batace komai ba Mami ta juya ta fita daga dakin tajiyo shiganta dakin nafisa.
Bayan tayi wankan ta shirya cikin simple black abaya mara nauyi tayi daurin dankwali da mayafin ta fice, tasamu nafisa a falon har ta fito itama suna magana da Al'ameen da Abubakar wanda yadawo daga school babu jimawa.
Abubakar ya taso da fara'a yace "Anty nah oyoyo" na'ima na murmushi ta shafa kansa tace "kaima oyoyo".
Cikin walwala suka zauna nan falon aka fara hiran yaushe gamo.
Mami ta fito daga kitchen dinda ke babban falon? hannunta riqe da food flask tayi gurin dinning area tana jerashi jikin sauran 'yan'uwansa kan table? tace "abar surutun haka,kuzo kuci abinci tukunna" suka miqe dukansu suka qarasa dining din , bayan sunyi settling nafisa tace "Mami, Abba fa??" Mami tace "yana gurin aiki ai kinsani,bakuyi waya bane" nafisa ta janyo coolern dataga favorite dish dinta ta fara zubawa a plate tace "yacemin he'll be home when we arrive" Mami tace "bai baro gurin aikin ba tukunna" ta juya tana maida hankalinta kan Na'ima data fara cin abincin da ta zuba, tace "Habibti ki dudduba coolers din ko akwai favorite dinki" Nafisa tace "tuwon da ta zuba shine favorite dinta Mami" Abubakar juya yana kallon Na'ima yace "tuwo kuma anty" Na'ima ta gyada kai sannan tace "Ina yah faruk fa" Al'ameen yace "wannan ya fice aiki tun safe ai" Mami ta qara da "sai dare ma zai dawo halan, yace they have a lot of works" na'ima ta gyada kai tacigaba da cin abincinta.

Daren ranan bayan Abba yadawo yaci abinci ya huta sukaje gaishesa cikin babban falonsa, bayan sun shiga da sallama nafisa ta qarasa kusa dashi ta zauna tana fara'a tace "Abba" shima cikin fara'a ya amsa da "yaran Abba, kun dawo lafiya" na'ima ta qaraso zata zauna nan qasa yace "tashi ki zauna a kujera daughter"? tana dan murmushi tace "nan yayi" ya sake insisting ta tashi din sannan ta tashin ta zauna a wani kujera dan nesa dasu,Mami ta shigo falon hannunta riqe da tray na tea flask da cups akai na'ima ta miqe ta karba ta qarasa? ta ajiye nan table din dake gaban Abban ta koma ta zauna, Mamin ta wuce dakin dake nan falon yin uzuri.
Suka gaishe da Abban ya amsa yana tambayansu karatun nasu
Nafisa na tsiyaya masa tea din a cup tace "Abba abokinka dinnan has been very helpful a lot, watanni biyu ma dasuka wuce shi yakaimu London gidan anty Amnah" Mami ta fito daga dakin ta qaraso ta zauna nan gefensa itama, Abban yace "haka yakamata ai, kuma yana bani report ai yace kuna qoqarin karatun balaifi" ya juya yana kallon Na'ima yace "haka ko na'ima"? na'ima tace "Eh Abba" Mami tace "nafisa zaka tambaya don na'ima bani da haufin tana karatu" murmushi na'ima tayi tace "nafisa tana karatu fa sosai Mami" Nafisa tayi saurin amsawa da " sosai sosai ma" Atare Abba da mami suka juya suna kallonta, Abba yayi murmushi yana kai cup din shayin bakinsa while mami da na'ima suna yar dariya sanin halinta.
Sunanan falon suna hira Al'ameen yashigo falon da sallama yayi settling shima a kujera yadan dukarda kanshi tareda cewa "barka da dare Abba" Abba ya amsa then followed by Abubakar shima yaqaraso ya zauna kusada Al'ameen din.
Har kusan karfe tara suka kai suna hira, na'ima ta sake anata hiran da ita jefi jefi take sa baki, nafisa na bawa iyayen nasu labari game da rayuwarsu a England din na'ima na tayata kadan kadan, by then sun sauqo qasa itada nafisa da Abubakar kan babban carpet din dake shimfide a falon hannunsu riqe da kofin shayin da nafisa ta zuba musu daga cikin na Abban.
Faruk ne yayi sallama ya shigo cikin sanyi alamun gajiya a tattare dashi, yan'uwan na amsa masa tareda sannu, nafisa ta ajiye tea din ta miqe tana riqo hannunsa yana fara'a yace "yan gatan mami sun dawo kenan"? yajuya ya kalli Na'ima yace "habibtin mami, kun iso lafiya" tana murmushi ta amsa da "lafiya yaya" suka gaisheshi gaba daya ya amsa tareda zama nan qasan carpet shima yana me gaishe da iyayen nasa, suka amsa Mami na tambayanshi gajiyan aiki? Abba yace "arinqa sararawa jiki da brain din dai babana" faruk yace "Abba aikin ne these days suna buqatan lokaci sosai" Abba yace "Allah ya bada sa'a" ya amsa da Amin Mami ta tambayesa ko yaci abinci ya girgiza kai. Nan falon nafisa ta kawo masa abincin yanaci aka cigaba da hiran dashi cikin raha.??
Cikin walwala da fahimtar juna iyayen ke gudanar da hiran tsakaninsu da yaran nasu, wanda hakan yasa yaran suke bude cikinsu openly suna fadan abunda ke mind dinsu wajen iyayen, idan fannin gyara ne take iyayen suke gyara musu cikin lumana,idan na raha ne suma ayi dariyan dasu.
And for that moment
Na'ima knew..This is home
These people right here
Are like missing piece of her heart
And she won't trade them for anything.

Wattpad: Bintu Musa @bintuuu02

('KUNCIN ZUCI('
Na Bintu Musa

Read my book "KUNCIN ZUCI" on ArewaPen, Platform available: "all" :: https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c

WhatsApp group =?G?
https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z

Chapter 08

Washegari....
Na'ima ce zaune kan sallaya bayan ta idar da sallahn asuba hannunta riqe da qaramin carbi tana azkhar, bayan ta gama ta dauki Quran din gabanta ta kaishi ta miqe ta kaishi ma'ajiyansa sannan ta nade sallayan, bata cire hijab dinta data dora kan dogon kayan baccin jikinta ba ta fice daga dakin ta shiga falon mami dake nan kusa da nata dakin, ta samu Mami zaune itama bisa sallaya tana azkhar
Mamin tace "na'ima kin tashi" cikin sanyi tace "Eh" ta qaraso ta zauna tace "Ina kwana Mami" Mami ta amsa "lfy habibti,how was your night" tace "Alhamdulillah" suna nan zaune nafisa ta shigo itama sanye da hijab ta zauna tana gaishe da Mamin sannan ta juya suka gaisa da na'ima
Mami tace "baby, meya samu idonki haka?" dan wutan falon tar yake a kunne hakan yasa ta ga idon nafisan wanda yadan kumbura, nafisa tafara hamma tace "bacci ne bai isheni ba Mami"? Mamin tace "aikuwa kije kiyi don ga idonki nan ya nuna" Nafisa ta miqe ta shige dakin Mamin
Sanin Mami zata Dade zaune nan bata tashi ba yasa Na'ima miqewa ta shige dakin itama, ta qarasa kan gadon Mami da nafisa ke kai ta kwanta tana jawo bargon, nafisa ta juyo tace "kinsan Allah, har wani banging kaina yake" Na'ima tace "sannu sis,halan bakiyi bacci da wuri ba jiya" nafisa tace "fada mukayi da mutumin,in na tashi zakisha labari" na'ima tace "kuma dai, yi baccin to" nafisa ta juya tana gyara

3 / 25