Author : Feenerh Category : Romantic Hausa Novels
ma momy da kanta ta musu ankon duka na events din da yake akwai shegun,
Duk nacin Abdulraheem baisamu ganin Khadija ba haka ya koma domin sun kule part din mama Suda su Safeena kirjin biki itace da kawaye ayi nan ayi nan yanzuma sun shigo suna cewa wow " sister munje munga gida kunga yanda kayan suka yi kuwa wallahi mun zabo kaya ba a magana sai kunje kungani,
Zabura Amrah tayi " muje ingani SAfNAH ma ta mike please muje inason ganin yanda purple zaiyi a gidana,
"Duk wacce ta fita gidan nan ranta zai baci momy Raliya tafada da ta shigo dauke da katon tray tana mikawa daya daga cikin kawayen,
"Marasa kunyar banza ina kuka taba jin Amare na zuwa ganin gida basu tare ba inji ingani,
"Ai ni na gama gani Aunty Raliya Allah dai ya kyauta, inji mama da ta shigo da wani tray din,
" kuci Abinci kunji Y'an mata kafin ku samu ganin angwayen ku kuma kwakule su da kyau karkuga ba Abinda zakuyi ni nace ku caje su bari ma inkira Sadiq ku manne mai inji mama tana dariya, domin tana cikin farin ciki ganin yaran sunyi kara don Azamanin nan ba duk iyaye ke barin ya'yan su zuwa biki ba sai sun yarda dasu kuma yaran yaran masu hali ne don haka dole su basu special treat karsu ji daban,
Sunkoyi farin ciki sun saki jiki komai a wadace a sake sukeyin shi kamar gidajen su, wata Bilkisu ce a cikin su y'ar wani sanator ce yarinyar tuntuni tana son su Amrah sune ke kin kulata Amma tana ganin invitation ta zo musu biki, yarinyar kyakkyawa ce sosai ga natsuwa saidai miskilanci shiyasa su Amrah suke kinta Amma gashi yau sun sake sai hira sukeyi,
Washe gari tun karfe shida aka fara shiri masu aiki aka kwaso daga hotel katon store dady Babba ya ware ya zuba Abincin biki dasu drinks shanu an yanka sunfi Biyar kaji kuwa katon katon na kwali aka sauke,
Girki kawai sukeyi,
Su momy duka kai yayi zafi kowane side cika kuloli ake Ana kaiwa, ga security ta ko ina kamar Ana bikin ya'yan gwamna,
Harabar gidan an zuba wasu kayatattun canopy masu dauke da tanbarin ASHRAB family kayatuwar wurin bata baki ne,
SAfNAH tayi matukar mamakin ganin har gari ya waye Abdulkareem bai gantaba kuma bai nemeta ba, Abin ya sosa mata rai sosai, dariya kawai takeyi ita kuwa Amrah ko a jikin ta......... π
"Mu hadu a mothers night fans kowa ta dinka buje ta dauki burgamen ta saboda debo Angara,
Ina godiya da Addu'oin ku tank you
*Matar soja*
[12/22, 2:27 PM] Asli Smasherπ: π»π»
*WA NAKE AURE*
π»π»
By FENERH
*ga masu bukatar karanta wannan labarin ku turo katin waya ta wannan numbar 09011251444 na 200 Airtel ko kota A susun banki na 7304736012 nafisa sani Fcmb sai najiku masoya*
6β£1β£&6β£2β£
Ado aka tsantsara musu cikin lafiyayyan less mai sunan less da kyau da tsada anyi mai bridal style kowa da kalar nashi SAfNAH purple Amrah dark green sai Khadija blue sunyi matukar haduwa da kyau ga rigar na jan kasa ta baya kowanne kanshi nade da beautiful head da aka nada musu golden haka pos din su sai net da yasha stones yana sheki aka fito dasu Y'an mata suka take musu baya cikin material pink da Ash color din head sunyi mugun haskwa,
Gefen Amaren ya matukar kayatuwa kujeru uku ne a jere suma haddadu sunsha kyau ba a fada sai gefen su momy suma cikin haddadun code less na mata masu Aji golden suma sunji nadi Suda Y'an Uwan su duka wurin ya matukar kayatuwa da tsaruwa gefe daya police band ne aka Ajiye domin bude fage, saida taro yayi taro Angwayen suka iso cikin shigar sky blue shadda y'ar gaske tana kukan kudi,
Tun dosowar su Suka zubawa wurin Amaren nasu idanu cikeda burgewa domin kowa yasan sit dinshi don haka kowa wurin zaman shi ya nufa,
Sun sha malum malum suna sabata ga hulunan su sunsha k'ari, harda sadiq kaya iri daya sukasa Abokan su na take musu baya cikin shigar manyan kaya sunyi mugun haskawa tun isowar su wurin police band suka fara sakin kida Abokan suka fara ruwan dollars da dubu dubu har zuwa mazaunin kowanne su,
Gefen Abokan ango daban gefen Y'an mata ma daban ganin wainnan matasa masu aji da kudi tuni Y'an mata akafara gyara dauri da yanga, suma samarin tuni suka fara baza idanun su,
Bilkisu dai tuni Sadiq ya dafe har an kulla harkar arziki domin yace shidai yaga mata,
Tun jiya suka jone, gabatar wa aka farayi gefen su MOMY suma harda gilasai irin na manyan mata a takaice aka nemi Amrah da Abdulmaleek suka fara mikewa suka fito tsakiyar fili domin gabatarda tarihin juna baki daya zagewa sukayi kuwa suka fara zubo magana Amrah ce ta bada tarihin rayuwar su baki daya cikin harshen turanci da kwarewar ta har zuwa yau tareda godiya shima Abdulmaleek yafara da godiya kafin yafara bada tarihin soyayyar Abdulraheem har zuwa Abdulkareem,
Kafin ya natsu cikin natsuwa ya juya gefen iyayen su mata dake zaune baki daya yace
Alhmdulillah Alhmdulillah Alhmdulillah muna godiya ga ubangiji da ya nuna mana wannan ranar a madadin Y'an uwa na ina mika godiya ga iyayen mu da sukasha fafutuka a rayuwar mu domin ganin ci gaban mu baki daya and duk wani ci gaba a rayuwa yana tattare ga iyayen mu mata I remember lokacin muna school a London ya riko hannun Amrah yace am sorry a natse kafin ya juya cikin natsuwa
Tareda Ajiyar zuciya "when I said behind every successful man there is woman I thought that woman is your girlfriend or wife but am mistaking yes your wife has a role but not like your mother,
We are who we are today because of our mother so this one for you All our mothers we love you so much may Allah S.W. A repay you with Aljannatul firdous kowa ya Amsa da Ameen gaba daya emotion ya kama kowa domin magan ganun shi ba yawa amma akwai ratsa zuciya momy saida ta share kwalla ganin irin yanda yaranta suke cikin farin ciki,
Abdulkareem tunda ya zauna a gefen SAfNAH ya matse fuska tam kamar bai Santa ba nan kuwa tayi mugun tafiya da ruwan kwakwal war shi ga kamshin da take fitarwa mai tada hankali domin humra ce y'ar gaske ta saudiya aka wanke su da ita ga kuma turaruka masu mugun dadi suma akabi kai,
Itama ganin yasha kamshi ta daure fuska dama a kule take da shi don haka ta kara shaka sosai,
Su Khadija kuwa yana nan ram da hannun ta suna magana kasa kasa, kazomin da agwalimar bakina nataruwa da yawu nagaji da Tarawa tafada kamar zata mai kuka tashi yayi ya riko hannun ta saida suka nufi can gefe yace ta zubar kafin ya ciro mata agwalumar ta karba da murna ta cire hancin kafin su koma mazaunin su,
Mc ya umarci Amare su fito da angwaye domin baje rawa tuni su Amrah da SAfNAH sai Safeena da ke cikin Y'an mata itama ta hadu,
Suka fara mikewa kallon ta Abdulkareem yayi tareda matse fuska yace ina zakije? Ko kallon shi batayi ba ta wuce tundaga farko suka fara debo shoki momy Raliya ta dafe kai kannin ta na dariya ganin wainnan Y'an biyu na Raliya Aunty Khadija dai tace um um ba inda zataje,
Dole Abdulkareem ya mike ya bita baida zabi amma ya mugun shaka balle hancin kudi yayi yafara zuba mata rawa take debowa tundaga kasa tareda girgiza gashi ta iya rawa Abokan su suka fara ruwan dollars a wurin mc na koda su suna ma Y'an mata ruwan kudi,
Kafin iyaye su shigo suma sufara nasu kudi ne akwance akasa kamar ruwa saida aka tsagaita aka fara kwashewa sudai masu ciki na gefe da agwaluma cikin net,
Wai ina WANAKE AURE FANs? my a she tunda suka iso sika samu gefe suka labe ganin Ana ruwan dollars su kuma sunyo canjin Y'an Biyar Biyar Ummu jidda ce ma na hangota da yan Ashirin Ashirin tana boyewa ni dama jira nake su mom Muhammad su lika su sammin Aunty habeba lawal kuwa ganin zamuji kunya dole ta ciro wasu kananna daddun yan Hamsin Hamsin ta je ta lika, ina kallo police band suka watsasu cikin dustbin saboda sun kwashi dollars me zasuyi da chicken change,
Amma wurin rabon gift sunfi kowa kwasa don sunyi mugun guzuri cikin su kuwa ya dauka harda masu sawa a jaka nidai ganin momy Raliya na Hararar gefen mu nasha jinin jikina nabar su maman ilham da shishshigi,
Duk rawar da akayi SAfNAH sai sun shiga tun Abdulkareem na daure fuska har yasaki rai domin mugun burgeshi rawar keyi saida aka tsayar da Kidan ne ta zauna tana maida numfashi ya mata rada a kunne " may God help you kiyi irin rawar nan gobe wallahi sai na Tara miki gajiyar da tafi wannan kallon shi tayi wani iri itafa ta lura this is not her old Abdul and kuma if new Abdulkareem din ne ma he change
Amma ta share shi, koda aka tashi mama tasa su gaba suka koma part din ta domin sunyi mugun gajiya musamman su SAfNAH Amrah ma Abdulmaleek yayi naci a waya taki fita don tasan kwanan zancen Abdulraheem ma shi ya daga kafa don ya riga yayi aika aika,
Washe gari ranar tarewa aka shirya dinner wanna samari ne kawai da Y'an mata a hotel don haka basu tashi da wuriba sai goma mama tabasu breakfast suka ta hayaniyar su kafin suyi wanka su shirya cikin atanfar su mai kyau ta wunin biki Amaren ma cikin shigar English wax kowanne yasha ado kafin akaisu wurin dady domin mama tace tunda ba nisa kowacce a kaita dakinta da wuri ta shirya kafin dinner inyaso suna dawowa kowacce mijinta ya wuce da ita, don haka suka yafa manyan gyaluluwa kafin kannin momy Raliya su rakasu falon da su dady suke,
Afalon harda Alhaji Adamu yazo domin taya su dady murna domin sam dady bai rike shi ba yasan Albasa ce batayi halin ruwa ba domin Alhaji Adamu ya mugun shiga damuwa iyali a prison,
Sunyi musu Nasiha sosai mai kashe jiki kafin Alhaji Ashiru ya fara musu nashi shima wanda saida sukayi kuka yace " meye na kuka kuda kuka samu gata, ba duk yarinya zata samu irin nakuba kuna rayuwar Aure a cikin gidan iyayen ta tana ganin kowa nata I think wanna ma wani baiwa ne kukeda shi da Allah ya nufeku da rayuwa a karkashin inuwar mu domin haka Allah ya baku zaman lafiya da hakuri kunadai ganin iyayen ku shakaru da yawa ba wani tashin hankali a cikin gidan nan saboda sun san Abinda sukeyi I no kuma sunyi iya bakin kokarin su wurin baku tarbiya don haka Allah ya ma rayuwar ku Albarka baki daya,
Al qur ani ya mika ma kowacce da sabuwar dadduma masu kyau da tsada yace a wuce dasu,
Dady usman saida ya share hawaye a boye shima ganin yanda suke kuka baki daya,
Nidai nace samun wuri ne kukan su Suda zasu rayu a cikin gidan su,
Kafin a koma dasu wurin iyaye mata suma sukayi nasu Amma fir momy Raliya ta kasa tsayawa saboda kukan da taga sunayi sai su momy Zainab da mama ne sai Y'an uwa suka musu kafin a dunguma gidajen su dama Y'an mata nacan,
Gidajen su aka wuce dasu can karshe kowacce gidan ta masha Allah fadar haduwar shi bata lokaci ne saida duka suka shigarda Albarkar su kafin su koma gidan Khadija baki daya saboda shirin dinner,
Yammma ta tuni sun fara shiri ganin magrib ta doso dama Y'an mata Ba cika salla sukeyi ba kar kwalliyar ta goge Abun saidai Allah ya kyauta,
"Mu hadu a dinner my fans in Allah ya kaimu,
*Matar Soja*
[12/23, 12:02 PM] Asli Smasherπ: π»π»
*WA NAKE AURE*
π»π»
By FENERH
*ga masu bukatar karanta wannan labarin ku turo katin waya ta wannan numbar 09011251444 na 200 Airtel ko kota A susun banki na 7304736012 nafisa sani Fcmb sai najiku masoya*
6β£3β£&6β£4β£
Karfe Tara Y'an mata da Amaren sunfito cikin fararen bridal gown sunsha nadi irin na Amaren larabawa akansu sunfito sunyi matukar yin kyau, motocine birjik a harabar gidan tundaga farkon estate din har zuwa kodmfar gidajen su ga motocin Amare kowacce taji ado da balloons da kuma flowers haka aka jero dasu Khadija ce aka fara budewa mota tashiga sai Amrah kafin SAfNAH,
Tunda Aka bude mata motar ta shiga tasha jinin jikinta domin yanzu idanun ta Sunfara clear don tasan suna dawowa sun gama zama gidajen iyayen su sai da rayuwar Aure da mazajen su,
Angwayen dama su suna hotel din domin tun zuwan Abokan su suka tare can tareda su su don haka Amaren kawai suke jira a fara event din, motocin na tsayawa kawayen dake cikin maroon color material da fararen head sunyi kyau suma suka bubbude musu motar tareda take musu baya,
Ajiyar zuciya duka suka sauke ganin juna domin angwayen ma ba baya ba sun shirya cikin suit bakake masu tsada suna kyalli da sheki, kowa gefen Amaryar shi ya tsaya, tareda riko hannun su aka fara sakin kida tundaga farkon shigowar sukejin sautin kidan m inuwa na wakar Amarya,
Yamma ta na take musu baya da rawa da Abokan ango suna barin kudi basa jin gari,
Sadiq kuwa rawa yake debowa gefen shi Safeena ce itama tana cashewa kamar ba kanwar shi ba,
Har wajen zaman su aka rakasu wurin ya hadu karshe ga kujerun mutum bibbiyu aka tsara kowane namiji da mace aka shirya,
Gefe daya wani katon table ne dauke da cakes guda uku manya taron ba wani hauka ko cunkuso ya'yan manya ne kawai suke shan kamshi a can gefe guda aka ware min kujera kamar mayya kuma nima na shiga Ankon Y'an mata kuma ba laifi amin make up nayi kyau sosai Amma tunda banda naira akayi one gefe dani π
Fadin yanda taron ya kasance bata baki ne saidai ince ku hanga ku hango yanda akayi harka ta masu aji da gidan rana an yanka cake sun ciyar da juna duka kafin atashi karfe sha daya na dare,
Bayan sun karbi gift da dama daga Abokan su, kafin su shiga motocin Amaren su zuwa gida, tun da ta shiga motar jikinta ya kara sanyi musamman ganin ya shigo shima ga wani farin ciki da take hangowa a kwance a kan fuskar shi duk da ya shareta a wurin fatin amma yanzu yana shigowa motar ya matso jikin ta,
Tareda janyota yana sauke Ajiyar zuciya, "Alhmdulillah ya furta can kasan makoshi tareda riko hannayen ta da yatsunta da sukasha jan lalle ya sunbata kafin ya saki, shiru yayi tareda daukar waya ya Kira Sadiq " hope everything is ready brother?
Ok kawai yafada ya Ajiye wayar tareda rungume ta tsam a jikin shi har suka isa gida baice mata komai ba itama haka zuciyar ta na bugawa,
Har kofar gidan su aka tsaya ya bude mata ta fito kafin driver ya gyara parking suma su Abdulraheem duka sun iso lokaci daya,
Wucewa SAfNAH tayi ciki domin tayi mugun matsuwa ta cire rigar da take ta kwasota daga kasa saboda tsawo da nauyi,
Abdulmaleek ya matso kusa da Abdulkareem yace " slowly brother don't hurt my sister please,
Mugun kallo ya jefa mai ya wuce Abinshi ciki tareda garkame kofar nashi gidan yana Addu a,
Suma haka sukayi kowa yayi nashi gidan,
Y'an mata kuwa side din mama suka nufa domin dare yayi dole sai gobe zasu tafi gidajen su Safeena keta dawainiya dasu kamar sun saba,
Mu leka gidan su Khadija
Tunda ta shigo ta zube ta fara bacci saboda gajiya da kanshi ya rage mata kayan ya ajiye yaso ta daure tayi wanka Amma ina bazata iya ba, dole yaje ya rage nashi yayi wanka kajin ms da aka kawo frij ya kaisu tareda tsinewa zalama a yau da yayi hakuri shima yau morewa zaiyi Amma ciki na jamai tsiya yanda ya shiryawa daren nan,
Amma wani gefen sai yayi murmushi idan ya tuna in eight months zai zama Dady shima, haka yayi wanka ya rungume ta suka fara bacci,
Abdulmaleek kuwa harkoki ba sauki suna shiga ya kwabe mata kaya shima ya kwabe suka shige wanka tare suna fitowa sallah suka farayi kafin suci kazar Amarci da ice cream da tace zata zatasha sun ciyar da juna sosai kafin suje suyi brush,
A yau ma ta d'an taba raki domin ji tayi kamar karon farko saidai zafin bai kai nafarkon ba shikuwa ai sai shiru domin bayaji baya gani,
Abdulkareem da SAfNAH
Bata wani tsaya jiran shi ba ta shige wanka tareda gasa jikinta cikin ruwa mai zafin gaske wanda taji mugun dadin hakan saboda mugun gajiya da tayi saida ta dauki dogon lokaci kafin ta goge jikin ta ta fito dakin da yake nata tana kallon ko wane sako da lungu, Alhmdulillah Allah ya sakawa