WA NAKE AURE BOOK (COMPLETED) BY FEENERH.txt

Author :  Feenerh Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   6 / 34

15K to 18K   out of 101.5K words

ko me ya korota? Allah ya shiryaki SAfNAH tafada tareda wucewa sabgar gabanta,




SAfNAH kuwa saida ta samu hankalinta ya dawo jikinta ta mike tareda kwabe komai na jikinta ta y'ar harda pant dinta da yayi sharkab ta dauka ta wuce dashi bathroom plushing dinshi tayi kawai ta sakinma kanta ruwa,


Saida ta yi wankan tsarki tareda daura towel ta fito ta goge jikinta da towel din ta shafa mai tareda bude walldrp ta ciro wata simple doguwar riga ta zura,


Ta fada gado, tunanin Abinda ya mata kawai takeyi ta shafa west dinta tareda cewa " meyasa kakeson ta? Zancire kana jimin da ita , kallon kirjin ta tayi tareda shafawa ta tuna wani labari da Amrah tabata takaranta,


Maza na son nono sosai why shi ya ganshi yakasa tabawa shi basa burge shi ne why yakeson kallon west dinta?



Saurin kwabar kanta tayi ta hanyar istigifari domin sam mantawa takeyi da igiya ukun da suka zargeta,

Wannan Auren zai kawo mata tsaiko a rayuwa ga mijin ma tasan waye shiba ga shi baya ko kaunar ta ita da dady yayi shawara da ita da ya hadata da Abdulkareem ,


" Abdulkareem?? Why ta tanbayi kanta tareda yin wani tunani ta zabura zaune " Ina son shi ne?? " yes I love him Ina son shi sosai Ina son ya Abdulkareem tunda ko ya Abdulraheem bata tabajin yanda takeji akan Abdulkareem ba Shima da ya furta yana sonta,



" meye Amfanin soyayyar tunda da Auren wani akaina?


Shikuwa yana fitowa direct gidan momy ya nufa don yasan can take zama ya shiga da wani irin Annuri wanda ba wanda

yataba ganin irin shi a fuskar shi Amrah dake gefen Maleek tana ganin yanda ya shigo ta zungure shi " love look,


Kallon shi yayi tareda cewa Abdulraheem " tofa brother yau fa za ayi ruwa da kankara ko dai ko dai KO dai yasamo matar Aure ne irin wannan Annurin,
Khadija ce tafito daga kitchen dauke da tray ta Ajiye wa Abdulraheem tareda gaida shi yace kawo min Abincin or call Zainab to bring it to me ya mike tareda nufar dakin su dake gefen momyn batareda Yabawa Abdulmaleek Amsa ba don bayason surutu,


Abdulraheem ne yace " brother let eat together wannan zai ishe mu,
" nop indomie is ok call Zainab to cook you can carry on with your love, yafada yana kallon ta,


" ya SAfNAH bata nan ban san Ina taje ba ko tana gidan momy ne? Shiru yayi tareda juyawa ya fita zuwa gidan momy.......... 🖊



" we just started my fans muje zuwa
Love you all my real fans Allah yabar kauna da soyyaaya masoyan Asali yanzu ne nake sanin masoyan FENERH yanzu. nake sanin masu sona fisabillahi ,

Ina rokon wanda duk ya san ya tura min kudi banyi Adding dinshiba a paid group ya mun magana tank you so much,




*Matar Soja*
🌻🌻
*WA NAKE AURE?*
🌻🌻


By FENERH


Free page


*ga masu bukatar karanta wannan labarin ku turo katin waya ta wannan numbar 09011251444 na 200 Airtel ko kota A susun banki na 7304736012 nafisa sani Fcmb sai najiku masoya*



1⃣3⃣&1⃣4⃣


Jin bugun kofar yasa ta yi saurin mikewa daga kwancen da take ta duro domin bude kofar domin tana tunanin su Khadija ne,

Tana budewa ta juya batareda ta tsaya ganin wazai shigoba ta koma kan gadon ta kuma kifewa, jin ankuma Garmin kofar yasa ta dago kanta taga waye ke kulle kofar kuma?

Saurin zabura tayi tana zare ido cikeda fargabar ganin shi ta fara rawar baki, " Yaya!


Kallon cikin idon ta yakeyi kur domin yanason yagano meye ainihin abinda yake tunani, kujerar mirror dinsu ya nufa tareda zama ya gyara yana fuskantar ta,

Ta Dukar da idanun ta domin bata iya jure kallon shi, " do you love me? Tanbayar da yafara jefo mata kenan,

Tayi matukar mamakin tanbayar tashi ta zuba mai idanun ta cike da tunanin me yasa zai raina mata wayau wato ta fito tace tana sonshi yakeso saboda ya ji dad'in disga ta don ta lura mugun d'an y'ar fi ne,



" idan bakida Amsa I can go kuma inaso ki fita hanya ta kidaina nuna min fuskar ki tunda bakisan abinda yake ranki ba,

Yafada with confidence sannan ya mike yana kallon cikin idon ta ya fita cikeda jin takaicin rashin bashi Amsa,


What if she loves you? She is Already married, wata zuciya tafada mai, falon ya fita ya zube tareda runtse idanun shi yadafe kanshi da karfi ji yake kamar kanshi ya tsage saboda ciwo,


Abubuwan sunyi mai yawa ga ciwon zuciya gana ciki shi yasan yanda lafiya domin baya iya kwana guda ciwon cikin shi bai tashiba,

Wasu irin hawaye masu zafi suka fara zubomai suna Ambaliya a idanun shi,
Cikin tsananin damuwa ya furta I need to get married before I kill my self,


Ya dafe saitin zuciyar shi yana sambatu shikadai yake fitarda damuwar shi a bayyane yanajin wani irin dadi, dafashi da Akayi ne yasa ya bude idanun shi ya zubawa dady karami ido,

Saurin tashi yayi zaune yace " welcome Dady, dafa kanshi yayi cikeda damuwa " why my boy kake boye damuwarka why? gashi daba don najiba haka zaka yita wahala ko kafaya zurfin ciki,


"Yaushe kafara son SAfNAH? Dukar da kanshi yayi cikeda damuwa da kuma kunya ya kasa cewa komai, " forget that yanzu dai kasan tanada Aure ko?


"Yaya ya mata Aure da yaron Aminin shi badon hakaba yanzu zan iya daura maka Aure da SAfNAH Abdulkareem Amma karka damu ni zanyi maka gata a yau dinnan zankira mamanka ta turo safeena tazo in hada Auren ku ku duka don nasan Abdulmaleek nason Amrah ne da zanbaka ita,


Wani irin kwarewa yaji yanason yi Tsabar rudewa shi za a hada da safeena wannan yarinyar da takenan kamar bulala he don't like her at All shiyasa baya son zuwa saudiya koda suke London saidai su Abduls suje bayason rawar kan yarinyar tafaya son maza, mama har surutu take mai shi bayason Y'an Uwan shi shiyasa baya zuwa wajenta,


Impact shifa Zainab kawai yakeso kuma laifin ta yake gani tunda taki making any effort a rabata da Auren wanda bata sanshi ba,


Dafashi dadi yayi " Abdulkareem ka sakawa zuciyar ka da safeena da SAfNAH duk daya ne domin jini daya muke baki daya you will be proud Abinda yayi SAfNAH shi yayi safeena,


Saurin girgiza kai yayi " Dady no akwai yarinyar da zan iya Aure tana aiki damu a companin mu banason safeena please Dady forgive me,


" no problem my boy you can count on your father ok?

"Please Dady karka nunawa Dady ni keson Auren ka nunamai kai ka nemomin Auren, "as you wish my son just go and relaxed zanyi binciken yarinyar ingani kafin muyi maganar da Yaya don kasan idan akwai matsala yaya bazai yarda ba don haka saina gama bincike,



Godiya yayi tareda mikewa zaifita ya ganta atsaye tana mai wani irin kallo mai cikeda karaya har wasu irin hawaye yake hangowa cikin idon ta, kafadar shi yadaga Alamar he don't care,



Yafice Abin shi yana wani irin murmushin jin dadi saidai can kasan zuciyar shi damuwa ce akwance mai tarin yawa, he loves Zainab morethern his life All his life ya ginata akan tsari tun tana karama yafara sonta tun batasan kantaba,



Yayi renon soyayyar a cikin zuciyar shi har ta girma, tun tasowar ta baya kaunar yaga ko masu gadin gidan tana gaisawa dasu sometimes matsin da yake nuna mata idan yaganta tana hira dasu idris ko masu sharar harabar gidan


Lokacin da zasutafi London hankalin shi yayi matukar tashi gashi sam bazai iya fada mata yana sonta ba she is too young ko zuwan da sukayi bayan sunyi shekara biyu a London lokacin takara wayau yakasa fada mata saidai kowa ne lokaci kallon ta yakeyi, saboda kyanta da tsarin jikinta he loves her tun kirjinta ba komai tunkafin tafitarda wannan figure din dake dauke mai hankali yanzu,

Yasan cewa soyayyar da yake mata a jini take yana sonta badon tsarin jikinta ba soyayyar da yakewa SAfNAH badon sha'awa bane pure love yake mata mai girman da bazai iya misaltawa ba,


But zuwan da sukayi na karshe kafin su kammala karatun su hankalin shi yayi mugun tashi ganin yanda makerin budurci ya kerata komai nata yafito, hankalin shi bai tashiba saida ya same ta a kitchen din momy daga ita sai shigar tata ta tree quarter da T-shirt yaga yanda figure 8 dinta ya bayyana ga komai nata ya fito,


Ranar baiyi bacci ba yakwana yanajin tsoro kar yatafi wani yayi mai kafa, da safe yana fitowa yagansu sun shirya zasuje school suna sanye da uniform ga sket din guntu sai farar socks doguwa da kuma Sanders dinsu mai kyau na fata kansu da school beret kana hango sumar kanta data dunkule ta daure da band,


Tayi yi kyau sosai tsawa ya daka musu tareda matsowa ya basu wani irin mugun kallo, gaba daya daga ita har Amrah sun tsorata da ganin yanayin shi,


" don iskanci haka kuke fita? Ina hijabin ku? Zaro idanun su sukayi waje domin shima ai school din yayi yasan mata haka suke zuwa, Amrah tace " yaya ba asa hijab..



" keep quite daga yau idan zakuje kusaka hijabi inkunje school ku cire, kunjini?
Don haka kuwuce ku dakko hijabin ku, bayan sun tafi ya samu momy tareda rokonta ta sa surika fita da hijabi domin suma sunyi sunsan me school ya kunsa, hardai wanda yake mix maza da mata,



Dariya tayi tace " kareem inban da Abinka Suda driver zai kaisu kuma ai ko sun saka idan sunshiga dole su cire, ganin baida bakin magana yasa kawai yaja bakinshi yayi Shiru don momy bata bashi goyon baya ba,



Amma yabar nija da mugun fargaba , one thing da ya faranta mai rai kafin zuwan bakin cikin dake cikin zuciyar shi shine ganin yanda take mu amala da hijabi akoda yaushe yasa yaji mugun sanyi da salama,


Babban tashin hankalin shi shine mugun labarin Auren ta ya zaiyi rayuwa babu farin cikin zuciyar shi " he loves SAfNAH beyond imagination so mai mugun zafi

Yakamata ta fahimci zuciyar shi at least zai samu wani saukin tuna cewar tanada Auren wani akanta is killing him slowly ga wani salon sha'awarta dake mugun dibar shi da baisan lokacinda yafara ba,


Yasan cewa soyayyar da yake mata ce sanadi meyasa baya jin sha'awar wasu matan duk rayuwar da yayi a turai baitaba jin feelings akan wata ba, koda kuwa zasu rungume su,

Jinsu yake kamar ya rungume triple brothers dinshi,
Yarasa inda zai saka zuciyar shi yaji salama seeing her around him make him feel relief,


She have no idear how happy he is datazo dakanta wurin shi hakan ya nunamai she Also care for him, koba komai yaji sanyi kadan knowing that ta damu dashi,


Yarinyar da yake magana kuwa a companin su, tunfara aikin su take bibiyar shi nufe ce yarinyar sunan ta Fatima ta mugun takurawa rayuwar shi, ya mata wulakanci har ya gaji yanzu ma tausayi take bashi because yasan how it feels kaso mutum da kasan bazaka taba samun shi ba


Da ace SAfNAH batayi Aure ba ko bata son shi he can fight for his love amma yanzu meye Amfanin soyayyar da yake mata tana mallakin wani,

Da gangan yayi maganar Fatima domin yasan baza a taba yarda ya Auri nufe ba domin yasan momy ma bataso, shiyasa kawai ya fadi hakan kuma yaganta lokacin da ya furta zancen domin yagano gaskiyar zuciyar ta, ya kuma hango kishi mai mugun zafi a idanun ta,


Itama taji ko kadan ne zafin da yakeji a zuciyar shi,,


************************



Tayi matukar damuwa da jin zancen Auren da yayi har zazzabi tayi a ranar shikuwa yana can ya wuni cikin tunanin moment din su tare , da Annuri ya wuni a ranar har fita yayi ya siyo mata waya sabuwa mai tsada tareda wasu kaysn harda hijabai wannan shine karon farko a rayuwar shi da yakewa wani shopping


He is enjoying the moment saidai koda yadawo bai nemeta ba sam a ranar impact yanason ya nuna mata da gaske auren zaiyi,



Wasa wasa yaki yarda ya ganta kullum sai ya kalli shopping din da yayo mata yaji kamar yakai mata sai ya fasa,
Ita kuwa mugun fushi take dashi don jin zaiyi Aure,


Yau ya kama jumu'a gaba daya gidan kowa yadawo gida da wuri har su Dady na gari ga shi Al adar su indai Dady Babba na nan to haduwa sukeyi a katon falon shi,


Ranar kamar salla sunyi girke girke Kala Kala gasu snacks da namomi Kala Kala a baje su momy sunci Adon su suma suna gefe suna magana akan aikin su da business dinsu kowa sabgar gabanshi yakeyi su Khadija da Amrah suna kitchen gimbiya SAfNAH ce kawai a daki a gado domin batason girki a rayuwar ta,


Momy tayi fama harta gaji Amma taki momy Raliya tace ta barta idan taje gidan mijin zata gane ai,

Saida ta dai daici sungama komai ta tashi ta caba wanka da Ado cikin shiga mai matukar burgewa Atamface da aka yimata dinkin yayi tayi matukar yin kyau a ciki make-up tayi tareda shafa wani purple janbaki da ya masifar tafiya da ita,


So take ta burge shi Amma bazata kulashiba fushi take dashi tunda ko neman ta ba yayi , wani cool perfume ta fesa mai taushin kamshi da kuma dadi ta fesa cikin kayan da Abdulmaleek yabasu tsaraba tana son kamshin shi,


Wani bakhour culaccca ta kara murzawa da ya sa kamshin ya bada wani irin salo,
Simple silifas ta saka ta fito zuwa falon Dady Babba, tundaga kofar shiga take jiyo kamshin shi mai tsaya mata a zuciya,


Sai dai ta daure fuska tareda kallon kanta ta glass din kofar ta ga tayi masifasr fitowa ko gyale bata yafaba yau so take yaganta da kyau,


Shiga tayi da sallama cukin muryar ta mai dad'in saurare, dago kansu sukayi kowa ya kalleta, harda su dady, momy Raliya tace " Hamshakiya kinfito? Hajiya Zainab bana fada miki ba sai angama komai zata fito ayi mace a rayuwa batason girki,?


" zatayi dole ai inta je gidan mijin ko inji momy Zainab, turo baki tayi tareda matsawa tana gaida su Dady cikeda ladabi, Dady Babba yace " Allah ya muku Albarka baki daya Zainab kiyi hakuri mijin ki ya kusa dawowa ko,


Wani irin mashi yaji ya cakeshi a kirji takaici biyu ya hade mai na farko ta shigo bata san ma yana rayuwa a falon ba na biyu maganar zuwan shegen mijin nata,

Uwar me ma zaizo yayi inya dawo?



Saida ta gama dasu dady ta nufi gefen da su Amrah suke itada Abdulmaleek suna magana kamar munafukai,
Ta rage murya tace " love birds kullum kunada damun mutane da soyayya a gida su kuma wa incan soyayyar su takare a lecture kullum yana koya mata karatu,


Abdulmaleek ne yace "matso kiji wani Abu All this while sai dai yace ma ta you look beautiful or cool girl shikenan soyayyar ba ya iya bude baki yace I love you,

"I hear that ' Abdulraheem yafada musu tareda matsowa shima don falon nada fadi kusan set uku ne a cikin shi su kowa na gefen shi bamai jin wani,


Cikin natsuwa yafara magana yana kallon idanun Khadija yace _love is not About saying how much I love you, but how much you prove that it's true_


Kungane? Yafada yana musu murmushi, Tabe baki Abdulmaleek yayi yace " banyarda ba inada ja that's is your opinion not mine in my opinion telling the person you love how truly you loves him make him love you more and more,


"Idan har kana son mutum shima yana sonka a idanun shi zaka gane no need to express your feeling zuciyoyin ku zasu isar da sakon,

Saurin kallon shi sukayi gaba daya domin jin bakinshi a cikin hirar su for the first time, baki suka saki gaba daya ita kanta tasan akwai babban dalilin da yasa yayi maganar he is trying to send msg to her,

Kallon shi tayi a karon farko tun shigowar ta saidai idanun shi sam basa gefen ta impact a kishingide yake idanun shi na rufe, yayi matukar haduwa a cikin ya din da sukayi anko kusan komai nasu iri daya suke siya,



Shikanshi bai san zancen zai fitoba saida Abdulmaleek ya dafashi yace " brother are you in love? Ya tanbaye shi cikeda so much excitement,

Saurin bude idanun shi yayi ya kallesu kafin ya mike yabar falon
Abdulraheem ne yayi wani tunani " for sure Abdulkareem na son wata a zuciyar shi tunda har ya iya bude baki yayi magana a yau,



Wani iri SAfNAH tayi domin tasan kila maganar yayi tane saboda

6 / 34