Author : Feenerh Category : Romantic Hausa Novels
"Ahh rowa ko baby, ok ba komai duk ranarda kika dawo gidana zan rika sata idan kina bacci,
Dariya kawai tayi ta fara kokarin cire Y'ar a nono yayi saurin riketa " no kubarmin yarinya ta Koshi, bazai yuwu kimin rowa kima yaya na ba, "tafa Koshi, "kibarta ta cire da kanta, haka tana ji tana gani ya hana ta ciresu kan nonon ta kamar ya tsinke saboda zafin tsotson su,
Saida yaga dama ya sauke Y'ar tareda dorata saman kafadar shi yafara shafa mata baya Har tayi gyatsa kafin ya sauketa,
"May Allah bless your life my little SAffNAH, you and little Dady yafada yana bata sumba a d'an karamin bakin ta,
Kallon shi tayi " meye sunan ta? Zainab Abdulkareem ASHRAB, and this one is my father Usman Abdulkareem ASHRAB, he is my hero, wani irin farin ciki taji ta rasa bakin magana kawai sai hawaye, hannu yasa ya goge mata tareda girgiza mata kai, " no my heart desire you are not suppose to cry, kin wuce kuka bana kaunar kukan ki yanzu rayuwar mu zamu fuskanci farin ciki ne kawai, to me muke nema? Alhmdulillah we have everything baby family status and now the must precious thing ever, that's our lovely children,
Sun dade a dakin har saida momy ta zo ta kwankwasa kofar, ya tashi da sauri ya bude, lokacin ta mayarda rigar ta ts na gyarawa,
Kallon ta tayi da ya bude kofar tace kwaso min su kizo ki wuce, kinzo yasaki a daki ya kulle, anata jiranki tundazu, kai kuma ka kiyaye ni, kazo ka barmin gida kunada gidaje har biyu a estate din nan don haka banason damuwa kazo ka barmin gida,
Murmushi yayi tareda tashi ya kakkkabe rigar shi ya dago babyn shi ya mikawa momy, "ga takwarar ki momy, ita dai SAfNAH rabewa tayi da yaron ta ta fice, momy kuwa tuni fuskar ta ta washe tace " ikon Allah Satar suna kuka yimana bayan duk ta sacemin komai na kamannin baby yanzu kuma sunan babyn ka mayar? "To Allah ya raya mana Zainab, shikuma namijin fa? Usman mukasa, shi kuma na Amrah Ashiru,
"To madalla Allah ya raya mana su akan sunna,
Momy Raliya ma tayi farin ciki da sunayen da sukasa, tuni ta dauke Usman tace ga megidan ta ita ai shikenan Amma kishiya akai kasuwa, momy Zainab ta rungume takwarar ta tareda Ashiru tace ai ni duka ina so da mijin da kishiyar,
Ba karamin hidima yaran nan sukasha ba ta kowane gefe du dady sunyi su momy ma haka bare gefen iyayen su da sukejin kamar su karar da dukiyar su kansu baki daya,
Bakaramin kuka kudi yayi ba, fadin hidimar da akayi bata lokaci ne,
Ansha suna da sati ya zagayo wanda masu jego suka shiga suka fita harda Khadija ma, komai tare akayi musu domin anata haihuwar ma aka sukayi,
Harda sababbin motoci mazajen su suka siya musu, duk da ba wani fita sukeyi ba, Ansha suna lafiya an watse lafiya, mazajen su na zuwa aikin su Sam yanzu basuda time sosai saidai idan sundawo su lekosu su wuce part dinsu,
Domin Abdulkareem da Abdulmaleek kowa yaki komawa gidan shi suna jiran matansu su koma tare,
Yau kimanin sati kusan Biyar da haihuwar su, yaran sunyi mulumul dasu iyayen ma sunyi shar dasu domin gyara momy ke musu bana wasa ba, don musamman suka kawo mai gyara take gyaresu ciki da waje,
Don haka momy Sam ta hana su fita wurin mazan da sunneme su zata tura musu yaran su, tareda masu akin da ta karo musu saboda kula da gida,
SAfNAH ce zaune tana shan wata madarar hadi, wayarta tayi kara, ganin number shi yasa ta daga tana murmushi, domin ya dade bai kirata ba tun sati biyu da suka wuce yana fushi da ita yayi ta lallaba ta yayi yayi tazo wurin shi taki ita kuwa tsoro takeji ganin take tana zuwa zai iya kwanciya da ita,
Shiyasa taki zuwa,
"SAffNAH, yafada muryar shi a kasa kasa " kizo wurina yanzu kafin infada wani hali, " um um ba fushi kakeyi da niba I call you didn't pick , " please am honey baby please, banfa yi ar aba'in ba,
" to shine me nidai kizo ko jinin bai dauke bane? " akwai jini, " no kizo ingani da kaina intabbatar, " uhm tafada tareda kashe wayar baki daya tace wallahi ba inda zani, yara biyu banyi ko fourty days ba inkoma maka gobe kaje neman wani Auren inkajini a bude,
Haka yayita jiran ta taki zuwa ya dauki mugun fushi kuwa domin bai kuma kiranta ba saidai yasa akawo mai yaran shi ya musu wasa ya mayarda su,
Har suka cika ar aba'in, ranar ya shigo falon momy suna zaune dukansu a falon taci ado cikin wani rantsatsen less kana ganin ta kaga Matar manya, kunbar ta take gyarawa, tun shigowar shi ya kalle ta sau daya ya nemi zaucewa domin ya dade bai sata a ido ba,
Ita ma kallon shi tayi ganin shi cikin kana nan kaya yana nan kamar wani saurayi, taji wani mugun kishi ya tsarga mata, ji tayi kamar tayi mai magana,
Sai ta share shi,
Amrah ya kalla, " ke ina momy? "Tana ciki, wucewa yayi batareda ya kalleta ba,
Abun ya mata ciwo sosai tuni ta shaka, ta wuce dakin su wurin yaranta,
"Kadai ji me nace maka zasuje yawon Arba'in dama bata raka Safeena ba ka hana to zasuje suyi sati biyu, "yanzu momy da izinin wa zata tafi? Nidai gaskiya banyarda ba, " to ubana zamu gani, ko ka barta ta tafi sati daya ta dawo ko kuma ta kara wata Arba'in din a nan kafin ta koma, gidan ka,
"Adawo lafiya ya fada zai juya, "dawo ka bamu kudin jirgi da kudin tsaraba, " tafiyar shi yayi yace " ni banida ko kwandala,
"Au Allah to naji jeka d'an ubanka ai dad'in Abun munada shi mu ma a sauka lafiya,
A zuciye ya fita yana zuwa falon bai ganta ba ya nufi dayan dakin nasu da yasan for sure tana ciki, ya shiga, lokacin ta shinfide Little SAffNAH zata mike,
Fisgota yayi tareda zuba mata ido " ke kika shirya wannan ko? Wato Saudiya zakije har na tsawon sati, ok ba damuwa zan nemawa kaina mafita kuwa kafin ki dawo don ni ba lusarin namiji bane, ya saketa batareda ya tsaya takan yaran shi ba ma ya fita zuciyar shi kamar ta faso saboda takaici,
Yanaji yana gani shida matar shi sai kallo gashi sai wani karo sinadirai takeyi, kwanan nan duk a wahalce yake bacci,
Bayan fitar shi jitayi kamar ta bishi taji matakin da zai dauka, domin Kalmar ta bugeta, duk ta kasa sukuni,
Amrah ta shigo, "waike daga haihuwa kin kyale miji yana gararan ba, ko jiya baban Dady ya fadamin saida ya kwana da ciwon ciki Amma kinki yin wani Abu akai,
Kallon bakida hankali tayi mata" me kikeso inyi akai? Abinda nayi zakiyi, I always give my husband his happiness baby, ko yanzu ya kirani zuwa zanyi wallahi,
"Kina nufin,? "Yes tuni mun maida mahaifa baby ni zanbar mijina yayita gararan ba bayan nasan bai haramta ba inada tsalki na,
"Tsoro nakeji Amrah, "tsoron me ke kinsan gyaran da momy tayi mana kuwa? Wallahi koni da na koma kafin inyi Arba'in dakyar ya shiga bare ke, Karki je ki gyaro Aurenki ki jira amiki kafa ke kika sani,
Ji tayi duk ta damu ta kasa sukuni ta dauki wayar ta tafara neman shi, Yana kallon wayar yaki dagawa, saida takira sau kusan uku ya daga, " lafiya? "Kana ina ne?
"Zanje tadi ne ina hanya any problem?
Kuka tasa mai "wallahi kaje ban yafe ba ka dawo kawai yanzu gida yanzu ma inkanaso zankoma gidan mu Wallahi,
Wani irin murmushi yayi na jin dadi, " OK ki dakko yarana kije gidan mu am coming back,
Cikin sauri ta saka hijabi ta dauki yaranta ta ssbasu a kafada tareda daukar wayar ta Amrah nata mata dariya tace " bye sai mun kawo miki kayanki, ko sauraran ta batayi ba, ta fice Abinta da sauri,
Saida ta ga bakowa a falon ta fice,
Gidansu ta nufa, bata hadu da kowa a harabar ba sai masu aiki daketa kai da kawowa, a ko ina na estate din, tayi matukar mamakin ganin kofar a bude ta tura ta shiga, tundaga falon tafara ganin fulawowi da wasu irin box anyi raping dinsu, ta bude baki tana kallon ko ina NA gidan taji an bata hug ta baya, rike yaranta tayi gam karsu fadi domin taji shock har cikin jinin ta, kuma tasan waye,
Juyowa yayi ya karbi SAffNAH yace "I no zakizo tunda kinji zancen kishiya, bata fuska tayi , dama kana gida ka sa hankali na ya tashi? "Um bani yarana, karbarsu yayi ya nufi wani daki tabi bayanshi, dakin yarane yaji kayan Alatu na ado ko ta ina ga gadajensu na furniture da na company kuma, Y'an matan dake mata aiki ne keta gyara komai, ya mika musu yaran yace ku kula dasu ku bar aikin nan,
"Muje kiyi min nawa aikin ko ina na dakina kayane nima, ba musu ta bishi,
Ganin dakin fes sai sababbin ado da flowers da aka kayata ko ina yana baza kamshi, tace " ina kayan? Nuna mata kanshi yayi " nine kayan sannan kinsan me na Tara to muje ki kwashe min su yanzun nan,
"Hmmmm shiru kakeji Aranar saidai ya fito ya karbo yaran insun sha ya mayarda su jin ta yake kamar sabuwar Amarya ranar yazama bita zai zai,
Momy dai data laluba taji shiru tuni ta kada Amrah ma tace kema tattara wuce kafin inga ba daidai ba, wanda Abdulmaleek yace Abu yayi Armashi, Allah ya biya Abdulkareem da Sgida. H,
****************
Alhmdulillah cikin shekaru kadan wannan family ya cika da Albarkar jikoki domin cikin shekara Biyar SAfNAH nada yara hudu, Amrah uku Khadija uku yanzu tana dauke da wani cikin,
Fadin cigaban da suka samu kuwa basai nafada ba domin suma har degree dinsu sun kammala mazajen su sun bude musu nasu company suma suna gudanar da business daban daban Safeena ke musu supply daga saudiya itama tana nan da Y'an yaran ta Sadiq ma matar shi ta haihu, Y'ar su na nan Raliya,
Gefen kareema kuwa Alhaji Ashiru ya Aurar da ita ga Amir domin an sakoshi tuni saboda rashin lafiyar da yayi wanda yasa ya shiga taitayin shi, yazama da nagari momyn shi ma ta shiryu domin ba karamin wuya tasha ba duk da ita Y'an watan ni tayi a prison, Alhaji Adamu ya kara Aure da matar shi har ta haifa mai wasu yaran wanda dole momy Rukayya ta rungume su kodan zamanta lafiya a gidan mijin ta domin batada wata power yanzu,
Kareema ta murmure su momy Zainab sunyi mata gata fiye da tunani yanzu ita ke Auren Amir Hmm duniya kenan, duk wani munin ta da yake gani ya daina ya rungumi kayar shi, ya gyara ta fess
***********
SAfNAH ce a cikin tafkekiyar motar ta ta kwaso yara a school su duka Little Dady little SAffNAH dasu Ahmad ne da kuma su Ashiru sai hayaniya suke a cikin motar kamar kaji, kafi jin muryar Little SAffNAH saboda karadi,
Ta buga musu tsawa " kumin shiru da surutun ku dama don na ga lokaci yayi ne na tsaya dakko ku da ba Abinda zaisa in kwaso ku ku dameni a mota yara saikace parrots hardai ke little, tsit sukayi har ta isa gate din su ta nufi gefen gidajen su suna tsayawa Mazajen na fitowa sun sha anko su uku, gefen su su Amrah ne suma sun fito fess cikin shiga iri daya,
Da sauri ta fito " am sorry guys wallahi na tsaya duba aikin farm house din ne bari in shirya sharp sharp, bin ta yake da kallo har ta juya, yaran sun nufo iyayen su Maza, riko little SAffNAH Abdulkareem yayi "come here little princess waya taba min ke? D'an mutsilin bakinta ta tura "Dady ba momy bace wai na cika surutu kamar parrot,
"Oh this momy ko bari insameta ku wuce gidan grand ma kunji,
Da gudu suka wuce gidan momy Raliya domin momy Zainab korosu takeyi saboda barna da bata gida.
Cikin Ado ta fito irin na Y'an Uwan ta, itama tana haskwa ya tare ta a falon tareda rungume ta, " uwar gidan Abdulkareem Ashiru Ashrab,
"Waye Amaryar to? "Kece hajiya ta, "Amma me yasa kike Kira min baby da parrot bayan ku ta gado da zance,
"Allah ya kyauta wallahi bata biyoni ba, " uhm nidai nasan kece kawai and I love my baby so much my little SAffNAH,
Yeah I no ta kwace min fada, " no bata kwace duka ba muje mu dawo I want more twins but this time triplet zan saka,
Muje suna jiran mu, Agama zuba kayan a store triple wife's kunzama business women a Niger state saura ku zagaye Nigeria like your husband's,
Alhmdulillah Alhmdulillah Alhmdulillah
Allah ina godiya Agareka da kabani damar kammala wannan labari nawa lafiya Alkhairin dake ciki Allah ka bani ladar shi haka duk wani sharrin da ke cikin shi Allah ya yafe min kuskure na, ina godiya ga dukkan masoya na my real fans da kuka bani goyon baya tareda kauna ta Asali Alkharin Allah ya biyaku da Aljannah masoya,
My comment box members you did wow Allah ya barmin ku har gaban Abada haka my vip you are my special people for ever I love you All masoya FENERH har Abada son so,
Gareku Garkuwa ga FENERH
Aunty sa'adau Wato ta wajena Ummu jidda Alkhairin Allah ya raya mana su jidda da Ummu kulthum son so fisabillahi,
"Hmmm Salaha Ibrahim kawar Arziki da rufin Asiri har abada ke ta dabance kin nuna min so na gaskiya Allah yaraya mana zuri'a,
"Aunty Aisha Dahiru ke Aunty nace ke bazance komai ba you are my elder sister wanda I can express my love to you, saidai fatan Allah yakaro shekaru masu Albarka,
Sai mun hadu a sabon littafina mai zuwa insha Allahu ma assalam,
*MATAR SOJA*🖊