Author : Feenerh Category : Romantic Hausa Novels
zuwa lokacin da ya fita,
**************
Dady usman ya kirasu domin jin wa zai tafi sukace Abdulkareem ne, a nan ya bashi bayanin komai tareda ticket yace get ready nan da kwana Biyar jirginku zai daga, and Matar ka tunda tanajin tsoro ka turata wurin momyn ta har ka dawo tunda ba dade wa zakuyi ba wata daya ne kawai ko,
Wani irin maruru yaji ya tokare mai makoshi tuni yaji ranshi ya baci Ashe ba za aje da mace ba suka tunkuda shi bayan yasha dadi jiya yana jin bazai iya hour guda basa tare ba shine yanzu zaije har Amsterdam ba tare da itaba,
Kallon Y'an Uwan yake bayan fitar dady karami ya ce " wato shigo shigo kukayimin ko kunsan bazan iya tafiya da matata ba kuka turani inyi har wata daya batareda itaba to sai Allah ya sakamin wallahi,
Ya fada yana mikewa, dariya Abdulmaleek ya saki dama mugun riketa yayi tundazu,
"Tab Ai malam nasan kwanan zancen shiyasa nayi back out tunfarko, Allah na tuba Ina ni ina iya kwana biyu ba Amrah ai sai in bi matan Amsterdam kaga gwara kar inje kaga kai dama ustaz ne shi kuma Alaramma yana rainon ciki,
Fitar shi yayi ranshi abace Abdulraheem dai baice komai ba, gidan momy ya isa fuska a murtuke, tana danna system dinta, ya zauna batareda yace komai ba, ta dago kanta kadan ta kalleshi taci gaba da aikin ta tana cewa, " halin ya dawo? Ina fatan dai babu matsala tsakanin ka da SAfNAH?
Saida ya dauki dogon lokaci kafin yace " nothing kawai nazo karbar abinda kikaba wa SAfNAH jiyane tace tana son wani,
Saurin dago kanta tayi tareda cire glass din idon ta tace, '? " ita ta aiko ka? Ko rashin kunya ya kawo ka?
" no momy ko babu ne yakare inbada kudin asiyo mana baby na so wallahi,
"Ikon Allah ni Zainab wannan zamani tafada a cikin ranta kafin ta kalle shi, " ni zaka fadawa zaka bada kudi a siyo muku Abu don rashin kunya yaushe ma ka fara rike kudin kanka ka dakko fuska kamar sabon soja ka shigo min gida kamar wanda ya fito fagen fama,
Shiru yayi saida ta gama ya ce " mudai momy ki taimaka kibamu wallahi munaso,
Tashi kaje zanba kareema ta kai mata, " to momy a kawo da yawo fa, yafada yana fita,
Ta girgiza kai tayi dariya, " Allah mai iko yaran yanzu,
**********************
"A cikin kwanakin sai shiri yakeyi gaba daya SAfNAH ta damu shima yayi matukar damuwa saboda bayajin zai iya natsuwa bata tareda shi,
Da tai makon ta ya hada komai nashi, gashi yanzu yasaba da hakar ta ba dare ba rana da taimakon kayan gyaran momy da suke nacin damun ta, daga karshe ma hada SAfNAH tayi da Matar da ke kawo mata kayan, tace su siya da kudin su,
Idan ka kalli Amaren da Angwayen zakasan hankali a kwance yake ba wata matsala a tattare dasu,
Su Abdulraheem duk sun koma bakin aiki Abdulkareem ne yace ba inda zaije yayi serving sauran kwanakin domin samun lokaci da iyalin shi,
Ta riga ta gama tsara komawa gidan momy bayan tafiyar shi, Ana gobe zai wuce ranar basuyi bacci ba sunsha soyayyar su tareda raya daren da bautar Allah a gado sun raya sunna fiye da tunani ji yake kamar ya cire ya jefa a jaka,
Koda Asuba da ya tashi saida ya kara,
Kafin ya shirya,
Karfe bakwai ya fito tareda Sallamar kowa su Abdulmaleek suka rakashi filin jirgi, harda SAfNAH ta bisu suna like a bayan motar gaba daya jikinta yayi matukar yin sanyi ta narke a jikin shi ga wani irin zazzabi da takejin kamar yana taso mata,
Dakyar suka rabu a motar saida suka gama mai komai sannan suka dawo bakin motar sukace ya fito, kallon idanun shi kadai sukayi yabasu tausayi suka rungume juna tareda mai fatan Alkhairi,
SAfNAH kwanciya tayi a bayan motar ko fitowa bata iya yiba jin jikin ta takeyi kamar anyi mata duka ga wasu hawayen kewa dake bin kumatun ta, mugun tausayin kanta takeji yanda zata rayu tsawon wata batareda shiba,
Shi bama zai iya fadin yanayin da yakejin zuciyar shiba, har saida ya shiga jirgin ya zauna tareda runtse idanun shi gam yanajin kamar yabar numfashin shi ne a nan,
************
Tun tafiyar Abdulkareem SAfNAH take fama da zazzabi gashi momy tayi ta fama suje Asibiti taki, dole yau ta Kira doctor yazo ya dubata, jinin ta ya diba ya tafi dashi, saida ya gwada ya Kira momy yafada mata,
Ai kuwa farin ciki a wurin momy ba a magana domin ganin cikin SAfNAH kamar ba ta taba ganin ciki ba ga Amrah ma tana zargin cikin ne da ita duk da bata laulayi Amma ta cika wuri, tayi jajur itama, SAfNAH tayi farin ciki sosai da zancen cikin nan tuni taji ciwon nata ma na dadi ne domin ganin ta dauke da cikin Abdulkareem A yau, ba Abinda yafi wannan dadi a gareta da farin ciki,
, su mama sun koma saudiya kafin Auren su Safeena da Sadiq da za ayi nan da wata daya, lokacin Abdulkareem ma yadawo,
Kullum sai sunyi waya duk da baida isasshen lokaci amma koda yaushe yana iya bakin kokarin shi wajen jin muryar ta sam bata iya fada mai batada lafiya ba ta kuma roki momy da karta fadamai maganar cikin sai yazo ta mai surprise
Duk da tanada ciki kullum kokarin gyara takeyi wanda bazai cutar da itaba da lafiyar babyn ta har su Khadija ta dorasu a kan hanya itada Amrah wanda mazajen su sun yaba suma, ta kuma gode cikin nata ba Amai sai d'an zazzabi lokaci lokaci,
Komai ci takeyi tayi him da ita Gwanin burgewa,
Taki yarda ko video call suyi da Abdulkareem kullum idan ya cirata sai ya mata naci baby na damu am missing you very very badly, saidai ta bashi hakuri tace ya kusa ai yayi hakuri,
Yau saura kwana biyu ya dawo gaba daya ta tasa masu aikin su sunje gidanta an kalkale ko ina yayi tas gashi d'an zaman da tayi ta kara koyan girke girke Kala Kala wurin momy,
Idan ma ta shiga gidajen Y'an Uwan ta tana kara course ,
Tayi matukar shiri a jikinta wanda tasan zata rikita mai gida idan ya iso, tayi shiri sosai, in and out yaji gyara wanda momy tayi farin cikin ganin yanda SAfNAH ta rike gidanta tareda cire kuiya take komai nata kamar na sauran mata harma tafi Y'an Uwan ta,
Momy Raliya ma tana farin ciki da sauyin SAfNAH, a ranar da zai iso kuwa girke girke Kala Kala ta shirya mai,........ 🖊
"Hmm aski yazo gaban goshi don haka akwai zafi afuwan.
*Matar Soja *
[12/30, 12:15 PM] Asli Smasher💕: 🌻🌻
*WA NAKE AURE*
🌻🌻
By FENERH
*ga masu bukatar karanta wannan labarin ku turo katin waya ta wannan numbar 09011251444 na 200 Airtel ko kota A susun banki na 7304736012 nafisa sani Fcmb sai najiku masoya*
7⃣7⃣&7⃣8⃣
Gidan ya kacame sosai da shirye shirye su SAfNAH ba zama duk da a kwanakin batajin dad'in jikinta yau ciwon kai gobe zazzabi, yau ma Ana sakun lalle duk kowa ya gama shirya wa ta wuce can kuryar dakin momy Zainab ta yi kwanciyar ta,
Saboda mugun zazzabin da ya rufeta,
Da zani a kirji ta kife ta dukunkune a bargo,
Abdulkareem ne ya gama zagaye ko ina NA harabar gidan wurin da yake ganin taron matan yana neman ta Amma bai ganta ba saida ya nemi Aunty Khadija ya ce mata baiga SAfNAH ba,
Tafada inda take, cikin sauri ya juya gidan momy, duk da falon na momy akwai mutane haka ya ratsa su ya shige ciki,
Da saurin shi ya karasa kan gadon ya bude ganin yanda ta dukun kune, "baby ya Kira sunan ta tareda taba jikinta yaji zafi rau,
"Subuhanallah baby zazzabin ne?
Dakyar ta bude idanun ta ta kalle shi dasu duk sun juya saboda ciwon kai da takeji,
Tashi yayi ya cire rigar shi ta shadda dake sheki ya haye gadon tareda cire singlet dinshi ma, ya janyota cikin jikin shi tamau ya lullube su,
Shigemai tayi ta rungume shi itama domin samun dan dumin jikin shi,
A haka har bacci ya dauke su,
Shigowar momy daukar Abu a cikin dakin yasa taga rigar shi a kasa gefe daya kuma singlet, tayi saurin daukar Abinda tazo dauka ta fita tana Allah ya shirya min kai Abdulkareem,
Har aka gama saka lalle Y'an Uwan shi na neman shi basu ganshi ba,
Sai gab da magrib momy ta dawo dakin ta tsaya can daga nesa ta Kira sunan shi, sannan ya bude idanun shi a hankali ya kalleta tareda taba jikin SAfNAH yaji da saukin zafin,
" momy baby ce batada lafiya shiyasa na kwanta tareda ita saboda ta rage jin sanyin, " ok doctor, to tashe ta ta yi wanka kafin Akira sallah ko, ta juya ta fita tana dariya,
Da taimakon shi tayi wanka ya kawo mata simple kaya tasaka kafin ya ce su tafi gidan su, ba musu ta bishi domin baccin bai isheta ba,
Bai kuma fitowa ba yana daga ciki, a ranar yama saka wayoyin shi a silent don kar a nemeshi,
*****************
Washe gari da karfe bakwai yana kitchen yana hada musu breakfast din da zasu karya, aka fara buga kofar gidan, da sauri ya nufi falon jikinshi daure da apron ,
Ya bude, gaba dayan su suka zuba mai ido tareda cewa, " Amma wallahi daga Y'an iska sai kai, inji Sadiq,
Matse fuska yayi " me nayi?
"Meye ma Bakayi ba how many miss call muka baka daga jiya zuwa yau?
Juyawa yayi ya shiga cikin falon suka biyo shi, " I don't know ko wayar ban duba ba saboda ina important thing, " zaka fada mana me kakeyi tunjiya a cikin gidan?
" not of your business, saboda Auren naka sai in bar matana da baby na intafi wani taro, baby batada lafiya I can attend any of your event inba taji sauki ba,
Wata irin uwar dariya Abdulmaleek ya buga harda buga cinya, " yanzu brother cook ka koma saboda Aure kaida ko ruwan tea baka iya dafawa, "yes this is about my wife and baby zan iya yin komai for there happiness and look kafin kuzo ku dami matana tana hutawa ku tafi,
"Ai wallahi baka isa ba kafar mu kafar ka yau, ya zamu Tara mutane kai ka wani ware ka dawo gidan ka wai kai mai jinya muma fa cikin nan mun yishi,,
"Uhm nidai bazan fita ba sai naga baby taji sauki sosai,
Sadiq ya kalle shi, " to bari mujira ka Amma kafar mu kafar ka, aje a bamu break fast muma Mr cooker or Mr chief,
Daga kafada yayi ya koma kitchen ya karasa girkin shi,
Tray ya hado mata komai ya fito tareda nufar dakin ta, suna "mufa? " kujira in ta rage ko ku koma naku gidajen wanda baida Auren kuma ya jira har yayi,
"Allah yasa dai gobe ne ko nima dai zanji Abinda ya haukata da sarkin miskilaye yazama so soft and simple,
Abdulmaleek sarkin shakiyanci yace " kai malam ai wannan babban sirrin ka bari ka shiga daga other room zaka gane Meke haukata brother, bare as this time madam is pregnant wow, ya fara shafa kirjin yana rufe ido, dungureshi Abdulraheem yayi da tundazu baice komai ba, yace kubar brother ya kula min da sister na lokacin tane yanzu,
Hirar su sukeyi bai fitoba sai can wajen kusan hour guda suka, jero tare sanye cikin shigar Alfarma ba laifi jikinta yayi karfi yanzu ga tarairayar gwarzon mijinta, tana lafe a gefen jikin shi, ya riketa kamar kwai suka fito,
Ganin su a falon tayi saurin sakin shi tareda gaishe su,
Sadiq yace " oh my god sister please ki sassauta kin rike wuta da yawa kinsa bros yazama mijin hajiya,
"Koma mijin kande ne ni ba ruwan ka, muje baby inraka ki,
Saida ya kaita gidan momy Raliya ya dawo suka fita zuwa nasu uzurin,
Domin gobe ne daurin Auren,
Alhmdulillah komai yai farko zaiyo karshe
Andaura Auren su Sadiq da Safeena cikin kwanciyar hankali tareda farin ciki Sadiq da ya kankara gidan shi a low cost ya tare da Matar shi Safeena kuwa ana shirin tafiya da ita kasar mijinta, tare zasu wuce da su mama,
Duk sun gama shiryawa har da momy dasu Khadija zasuje rakiya su dawo Amma Abdulkareem ya hana SAfNAH, yace bafa inda zataje ta yi hakuri yaushe ya dawo zata ce zatayi tafiya tabar shi ta jira idan ya huta da kanshi zai dauke ta suje,
Fushi takeyi dashi sosai shikuwa yace ina zata sakko bazai iya zama gidan nan bata reda itaba,
Don haka yau da wuri ta kwanta tareda kulle kofar ta, koda ya dawo ya buga taki budewa ya juya nashi dakin ya kyaleta domin yasan halin ta da kanta zata biyoshi idan baby ya bukace shi domin wani irin mugun bukata cikin yasa mata wanda hakan ba karamin dadi yakewa Abdulkareem ba koda yaushe ya taba za a bashi, kowa ya ganshi yasan yana cikin farin ciki da walwala,
Wayar shi kawai ya dauka yana danna wa yanayi yana kallon kofa domin yasan dole ta biyoshi,
Wani irin tsadadden murmushi yayi jin takun tafiyar ta ya ajiye wayar tareda juya baya kamar mai bacci,
Zani ne kawai a jikinta ta shigo dakin domin tanajin Abun ya taso ta shiga ta watso ruwa ko zai kwanta Amma karuwa ma Abin yayi,
Don haka tana fitowa ta fesa turare kawai ta nufo dakin,
Wurgar da zanin tayi ta haye gadon tareda kwanciya ta rungume shi ta baya tareda dora hannun ta mai laushi saman kirjinshi da ba riga ta fara murza mai..
Wani irin tsadadden murmushi yayi tareda runtse idanun shi gam domin yaji salon nata har cikin kanshi saboda tasan weak point dinshi,
Ganin yaki motsawa tayi saurin tashi tafara bugashi, " nurul hayat, ka tashi please, dakyar ya bude idanun shi da suka shiga yanayin ya kalleta, " yaya? Turo mai Baki tayi tareda cewa " ai kasan me nakeso nidai ka tashi ka bani,
Ware idanun shi yayi " me Zanbaki ina bacci na zaki zo ki dame ni? " wallahi ni yaya ka sani kabani kawai, " uhm tom tunda bazaki fada ba ki bawa kanki koma meye inkingan sh...
Y'ar karamar kara ya saki jin hannun ta a cikin jikin shi ta bashi wani irin hurt and soft touch with her magical hands,
" oh come on baby me kikeso? Ya fada murya a shake, " wannan nakeso nurul hayat tafada tana kara bashi wani salon,
" to naji sakeni Karki kashe ni da salonki Zanbaki, amma why did you lock your door? " because am angry with you, " no baby don't do that again komeye a tsakanin mu we can solve it kar mu kuma tunanin kauracewa juna you no is impossible for me to sleep without you nasan zaki zo shiyasa bandamu ba but don't do that again,
" am sorry yaya na bazan kuma ba kawai ina son zuwa raka Safeena ne, " yanzu baby keda bakya iya bacci sai na jagwal gwala ki shine kikeso kiyi nesa dani? You no that am not going with you munada aiki sosai, so ki bari idan nasamu lokaci zamuje daga can muyo shopping din baby na,
Yafada yana shafo marar ta,
Wani irin zullo tayi tareda hade bakin su ganin Abin nashi harda yanga,
Nidai ganin sun dau hanya na fito domin Ummu jidda ta jamun kunne tareda Aunty Aisha Dahiru sunce na faya ganin kwakwab to na tuba,
**************
Kwana Atashi hasarar mai rai su SAfNAH ciki ya tsufa yayinda Aunty Khadija ta sauka lafiya da katon bouncing baby boy dinta kyakkyawa mai kama da iyayen shi Maza, mai suna Ahmed yaron na ganin gata kowa ya dauka saboda shine kawai karamin yaro a gidan yanzu, su Amrah an cika wuri him itada SAfNAH duk sun kunbura, zama dakyar tashi da dubara tuni suma sungama shiryar tarbar haihuwar su kullum cikin lissafin edd dinsu sukeyi,
Saboda kusan atare zasu haihu,
SAfNAH duk ta kagu taga babyn ta domin ganin Ahmad din Khadija yasa taji ts matsu nata bai fitoba,
Kullum zancen su itada Abdulkareem, baby ranarda edd ya cika zamuje Asibiti?
Saidai yace mata eh kawai saboda yasan halin shirmen SAfNAH,
Edd dinsu ya wuce da kwana biyu suna zaune a katon falon Khadija Ahmad na tsakiyar su suna mai wasa itada Amrah Khadija na gefe tana gyaran akaifarta tace " waiku bazaku rika motsa jikin kuba irin wannan nauyi haka kun samu wuri daya kun tule kamar kaya,
Allah dai ya sauke ku lafiya mazajen ku su huta da ganin Abin haushi,
"Kaji Aunty Khadija don Allah bakya ganin yanda mutum duk ya yi kiba saboda ciki ni dai Allah yasa inna haihu in sabe wallahi I love my slim body, inji Amrah,
SAfNAH tace "Aunty wai yama ake yi wajen haihuwar akwai zafi ne?
"Aa SAfNAH kina bacci zaki ji kawai yaro ya fado, kinji,
" don Allah Aunty fadamin akwai wahala? "Babu SAfNAH ki je kiyi baccin ki kila ma sai an shirya yaron kifarka